← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 52

Sashe 43

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fatan lokacin ya yi. Har ga Allah ganin Jimmalo ta shiga raina sosai. Tausayi sosai ta ba ni domin duk abin da take yi ba laifinta bane. Shi yaro yana tasowa ne da irin tarbiyyar da ya ginu a kansa. Duk wannan sakarcin da take yi laifin kakarta ce da so ya rufe mata ido, amma tun da ta rasu, sai mu yi mata addu'a, sannan kuma mu yi ƙoƙarin gyara kuskure da ta yi."

"Haka ne Allah ya bamu ikon gyara, tun da kin zo don Allah ki shiga ciki na iban mata kaya sosai a cikin na Umma, kafin na samu na shiga da ita kasuwa a siya mata duk abin da take buƙata."

"Ba matsala zan ji da ita." Ta ce tare da miƙewa ta shiga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mommy ta yi, sai ta ji zuwanta kamar an sauke mata dutsen da aka ɗora mata a kai.

Jimmalo tana tafiya, xuciyarta cunkushe da takaicin jin ba a gidan take ba. Har ta isa zuwa cikin ɗakinta jefar da hijabin da ɗan-kwallinta suka ɗora mata a ƙasa. Takalminta kuma ta yi jifa da shi a saman gadon. Ta miƙe ta shiga cikin bayi, saboda wani irin fitsari da ya matse ta. Da ta shiga bayin ta yi fitsari. Har ta murɗa ƙofar za ta fice, amma sai ta dawo sakamakon ganin kanta a madubi. Da sauri ta janye gashinta ta buɗe bakinta. Tabbas ita kanta ta ga canjin da ta yi, domin za ta iya cewa ba taɓa ganin ta yi kyau irin haka ba.

"Ashe ina da gashin haka?" Ta furta tana fincike lobalin da suka ɗauke mata da shi, sai dai duk kyan da ta yi ba ta jin za ta iya cigaba da tsafta, domin ita takurar ce ba ta so a rayuwarta.

Daidai lokacin da ta fito sai Anty ta shigo. Tsintar kanta ta yi da sakin murmushin da bai wuce iya leɓe ba, a maimakon ɗauke kanta da ta so ta yi.

Ba ta ce mata komai ba, ta ƙarasa kan gadon ta zauna, wanda ganin hakan Anty ta zauna a gefenta.

"Yauwa ga kaya Mommy ta ce ki canza."

"Ni bana so na sanya wasu kaya in ba na Kakata ba." Ta furta tare da janyo kayan ta ɗauki wata riga da sani da take zama a tsakar gida.

Da mamaki ta kalle ta, ganin yadda kayan sun yi tsufan da ko goge-goge ba za ta iya yi da su ba."

"Jimmalo, waɗannan kayan za ki saka? Kin san kuwa a gidan da kike rayuwa?" Ta yi mata maganar cikin zallar mamaki.

"Ni ina ruwana su na ke son na saka." Ta ce tana ƙoƙarin ɗaukar zani.

"Ƙona su za a yi, daga yau ba za ki ƙara sanya su ba." Ta ce tare da fisge kaya ta miƙa mata doguwar riga mai kyau kalar pink.

Kallon kayan ta yi, cikin damuwa kuma ta kasa musu da ita. Ganin haka ya sanya ta miƙe, tare da ƙarasa gurinta kamar za ta taimaka mata ta cire kayan.

"Wai mene sunan ki? Saboda Jimmalo sunan rana ne?"

"Jimmalo Jikar Tani na fi son a rinƙa ce mini, bana son Sahiya da wannan mai kama da arnan ya ce dole shi za a sanya mini."

Dariya ta yi jin wautarta. "Ok, sunan ki Safeeya kenan? Wow kina da sun mai daɗi, kuma ƙanwata sunan ku ɗaya da ita, amma ana kiranta da Surfy."

"Hmmmmh, ita ma kun mayar mata da sunan arna." Ta ce lokacin da ta cire rigar makarantar, ta sanya doguwar rigar tana yi wa kanta wani irin kallo.

"A'a suna ne da zamani ya zo da shi." Ta ce mata lokacin da take duba chatting ɗin Aliyu, da yake gaya mata yana hanya, don bai samu wanda ya je nema ba.

"Wow, kin ga yadda kika yi kyau?" Ta yi mata maganar tana gyara zaman rigarta.

"Ban gani ba saboda na tsani shigar birni ba ta mini kyau."

"Daga yau ita zaki rinƙa yi, don kin zama 'yan birni, ga shi har kin shiga makaranta. Surfy zan rinƙa kiranki da shi." Ta ce mata lokacin da ta miƙe ta kwashi kayan.

Ganin ba ta tanka mata ba sai ta kwashi kayan ta ce,"Ƙona su za a yi saboda ba su da amfani a gurinki."

Kama kayan ta yi ta ce,"Don Allah kar ki ƙona mini kaya, saboda su kawai na ke gani na tuna da Kakata." Yadda ta yi maganar sai ta ba ta tausayi.

"Kin yi alƙawarin ba za ki ƙara sawa ba?"

"Eh na yi." Ta tsinci kanta da faɗin haka cikin rawar murya.

"Ok, tom shikenan ki fito ki ci abinci."

"To," Ta furta mata daidai lokacin da za ta fita, domin har ta kama ƙofa sai ta tsinci muryarta tana faɗin,"Don Allah ki zauna a gidan nan, ko kuma ki tafi da ni can gidanki. Bana son rayuwa a gidan nan, saboda wannan mugun mai kama da zabiya dukana yake yi har ya fasa mini baki."

Jin abin da ce sai tausayinta ya kamata. Ta san cewa Aliyu ba shi da tausayi zai iya abin da ya fi haka. Dole zata kawo sasanci a tsakaninsu, domin ita bata ga girman da Jimmmalo ta yi ba, da har zai rinƙa faɗa yana tada jijiyar wuya a kanta.

"Kin ga kuma a gidan nan, bani da wanda muke gyaɗar doguwar fiye da shi, domin zuwana saboda shi na yi."

Lokaci guda annurin fuskarta ya canza ta kalle ta da wani irin fuska. Sosai ta ji haushin matar da ta ji ba ta da kamarta jin suna shiri da shi, sai ta fara ƙoƙarin cire ta daga xuciyarta.

Ganin yadda ta canza fuska, ta saki murfin ƙofar ta kama hannunta."Kar ki damu, zan yi masa magana in sha Allahu zai daina hantararki, sannan ba zan iya tafiya dake ba, amma in sha Allahu in kuka samu hutu zan sanya Mommy ta kawo mini ke."

"Ki bari kawai bana son zuwa, saboda duk wanda yake hurɗa da shi na tsane shi, dalilin da ya sanya na tsani mutanen gidan nan kenan, don na rantse tun da ya cutar da ni don ya ga babu kakata, sai na zaman masa kaɗangaren bakin tulu." Ta furta tare da ƙarasa gefenta zauna.

Jin bin da ta ce sai hankalinta ya tashi, domin har ta fara jin daɗi sosai za ta samu kyautar yabo a gurin Mommy da Daddy, amma ganin yadda ta yi sai gwiyarta ya sage.

"Ba a faɗa da maza musamman shi da yake soja. Zai iya sanya bindiga ya harbe ki. Yayanki ne ki ɗauke shi a matsayin yaya."

"Ba zan taɓa kiran shi da Yayana ba, kuma bana jin tsoron shi domin nima soja na ke son na zama." Ta furta fuskarta cike da gaskiyar abin da ta faɗa.

Cikin mamaki ta kalle ta domin tana da dakiya da kuma rashin tsoro.

"To yanzu fito kici abinci, anjima za ayi maganar, domin har na fara tunanin ture gwamnatinsa a gurina ki zamo 'yar gidana ke kaɗai."

Murmushi ta yi ta ce,"Kin tabbata za ki daina kula shi, ni kuma zan zamo ƙanwarki."

"Yauwa ƙanwata Surfy, ta shi mu je kici abinci." Ta furta tare da miƙa mata hannu.

Hannu ta bata ta miƙar da ta sannan suka fita falo.

Mommy sai lamarin ya daina ba ta mamaki sa almara, sai kawai ta kama baki tana kallonta.

"Na yarda babu abin da ya gagari Allah." Ta ce daidai lokacin da ta fito suka zauna a kujera.

Su kansu 'yan matan falon, mamaki suka bita da shi, musamman Nufaisah da Umma.

Zama ta yi, ba tare da ta kalli mutane falon da suke mata kallon mamaki ba.

Anty da kanta ta zuba mata abinci ta fara ci. Yadda take cin abincin da zaman da ta yi, zai tabbata mana da rashin wayewa da gidadanci a kanta, domin kana ganinta ka san ta bambanta da sauran 'yan matan falon.

Bayan ta gama cin abinci. Ta yi gyaza ta samu gefen Anty ta zauna tana kallo kamar za ta shiga tibin, ba tare da ta yi tunanin ta ɗauke kwanon ba. Sosai Mommy ta ƙosa Daddy ya dawo don ta yi masa kyakyawar albishir.

Suna zaune ana kallo sai surutu Jimmalo ta ke da Anty, wanda ya cika duniyar Mommy da mamaki. Labari take ba su yadda ta shuka tsiya a Damagaran. Suna ta dariya sosai domin har Mommy sai da ta dara. Mufida da Hanifa suke ƙara zugata in ta yi shiru, domin dariya take ba su sosai, tamkar wata 'yar comedy suka ɗauke ta.

Tunawa da abin da ta yi wa Captain, a lokacin da ya zo Danagaran ta yi, sai ta fara gaya musu haɗuwarsu ta farko tana kan mangaro. Sosai suka yi dariya har da Mommy, da ta tuna da yadda ya tsorata ya ce su bar gurin akwai aljanu. Ashe Jimmmalo ce.

"Lallai Surfy kin ranazar zuciyar mazan fama." Anty ta ce tana dariya sosai.

"Allah wallahi, kawai na fara kukan jaki ina girgiza bishiya, sai ga shi ya riga da gudu. Ashe ma zabo ne ku ke kiran sa da soja."

Aliyu ya tsinci muryarta tana faɗin haka falon ana ta dariya sosai. Da fari ya so ya shigo da motar, amma tuna bayan sun gama magana da Anty zai fita sai ya bar motar a waje. Cikin rashin sa'a ya shigo ya ji tana ba su labari.

Cikin tsanannin mamaki ya tsaya yana jinjina kansa. A wancan lokacin in qur'ani za a ba shi zai rantse da aljani ne, amma ashe ita ce ta haye bishiyar ta rinƙa maka masa mangwaro kayansa suka ɓaci, har ya firgita ya dauka jinnu ne. Lailai Jimmalo ta wuce tunainsa.

Cikin zafi ya shigo cikin gidan ya yi kanta da takaici."Dama kece kika ɓata mini kaya saboda ba ki da mutunci.." Maganar ta katse mishi ganinta gefen Anty jikinsu na gogan juna.

"What Anty! Da wannan ƙazamiyar yarinyar za ki haɗa jiki, bayan kin san babu wacce na tsana a duniya kamarta."
Chapter 43 · 0% Book details