Sashe 41
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Don takaici Mufida ba ta amsa ba, sai Hanifa ce ta amsa gwiyarta a sake. Mufida duk yadda take jin xuciyarta na tafarfasa saboda ƙaunarsa, hakan bai hana ta watsa masa harara ba, saboda ya cika ɗan wulaƙanci na ƙarshe.
Hankalinsa a tuƙi yana hira da Anty Amarya har suka iso.
A lokacin da suka iso, Mommy tana zaune xuciyarta cunkushe da damuwa, ganin ya yi fushi ya tafi. Sosai take son ɗan nata da damuwa da rashin sa a kusa da ita, amma kuma ga shi ya samu hutu Jimmalo ta kore shi. Nan take ta fara ganin rashin adalcin Hajiya da ta jajibo musu ita.
Tana wanan tunanin ta ji hon ɗin motarsa. Da sauri ta miƙe tare da yaye labulen falon. Ganinsa sai mamaki sosai ya kamata.
Har ya shigo ya yi parking idanunsa na kan motar, sai kuma ta lura da mutane a cikin motar kuma mata. Tana tsaye tana kallon su da tunanin su waye, Anty Amarya ta fito daga cikin motar, sannan su Mufida da Hannifa.
Murmushi ya bayyanaa fuskarta, ganin baƙin da suka yi, domin yadda Anty Amarya take son ɗanta haka ita ma take sonta.
Fuskarta ɗauke da farinciki ta fita zuwa harabar gidan. A lokacin Anty Amarya ta fito, sai kuma Mufida da Hannifa da suke ƙoƙarin fitowa.
"Zuwan bazata amarya? Ai kya sanar da ni, duk da na san cewa ba don ni aka zo ba."
Murmushi ta yi tare da ƙarasawa gabanta. "Da gaskiyarki Mommy ba zuwanki bane, amma kuma sai na kusa rashin sa'a don ya ce mini har ya shiga mota zai juya."
"Kin ga da sai ki yi zumuncin dole" Ta ce tana kallon su Hanifah da suke gaisheta.
"Lafiya lau kun iso lafiya?"
A tare suka haɗa baki gurin,"Lafiya lau."
"Masha Allah mu shiga daga ciki."
Mufida take bin gidan da kallo cikin birgewa, duk da cewar wannan ba zuwan ta na farko kenan ba, sosai take son ta kasance surukar gidan, saboda ita a rayuwarta tana son rayuwar kuɗi yadda za ta fantama ta yi rayuwarta cikin daula.
Suna hira suka shiga cikin falo da Mommy. Aliyu yana riƙe da jakar Anty Amarya ya kawo mata kusa da ita.
Kallonsa ta yi tana dariya ta ce,"Na gode soja mazan fama. Da su Hanifah ka bar musu suka shigo da shi."
"Kar ki damu Atyna kin san kin wuce haka a gurina. Ni dai na ƙosa da kika ce za mu yi wata magana, saboda bacin zuwanki da yanzu ma yi nisa."
Da ido ta yi masa alamu da ya daina maganar za su yi sirri. Sai ta wayance da dariya tana kallonsa ta ce,"Haka ne ai zuwan mai dalili ne, saboda faɗa na zo maka."
Gane abin da take nufi ya yi, domin duk 'ya matan sun zura mata idanu, ko wacce tana burin ace ita za takura masa ya aura.
Mufida ta san ba ya wuce 'yar mijinta, amma duk ta ƙosa ta samu ta sanya masa maganin, don haka ta fara tunanin yadda za ta shiga kofin ɗin.
Aliyu hijira ya so ya yi mana, saboda mun ɗauki yarinya muna son mu yi aikin lada."
Anty Amarya ta kalle shi lokaci guda fuskarsa ya sauwa, sai ta kalli Mommy da ita ma shi take kallo ganin ya haɗe rai.
"Wannan yarinyar ce ko Captain?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa.
"Ita ce suka kawo wai za su riƙe ta a gidan nan. Ni kuma in har za su riƙe ta, ba zan ƙara zuwa gidan nan ba, saboda na tsane na. Wallahi ko tunawa na yi tana gidan nan sai na ji xuciyata tana tashi."
Dariya mai sauti Anty ta yi, ganin yadda yake maganar da gaskiyarsa. Ta san cewa in har ya tsani abu to ya tsane shi.
"Mu kanmu, bisa tursasawar Hajiya ya sanya ta zauna a gidan nan, amma wallahi da na zauna da Jimmmalo, gara a haɗa mini jarirai biyu na riƙe, gabakiɗaya babu wanda ya isa ya sanya ta ta yi ko ta ji magana. Kakarta ta yi mata wani irin tarbiyya mara kyau. Ga ƙazanta ga rashin jin magana babu sallah ba salati."
"Innnalilahi! Wannan wace irin yarinya ce?" Anty ta yi tambayar da mamaki.
"Hmmmmh! Za ki ganta sun kusa dawowa makaranta, saboda yau aka sanya ta a makaranta. Na rantse duk bayan minti sai na kalli agogo xuciyata ta buga."
"Ikon Allah gaskiya tana da rigima." Ta furta ganin yadda damuwa ya bayyana a fuskarta.
Aliyu ƙaramin tsuka ya ja, ya kalli 'yan matan da suke kallonsa kamar za su cinye shi, sai kuma ya kalli lokaci ya sanya idanunsa a fuskar Anty.
"Na ba su zaɓi ko ta bar gidan nan ko na daina zuwa. In har suna son ganina sai su biyo ni Abuja. Anty bari na je na watsa ruwa sannan na shigo." Ya ce mata kafin ya jira amsa ya wuce.
Mommy ta yi ajiyar zuciya, daidai lokacin da mai aiki ta fara kawo musu ruwa da drinks." Humh! Na kasa yanke shawara game da lamarin. Na cika ki da surutu ga ruwa kusha." Ta ƙarashe maganar tare da ɓalle murfin ruwan tana zuba musu.
"Ba komai kan ɗan gidana ne dole na tsaya da komai na ji."
"Haka ne kuma, ko wannan zuwan na san wani abu za ku ƙulla, domin ban yarda da ku ba, amma ya kamata ki yi masa faɗa a samu ayi aure a bar magana, yadda mutuwa ke wuf da mutane, ya tsaya ruwan ido ko wace mace ya ce bata yi masa ba."
"In sha Allahu, zai yi lokaci ne domin aski ya zo gaban goshi." Anty Amarya tace tare da karɓar ruwan.
"Mommy ina Nufaisah, ko tana school?" Hanifa ta yi tambayar ganin bata ganta ba.
"Yau ba su da lecture, tana cikin bayi wanka ta shiga, domin ba ta jima da shiga ba."
"Ok," Ta ce tare da mayar da hankalinta kan wayarta.
Ba ta jima da maganar ba Nufaisah ta fito daga cikin ɗakinsu da tawul ɗauke, sai kuma hijabi da ta sanya. Cikin farinciki suka hada, sannan ta koma ciki don ta sanya kaya.
Duk da Mommy ba ta san da zuwan su ba, amma ta yi musu tarba ta musamman domin kafin su gama shan ruwa da drinks aka cika gabansu da snacks, sannan ta miƙe ta ce musu." Bari na shiga na bayar da odar na abin da za a dafa, ga shi na ga lokaci ya ƙure gab da 'yan makaranta su dawo."
"Ok, mu je na ta ya ki." Cewar Anty tana ƙoƙarin miƙewa.
"Kai haba kar ki damu, akwai mai aiki da ga zuwanki sai ki kama aiki. Ki zauna ki huta zuwa yamma sai ki yi mana gudun kurna tun da kin zo."
"Ok, tom shikenan." Ta ce tare da komawa ta zauna
Murmushi Mommy ta yi ta shiga kofin ɗin. Sosai jininsu ya haɗu da ita, domin akwai hankali da natsuwa.
Abin ka da aikin da gas, babu jimawa aka gama abinci aka kawo musu. Suna zaune suna ci Aliyu ya shigo cikin shirin fita.
"Anty Amarya zan fita, amma ba zan jima ba, wataƙila kuma na kai dare. Kar ki yi bacci domin yau za mu yi maganarmu."
"To shikenan, babu matsala ɗan gidana sai ka dawo, amma abinci fa?"
"Ni Allah ya kyauta! Ko ruwan cikin gidan nan ba zan iya sha ba in har tana cikin gidan."
Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba. Mufida da Hanifa sai suka ƙosa suka ganta ganin yadda ya tsane ta.
"Kallon Mommy ya yi da take cin abinci."Mommy, sai na dawo."
"A dawo lafiya Allah ya yi maka albarka."
"Amin,"Ya ce tare da fita yayin da 'yan matan suka raka shi da kallo suna faɗin,"Sai ka dawo Ya Captain."
Sun so su ji ya amsa ba ko bai amsa ba, domin ya tsinci maganarsu, daidai lokacin da ya kai ƙofa
Jimmalo
Kafin a tashi makarantar ta yi mugun gajiya da zama, domin ita sam ba ta san a takurata. Sosai ta ƙosa a tashi duk da zaman cikin gidan ba daɗi yake mata ba, amma ta gwammce ta koma ko ta huta da gwalan-gwalan, yaren da ake mata tun da ta shigo cikin makarantar.
Ga wani azzabben yunwa da ya ke ƙwakwularta, saboda tun da Kaka Tani ta rasu ba ta samu ta ci abinci sosai ba. A dalilin hakan sai gabakiɗaya hankalinta ba shi a makarantar. Tana takure har lokacin tashi ya yi. Kallon makarantar ta yi a ranta ta yi mata kallon ƙarshe, domin ta saka ko sama da ƙasa za ta haɗe ba za ta je makarantar ba.
Da aka tashi direba ya zo ɗaukar su. Sosai yaran suke kallonta ganin yadda ta canza ta yi fasali. Babu wanda ta kalla a cikinsu ballantana ta tanka musu tun da aka tashi. Motar ta shiga ta kwantar da kanta, don yunwa take ji sosai.
Tun da suka doshi hanyar gidan sai kawai ta fashe da kuka. So take ta fara kuka tun yanzu yadda za ta tunzura Mommy, don ta fahimci tana da saurin fushi.
Direba ya waiwayo ya kalle ta zai yi magana, sai dai kallon da ta yi masa ya kauda kansa ya ci gaba da tuƙi, domin shi ma a zuciya yake ba shi da haƙuri kamar zawayi.
Su Umma suna jin kukanta, babu wanda ya tanka don sun san ba za ta kula su ba.
Ganin an buɗe musu get, bayan ya yi hon sai ta ɓare baki iya ƙarfinta. Mommy dake zaune da Anty Amarya a falo suna hira jin kukan gabanta ya buga.
Dama tun da karfe biyu da rabi ya yi, ta ɗan canza tana fargabar dawowarta.
"Ya Salam ta dawo! Kina jin ta da kuka za ta shigo cikin gidan nan kamar jariri ya. Ni kam Hajiya ta haɗa ni da bala'i." Ta furta tana jin kukan har cikin ranta.
Anty Amarya, Mufida da Hanifa sai suka zuba ma kofar idanu suna son suga Jimmalo, da ta zamar wa mutanen gidan ƙaya a maƙoshi, domin duk bayan minti sai Mommy ta kalli agogo ta sako hirarta.