← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 52

Sashe 10

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kar ki yi mini rashin kunya, na ci uban haure mai gindi. Kin san duk da ƙawata ce ke, wallahi rufe idanu zan yi, na gurza miki rashin mutunci. Yanzu zan wanke miki baki da yashi. Da ma na ga kwana biyu ba kya wankewa, haka juya kika dame mu da wari da kina waƙa a dandali."

"Hmmmmh! Wai sauba na gaya wa dirimi nisa. Ba gara ni ina wankewa watarana in Innata ta matsa mini ba, ke kuwa haƙoranki har gansa kuka suke yi."

"Kutumar uba! Wallahi yanzu zan canza miki kamanni, yau ba ki ba fitowa dandali. Sai dai ki yi kunyar bakinki." Ta ƙarashe maganar tana gyara ɗammara za ta shaƙota.

Dariyar yaƙe ta yi jin abin da ta ce." Ke kuma ba ki san wasa ba? Kamata ya yi ma ki yi mini kyauta, saboda alkhairi na zo na gaya miki"

"Aikin san bana ɗaukar raini. Ko kujerar maka kika ba ni zan iya gurza miki rashin mutunci, in na gama sai na yi miki godiya." Ta ce tare da kwance ɗammarar da ta yi.

"To ki yi haƙuri na yadda kin ƙona aljani. Kina jina ko? Yanzu na zo wuce ta ƙofar gidanku, kawai na ga jirgin sama an faka ta a ƙofar gidan wai kun yi baƙi daga birni."

"Jirgin sama da yake yawo a sama, shi ne aka faka a ƙofar gidanmu.?"Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki.

"Zai iya faruwa mana, ba yanzu kika gaya mini kin ƙona aljani ba?" Ta ce mata cikin gatse.

"Share zancen jirgi. Kika ce mun yi baƙi 'yan birni?"

"Eh, wallahi masu kyau, sai shiga ake da abincin birni a gidanku."

"Da gaske kike 'yan birni sun zo gidanmu? Kin san a ƙauye nan, babu wasu wanda suke da 'yan'uwa a birni, sai ɗan maigari da ya yi karatu ya ke aiki a can?"

"Eh mana ba ki ga wani namiji ba, na ɗauka daga sama ya faɗo saboda tsananin kyansa."

"Wallahi in kika yi mini ƙarya sai na koya miki hankali, don har na fara tunanin rashin mutuncin da zan yi, in rama yangar da yarinyar mai gari take mana."

"Da gaske na ke yi kike ki gan..."

Wani irin sufa ta yi, kawai sai ta ganta a can nesa da ita tana gudu.

"Jimmalo, ki jira ni." Ta furta tare da bin ta da gudu.

Gudu take yi, ba ni da iya gudu ba kamar ba mace ba, duk wanda ya ganta sai ya ɗaga mata hannu yana faɗin,"Jimmalo jikar Tani."

Ba tare da ta kula su, ba ta ƙarasa ƙofar gidan tana nishi, sai dai da sauri ta tsaya tana zare idanu. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta dafe ƙirjinta tana faɗin haka, a lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan.

"Wa innahu sulaimanu, tuff!tuf." Ta ce cikin razana tana tofawa, ganin Captain Aliyu a tsaye ya jingina da mota, saboda rashin haƙuri ji yake kamar ya shiga mota ya koma. Sam ya ji ƙauye bai yi masa ba, da mutanen ƙauyen musamman 'yan matan da suke kallonsa.

Ya saki tsaki, daidai lokacin da wata mai tallar rogo ta zo za ta wuce ta gabansa. Ganinsa da fari ta tsorata sai da ta fahimci mutum ne sannan ta washe haƙora tana waigensa, har sa da ta kusa kifewa sannan ta daina kallonsa.

"Banxiya ƙazama kawai." Ya ce yana dafa motar cikin ƙosawa.

"Jimmalo lafiya kika tsaya..?" Ta yi mata tambayar lokacin da ta ƙaraso tana haki.

"Ke na shiga uku! Wallahi aljanin da na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar cikin razana, kawai sai ta ruga cikin gida tana ihu.

"Wayyo Kaka Tani aljani na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar tare da shallake su Daddy ta haye kan Kaka Tani.

"Ke Jimmalo, lafiyarka ƙalau kuwa?" Kaka Tani da hankalinta ya yi mugun tashi ta riƙe ta tana tambayarta.

"Aljani ya biyo ni har ƙofar gidanmu saboda na ƙona sa."

"Ina aljanin yake?" Suka haɗa baki har da Mommy da Daddy gurin tambayar hakan cikin tsoro, tunawa da suka yi Aliyu yace da aljanu, yanzu kuma ita ma ta faɗa.

"Eh, wallahi aljani ne a waje ya biyo ni, saboda na ƙona....". Maganar ta maƙale mata, sakamakon masu kama da shi da ta gani.

"Kaka Tani, su waye waɗannan?" Ta yi mata maganar tana nuna Nufaisah da ta fi kama da shi sak! Wacce ta ƙanƙame Mommy tana duk addu'ar da ta fito cikin bakinta.

"Ki natsu baƙi muka yi daga birni." Cewar Kaka Tani tana sakinta ganin ta natsu.

"Birni! Dama muna da 'yan'uwa a birni?"

"Eh mutum ɗaya ce,mahaifiyarta da mamana yan uwane ita ma mijin da ta aura birni yake zama yana kasuwanci, shi ne da Allah ya buɗa masa ya zo ya tafi da ita. Waɗannan jikokinta ne da ɗanta ya haifa."

"Har da wanda yake waje?"

"Eh, shi ma ɗan uwanmu ne. Shine ɗana na fari." Daddy yace yana mata wani irin kallo, ganin yadda ta yi shiri, kamar wata mahaukaciya.

Wani irin dariya ta saki tana kallonsu tana matsawa cikin tsananin farinciki.

"Yan'uwanmmu daga birni?" Sai ta ƙara kecewa da dariya ta nufi Nufaisah da ta yi matuƙar tsorata da ita ta rungume ta.

Da sauri Nufaisahh, ta matsa saboda wani irin wari da cika mata hanci.

Kallon da take mata ya sanya ta tunzura." Ke dallah me mai yasa kike kallona kamar kin ga kashi?"

"Ba komai." Ta ba ta amsa da sauri ganin kallon da take mata.

"Kaka Tani ina zuwa."Ta ruga da gudu waje tana faɗin haka.

Kaka Tani dariya ta saki tana kallon inda ta wuce."Jikalle ta ɗaya tamkar da dubu kenan. Ita kaɗai iyayenta suka haifa suka mutu sakamakon kwalara da suka yi.

"Allah Sarki Allah ya jiƙansu." Suka haɗa baki gurin faɗin haka.

A waje tana fitowa da gudu ta taho zata rungume Aliyu.

"Oyoyo, Yayana daga birni. Yau zagaye ƙauyen nan zan yi da kai, kowa sai ya ga ina da 'yaya ɗan bir...."

Maganar ta katse sakamakon ingije ta da ya yi, domin da farko ya ɗauka mahaukaciya ce zai gudu.

"Ke! Are out of your mind?" Ya ce mata tare da wanka mata mari, sai kuma ya matsa yana gefe, sakamakon wani irin juyawa da jikinsa ya yi, saboda warin da ya shaƙa na jikinta. Kafin ya wani yunkuri ya shiga kwara amai, saboda ji wani irin ƙarni da hamami jikinta ya ji yana yi.

Marin ya sanya ta tsaya tamkar gunki, domin ta ji shigarshi sosai, har sai da ta ɗauke wuta, idanunta suka daina aiki na wucin gadi, amma da yake jaruma ce, ba ta nuna ta tsorata ba, sai kawai ta daure.

Haƙoranta ya kalla, har sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan cikin shi, ganin yadda suka dafe, ga sauran abincin duk sun maƙale sun zama gansa kuka.

Ranta ne ya ɓaci ganin aman da yake kwarawa, wanda ya tabbatar mata da ƙyamarta ya sanya shi amai.

"Banza ƙazamiya shashasha mahaukaciya! Ke a ba ki da han kawai sai ki zo da nufin ki rungume ni, saboda ba ki da hankali. Dubi jikinki kamar mahaukaciyar kina ta wari. Dirty girl kawai."

Zagin da ya yi mata, da abin da ya faɗa wanda ba ta gane da Ylyaren da ya yi mata ba, suka haɗu suka hautsina ƙwaƙwalwarta wacce ba ta aiki bisa ƙa'ida.

"Kan uba! Ka mare ni? Wallahi daina rama, domin duk faɗin ƙauyennan, babu uban da zai kare ni ban rama ba." Ta ce tare da nufarsa za ta mare shi.

Captain Aliyu sai mamaki ya kama shi sosai, na jarumtakar da fitsarrarta da kuma rashin tsoronta. Idanunsa ya xaro yana kallonta. Ganin ta ɗaga hannun da gaske za ta mare shi, sai kawai ya ƙara ɗaura mata mari ya fara dukanta.

Tun da ta fita hankalin Daddy ya tashi sosai. Ya san cewa da wuya su kwashe lafiya, ganin yadda take abu kamar sabon kamu.

Jin kukanta ya sa Kaka ta mike cikin tashin hankali tana faɗin,"Innalillahi! Wa ya sanya jikalle kuka?" Da gudu ta ƙara da har zaninta na shirin faɗi.

Mommy da Daddy suka rufa mata baya, a ransu suna addu'ar Allah ya sa ba zarginsu bane.

Turus! Suka tsaya suna kallonsa da yake kai mata duka.

"Kai mahaukacin ina ne za ka kama jikata da duka?" Kaka Tani ta yi masa tambayar cikin ɓacin rai.

"Kafin nan sai ki tambayi fitsarrarriyar jikinki mai ta yi mini." Ya ba ta amsa cikin ɗaurewar fuska.

"Amma kai kuwa an yi mara kunya tambadaɗɗe, saboda rashin ta ido ka biyo ta har cikin ƙauyen su ka buge ta?"

Jin abin da ta ce Daddy ya lalle shi ya ce,"Aliyu bana son hauka kar ka ƙara dukanta."

"Tunanin kasheta ma nake yi, tsaf zan iya sanya bindiga na harbe ta."

"Aiko da wallahi ka jawo ma kanka tashin hankali da bala'i, kuma ba ƙyaleka zan yi ba, saboda tun da nake da jikalle ta babu wanda ya taɓa sanya kuka."Kaka Tani ta Male shi cikin tsananin fushi yana faɗin haka.

"Ko yi haƙuri don Allah mu shiga ciki zan yi masa faɗa."

"A"a mugunta ce bana so, haka kawai ya zo ya duke ta? Ya bar ganin don kun kawo mini abu, wallahi keta masa rashin mutunci zan yi, don zan iya haƙura da kowa a kan jikalle."

"Ki bar shi da ni Kaka Tani. Aradun Allah yau sai na zubar masa da haƙora, sai dai ya sanya na roba, in ya koma birni." Ta ce tana neman abin da zata rama dukan da ya yi mata.

Zaro idanunsu suka yi, cikin tsananin tashin hankali, ga in ta ɗauko ƙarin dutse ta buge shi.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don Allah Daddy ka yi wani abu kar ta buga masa..." Kafin ta ƙarasa da daddy ya yi wani yunƙuri ta wurgar masa tana faɗin,

"Na rantse yau sai ka gane ka dauki Jimmalo, sai na canza maka halitta, na bar maka tabon da za ka rinƙa tunawa da ni."

Cikin sa'a ya kauce dutsen ya bugu gilashin motarsu. Mamaki ya kama su, suna kallon gilashin da ya tarwatse har sai da suka matsa a gurin.
Chapter 10 · 0% Book details