Sashe 37
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Never!"Ya ce tare da ɗaga hannunsa jin abin da ya ce, ganin Daddy ya yi shiru sai ya ɗora da cewa,"Never wannan gidahumar ta zama sister na. In har yarinyar nan za ta ci gaba da zama a nan, ba zan ƙara zuwa Kaduna ba." Yana ƙarashe faɗin haka, ya wuce cikin ɗakinsa, ba tare da ya damu da kiran da suke masa ba.
"Ka gani ko? Dama na san haka zai faru, babu yadda za a yi su yi rayuwa under roof ɗaya."
"Ya zama dole su yi I know what I will do." Daddy ya ce tare da juyawa ya shiga cikin falo.
Hannunta Mommy ta kama cikin takaici da take kuka miyau da jini duk ya haɗe. Kallonta ta yi sai taji tamkar za ta yi amai.
"Please Jimmalo, wannan abin da kike yi don Allah ki daina. Kin wuce yin haka duba ki ga yada kika yi ƙazanta?"
"Ni dai a mayar da ni Damagaran, na tsani kowa a gidan nan." Ta furta ba tare da shayin komai ba.
"Ok, shiga ciki ki wanke bakinki yanzu driver zai mayar da ke." Ta faɗi hakan ba tare da yanke shawarar ba.
"Ƙarya kike yi haka jiya haka kika ce mini, don haka sai kin rantse."
Jin abin da ta faɗa sai mamaki sosai ya kamata. Ganin duk girmanta ta tsare ta sai ta rantse.
"Let's go in Jimmalo." Ta kama hannunta da ƙarfi suka shiga ciki.
Daddy da yake safa da marwa ciki tsananin damuwa a falo. Ganin sun shiga cikin sai ya wuce sashin Aliyu, wanda ya gama haɗa kayansa yana shirin fita.
"Aliyu." Ya ji muryar Daddy ya kira sunansa. Cikin fushi ya jiyo zuciyarsa har tafarfasa yake yi.
"Aliyu you are no going anywhere and dole ka ɗauki Jimmalo a matsayin ƙanwarka, don haka ka ake jakarka yanzu ka kaita makarantar su Umma ayi..."
Kallon da ya yi masa sai ya kasa ƙarashe maganar, domin dama ƙarfin hali ya ke yi, amma kuma ya zama dole ya san yada zai yi ya haƙura da tafiya.
"Ni na ɗauki wancan kucakar a mota ta? Over my dead body!" Ya ce tare da zagaye kansa da yatsu biyu ya murɗa shi.
"Dole za ka ɗauke ta, a matsayina na mahaifinka na yi maka umurnin haka." Ya ce yana kallon sa cikin ɓacin rai.
Lokaci guda ya yi dana-sanin zuwa Kaduna, domin abin da ya gani ya gwammace bai zo bikin ba. Idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, saboda tsananin tashin hankali. Tunani yake ya za a yi ya sanya ta a cikin motarsa, har ya shaƙi numfashi da wannan bordy odour da take da shi.
"Am sorry daddy, I can take her to the school you can send your driver, saboda kafin na ƙarasa na tabbatar na amayar da kayan cikina."
"You must go and it is an oder." Daddy ya ce tare da juyawa zai fita.
Ganin haka ya tari gabansa cikin tashin hankali."Daddy, you are going to waist your money, saboda wannan mahaukaciyar nan, da ko alphabets I don't think she can read."
"Ko da ace ba ta iya ba dole zan saka ta, saboda babu yadda za a yi na zauna da ita ba ta zuwa makaranta, alhalin nawa yaran suna zuwa. Taimakonta zan yi ka san yadda taimakon maraya yake, don haka ina maka kwaɗayin samun wannan lada.
"Then You can go ahead, amma am not going anywhere."
"You must go bari na ke na yi mata magana ta yi wanka." Ya furta cikin muryar da yake gasganta masa da umurni ya ba shi.
Yana fita ya kaiwa iska naushi, tare da zama cikin ɓacin rai."Mai ya sanya na zo Kaduna? Da na san wannan mahakauciyar na nan, babu abin da zai sanya na zo, saboda na tsane ta sosai." Ya furta cikin takaici.
Tun da Daddy ya ce dole sa ya je, ya san cewa ba shi da mafita, abu ɗaya ya sani yana dawowa zai koma Abuja.
Ɗaukar turare ya yi, wanda zai rinka fesawa a motar duk bayan minti, kuma ya rantse ba dai a motarsa zai kai ta ba.
Haka ya zauna cikin takaici kamar zai fashe da kuka. Daddy da ya shiga ciki kai tsaye ɗakin su Umma ya wuce, ya samo Mommy tana zuba mata ruwa tana wanke jinin da yake zuba.
"Allah sai ya saka mini mugu azzalimi mai kama da zabiya wa..."
"Ke Jimmalo, wa ya gaya miki ana zagin babba? Ɗan'uwanki ne don haka karki ƙara zaginsa daga yau ya Aliyu za....."
"Da na kira shi da Yaya gara bakina ya sari kashi. Shi ba Yayana bane, kuma zan ci gaba da zaginsa inhar zai cigaba da mini mugunta. Ni ma soja zan zama na sanya bindiga na harbe shi, bayan na rama zalincin da yake mini." Ta ƙarashe maganar cikin zallar rashin kunya.
Mommy kasa ce mata komai ta yi ganin yadda take maganar. Sai kuma ta fashe da kuka."Kaka Tani ki taso ki ga azzalimi nan ya ƙara dukana. Ko yi masa fatalwa ki mayar da shi musaki."
Daddy ne ya yi gyara murya, wanda duk ba su san ya shigo ba. Mommy ta kalle shi tare da sakin ajiyar zuciya da ƙarfi.
"Ko sanya ta, ta yi wanka Aliyu zai kai ta a sanya ta boko da islamiya, sai daga nan ya kai su Umma."
Kallonsa suka yi a tare, Jimmalo jin za a sanyata makaranta, ya sanya ta yi masa banzan kallo. Mommy kuwa jin Aliyu zai kaita.
"Aliyu, ne zai kaita makarantar?" Ta yi masa tambayar cikin razana.
"Makaranta? Aradu babu makarantar da zani har da makarantar arna!" Jimmalo tace tana jijjiga.
Takaici ya sanya Daddy kasa amsa mata, sai ya kalli Mommy ya ce,"Eh, kuma na yi magana da shi."
"Kar ya je ya kashe yar mutane?" Ta ce a razane.
"Ba zai fara ba, tun da yana da ilmi ya san hukuncin wanda yayi kisa."
"To in ya cutar da ita fa? Kasan Jimmalo, ba kunya ne da ita ba, dole tayi masa abin da zai harzuƙe shi, sannnan shi kuma bai haƙuri."
"Zan haɗa shi da su Nufaisah, kuma baya haka ya zama dole na kawo sasanci a tsakaninsu. Ban san lokacin da zan mutu ba, kin ga duk ranar da na kwanta dama Aliyu shi zai zama uba a gidan nan, in har basa shiri ba zai kula da rayuwarta ba."
"Hmmmmh!" Tace don sam shawarar bai yi mata ba.
"Ki sanya ta ta yi wanka ta canza kayan jikinta, sannan ta fito bari na yi wa su Nufaisah magana na ga suna falon sama."
Ya yi saurin fita kafin ta gaya masa ba za ta iya ba, domin abin da ya karanta a idanunta kenan.
Mommy kallon Jimmalo ta yi sai ta kasa cewa komai.
"Ki bar kallona, saboda ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi wankan nan ba, sannan a mayar da ni Damagaran."
Dubara ce ta faɗo wa Mommy ta ce,"Kin ga kuma in kika yarda kika yi wankan nan, sannan kika bi su aka kai ki makarantar kin samu hanya mafi sauƙi da za ki koma Damagaran, kawai guduwa za ki yi." Ta furta mata hakan, don ta san babu yada za a yi ta samu ta gudu.
Shiru ta yi kamar mai tunani sai can ta nisa ta ce,"Amma ba zan yi wanka ba dakatsami...."
"Ke da an yi magana kice daka tsami za ki yi. Kin san irin warin da kike yi? Zan gaya miki gaskiya wallahi, in har ba kya wanka Jimmalo mutane gudunki za su rinƙa yi."
"To ni ina ruwana dama ni kaɗai nake son na yi rayuwa." Ta furta ba tare da ta damu da warin da ta ce tana yi ba.
"Ki yi wankan dai na yau, tun da ana sanya ki a makarantar guduwa za ki yi." Mommy ta ce cikin rashin dubarar abin da za ta ce mata, wanda zai sanya ta wankan in har ta ƙi.
"To bari na yi wankan, amma na rantse ba zan zauna a gidan nan ba, wancan mugun mai kama da zabiya yana nan."
Tun da Mommy ta ji ta amince, sai ta nufi hanyar fita kawai don ta gaji da rarrashinta.
Jimmmalo tsaya ta yi cikin takaici, domin an takurata tun da aka ce ta yi wanka. Ita babu abin da ta tsana kamar wanka. Ta ɗauki tsawon lokaci tana tunanin ta yi ko kar ta yi? Sai kuma ta rarrashi zuciyarta bayan ta ɓata lokaci.
Miƙewa ta yi tana gungunai ta shiga cikin bayin. Turus ta yi tana kallon bayin da za ta iya kwana a cikinsa, domin kyawunsa da kyan da ya yi.
Saboda jaraba da safe ba ta shiga cikin bayin ba, tana tashi ta fita zuwa kicin. A maimakon ta fito ta kira a nuna mata yadda za ta yi amfani da shi, sai ta yi xamanta ta kunna can ta murɗa can.
Mommy cikin damuwa, ta kira Umma ta zaɓar mata doguwar riga da hijabi mai kyau. Jin shiru ba ta fito ba sai ta kwanƙwasa bayin.
"Jimmalo, har yanzu wankan kike yi Aliyu yana jiranki ba." Ta yi mata ƙaryar.
Buɗe ƙofar ta yi ta tsaya tare da kama murfin."Ni ban san yadda ake kunna famfon ruwa ya zo ba, kuma na fasa wankan saboda gaskiya sanyi nake ji."
Mommy ji ta yi kamar ta kife ta da mari. Xuciyarta ce ta harzuƙa domin mace ce mara ɗaukar raini.
"Ba sai ki kira a zo a nuna miki ba, amma kin zauna a cikin bayi kamar kina ɗaki?"
Tambayar da ta yi ta cikin tsawa sai ta ɓata ranta."A mayar dani Damagaran na yi rayuwa a kusa da ƙabarin Kakata Tani." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka kamar wata yarinya.
Mommy watsa mata harara ta yi ji take da ace daga danginta take babu bin da zai hana na ta kai mata hannu ba, amma duk da haka ba ta tunanin zata iya jurewa.
"Ki je ki yi wankan ni ma na ƙosa ki tafi saboda zama dake sai mara zuciya." Ta furta tare da yin tsaki ta shiga cikin bayin.