← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 52

Sashe 31

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya suke?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa. Wayarta ta ɗauko ta duba lokaci sai ta ga ashe har an kira sallar asuba. Miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a sosai ta ƙara yi tana fatan suna lafiya. Da carbi a hannunta ta shingiɗa tana ja. Kafin safiya xuciyarta ya gama kitsa mata ta je Ƙauyen Damagaran, saboda gabakiɗaya ta kasa samun sukuni. Da Kaka Tani ta faɗo mata sai ta ji gabanta ya yanke.

Wayarta ta ɗaga ta kira numbar Daddy. Yana ɗagawa ya yi sallama, sannan ya gaishe ta.

"Ka shirya safiya za mu je Ƙauyen Damagaran, saboda jiya kwana na yi ina mafarkin Tani."

Mamaki sosai ya yi, jin abin da ta ce har sai da ya cire wayar ya kalli numbarta, saboda ya yi mamakin jin cewar za ta ƙara shiga rayuwar su bayan ta ce ita da su har abada.

"Kana jina ko Abubakar? Mugun mafarki na yi na Tani. Ba a gasganta mafarki, amma ina jin kamar babu lafiya, don Allah ka shirya mu wuce da safen nan."

"To Hajiya Allah ya sanya lafiya. In sha Allah ina karyawa zan yi na fito."

"Amin, ka yi sauri don ba zan iya karyawa ba sai a mota."

"To gani nan zuwa." Ya ce tare da kashe wayar yana kallon Mommy cikin mamaki.

Dariya mommy ta yi ta ce,"Ba za ta haƙura da su ba, dama ni na san haka. Hajiya da kullum nasiharta mutum ya kula da zumunci, sai ta yi watsi da nata? Na san cewa hushi ta yi kuma za ta huce ta neme su. Yana da kyau ta haƙura ta samu ta ci galabarsu har ta canza musu rayuwa, wallahi Jimmalo tausayi take bani. Yarinyar nan ba ta san wace ce ita ba, ballanatana ta gane irin rayuwarta ta dosa. Babu ilmi babu natsuwa ba tsafta. Wannan wane irin rayuwa take yi."

"Duk yadda zaki so ki kawo gyara a cikin lamarinsu sam ba za su yarda ba. Ni fa ba taɓa ganin mutane irin su ba."

"Gaskiya yadda ka san ba su da hankali. Da ace Kakar tana tsawata mata, wataƙila da an samu sauƙin haukar da take yi."

"Duka duk halinsu ɗaya. Fito mini da kayan bari na shiga wanka." Ya ce tare da kama hanyar bayi, ita kuma ta nufi wandrop ɗinsa.

Bayan ya shirya ya karya, sannan ya yi musu sallama ya nufi gidan Hajiya.

Hajiya da ta riga ta shirya, tana jin motarsa ta fito tun kafin ya shigo."Na shirya muje kawai saboda hankalina a tashe yake."

Yadda ya ga ta tayar da hankalinta, sai ya shiga bata baki har ta ɗan saki."Mafarki ba gaskiya bane in sha Allahu suna lafiya."

"Ina fatan hakan." Ta ce bayan ta zauna a cikin motar suka fara tafiya.

Kasancewar sun fita da wuri, kuma Daddy ya yi gudu sosai sai suka isa daidai lokacin da aka ɗaga makarar Kaka Tani. Jimmalo tana ihu tana riƙe da ita aka fito ƙofar gida.

"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Ni dama na ji a jikina ba lafiya ba, ashe Tani rai ya yi halinsa. Shikenan ba ni da kowa a dangin mahaifiyata." Ta furta cikin kuka tare da fita daga cikin motar.

Daddy cikin sauri, ya kashe motar ya fito domin ganin mutuwar jikinsa da ya yi sanyi.

"Ya Salam ashe mutuwa ta yi!" Ya furta cikin damuwa.

Hajiya na zuwa ta rungume makaran ta fashe da kuka."Tani ashe ganawarmu kenan ba za mu ƙara ganin juna ba? Sannan ba mu yi rabuwar farinciki ba."

Ganin Hajiya, Jimmalo ta saki makarar ta kama hannunta. "Yauwa gara da kika zo, don Allah ki gaya musu ba ta mutu ba bacci take yi. Kin gani za a raba ni da ita?" Sai ta saki hannunta ta kama hannun Daddy da yake tsaye jikinsa ya yi sanyi sosai.

"Ba ta mutu ba duba ka gani so suke su raba mu."

Kamar ya yadda da maganarta sai ya ƙarasa ya ɗaga likafanin. Da sauri ya mayar yana hawaye."Ki yi haƙuri Kakarki ta mutu."

Duk yadda suka yi ta bari akai ta makwancinta ta ƙi, har sai da Daddy da Hajiya suka riƙe ta sannan aka tafi da ita.

Ta yi ihu da kuka, har da zagi ta haɗa musu don su ƙyaleta, amma Daddy ya yi mata riƙo sosai. Duk yadda ta so ta ƙwace haka ta haƙura, domin duk ƙarfinsa ya sanya ganin tana son ta ƙwace.

Bayan an je an kaita aka zauna zaman gaisuwa. Sosai Daddy ya yi mamakin irin kukan da Hajiya take yi. Duk da y an cewar 'yar'uwanta ne, amma ba su yi shaƙuwar da za ta rinka risgan kuka haka ba. Sai suka zame mishi su biyu. Ita Jimmalo dama duk haƙurin da yake bata kamar yana ƙara cewa ta yi ne, saboda tunaninta yau Kaka Tani ta rasu to da wa za ta yi rayuwa?

Daddy ne ya siyo duk abin da ake bukata, duk da cewar da sauran abincin da suka kawo musu, don haka ya ƙaro wasu.

Jimmalo sarfatan mutane ta yi, ta gudu zuwa ƙabarin da aka rufe Kaka Tani ta kwanta tana ta kuka ta ce,"Kaka Tani dama ba za ki rayu da ni ba, kika yi mini alƙawarin sai kin ga jikokina? Kaka Tani kin tafi kin barni mutane sun cika gidanmu ana ta cinye mana abincin da muke ci da ga ke sai ni. Kaka Tani kina jina ki taso mu koma gida, mu ci gaba da rayuwarmu, domin in har ba ki tashi ba, ni ma a nan zan dawo da rayuwa."

Kuka take yi, tana faɗin suratai da kalamai waɗanda ba su kamata ba. Daddy da Hajiya suka taho zuwa ƙabarin. Ganinta kan ƙabarin tana kuka sai jikinsu ya yi sanyi sosai. Da ma sun san za a rina, dole ta yi kukan rashinta, saboda yadda ta shaƙu da ita kuma ita kaɗai ce danginta.

"Jimmalo, Kakarki ta mutu sam ba za ta dawo ba, saboda lokacin tafiyarta zuwa ga mahallicinta ya yi. Duk wanda kike gani a duniya mutuwar yake jira. Ke ma za ki mutu, don haka ki taso mu koma gida ki fuskanci rayuwar gaba."

"Ba zan koma gida ba, in har zan mutu to zan jira nawa mutuwar a birne mu da ita." Ta ce wa Daddy tana zare idanu jin abin da ya ce.

"Jimmalo, ki tashi mu koma gida na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarmu fiye da yadda Tani ta yi, saboda zan baki gishiri zaman duniya zan i..."

"A'a ba na son ji!" Ta furta tare da toshe kunnuwanta, sannan ta ɗora da ce wa,"Babu wanda zai iya kulawa da rayuwata, kamar yadda Kakata wacce tafi ƙaunata ta yi. Don haka ku tafi bana son ganinku na tsani kowa." Ta ƙarashe maganar, tare da ƙara kwanciya kan ƙabarin tana kuka tana kiran sunanta.

Ta ba su tausayi sosai har sai da Daddy ya yi ƙwalla. Dama ita Hajiya kuka take yi.

Ganin da gaske take yi ba za ta koma gida ba, saboda har an yi kiran sallar magariba, sai Daddy ya sanya maza suka kai ta gida aka kulle ta.

A ranar bana tunanin ko ruwa ta ka bakinta. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Idanuwanta sun kumbura sosai. In ta duba ta ga babu Kaka Tani sai dai kayanta sai ta ji kamar za ta shiɗe. Za ta iya cewa tun ta girma ba ta taɓa nesa da ita ba, domin ko anguwa za ta je da ita take zuwa na kwana. In har ba tallah ko dandali suka je ba suna tare, saboda watarana har wasa take taya ta. Yau ga shi babu ita kuma ana tsammanin ta ci gaba da farinciki? Ita da farinciki har ƙarshen rayuwarta, domin za ta yi ta ƙunci, tana jiran lokacin da nata mutuwar za ta zo, ta je gurin Kaka Tani.

Duk rarrashin da suka yi mata, taki yin shiru kuma ta ci abinci. Jimmalo ko haka kawai akwai kafiya, ballantana an raba ta da abin da take ganin babu na biyunsa a cikin rayuwarta.

Haka ta kwana cikin dare, zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Ba ta sha magani da Hajiya ta bata ba, don haka zazzaɓi mai zafi ya kamata har asuba tana makyarkyata.

Hajiya da Daddy, kwanar wahala suka yi, saboda babu gurin bacci mai kyau. Haka dai suka daddage har aka yi sadakar uku. Aka raba gadon da ta bari aka bawa Jimmalo dama ita ce kawai. Tunkiya guda uku sai kaji da kuma hatsi da take tarawa, sannan sai gidanta ya rage.

A fadar maigari akayi rabon gadon. Maigari ya kalli Hajiya da Daddy ya ce,"Tani ta rigamu gidan gaskiya Allah ya yi mata rahma."

"Amin," Suka amsa ban da Jimmalo da take sharan hawaye.

"An raba abin da ta bari saura gidanta, domin shi ma ya kamata a siyar a bawa Jimmalo gadonta."

Jin abin da maigari ya ce, sai ta miƙe tana zare idanu."Wallahi babu wanda ya isa ya siyar mana da gidan da na ke gani nake tuna Kakata! Kuma in kuka siyar a ina zan rinƙa rayuwa?"

"Ba ki san Kakarki ta bada wasiyar ki koma birni ba? Ai ta gaya wa Audi mai kyamis da Innar Salame 'yan birni su tafi da ...."

"Kan uba!" Ta furta tare da miƙewa tana zare idanunta, domin ji ta yi kamar wasa ko tsokanar ta yake yi.

"Ni ce zan koma birni! Saboda me na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan, domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta mutu."

Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu.

Jimmalo ina taya ki rashin Kaka Tani domin mutuwa babu daɗi, musamman da ta sangartata ki.

Yanzu ne za a fara wasa yanzu za a shiga cikin littafin. Ƙiyayyar jini akwai cakwakiyar gaske. Ku ci gaba da bibiyar labarin sannan da sambaɗo zafafan comments.
Chapter 31 · 0% Book details