← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 52

Sashe 26

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗinsa ta Whatsapp ba ya reply. A cikin satin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta mutu.

Ganin halin da ta shiga sai Hannah ta kira gida ta sanar. Duk abin da take ɓoyewa ta sanar musu har zuwa kwanar da take yi gidansa. Hankalin iyayenta ya tashi sosai, inda duk suka ɗauki laifin suka ɗora mata, domin da ace tuntini ta sanar da sun yi wa abin tufka hanci.

Mahaifinta ya yi fushi sosai, cikin tsananin ɓacin rai ya zabga mata mari."Irin tarbiyyar da na baki kenan Lubaynah? Ko da kika ga na ƙyale ki kina rayuwa yadda kika dama, ban taɓa tunanin za ki iya, zuwa gidan namiji kina kwana, a tunaninki hakan da kike mishi zai sanya ya aure ki?"

"Daddy Anty karya take mini, Captain Aliyu sona yake yi, ban taɓa zuwa na kwana a gidansa ba, kuma zan tabbatar maka da hakan da zarar ya dawo zan sanya ya turo iyayensa."

"Ƙarya za ta yi miki kenan? Mene ne ribarta don ta yi miki karya?"

"Eh na san cewa ina zuwa gidansa na taimaka masa da aiki, amma Captain Aliyu bai taɓa riƙe ko da hannuna bane."

"Wallahi Daddy yarinyar nan ƙarya take yi, ko Daddyn Fadil ya san abin da take aikatawa, kuma shi yace na sanar daku tun kafin lamarin yafi ƙarfinmu."

"Ki barta tun da ta ƙaryata na ba ta izinin ya turo iyayensa, sannan ba za ta ƙara zuwa Abuja ba."

Kuka ta fashe da shi, jin tsautsaurar hukuncin da ya yanke mata. Ta san cewa da wuya Captain ya turo iyayensa. Wayarta ta ɗauka ta shige cikin ɗakinta.

Layinsa ta fara kira, amma kamar kullum ba ta shiga. Sai ta yi jifa da wayar tare da fashewa da kuka. A zuciyarsa tana jin ba za ta iya bin umurninsa na hana ta zuwa Abuja ba, domin ya zama dole ta je gurin sa, don ta ji dalilin ƙin ɗaukar wayarta.

Tana cikin damuwa har tsawon sati bai ɗauki wayarta ba, sannan an sanya mata tsaro sosai domin idanun mahaifiyarsu yana kanta. Zazzabi sosai ya kamata har sai da aka kaita asibiti.

Ita da Mommy suka je sibiti. Tunanin hanyar da za ta gudu take yi. Tana cikin wannan tunanin likita ya ba Mommy takadda ta je ta siyo magani. Da sauri ta miƙe ta fice daga asibitin.

Bayan ta dawo ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Hankalinta ya tashi sosai ta kalli likitan."Please Petient ɗin da na zo da ita fa?"

"Ta ce za ta je bayi." Ya ce mata hankalinsa a kan laptop ɗinsa.

Cikin sanyin jiki tafiya tana duba ko'ina, amma ba ta ganta ba. Ganin ta duba kaf asibitin babu ita, sai hankalinta ya tashi ta ɗaga waya tana kuka ta kira Daddy.

Hankalinsa a tashe ya iso asibitin, amma sun duba ko ina ba su same ta ba. Mommy ce ta fashe da kuka tana faɗin,"Lubaynah na da hankali kuwa? Namiji ne za ta gudu ta je gurin sa?"

"Lailai bata da hankali kuwa, amma ki barta in har ta dawo sai na ɗauki mataki a kanta."

Cikin ɓacin rai suka koma gida. Mommy sai kuka take yi Daddy yana bata haƙuri.

Hannah suka kira ko ta san gidan Captain, amma sai ta gaya musu ba ta sani ba. Fushi sosai suka yi da ita, suna jiran ta dawo sai sun ɗauki mummunar mataki a kanta.

Lubaynah na fita daga asibitin ta shiga cikin napep ya kaita tasha. Sai da ya kaita sannan ta cire kuɗi a p.o.s, don transfer ta yi musu saboda ba ta zo da ATM ɗin ta ba.

Kuɗin mota ta biya zuwa Abuja. Ba ta iso Abuja ba sai bayan magariba. Kanta ne ke ciwo sosai ga wata uwar yunwa da take ƙwakularta. Tun a hanya ta kira shi yafi sau nawa, amma baya shiga. A mota tana kuka sosai domin ta san son Captain jarrabawar ta ne.

A lokacin da ta isa gidansa tana addu'ar yana nan.Cikin sa'a Solo ya sanar mata yana nan, amma ya ce kar su ƙara buɗe mata gidan. Hankalinta ya yi mummunar tashi ga yunwa ga zazzaɓi a jikinta."Mai Captain yake nufi?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali.

Ganin yadda take daga ganinta ka ga mara lafiya, sai Solo ya shiga cikin gidan. Yana zaune daga shi sai gajeren wando yana ta aiki a Laptop ɗinsa..

Solo ya nemi izini ya shiga."Sir, Lubaynah is outside like she is not feeling well."

Tsaki ya saki lokaci guda zuciyarsa ta ɓaci. Ya rasa yadda zai yi da ita ta fita cikin rayuwarsa, domin ta zame masa ƙarfen kafa.

Agogo ya kalla ƙarfe bakwai da rabi."Don't open the get for her."

"Ok sir." Ya ce tare da juyawa ya koma yana mamakin rashin zuciya irin nata.

Zuwanta ya canza mood ɗinsa har ya kasa aikin da yake yi. Kashe laptop ɗinsa ya yi sannan ya koma ya zauna, bayan ya janyo sigari ya kunna. Miƙewa ya yi zuwa cikin ɗakinsa ya kwanta.

Lubaynah tana gurin har zuwa sallar Isha. Saboda karya ganta a gida ya yi sallarsa ya kwanta. Ganin ya ƙi fitowa sai ta nufi gidan Kalim.

Kalim yana zaune a cikin falonsa yana kallo shi da Nadiya da ta zo masa kwana biyu. Mai-gadinsa Dupe ya knoking ya shigo.

"Sir a lady is looking for you outside."

Kallon juna suka yi shi da ita. Ranta ne ya ɓace amma ba ta ce masa komai ba, ganin haka ya ce,"Ok"Sannan ya miƙe ya ce,"Please, ina zuwa I don't have any appointment with another lady but lemme see her."

Ba ta ce masa komai ba, ganin haka sai ya sanya doguwar riga ya fita. Ganin Lubaynah da tana ganinsa sai ta fashe da kuka.

"Lubaynah lafiya?" Ya furta tare da ƙarasawa gurinta ganin yadda take kyarmar sanyi.

"Mai na yi wa abokinka wanda ya zaɓi ya wulakanta rayuwata, ko soyayya yana zama laifi ne?" Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.

"Is ok Lubaynah let's go to his house, I will talk to him." Ya ce tare da fara tafiya zuwa gidansa.

Kasancewar babu nisa suka isa. Layinsa ya kira, sannan ya sanar masa yana ƙofar gida."Are you with Lubaynah?"

"Please Captain open the get we need to talk." Ya ce nasarar da kashe wayar ba tare da ya amsa masa ba.

Solo ya kira ya sanar mishi da ya buɗe get ɗin. Lubaynah na shiga falon ta saki kuka sosai tare da zuwa za ta rungume shi. Da sauri ya janye jikinsa yana watsa mata mugun kallon daya sanya jikinta sanyi sosai.

"Captain Aliyu, Lubaynah ba ta cancanci haka a gurinka ba. Please settle with her, the girl deserve your love."

"I already broke up and a told her am done into this toxic relationship. Kalim, mahaifina ya yi matuƙar yarda da ni sosai, haka family ɗina suna mini kallon mutumin kirki, na zama kura da fatar akuya. I need to change tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada. Duk ranar da mahaifina ya gane abin da na ke yi ba zai yi sausauci a gare ni ba, sannan zan rushe duk yardar da ke tsakaninmu."

"Then ka aure ta tana sonka kai kaɗai take kulawa."

"No, it is absolutely impossible!" Ya furta babu kunya.

Jin abin da ya ce sautin kukanta ya ƙaru.

"You know what? Lemme leave you with her, please reconcile." Ya ce tare da ficewa.

Yana fita ta miƙe ta kama hannunsa da yake shirin shigewa bedroom. "Aliyu don Allah ka so ni ka tura iyayenka, domin mahaifina ya tsaurara mini dokar hana ni zuwa Abuja, sannan ya ce in har sona da gaske kake yi ka turo iyayenki."

"Lubaynah am so sorry da na yi disvirgin ɗinki, but I can marry you. Go look for another man and marry. Na yi miki alƙawarin duk abin da kike so zan baki. Ki faɗa mini ko nawa zan baki matuƙar za ki fita daga rayuwata."

"I don't need your money. My dad has money on him. Zuciyata kai take muradi so na ke yi na mallake ka a matsayin mijina. Ina sonka don Allah ka aure ni. Na yi maka alƙawarin kasancewa duk yadda kake son matarka ta zama." Ta ƙarashe maganar tare da durƙusawa ta dafa ƙafafunsa.

Rintse idanunsa ya yi cikin damuwa. Zuciyarsa take son tausaya mata, amma ba ya amince ya aure ta ba, domin ya san ko da ya yi hakan, ba za su taɓa samun zama lafiya a rayuwar auren su ba. Don haka zai lallaɓe ya shawo kanta ya bata kuɗi sosai ta fita daga rayuwarsa.

Kamata ya yi ya miƙar da ita ganin haka sai ta faɗa jikinsa. Da sauri ya janye ta daga jikinsa, ya yi da zafin jikinta ya sanya shi jin wani iri.

"Is ok stop crying we will talk later. Yanzu kina buƙatar kici abinci ki samu lafiya."

"Sojana ka yi alƙawarin za ka aure ni?" Ta yi masa tambayar tana share hawayenta.

"I will sleep on it." Ya ce mata tare da kama hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Kwantar da ita ya yi kan gadon sannan ya kira doctor ɗinsa don ya duba ta.

Ganin yadda yake tattashinta, sai yaji hankalinta ya ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu. A ranta tana addu'ar Allah ya sanya ya amince ya aure ta.

Bai daɗe da kira likitan ba ya ƙaraso. Ganin yadda jikinta ya yi har ɗakinsa ya shiga ya yi treatment ɗinta. Bayan ya yi mata allura ya ɗaura mata drip, sannan ya yi masa sallama ya tafi kan cewar Aliyu zai cire mata.

Tana kwance a kan gadon tana bacci idanunta rufe. Tea ya ba ta da ƙyar tasha sannan ta samu bacci. Kallon kyakyawar fuskarta ya yi da baccin da take yi ya ƙara mata kyau. Ramar da ta yi sai ta ba shi tausayi.
Chapter 26 · 0% Book details