← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 52

Sashe 39

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A mayar dani kauyen damagaran, saboda ba zan yi makarantar arna ba." Ta furta a gatsale tana kallonsa.

"I said what is your name? Kina gaya mini makarantar arna. An gaya miki ni arne ne? Musulmi ne ni sunana Muhammad."

"Amma ka yi asara kana arne ka sanya sunan Annabinmu." Ta furta cikin takaici tana kallonsa.

"Ke! Ni ba arne bane." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.

"To amma kake shigar arna?" Ta furta hakan ganin suit ne a jikinsa.

Komawa ya yi ya zauna yana huci. Don ya rasa amsar da zai bata.

"Ka gani ko? Na gaya maka mahaukaciyar ce. Dole ku dage in ta yi muku haka ku yi mata shegen duka."

"Gaskiya na ga alama za mu yi aiki."

"Sosai ma kuwa." Ya ce tare da miƙewa domin so yake ya bar Kaduna da zarar ya koma gida.

"Za ki iya karanta mini A.B.C da kuma 1.2.3.4?"

"Kai ka sansu, don ni ko karatun allo da na iya na sallah na yafe wa kaina, saboda ba zan wahala ba. Haka kawai wani gardi ya duke ni."

Mari Aliyu ya kawo mata."Uban waye gardi?"

Da sauri ta matsa tana ƙunkunai."Kana ji ko? Ba zan koma da ita ba, saboda zan iya amayar da kayan cikina. A nan zan barta sai ka yi mata tambayoyin, amma da za ka ji shawara ku sanya ta a nursery one"

"Shikenan babu matsala, zan yi magana da mahaifinka duk da ya tura mini kuɗin komai, amma gaskiya bayan na makaranta dole a tura mana da wasu kuɗi, domin tana buƙatar proper care. Nanny's ɗin mu za su kula da ita, yau dole ayi mata wanka sannan ayi kitso ta canza ka..."

"Wanne me? Na rantse babu wanda ya isa ya taɓa mini jiki, duk wanda ya yi kuskure taɓa ni, sai na ragije masa kai." Ta furta tana ƙoƙarin ficewa.

Aliyu ya sanya kafa ya taɗiyeta sannan ya ce,"Good, ku yi duk abin da ya kamata. In kun kasa wanke gashin ku aske kawai." Yana gama faɗin haka ya fice.

Ganin haka ta saka kuka za ta bishi."Wayyo ba zan yi karatun arna ba, kuma babu wanda ya isa ya aske mini kai. Ba zan yi wankan ba. Wayyo Kaka Tani ki taso daga ƙabari za a kashe jikarki." Ta saki ihu tana faɗin haka.

Principal ɗin fitan Aliyu sai ya yi masa daɗi. Da sauri ya miƙe bayan ya kira nanny guda biyu.

"Mene ne sunanki?"

"Jimmmalo jikar Tani." Ta furta tana harararsa.

"Sunanki na gaskiya nake magana da na mahaifinki."

"Sahiya Audi." Ta furta tare da murguɗa baki.

"Ok, Safeeya Abdullahi kenan?"

"A ɗan dakata kar ka ɓata mini sunana, saboda Sahiya Audi nake, kuma Kaka Tani da Jimmalo take kira na, saboda ta ce ranar sa a aka haife ni. Ranar Juma'a don haka Jimmalo za ka kira ni."

"A makaranta dole sunan yanka za a kira ki da shi."

"Ni wallahi duk wanda ya kira ni da wani suna ba Jimmalo ba, sai ba gurje bakin mutum da yashi."

"To sai ki fara ta kaina mara kunya fitsarrarriya kawai." Ya ce yana harararta

Kafin ta yi magana nanny's suka shigo"Sir gamu." Suka haɗa baki girin faɗin haka.

Kallonsu ya yi ya ce,"Ku kira mini sajen Saminu, sannan wanna yarinyar ku kamata ku yi mata wanka, ku duba kayan da zai shige ta na uniform primary one za a sanya ta."

Zare idanunsu suka yi "Primary one sir? Yarinyar da ta girma haka?"

"Yar ƙauye ce ku yi abin da na ce."

"Ok sir." Suka haɗa baki gurin faɗin haka a tare.

Kallonta suka yi da take zare idanu."Na rantse duk wanda ya taɓa ni, saina sanya Kakata ta yi masa fatalwa ta lashe shi." Ta ce cikin rawar murya ganin kashedin bai sanya su fasa ninyar su ba.

"Kai this girl is smelling ke wace irin ƙazamiya ce bakya wanka?"

"Gyatumar ki ce ƙazamiy..." Kafin ta ƙarashe maganar ta ji an wanka mata mari.

"Kul! ba a zagi a makarantar nan, saboda ba za ki koya wa ɗalibanmu rashin kunya ba."

"Alllah ya isa mugu azzalimi."Ya ji tace kafin ya ƙarashe maganar.

"Please ku je ku yi mata wankan ku tsaftace ta."

Ihu ta saka za ta fita, amma sai sajen Aminu ya ɗauke ta cak zuwa bayi, saboda wani irin ƙato ne murɗadde.

Ihu ta cika makarantar tana kiran Kaka Tani, amma ba su kula ba har sai da suka danganata da bayi.

A cikin class ɗin su Umma, tana zaune ta gefen windo tana kallonta."Umma, wancan yarinyar ba 'yar uwarsu bace? Saboda kamar a motar Yayanmu ta zo?"

"Ba 'yar uwata bace ban san ta ba." Ta ce don bata son mutane su san suna da 'yan'uwa a ƙauye '.

Aliya komawa ta yi ta zauna, don ba ta yarda ba, musamman da ta nuna rashin gaskiya.

Tana kuka tana ihu, amma basu kula ba sai da suka fara mata wanka. Ihu da zagi kam ta yi shi har sai da muryarta ya rushe. Da ta san abin da za ayi mata kenan, da ba ta yarda da maganar Mommy ta zo makarantar ba.

Kanta kuwa, bayan sun sanya mishi mai, sai da suka yanke gashin da ya dunƙule, duk da kuwa gashin irin mai tsantsi da warwara ne, amma saboda rashin tsafta da kula ya sanya shi fita hayyacinsa. Abin takaici gashi tana da gashiin sosai, amma duk wanda ya kalli gashin sai ya yi mai. Da suka zo goge bakinta sai da suka ji kamar ba za su iya ba, saboda suna dirjewa jini yana zuba. Makilin kusan ɗaya ya ƙare, amma bai yi hasken da suke so ba, saboda ya riga ya dafe. Ga abinci da ya zama gansa kuka.

Sun samu sun yi mata wankan, don babu dauɗa jikinta, sai dai ba ta yi haske ba. An dai cire datti. Kayan makaranta suka ɗauko mata bayan sun shafa mata mai da karfin tsiya.

Babu laifi sai ta fito 'yar makaranta da ita. Kallon kanta ta yi cikin kuka saboda gani take babu tozarcin da ka yi mata yafi wannan. Jikinta kuwa zafi yake mata, saboda dirzansa da suka yi.

"In sha Allahu wuta za ku shiga mugayen azzalumai." Ta ce daidai lokacin da sister Lami ta miƙa mata sandal da sock.

"Rufe wa mutane baki mara kunya. A makarantar nan sai na koya miki hankali. Maza sanya sandal da sock ki je ofis."

Ganin ta ƙi sanya wa tana murxa bakinta da ta buge, sai ta janyota ta faɗi kasa ta fara ƙoƙarin sanya mata. Ganin haka Sister Ani itama ta janyo ɗayan kafar suka sanya mata.

Janta suke yi da ƙarfi har suka isa ofishin. Principal ya kalle ta ya ce,"Dubi ki kin ɗan yi fasali mai ake yi da mutum ƙazami?"

Harara ta aika masa da shi saboda ba ta son magana, domin bakinta da suka gurje zafi yake mata, sannan da ta yi magana sai jini.

"Ku je zan kaita primary one."

"Ok sir." Suka ce tare da juyawa suka tafi.

"Ki biyo ni." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka

Binsa a baya ta yi tana ƙunkunai har suka shiga primary one.

Yana shiga yaran suka miƙe suka haɗa baki gurin faɗin,"Good morning sir."

"Morning how are?" Ya ce musu yana kallonsu.

"Fine thank you sir." Suka ce suna kallon Jimmalo da ita ma take kallonsu.

"Sit-down you have a new mate sunanta Safeeya Abdullahi."

"A'a ni fa sunana Jimmalo, ku kira ni Jimmalo jikar Tani, domin na rantse duk wanda ya kira ni da Sahiya sai na karya mutum."

"Safeeya, za ku kira ta sannan ku rinƙa koya mata karatu, a jinku za ta zauna"

Zare idanunsu suka yi, jin abin da ya ce."Sir wannan sa'ar Addata Hafsat ce a kaita ajinsu, saboda ta yi girma a nan. Za ta zama maman aji" Faisal ya ce su suka kwashe da dariya.

"Kai ni ne zan zauna da waɗannan ƙananan yaran? Hahaha, wasa kake yi na rantse, in ba so kake yi na rinƙa ɗaukar su na maka su da ƙasa ba, don tsaf zan kashe yaro in har sun mini dariya."

"Ke Safeeya, ki natsu don wallahi kika cutar da wani sai na sanya an miki duka."

"Ni fa ka daina kirana da Sahiya Jimmalo dai." Ta ce tana harararshi.

"Kuna ji ku rinƙa koya mata karatu Anty don Allah ki sanya ido, sannan ki rinƙa koya mata karatu."

"Ok, sir." Malamar ta ce tana kallonta da take ta kumburin tana zaginsa.

"Na rantse duk yaron da ya yi kuskuren cewa zai koya mini karatu suna karya shi."

"Ki taɓa yaro a makarantar ki gani." Ya ce mata tare da tsaki ya fita.

Ganin za ta bishi Anty ta ce,"Ke Safeeya, come and sit down."

Tsayawa ta yi ganin ya rufe kofar sai ta dawo ta ɗage saman windo tana faɗin."Na rantse duk sai na yi maganinku, har ke da kike ji da ƙiba kamar doya."

Dariya aka kwashe da shi malamar ta yi musu tsawa."Ba zan lamunci rashin kunya ba, kuma zan mugun saɓa miki."

Ƙunƙunai ta yi ta haye zaman windo tana mamaki wai yau ita ce a makarantar boko?Gaskiya mutuwar Kaka Tani ya kawo mata cikas a rayuwarta.

Ganin haka sai ta ci gaba da karatun burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kai ta yi ba tare da ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ba ta iya ba ballantana rubutu.

To Jimmalo Jikar Tani an fara shiga wata rayuwa. Daga Jimmalon yau mun ji ainihin sunanki Safeeya. Sai na ce ɗaliba Safeeya Allah ya sanya ki tsaya ki iya karatu. Yau dai kawo ƙarshen kan Jimmalo da rashin wanka. Shi za ta goge ta waye ta zama student ko za ta ci gaba da gidadanci? Ku ci gaba da bibiyar labarin da zafafan comments.
Chapter 39 · 0% Book details