← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 52

Sashe 23

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuma haka ne dole a tsaya ka zaɓi mace ta gari, domin tarbiyyar zuriyar ka, musamman a wannan zamanin da muke ciki na tafiyar biri a yashi, amma kuma soja tun da har ka gaza samu a waje, muna da yaran mata kyawawa kuma sun sauke Alqur'ani da hadda. Ka dai san tarbiyar da suka tashi da shi. Duk yarinya da za ka samu a bayansu take. In har ba Zariya ka zo ka nema ba, sanin kanka ne yaranmu muna ƙoƙarin ba su ikon da hadda." Bance matan Zariya sun fi ilmi ba😁😁, amma kun san akwai ruwan shi boko da Muhammadiya lol😁😁

"Haka ne zan yi tunani."

"Shikenan Allah ya baka ta gari."Ya ƙarashe maganar daidai lokacin da ya fice. Har ga Allah yana son ya auri Mufida, amma ya san ba zai iya mishi dole ba.

Bayan ya gama gaisawa da mutanen gidan, sannan ya shiga cikin ɗakin Anty fuskarsa a ɗaure ganin yadda 'yan matan gidan suke rawar jikin gaishe shi.

Da fara a Antyn ta amsa sallamar sa tana kallonsa.

"Na ga ka yi sauri Captain? Lokacin da muka yi waya na tambaye ka don na ɗora girki, amma kari ga ka taso ko?"

"A'a lokacin wanka na fito." Ya bata amsa yana ƙoƙarin zama kan kujera.

Ɗakin ya bi da kallo cikin sha'awa. Tana da tsafta sosai, domin duk da sauran matan gidan ba a za kira su da ƙazamai ba, amma ita kaɗai yake iya cin abincinta ruwan ɗakinta.

"Na ga ka yi sauri sosai yanzu da ka shigo na sanya ganye." Ta karashe maganar tare da buɗe frij ta ɗauko ruwan faro da ta siya mishi, sai zoɓo mai sanyi da ta haɗa da kanta.

"Kar ki damu Anty, ni ma bana jin yunwa ki gama a tsanake."

"Ok, tom bari na je na duba, saboda ganin ka iso na mayar a gas."

Ba tare da ya amsa mata ba, ta fita ganin ya mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake kira. Ganin Lubaynah ce sai ya mayar bai amsa ba.

Hanifah da take tsaye kusa da kofar Anty. Tana ganin ta fito sai ta bita kicin.

"Kin cika zumuɗi Please ki bari ya ci abinci ya natsu."

"To Anty amma ganinsa da yadda yake haɗe rai na tsorata."

"Ya zaki yi? Hakannan za ki daure tun da kin ga ni kina so."

Haɗa hannayenta ta yi, ta murza cikin rashin dubara zuciyarta na bugu. Kallon kanta ta yi sai ta ga kamar bata yi kyau ba, ganin shiga da kyawun da ya yi.

Daga sashin Maman Mufida, tana zaune da Mufida da ta karaya, ganin ta gaishe shi ya ce mata lafiya kawai.

"Ki karɓa ki shafa a fuskarki Mufida ki daina jin tsoronsa, duk wannan ɗaure fuska da yake yi. Namiji ne fa yana fara sonki sai kin yi mamaki."

"Mama Ya Captain daban yake da sauran maza. Ko Hanifa da yake tare da Anty Amarya ba ki ga kallon bazan da ya yi mata ba."

"Kar ki karaya malamin na ya ce wannan maganin na farinjini ne, kuma mai kyau ne. In har Aliyu ya haɗa fuska dake zai kamu da sonki. A yarda ya yi mini bayani kece wacce ake son ya fara gani."

Ganin ta karɓi maganin mai kama da turare a sanyaye, sai ta ce,"Ki tashi mana ga Hanifa can da wancan makirar matar suna magana. Kika sani ko suma sun je gurin Malami ne? Ni wallahi na tsani yarinya can ƙarama da ita, amma sai kinibibi ko yadda ya shaƙu da ita bana tunanin haka ta bar shi. Tun damu da aka haife shi a gaban idanunmu, bai saki jiki damu ba sai ita zuwan jiya."

Mufida miƙewa ta yi, ta buɗe labulen windonsu, tana hangen Hanifah Anty Amarya da suke magana.

Ƙara gyara fuskarya ta yi, bayan ta shafa turaren maganin. "Yauwa kar ki karaya ma za ki je, sannan ki tabbatar da kun haɗa idanu."

"To," Ta ce tare da buɗe ɗakin ta fita cikin sanyin jiki.

Ganin haka ta kamo tare da riƙe mata hannu."Ki kwantar da hankalinki, ba ki da wani miji sai shi duk yadda zan yi na fita, sai na sai na yi kin auri Aliyu, don haka kije ko ya yi miki rashin mutunci kar ki damu kin ji? Dama duk abin da kake so sai ka wahala."

"To Mama." Ta ce tare da ficewa.

Anty ta fito daga kicin ɗin, ɗauke da kular dambu ta shiga cikin ɗakin. Yana zaune da waya a hannunsa fuskarsa ɗauke da murmushi. Chatting yake yi da Lubaynah tana gaya mishi ta yi missing ɗinsa. Hotonta ta tura masa, wanda ta ɗauka cikin wata rigar bacci, mai shigen kyau da ta siya boutique.

Lumshe idanunsa ya yi, lokaci guda suka yi ƙanana ganin kyawun da ta yi a cikin rigar. Kallon ta sosai yake yi yana jin feelings ɗinta na ta so masa.

Gwalo ta yi masa tare da sakin masa kiss da stikers. Murmushi yake yi sosai.

Sojana, ka yi sauri ka dawo Abuja in har rigar tayi mata kyau, saboda na siya sun fi kala goma. Ina fatan ina sanya maka ɗaya, sauran na yi amfanin da shi a matsayin matarka?

Tsaki ya yi tare da neman tsari da addu'ar da ta yi.

Yana ƙoƙarin bata amsa, Anty Amarya ta yi sallama ta shigo. Kashe wayar ya yi, sannan ya amsa yana kalonta.

"Abinci ya sauka azo aci dambu." Ta ce tare da ije mishi kula, a gaban shi tana kallonsa.

Ije wayar ya yi, sannan ya sauko ƙasa ya shaƙi ƙamshin dambun, tare da lumshe idanunsa."Kin san na yi missing dambun nan? Kwanaki sai da na ji kamar ki yi mini na turo a karɓa."

Dariya ta yi jin abin da ya ce,"A kawo dambu tun daga Zariya har Abuja?"

"Eh za a iya mana. Ina fatan matata macen da ta iya abincin gargajiya kamar ki, saboda Anty ina son abincin Hausawa don kawai Peter bai iya bane, amma kuma ina jin daɗin abincinsa."

"Auren dai shi ne za ka yi, sai ka samu wacce ta iya girkin Hausawa."

"Shi ya sa na ba ki zaɓi."

"Zaɓin ka yana da wuya, ba kowace mace za ka samu da abin da kake so ba."

"Za a iya samu zan ci gaba da nema. Ina da burin na auri salihar mace wacce ranar first night ɗinmu zai zama memorable, amma kin ga Anty duk 'yan matan nan yawancinsu second hand ne."

"Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara sosai a ƙauye waɗanda na sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba, sai ka ɗora su a hanya."

"God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa.

Hmmmmh Captain ka tsaya ruwan ido ba zan ce komai ba. Aci gaba da zafafan comments yanzu aka fara.
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 12

Tallah

Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast

Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano

"Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara sosai a ƙauye waɗanda ba sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba."

"God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa.

Ganin haka ta kalle shi cikin mamaki."Anty da na auri 'yar ƙauye gara na mutu ban yi aure ba. Matan ƙauye har wani abu suke dashi wanda namiji zai kalla? They are illiterate kuma ba su da wayewa."

"High expectations na ka yayi yawa kan matar da zaka aura. Ni kaina zan so na ga mai sa'ar da zaka ɗauko mana."

"In sha Allahu macen kirki mai natsuwa da kamun kai zan aura."
Chapter 23 · 0% Book details