← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 52

Sashe 18

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan numfashi ya yi sannan ya fesar. Ya zuƙi ta tabarsa ya ja fesar da hayaƙi. Lokaci guda ta yi nasarar sauko da fushinsa. Wani irin feelings na ta ya taso mishi domin ta saba mishi da kuma ya yi missing.

"Ok, ki zo gidana mu yi maganar na dawo."

"Gani nan zuwa babyna." Ta ce mishi tare da yi mishi kiss ta kashe wayar cikin murna.

Jikinta har rawa yake yi, tana haɗa kayan da za ta yi kwanaki da su. Ta rasa irin son da take mishi har yake wulaƙanta rayuwarta, amma ta kasa rabuwa da shi. Da ta kuma tuna Captain Aliyu, ƙarshe ne gurin sace zuciyar mace sai ta daina ganin laifinta.

Tana sanya kayan kwalliyarta a jaka Anty Hannah ta shigo. Tsayawa ta yi tana kallonta wacce ba ta san ta shigo ba.

"Lubaynah, ina za ki kike haɗa kaya?" Ta yi mata tambayar tana kallon ta.

Sosa kanta ta yi, cikin rashin gaskiya ganin yadda ta tsareta da idanu."Zan je bikin wata friend ɗina, kuma zan yi kwana biyu.."

"Ki fito ki gaya mini za ki je gurin lalataccen yaron nan Aliyu."

Ranta ne ya ɓace jin ta zage shi."Anty saboda me za ki zagi wanda na ke son aure?"

Dariya ta yi mata cikin takaici."Ok, a tunanin ki zai aure ki ko?"

"In sha Allahu ba ni da miji sai shi."

"Yaudarar kanki kike yi Lubaynah. Ki rubuta ko mata sun ƙare ba zai aure ki ba, domin kin riga kin sayar da darajar da kike da shi."

Ga mamakin ta sai kawai ta saka mata kuka."Fatan da kike mini kenan kar ya aure ni? Mai na yi miki kike mini wannan fatan? Domin gara ki yi mini addu'ar Allah ya ɗauki raina akan na rasa Captain Aliyu."

"Ashe za ki mutu kuwa, saboda na gaya miki ki rubuta ki ajiye ba zai aure ki ba."

"Na gode da fatan da kike yi mini, a matsayinki na 'yar'uwata wacce muka fito ciki ɗaya. In sha Allahu ba ni da miji sai shi. Sai kin zo gidana kin gammu muna soyayya."

"Ki dai yi tunani kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada."

Banza ta yi da ita ta yi, tare da ɗaukar trolley ɗinta da ƙaramar jakarta za ta fice.

Ganin haka ta sha gabanta tana faɗin,"Babu inda za ki kin san Allah zan kira Daddy na gaya masa abin da kike yi."

"Ki matsa mini na gaya miki bikin ƙawata zan je." Ta ce tare da ture ta

"Lubaynah, zan mare ki babu inda za ki j..." Maganar ta maƙale mata sakamakon ture ta da ta yi ta fice daga gidan.

Biyo ta ta yi tana kiran sunanta, amma da sauri ta shige cikin motarta ta ja aguje.

Bayan ya kashe kiran sai ya miƙe zuwa ɗakinsa. Sigarin ya kashe ya sanya a trash. Murmushi ya yi tare ƙara sawa gaban mirror yana shafa sajensa. Sosai yake jin ya yi kewarta. Ya san cewa Lubaynah mace ce, wacce ta amsa sunanta, amma sam ba zai iya zaɓawa yayansa ita a matsayin matarsa ba. Yana wannan tunanin wayarsa ta yi ƙara a tunkinsa ita ce ta zo, amma sai ya ga numbar Anty Amarya uwar ɗakinaa kuma ƙawarsa ce ta kira.

Ba tare da ya ɗauki wayar ba har sai da ta katse ya kira."Hello Antyna akwai news ne?" Ya yi mata tamabayar yana dariya tare da zama gefen gado.

"News daga gareka na ke sauraren ji, amma labarin da zan ba ka yadda ka rikita 'yan matan gidanmu da biki. Kowacce ta yi kwalliya ta yi burin ganinka don ta burge ka."

Tsaki ya saki yana mamakin rashin kunyarsu."Amma Anty sun raina ni. Marin da na yi wa bai sa sun daina haukarsu ba ko? Uban mai zan yi da su? Ko mata sun ƙare ba zan iya auren wata daga cikinsu ba."

"Bana son wulaƙanci soja. Yaran nawa kake gaya mini haka?"

Dariya ya yi yace,"Dole na gaya miki don ki sanar da su, su daina haukar da suke yi."

"To wa za ka aura kuma yaushe za ka yi? Captain na matsu na ga kana zuwan mini da matarka Zariya."

"Zan yi aure Anty ni kaina ina buƙatar haka, amma har yau na kasa samun macen. Kin san kalar macen da na ke so. Don Allah na ba ki cigiyar mai addini mahaddaciya kuma ustaxiya mai kyau."

Dariya sosai ta yi jin abin da ya ce."Ka san halin ka kuma kake son mace irin wannan?"

"Eh saboda yarana za zaɓar musu uwa ta gari, kuma irin wannan macen ne kawai zan aura hankalinsa ya kwanta."

"Saboda kana ɓata matar wani ko?"

Shafa kansa ya yi jin maganar da ta yi ba tare da shakka ba."Anty ke dai kin san komai. Ina fatan lokacin da zan yi aure Lubaynah ta fita daga cikin rayuwata. Zan daina duk abin da nake yi in sha Allahu, domin ba na fatan ranar da Daddy zai fahimci fuska biyu gare ni."

"Ya kamata ka daina, saboda in har kana son irin wannan matar dole ka zama na gari, kuma maganar auren lokaci yana ƙurewa."

"Na baki cigiya? Har yau na kasa samun wacce take da duk wannan halin."

"In ka ba ni zabi kana tunanin zan guji 'ya'yana na nema maka wata ne? Mene ne aibun su Hanifah sun da kyau kuma da natsuwa, in kuma ba ka so ya ga Mufida nan, da kuma sauran 'yan matan ka zaɓa a cikinsu. 'Yan mata huɗu da suke crushing ɗinka a family kuma duk cikinsu babu wacce ta yi maka? Kada haƙƙin su ya kama ka, musamman Hanifa yarinyar ta zurma da yawa."

"Bana son su, kuma bana son na auri mace wacce take sanya gyale. Matata ina aurenta Anty kullum cikin hijabi da niƙabi za ta rinka zama sam bana son wani ya kalle ta."

Mamakin abin da ya ce ta yi."Duk za ka iya canza Hanifah yarinyar tafi sonka kamar hauka. Kabar batun ita yarinyar mijina ne, ka san zan iya barin kowa na ɗauke ka, kuma kun dace da juna."

"Don Allah ba ita ba sam ba zan iya auren ta ba. Bana son mace da zan aura na canza ta. Matar da na ke son na aura wacce zan same ta a kan tarbiyyar da na ke so ne."

"Hmmmmh! Soja lamarinka sai kai."

"Ki dai bincika ba za a rasa ba."

"Ba zan yi maka wannan alƙawarin ba, saboda in har aka ji nice na samo maka mata zan yi baƙin jini,a yanzu ma haka ana ganin kamar yadda muka shaƙu wani abu na yi maka, ballanatana aji duk ka guji 'yan matan family na nemo maka wata? Don haka duba da kanka."

Shiru ya yi saboda ya kuma fahimci gaskiyarta.

"Ok, zan duba Anty ki taya ni da addu'a. Zan shigo Kaduna zan zo Zariya. In zan zo zan kira ki ki yi mini dambu."

"Shikenan ba matsala ɗan gidana." Ta ce tare da kashe wayar.

Wayar ya bi da kallo don kuma ya kashe yana murmushi. Sosai jininsu ya haɗu da ita. Tana da hankali sannan ta fahimce shi fiye da iyayensa. Babu abin da ya ƙara mata girma da mutunci. Ta san duk munanan halinsa, amma ko suɓutar kalami ba ta taɓa furtawa ba. Sai dai tayi ta mishi nasihar ya daina.

Yana ije wayar kiran Lubaynah ya shigo. Ba tare da ya ɗauka ba ya fita zuwa get. Da kanshi ya buɗe mata get ɗin ta shigo, saboda ya tafi kasuwa.

Tana shigowa ya ware hannunsa ta faɗa jikinsa. Bakinsu ya haɗe domin ya yi missing na ta kamar yadda ta yi na shi. Sakinta ya yi yana kallon ta ganin tana hawaye.

A ranar sai da ya sanya ta manta komai ta shiga lambun ƙaunarsa. Wannan dalilin ya sa take ji kamar za ta haukace duk lokacin da ya ce mata bai shirya aure ba . Tana ji a ranta saboda zarsa da ta ɗanɗana take kishinsa za ta iya kashe duk wacce ya aura.

A ranar sun sha soyayya tamkar wasu sababbin ma'aurata. Bayan sun yi bacci sun tashi. Wanka suka yi Captain Aliyu ya shirya suka fita zuwa gurin shaƙatawa. Sosai take murna ganin yadda ya sakin mata bakin aljihu ya yi mata siyyayya. Da suka dawo wanka suka yi sannan suka kwanta.

Kwana uku ta yi a gidansa suna shayar da junansu zumar ƙauna. Hankalinta kwance take shayar da shi madarar ƙauna. Burin ta kawai ta kawo hankalinsa ya amince zai aure ta, domin a shirye take da jure duk halayensa ta zauna da shi.

Damuwar da shi wani lokacin duk sonta da ƙaunarta da yake yi. Haka zai rufe idanunsa ya shukamata tashin mutunci, amma hakan nan za ta shanye sai ma ta ba shi haƙuri.

A ƙalla sai da suka yi sati, suna soyewa sannan ya shirya zuwa Kaduna. Kan dole ta tattara ta koma gida, ba don ta so ba saboda ta so ya barta a gidan tun da ba daɗewa zai yi ba amma sai ya ƙi.

Misalin ƙarfe sha ɗaya ya iso garin Kaduna. Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce, saboda ya yi kewarta sosai. Tun da incident ɗin nan ya faru bai kira ta ba, domin yafi jin haushinta fiye da komai. Sanin cewar zai sha ƙorafi sai ya siya mata kayan toshi.

Hon ya yi maigadi ya buɗe masa ya shiga. Parking ya yi sannan ya fito daga cikin motar. Yana sanye cikin ƙananan kaya riga da wando kalar kakin soja, sai hulan sojoji da ya sanya.

Kasancewar yau Hajiya ta tashi tana zazzaɓi sai ba ta fito ba, tana cikin ɗakinta tana bacci. Kaka Tani ita ma tana inda aka sauke su. Jimmalo ce kawai a falo tana kallo tamkar za ta shige cikin tibin. Sai surutu take yi ita kaɗai.

Da sallama ya shigo cikin falon fuskarsa a sake. Nufinsa ya yi ido biyu da rigimarmiyar kakarsa, amma sai ya ja ya tsaya cikin tsanannin ɓacin rai ganin wacce ya tsana fiye da komai a rayuwarsa.
Chapter 18 · 0% Book details