Sashe 14
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Soja?" Ta dafe ƙirjinta tana kallonta."Haba biri ya yi kama da mutum. Shi ya sa zuciyarsa sam babu imani. Wani naushi da ya yi wa jikalle sai da ta yi sati tana jinya. Kin san sojojin nan ba imani ne da su ba, haka kawai za su iya kashe mutum. Ni dama tun da na ga fuskarsa babu fara'a, na san cewa ba shi da imani."
Maganarta ta ƙarshe ya sanya Hajiya ta kalli Daddy, ganin babu kunya tana kwashe wa ɗansa albarka a gabansa."
"Hmmmmh!" Allah ya shirya." Ta furta tana son kauda zancen.
Dady kuwa kallon ta yake cikin tsananin mamakin ƙarfin halinta.
"Ka sanya direba ya shigo da tsarabar." Ta ce masa tana kallon da.
Fita ya yi daga cikin gidan ba tare da ya tanka ba.
"A Hajiya ba ku gajiya? Kayan da ku ka kawo mana bamu gama amfani da shi ba."
"Ai yiwa kai ne. Kune fa kawai kuka rage mini dangin mahafiyata, Allah ya yi mini arziki in ban taimaka muku ba, wa zan taimaka wa?"
"Haka ne Allah ya ƙara buɗi." Ta ce sannan suka ɓarke da hira ana tuna baya.
A guje ta shigo cikin gidan tana ihu murna. Da sauri Kaka Tani ta miƙe ta tare ta tana faɗin,"Jikalle, murnar mai kike yi haka? Ina tulun da kika je uban ruwa?"
Dariya ta ƙara saki ta ce,"Bala ya fasa mini tulu ni kuma na fasa masa kai. Wallahi sheme shi na yi yana can a rafi kwance, jini yana ta zuba a kansa." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin farinciki.
Hajiya ta miƙe da sauri tare da dafa ƙirjinta. Da ta shigo ta ɗauka mahaukaciyar ce, amma tuna Daddy ya gaya labarinta sai ta tsaya cikin mamaki tana kallonta. Ganin yadda take cikin dauɗa da ƙazanta ya sanya ta jinjina kanta.
"Yauwa 'yar albarka. Gara da kika ragije mishi kai, sai yan san ke ba sa'arsa bace."
"Wallahi na yi maganinsa domin a nan na sanya sandata na ragije shi, nan take ya zube babu numfashi. An gaya masa ni sa'ar ce? Ni ko mai gari maigari shakkarsa, domin duk wanda ya cuce ni ba zan yarda ba sai na rama. Ni fa Kaka Tani a yadda na ke jina zan iya zama soja."
"Za ki iya zama ƙarfi ne dake kamar 'yar doki. Allah ya yi miki albarka ba ki zama marainiya ba, tun da za ki iya rama ma kanki."
Hajiya ta zare idanu ta yi tana kallon ta."Tani mutum ta fasawa kai amma kike goyon bayanta?"
"Gara da ta yi maganinsa ya takura mata." Ta ba ta amsa tana kallonta.
Sai a lokacin Jimmalo ta ɗaga kai tana kallonta, don ba ta lura da ita ba. Tana ganin shigarta ta gane daga birni take. Cikin tsananin rashin kunya ta ce,"Ke kuma ina ruwanki dangin dagiro? Ni bana son shiga sharo ba shanu." A tsiwace ta ƙarashe maganar tana harararta.
Mamaki ya kamata jin abin da ta ce. So take ta toshe hancinta, saboda tsananin wari da ya cika hancinta. Kallonta ta yi yadda ƙafafunta suka farfashe, ga wani uwar faso da ya cika ƙafar har mutum zai iya ajiya. Babu abin da ya ƙara munanta fuskarta, sai haƙoranta da suka dafe da dadti. Sun yi jajur har wani gansa kuka suke yi. Amai ne ya taso mata, amma sai ta daure, tana jin yadda cikinta ke juyawa. Don kar ta yi ƙarya za ta iya cewa har zarni take yi. Wataƙila tana fitsarin kwance. Ko kuma tsabar dauɗa da ƙazanta ya sanya kayanta suke tashi. Kalar kayan da ta saka sam mutum ba zai iya ganewa ba, saboda sun yi duƙu-duƙu.
Bige bakinta da Kaka Tani ta yi tana faɗin,"Bana son rashin kunya 'yan'uwanmu ne daga birni."
Hannunta ta janye tare da kallonta ta balla mata harara,"Ni ki ƙyale ni saboda na tsani duk wanda zai zo daga birni, tun da ɗan su ya kira ni da ƙazamiya wawiya daƙiƙiya har yana kirana da dabba! Ita ma na san cewa za ta yi ba ni da tsafta."
Kaka Tani kunya ta kama ta ganin rashin kunyar da take yi, sai ta shiga yaƙen dole."Ki yi haƙuri kin san sha'anin yara, ta ɗauka kema mara mutunci ne kamarsa, ba ta san kina da mutunci ba."
Kasa cewa komai ta yi, tana kallonta jin abin da ta ce. "Sam Aliyu bai yi ƙarya ba, duk sunan da ya kira ta da shi ta cancanta."
"Amma Tani kina ji fa, kai ta fasa ma wani kuma kike goyon bayanta?"
"To sannu uwar zugai! So kike ta buge ni? Inda ya kashe ni an kawo mata gawata sai ki yi farinciki ko? Ki ji daɗi an kashe mata jikallenta ɗaya kamar rai da take da shi."
Kamata ta yi ta rungume tana rufe mata baki."Ki yi shiru ba za ki mutu ba,gara da kika rama kuma a shirye na ke na je kotun ƙoliya a kanki."
Mamaki ya ƙara kamata sai ta shiga jinjina kai. Daddy kuwa bai yi mamaki ba sam. A ransa ya ji daɗi da suka yi mata haka, don ta ga ainihin kalarsu. Ta daina tunanin jajibo su cikin rayuwarsu.
"Anya kina kyautawa rayuwarta, ita fa 'ya mace ce, wacce za ta tarbiyyantar da wasu. Irin wannan gurbata da kike ɗora ta kina ganin daidai ne? Haba Tine kar son zuciya ya sanya ki ɓata rayuwarta. Dubi jikinta yadda take cikin dauɗa babu tarbiya babu ilmi.
"Dama na san ita ma abin da za ta ce kenan. Na rantse ta ƙara ce mini ƙazama sai na...."
Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru cikin mamaki."Ina zuwa jikalle, na san ba zai wuce kiran mai gari ba."
"Shi ne tun da na ji muryar wannan mara mutunci, yana ji da wuya kamar mariƙin lema." Ta furta tana zabgawa Hajiya harara.
"Bari na fita yau ma kamar kullum muke da nasara. Wane dare ne jemage bai gani ba?" Ta furta tare da fita bayan ta yafa mayafinta.
Kallon wulaƙanci ta yi masa tare da ba ka masa harara."Kai dai ka zama mujiya ganinka ba alkhairi ba."
"Ko kuma kune ku ka zama ganinku ba alkahiri ba. Kun addabi ƙauyen nan, muna fatan ranar da Maigari zai sanya mu yi muku korar kare, donn har da jifa za mu haɗa muku."
"To in ya kasa korarmu kai ba sai ka kore mu ba, ina nan ina haƙonka watarana sai na ja maka asarar da har ka mutu ba za ka manta ba." Jimmalo tace tana aika masa da mugun kallo.
"Kafin ki aikata kin bar garin nan. Kwanan za mu ja miki Yasin ki mutu kowa ya...."
"Sai dai duk yaranka su mutu, amma ba jikalle ta ba." Kaka Tani ta ce tana kallonsa.
"Maigari yana kiranku kuma ya ce ƙafata ƙafarku."
"To sai ka kama mu ka kaimu."Ta faɗi hakan cikin tsananin rashin kunya ba tare da ta duba girman shi ba.
"Kar ku zo ku jira ya zo da kansa. Ni ɗan tsaƙo ne kuma na isar." Ya ce tare da wucewa.
Sororo suka yi suna kallonsu."Ɗauko mayafinki muje jikalle." Kaka Tani ta ce tana gyara nata mayafin.
"Mu je kawai na ci ɗanmara ba sai na yafa ba, amma wallahi yau duk wanda ya yi mini ba daidai ba sai na shuka masa rashin mutunci."
"Mu je wa ya isa ya taɓa ki." Ta ce tare da kama hannunta.
Har sun yi nisa suna bambami sai ta tuna da Hajiya. Dawowa ta yi inda take."Don Allah ki yi haƙuri yanzu za mu dawo."
"Mu je tare saboda na ga ba haƙuri za ku bayar ba."
"Saboda me zan ba da haƙuri? Yaron nan shi yake takalarta. Ana soyayya dole?"
Shiru ta yi suka kama hanya ba ta tanka ba, don ba ta da abin da za ta ce. Ganin haka Daddy ya bi bayansu cikin takaici.
Da suka isa gidan maigari, shiga suka yi ba tare da fargaba ba. Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana, amma sam ba su razana ba. A maimakon su ba da haƙuri yana faɗa suna mayar masa, musamman Jimmalo da harshenta ya fi na kowa. Da ma ga ta da murya zaƙwai. Su Hajiya da suka zo sai suka ɓuge da ba da haƙuri. Da ƙyar aka kashe maganar, bayan sun ɗauki alkawarin kula da lafiyar Bala.
Da suka kai shi kyamis ɗin Audi aka yi treatment ɗinsa. Sai da suka ba da kuɗin da za a kula da shi. Ransu ya ƙara ɓaci ganin ba babu nadama a fuskarsu, sai ƙorafin kuɗin da suka ba da suke yi.
"Tani tarbiyar da kika ɗora kenan? In kika mutu kika barta sawe irin rayuwa kike so ta yi?"
"Kuka kawai suka ji ta fashe da shi."Wallahi Kaka ba za ta mutu ba, sai dai ki mutu ki barta."
"Dole zan mutu amma ba yanzu ba jikalle. Share hawayenki ina nan tare da ke." Ta ce tana jijjiga ta sai ɓare baki take yi.
Gani lamarin yafi ƙarfin ta sai ta zauna ta yi shiru."Ki yi haƙuri yarinya ya ce, kuma ita kaɗai ta rage mini." Ta ce tare da zama a gurin ta.
"Ni zan koma." Ta faɗa cikin ɗaure fuska.
Jin abin da ta ce ya tabbatar mata da ta yi fushi."Ki yi haƙuri don Allah na ɗauka kwana za ki yi?"
"Ki barta ta tafi Kaka umma ta gaida ashsha." Jimmalo ta ce tana wasa da ƙasa da ta zuba ruwa ta kwaɓa.
"Ba a yi haka ba domin baƙonka Annabinka. Ta so mu ba ta haƙuri."
Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta shige cikin ɗaki tana wakar sharmandu.
Hajiya sai ta kasa cewa komai. Tunani ta fara dole ta yi haƙuri in har tana don ta canza su, amma to ta yaya za ta iya? Tambayar haka ya faɗo cikin ranta. Za ta gwada domin sai an gwada akan san na ƙwarai.
Zama ta yi sannan ta kalle ta."Ba kwana za mu yi ba, amma sai yamma za mu tafi, kuma ina son mu je damu sai kuga inda na ke zama tun da na zo na ga gurinka."
Fara'ar Kaka Tani ya ƙaru jin abin da ta ce."Wai kina nufin mu biku birni?" Ta yi mata tambayar cikin murna.