← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 52

Sashe 25

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya kaimu ya baka ta gari. Ina jin daɗi sosai yadda ka kama kanka bai ruwanka da bin mata ko shaye-shayen da wasu sojojin suke yi. Kowa a family yabon ka yake yi. Yana gaya mini in har za auri yarsa ya ba ka, duk wannan ya faru ne saboda riƙe tarbiyyar da na ɗora ka akai. Ko bayan rayuwata Aliyu karka canza. Ban taɓa zina da yar wani ba, kuma ina roƙon har na mutu kar zuriyana su yi ko ayi da su."

Jikinsa e ya kama rawa lokaci guda hankalinsa ya tashi."In sha Allahu Dady addu'ar da kake mini ina ganin amfaninta, domin ko da abokan aikina masu irin wannan halin sun ja ni, sai ka ga Allah ya tsare ni." Ya ƙarashe maganar cikin rawar murya zufa na keto masa.

"Ƙarfin addu'a ce ka ci gaba da ƙoƙarin kare kanka. Zina musifa ce da take shafan har waɗanda ba su aikata ba. Zina alfasha ne daga cikin manyan zunubin da Allah ba ya so, amma abin takaici da jimami har ma da zaman makoki al'ummar zamanin mu mun ɗauki zina ba a bakin komai ba. Namiji mai aure yana zina, matar aure tana zina samari da 'yan mata duk suna zina har da zawarawa, shi ya sa musifa ta yi mana yawa. Abinci yana gagarar wasu. Mutane an mayar da kashe su ba komai ba, dabba tafi mutum, domin sai ta yi yawo ba a taɓa lafiyarta ba, amma mutum har gida ake zuwa ake kashe shi. Wannan duk yana faruwa da irin manyan zunuban da muke aikawa ne."

Aliyu shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Ganin haka Daddy ya ɗora da cewa,"Ka ga ko karya alƙawari da mutum ya zama fuska biyu? Shi ma yana matuƙar sanya Allah yayi fishi sannan ni kaina Aliyu in har mutum zai zama fuska biyu a gareni zan iya yafe shi har cikin rayuwata. Na tsani haka domin babu kyau."

"Eh, Daddy Allah ya tsare mu da aikata zina." Ya yi ƙoƙarin sauya muryarsa ya furta hakan.

"Amin shi ya sa na ke alfahari da kai. Har gobe ina bugan ƙirjina a cikin abokai na yabe ka, saboda kyawawan halinka. Dangi damu kanmu muna alfahari da kai. Ubangiji ya yi maka albarka."

"Amin Daddy." Ya ce hawaye na zuba a ƙuncinsa, domin ya san cewa duk lokacin da ya sani akwai matsala. Ya zama dole a yau ya rabu da Lubaynah ya daina shan sigari.

"Daddy bari na kwashi kayana na kai mota zan shigo." Ya ce masa don ya keɓe.

"Ok, ba matsala sai ka shigo bari na gaya wa Nufaisah ta haɗa maka abinci." Ya ƙarashe maganar tare da shiga ciki.

Sashinsa ya shiga buga kansa kasa da bango. Sosai ya ke jin ya tsanar kansa, saboda yaudarar mahaifinsa da ya yi. Ganin yadda yake alfahari da shi, sai ya ji hankalinsa ya tashi. Da sauri ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin chatting da suka yi da Lubaynah na batsa da hotunanta marasa ɗa'a ya goge.

Goge numbarta ya yi, yana fatan ya zama shi ne na ƙarshe da zai yaudari mahaifinsa. Saboda tashin hankalin da ya shiga jin abin da Dady ya rinƙa cewa, domin ya ɗauka ko asirinsa ne ya tonu. Wanka ya shiga sannan ya canza kaya, ya tafi zuwa sashin iyayensa.

Mommy na zaune a falo da remote ɗin tibi a hannunta ya yi sallama ya shigo. "Yauwa ma yanzu na ke son na tura Umma, ta je ta yi kiranka mu yi dinner."

"Wanka na yi shi ya sa na daɗe." Ya furta tare da wuce dinning yana gaishe ta.

"Lafiya lau ya mutanen Zariya?"

"Duk suna lafiya Anty Amarya ta ba ni tsaƙo na kawo miki, na san bai wuce abin da ta saba. Su daddawa da kuka da barkono."

"Ba ta gajiya duk wani ya je sai ta yi hidima."

Murmushi ya yi sannnan ta zauna yana faɗin,"Anty Amarya tana da kirki sosai."

Bismillah suka yi sannan suka fara cin abincin. Kwana biyu Captain Aliyu ya yi ya koma aikinsa. A ranar da ya koma washegari suka yi tafiya, don haka Lubaynah ba ta samu damar ganinsa ba.

Jimmalo.
Cikin tsananin takaici suke tafiya suna tsinewa Hajiya da Captain Aliyu, domin inda ace zagi na fitowa a jikin mutum tabbas da ya yi musu tabo. Zagi kam sun zagu. Suna tafe suna zaginsu har suka isa Damagaran.

A lokacin da suka isa sai kunya ta kama jimmmalo, da ta fara haɗuwa da mutane ana kallonta ana tambayarta, dalilin da ya sanya ta dawo da wuri, sannan ta gama cika baki cewar za su dawo da abubuwa, amma sai ga shi duk dawo daga su sai kayan jikinsu kamar wasu korarru.

Mutanen ƙauye da suke haɗuwa, don su suka ci gaba da kallonsu suna gulma, cewar sun yi halin su an kore su. Kafin su isa gida labari ya cika ko'ina Jimmalo ta dawo birni babu abin arziki.

Da suka isa ƙofar gidansu Kaka Tani ta buɗe suka shiga. Zama suka yi sannan ta ibo ruwa ta sha."Allah ya tsinewa mutanen birni gabakiɗaya. Kaka Tani ni da birni har abada, saboda ba su da mutunci. Ki ga irin tozarcin da suka yi mana. Na gama cika gari ina gaya musu zan dawo da abin arziki, amma ko tsarabar biskit ban yi ba."

"Ai Hajiya ta ba ni mamaki sosai tun da ta fifita jikanta a kaina. Na rantse ko mutuwa ta yi ba zan je gaisuwa ba, kuma tsakanina da ita na yanke zumunci, sannan ni ma ko mutuwa a yi kar ta zo."

"Allah ya kawo su ma suga rashin mutuncin da zan yi musu, domin duk ranar da suka kuskura suka zo gurinmu na rantse da duwatsu zan raka su."

"Ai ba za su yi kuskuren zuwa ba." Cewar Kaka Tani tana ƙoƙarin miƙewa ta shiga cikin ɗakinta.

Jimmalo na tsaye a waje tana jijjiga, ji take yi kamar ta koma ta shaƙi wuyan Captain Aliyu ta kashe shi. Wani irin tsanarsa take ji yana zagaye ilahirin jikinta.

Tana zaune tsahare ta yi sallama ta shigo tana washe baki. Mugun kallo ta watsa mata tare da tamke fuskarta.

"Jimmalo ashe kun dawo? Lauratu ta gaya mini cewar ta ganku a da zaku dawo?"

"Ko ba ta gammu ba na san kece za ki fara zuwa, saboda kaf garin nan babu munafuka kamar ki."

"Laa! Jimmalo ba haka bane cewa nayi bari na maza na zo na karɓi alkawarin taliyar birni da kika ce za ki zo mini da shi?"

"To jikar mayu ban zo da shi ba, sai na ga uban da zai yi mini dole na baki."

"Ko kin zo da shi ba lailai ki ba ni ba, dama na san alƙawarin ki ba kya cikawa, musamman kan abinci ɓakin rowa ne dake."

"Ke Tsahare fita a gidan nan kafin yanzu jininki ya yi tsami."

"Dama ko baki ce na fita ai zan fita, alƙawari dai kaya ne duk wanda bai cika ba, Allah xai hukunta shi, kuma duk wanda ya ci shi kaɗai shi kaɗai zai mutu."

"Da na gaya miki da gyatumarki zan mutu?" Ta ce tare da fara tafiya da sauri za ta shaƙota, ganin haka ta ruga da gudu ta fice daga gidan.

Ba ta zame ko'ina ba, sai dandali ta sanar musu da cewar Jimmalo ta dawo daga birni, babu abin arzikin da ta rinƙa musu ƙaryar za ta dawo da shi. Kafin dare ya yi an gma yayata maganar wasu suna faɗin mugun halinsa da rashin mutunci suka yi aka ƙoro su. Maganar har da gishiri da magi, aka ƙara mata cewar koro su aka yi har da duka.

A lokacin da maganar ta dawo kunnen Jimmalo ranta ya ɓaci. Ɗanmara ta sha ta je har ƙofar gida ta samu Tsahare ta yi mata duka.Mahaifiyarta ta biyo ta, amma babu wani matakin da aka ɗauka.

Bayan dawowarsu suka ci gaba da rayuwarsu. Sun gwammace irin rayuwar da suka saba. Jimmalo tun safe take zuwa talla, da ta siyar za ta tafi sarin gwaiba ko ayaba, sai ta siyar sannan take dawowa. Bayan magariba ta ɗauki talla ta wuce dandali. A haka suke samun abincin da za su ci.

Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗin da ta Whatsapp ba ya reply. A cikin lokacin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta mutu.

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGA 13
Chapter 25 · 0% Book details