← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 52

Sashe 13

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kan uba sai ka ce za ki dafa ganda?"

"Ya ake yi kin san ba girki na ke yi ba?" Ta yi mata tambayar tana zare idanu.

Tukunyar ta sauke ta rage ruwan sosai, don kusan juyewa ta yi sannan ta mayar da tukunyar. Suna tsaye ruwan ya tausa ta zuba.

"Laa, Salame ashe wallahi da gaske ne! Kin ga Kaka Tani, har ta dahu." Ta ce tana kallonta cikin tsananin farinciki.

"Ikon Allah ta dahu sai ƙamshi take." Ta ba ta amsa daidai lokacin da ta ƙaraso.

Zaman ci suka yi duk wahalar da ta sha gurin girkin, kaɗan ta sam mata ta cinye tana lashe hannu. Bayan sun gama ci. Kaka Tani ta rarrashe ta don ta fasa ƙara girkawa da za ta yi."Kin ji jikalle, ki bari sai kin dawo sarin ayabar, kin ga rana ta ja yi."

"Ai da kin bar ni na ƙara wallahi daɗi ya ke da shi sosai."

"Je ki dawo kin ji?.Ga kuɗin ki kula kar ki yi faɗa da kowa."

"To,"Ta amsa tare da janyo ɗankwali tasha ɗammara suka fita.

A hanya suna tafe suna hira har suka isa. Bayan sun sari ayabar suka wace tasha, anan suke siyarwa. Sai da ta sayar duka, sannan ta shigo musu rogo da gyaɗa da za su ci da daddare.

A gajiye ta koma gida, babu tunanin yin sallolin da ba ta yi ba ta kwanta. Bacci ta yi kafin magariba ta miƙe ta shiga bayi. Da ta fito zama ta yi kan turmi tana irga cinikinn da ta yi."Ga shi Kaka Tani, wannan zan sayi ɗantamatsitsi da hanjin ligidi, a dandali."

"Allah ya yi miki albarka, amma ya kamata na saro miki gyaɗa ki kai dandalin?"

"Eh ki saro da yawa."

"Yauwa jikalle." Ta ce tare da ɗaukar mayafinta ta fita.

Ko wace mace ta yi wanka, tasha kwalliya cikin riga da zani daban ɗankwali daban. Jimmalo ce kawai ta buga daka tsami ta zo. Dama duk ranar da za ta je dandali take ƙuru ta ke yin dakatsamin. Duk wanda ya yi kuskuren zama kusa da ita sai ya rinƙa kauda hanci. Tana zaune da tiren gyaɗa suna hira da Ladiyo. Wani saurayi mai suna Bala ya ƙara so gurinta. Wani irin tsuka ta ja tare da kauda fuskarta tana harararsa.

Ganin haka ya tsaya sororo a kusa da ita."Jimm..."

Kafin ya gama kiran sunan ta taso masa kamar za ta cinye shi."Na gaya maka Bala ka fita idanunka, saboda wallahi ko maza sun ƙare ba za iya auren ka. A yadda kake siririn nan kamar tsinke, in ka ɓata mini rai tsaf zan sanya hannu na karya ka."

Kunya ce ta kama shi, ganin yadda take maganar cikin ɗaga murya. Samari da 'yan mata na dandalin suka tsaya suna kallonsu.

"Ke!" Ya daka mata tsara yan huci tamkar mesa, sannan ya ci gaba da da cewa,"Don kin samu na ce ina so ki?In ban da rashin zuciya irin tawa, uban me zan yi da mace ƙazamiya irin ki, da ko wanke baki ba kyau yi. Dubi kayan jikin ki, kamar wacce take suyan kifi. Kin taɓa jin warin da kike yi kuwa?"

"Kutumar ƙaniya!" Ta ce tare da ƙara sakin wani ashahariyar, sannan ta miƙe ta cakumi wuyarsa."Ni za ka yi wa rashin mutunci? Ka san ina wurin uban wa ya ce ka ce kana sona?" Ta furta tare da shaƙe masa wuya.

Duk iya ƙoƙarin su don su raba su, amma ta ƙwaƙume shi sai cizo da yakushi take kai mishi. Da ƙyar suka samu suka raba su. Kallonsa ta yi tana huci."Dubi yadda na yi maka jina-jina a haka kake so na so ka?"

Harara ya gallah mata ya wuce cikin tsananin jin kunyar yadda ta disga shi. Ihu da tafi suka ɗauka suna mata kirarin,"Jimmalo jikar Tani kin gagari kowa har da maigari."

Kanta ne ya fadi ta ji kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba, tare da murmushi a fuskarta. Saboda faɗan da suka yi, sai dandalin bai yi wani armashi ba. Ba su kai yadda suke daɗewa ba, suka tashi kowa ya nufi gida.

Hajiya tana zaune da littafin Hisnul Muslim a hannunta tana dubawa. Daddy ne ya yi sallama ya shigo.

Zare gilashin idanunta ta yi wanda yake medical. Kallonsa ta yi cikin tsananin ƙauna. "Barka da zuwa ka iso?"

"Eh, tun jiyada kika gaya mini kina son ganina, na so in zo, ban tashi kasuwa da wuri bane." Ya faɗa bayan ya zauna kusa da ita yana gaishe ta.

Amsawa ta yi idanunta na kansa."Kan maganar da muka yi da kai, na zuwa ƙauyen na ga inda 'yar'uwata take."

Gabansa ya faɗi jin abin da ta ce. Sam ba ya son zuwa ƙauyen nan, ba wai don abin da ta yi musu ba, hatta hanyar ƙauyen fargabar bi yake yi, musamman da Aliyu ya ce masa akwai aljanu.". Gyaran murya ya yi, don ya kawo uzurina da zai hana zuwansa.

"Hajiya na ɗauka mun gama maganar cewar tun da..."

"Ka ga ban son dogon bayani in har ba za ka je ba, sai ka haɗa ni da direba mu je."

Kallonta ya yi da sauri jin abinda ta ce,'Haba Hajiya, ace kina da ɗan da ya iya mota sai na bari direba ya kai ki?"

"To zan yi maka dole ne? In ka ce ba za ka je ba, ai dole na je tun da dangina ne."

"Shikenan, ki sanya rana yaushe za mu je?"

Jin abin da ya ce fara'arta ta ƙaru."Ai ni ko gobe ka ce a shirye na ke. Ka faɗa mini ranar da za ka je."

"Ki bari sai ranar sati Hajiya."

"Allah ya kaimu." Ta ce tare da cigaba da jan carbinta.Miƙewa ya yi jikinsa a mace ya ce,"Hajiya, zan wuce kasuwa."

"To shikenan, Allah ya yi maka albarka, sannan karka manta goro na ya ƙare."

"Hajiya ya kamata ki rage cin goro, sam ba shi da amfani."

"Allah ya kyauta, in ka ga na daina cin goro sai dai in bani da rai, ai goro ya zama tamkar abinci."

"Allah ya kyauta." Ya ce sannan ya doshi ƙofar fita.

"Amin," Ta ba shi amsa tana kallon sa.

Hajiya shirye shiryen tafiya ta fara ta haɗa musu kaya sosai. A ranar da ta kasance ranar da za su tafi, tun safe suka ɗauki hanya. Kallon hanyar take tana mamakin nisan gurin, musamman da ta ga sun shiga cikin turɓaya suke yi.

Da suka isa da ƙarfi ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta fito da gyalenta a hannun."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki.

Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida tana kasa ayabar da Jummmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

Follow the ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P

PAGE 7

Da suka isa da ƙyar ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta fito da gyalenta a hannunta."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki.

Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida, tana kasa ayabar da Jimmmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi.

Sallamar da aka yi ya katse mata hanzarin ta. Ba ta amsa ba, sai ta yafa gyalenta ta nufi ƙofar. Turus! Ta tsaya tana kallon Daddy, tana masa kallon kamar ta gane shi. Mayar da idanunta ta yi kan Hajiya. Ganinta ya sanya ta saki fara'a. "Ikon Allah Atine! Ashe za mu ƙara haɗuwa?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki tana kallonta.

Hajiya rungumeta ta yi tare da ƙanƙame ta."Ga shi Allah ya sake haɗamu Tani." Sosai suka rungume junansu kamar ba za su rabu ba. Da ƙyar suka saki juna sannan suka shiga cikin gidan.

Kallon gidan take yi wani iri mai ɗauke da ciki ɗaya guda biyu, sai kuma ɗan tsakar gida da kicin. Ruwa ta ibo mata a randa mai tsanannin sanyi ta kawo mata. "Ga shi kisha Tine, wallahi ban yi tunanin da gaske ɗanki bane, musamman da yaronsa ya zo ya yi mana ɗiban albarka."

"Ki yi haƙuri haka ya gaya mini, da san tare zai zo da shi zan hana shi, saboda shegen zuciya ce da shi kamar kuturu, ga shi saboda rashin tunani suka bar shi ya zama soja."
Chapter 13 · 0% Book details