Sashe 21
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayarsa ta yi ƙara alamun ana kira. Ganin Abdullahi Bakanike ne, sai ya miƙe ya fito ba tare daya ɗauki wayar ba, saboda ganin an buɗe masa get ya shigo da motar.
Karɓar makullin ya yi, bayan ya yi masa godiya ya shiga cikin motar.
Bayan fitarsa Hajiya sai ta rasa yadda za ta yi da su. Ta kalli Kaka Tani da take ta kuka tana face majina, sannan ta jiya kallonta ga Jimmalo da take aika masa da zagi buhu-bubu. Kanta ya kulle har ta yi dana sanin gayyato su gidanta.
"Wallahi Hajiya kin nuna mini jika ya fi ɗan'uwa. A gaban idanunki ya duki jikata, amma da yake ita ba mutum ya haife ta ba, sai kika kasa ɗaukar mataki."
"Haba Tani, yaron nan fa magidanci ne ba ƙaramin yaro da zan kama shi da duka ba. Ke baki ga rashin kunyar da ta yi mishi ba? Bayan zagin da ta yi masa har da yi masa faci."
"To don ta aikata haka ai ba sata ta yi masa ba, da zai sanya ƙafafunsa yana haurinta tamkar ta yi mishi sata."
"Da kin ƙyale ni na sakin masa gwafar nan. Aradu sai ya yi fitsari a wando.Mugu azzalumi mai idanun doki." Ta ce cikin zallar rashin kunya.
"Tani, zan gaya miki gaskiya ko da ba kyau so. Tarbiyyar da kike ba wa yarinyar nan cutarta kike yi. Wallahi in har baki gyara ba, har kika bari Allah ya ɗauki kwananki ba ki canza mata rayuwarta ba. Kin cuce ta kuma nan gaba sai ta yi dana sani sosai."
Sautin kuka Kaka Tani ta ƙara, saboda gani take kamar wulanƙanci Hajiya take mata don tana da kuɗi.
"Na gode da rashin mutuncin da kika yi mini. Yau zamu koma ƙauye ba zan ƙara zama a cikin gidanki ba, domin tozarcin da kika yi mini ya isa. Kin kira jikata mara kunya, bayan jiƙanki ne mugu azzalumi mara kunya. A gabanki ya dukar mini jika kuma ya gaya mini maganganu mara sa daɗi, amma ba ki ce komai ba tun da shi yana da kuɗi. Ni kuwa ba mu da komai dole ki wulaƙanta ni."
"Ba wulankanci bane, gaskiya na ke ƙoƙarin gaya miki wallahi tarbiyyar da kika ba a ba mai kyau bane, kuma kin cutar da rayuwarta. Za ta yi kuka ko da babu ke a rayuwa."
"A'a Hajiya, zan yi miki rashin mutunci wallahi in har kika ƙara faɗin Kaka Tani tana cutata. Kin san wahalar da ta yi ta ciyar da ni har na girma? Kaka Tani har aikin ƙwadigo ta yi don na samu abinci, amma saboda kin shigo cikin rayuwarmu jiya nan, don kin kawo mana abinci sai ki kalle ta gaya mata haka?"
"Jimmalo, gaskiya na ke gaya miki kuma dama ɗaci ne da ita. Idan akwai abin da yafi cuta tayi miki. Don da take miki da maraicin ki ya sanya ta yi miki tarbiyya mara kyawu. Rayuwa ba haka take tafiya cikin haukar da ƙazanta da rashin kunya ba. Dole ki fuskanci rayuwa ki yi ilmi in har kina son rayuwarki tayi kyau. Na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarki na ba ki ilmi in har za ki zauna da ni. Zan canza miki rayuwarki Jimmalo. Zan sanya ki a makarantar kuɗi, na kuma ɗauki ɗawainiyar rayuwarki har sai kin zamo wata aba"
"Allah Ubangiji ya tsare ni da wahalar da kaina gurin yin karatu. A yadda nake rayuwa haka ya yi mini, kuma babu wanda zai yi mini dole. Mai zan yi da karatun arna? Na addinin ma tun da na iya na sallah Fatiha da Kulhuwallahu na daina wahalar da kaina."
"Kwantar da hankalinki Jikalle, babu uban da ya isa ya yi miki dole in dai ina raye. Ma za je ki haɗa kayanki mu bar mata gidan nan, domin ba zan ƙara kwana ba."
"To Kaka Tani." Ta furta da sauri tare da shigewa cikin gidan.
Hankalin Hajiya ya tashi ganin yadda suka ɗauki zafi, tamkar wacce ta yi musu zagi. Hannu ta kai za ta dafa Kaka Tani, amma sai ta fisge cikin muryar kuka ta ce,"Karki taɓa ni na tsane ki. Ki manta kin san Ni a rayuwa, domin daga yau na goge duk zumuncin da yake tsakaninmu. Duk wanda zai aibata jikata bazan ƙaunace shi ba."
Da sauri ta janye hannunta ganin yadda take kukan. Jikinta ne ya yi sanyi sosai har ta kasa cewa komai. Lokaci guda yarda da maganar Daddy cewar ba za ta iya canza su ba, domin sun wuce tunaninta.
Abinci da turamen zani ta haɗa musu sannan ta kawo musu falo.
"Ku yi haƙuri ban so haka rabuwarmu ta kasance ba. Na so ace na karɓi Jimmalo daga gurinki na ba ta tarbiyya da ilmi, domin rayuwarta ta canza ta samu miji na gari, amma ga yadda abin ya kasance. Aliyu ya yi kuskure kuma zan yi masa magana."
"Kar ma ki yi masa ki ƙyale shi, ba sai ya gammu zai shiga gonarmu ba. Ya je ya yi abin da ya ga dama. Duniya ce ta ishi bagaruwa jima. Watarana in halinsa duka sai ya duki wacce da za ta sanya a kulle shi."
"Eh Allah yasa kuma ɗan makullin ya ɓata ya mutu acan." Jimmmalo ta furta har cikin zuciyarsa tana fatan hakan ya kasance, domin ta tsane shi sosai.
Hajiya dai kasa magana ta yi, ganin sam ba ta ganin laifin jikarta. Ƙosawa ta yi su tafi domin kanta har zafi yake mata.
"Zo muje Jimmalo, ba za mu ɗauki komai daga gareta ba. Hatta kayan sawa ki bar mata ai ba a tsirara ta gammu ba, sannan na raba zumuncin da yake tsakaninmu kar ki ƙara zuwa Kauyenmu, domin in har kika zo ko wani na ki, sai na sanya an yi muku rashin mutunci."
Kayyasa ni kaina ban taɓa ganin rikitattun mutane irin waɗannan ba😁😁😁 to ga shi dai sun yi zuciya za su koma ƙauye. Anya Jimmalo kina da rabon kilewa? Ku ci gaba da bibiyar littafin da kuma yin comments don ji an yadda za ta kaya. Wai ya ne da comments 🙄🙄🙄 ina ga tafiyarta hutu zan yi tun da bakwa comments
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 11
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano
Ganin sun kama hanya za su fita sai ta fara roƙon, su da su bari direba ya mayar da su, sannan su tafi da kaya da ta basu, amma suka ƙi.
"Na dai gaya miki bana fatan ƙara ganinki da zuriyarki, don haɗuwarmu ta biyu sam ba zai yi kyau ba."
"Ki barsu Allah ya sanya su yi gigin zuwa, sai na raka su da gwafata ina harbinsu." Ta ce tare da saita gwafar tana dariya.
Ganin haka sai ta tsaya cikin mamaki tana kallon su har suka fita.
Zama ta yi jaɓar kan kujerar tana mamakin halinsu. Tun da take ba ta taɓa ganin rikatttun mutane irin su ba. Hawaye suke zuba a ƙuncinta na tausayin Jimmalo, domin in har ta ci gaba da rayuwa a haka, nan gaba sai ta yi kukan da za ta ci gaba har ƙarshen rayuwarta.
Mai aikinta ta kira ta ce,"Don Allah ki fito da kayan ɗakinsu a wanke dakin sannan a sanya turare. Wallahi ko ina na gidan nan ji na ke yana warin jikinta."
"Kai Hajiya, ai wannan yarinyar ƙazamiya ce wallahi. Tun da ta zo gidan nan ba ta yi wanka ba, sannan ba ta sallah ballantana ta samu rahamar alwalan da take yi. Shi yasa gata nan ta yi baƙi ta fita hayyacinta. Inda za a sanya abu a kankari jikinta Allah sai kin ga dadti na zuba, sannan inta matso ni kamar zan yi amai. Ni wannan kan nata bana tunanin ta taɓa sanya masa ruwa?"
"Bana tunanin haka, saboda yarinyar nan ta iya ƙazanta ga rashin tarbiyya."
"Gaskiya Kakarta ta cuce ta da sunan so."