Sashe 34
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jimmmalo kuwa, ganin wani kallo na ƙaskanci da suke mata sai ta watsa musu nata. Ta so ace za ta iya zama ta gurje bakin duk wacce ta yi mata rashin kunya, domin ko yayansu mai kama da zabiya ba ta jin shakkarsa ballantana su ƙananun ƙwari, amma saboda tana son komawa, sai ta zauna a gefen gadon tana kallon tsaruwar ɗakin.
"Jimmalo bari na sanya a kawo miki abinci, amma in kina son ki tafi da wuri sai kin yi wanka da sallah."
"Ni fa ba zan yi ba kaina ciwo yake mini." Ta ce tare da kwanciya tana shaƙar ƙamshin dauɗar jikinta.
Wani irin kallo suka watsa mata, har da auta da ya shigo lokacin. Sai kauda fuska suke yi, saboda tun da ta shigo ɗakin ya canza.
Fita Mommy ta yi, tana tunanin yadda za ta shawo kanta ta zauna.
Lafiyayyen tuwon shinkafa da miyan agushi, sai farfesun nama Baba ta kawo mata. Duk daɗin da abincin ya yi bai ɗauki hankalin Jimmalo ba, domin ta ƙosa gobe ta yi ta koma Damagaran.
Sosai suke kallonta, ganin duk halin da take ciki sai data share malmala biyar. Mugun kallo ta watsa musu ganin yadda suke mata kallon raini. Miƙa ta yi sai ta miƙe kan gadon ba tare data wanke hannunta ba, ballantana su yi tunanin ta ɗauke kwanon.
"Anty Nufaisah, She is dirty girl. Ta ci abinci ba ta ɗauke kwanon ba, kuma ba ta wanke hannun ba. All her body is looking dirty."
"Kai xagina kake yi? Don wallahi ina yi maka ƙubula ɗaya sai ka sume!" Ta daka matsa tsawar tana faɗin haka.
Tsoro ta ba shi da sauri ya matsa gurin Umma. "Cewa na yi ki ɗauke kwanon da kika ci abinci sannan ki yi brush ki wanke baki, saboda Malaminmu ya ce in har ba ka yi brush ba, ka kwanta abincin zai rufe ya sanya maka ciwon haƙori, sannan kwanuka da kika ci abinci ki ɗauki saboda ƙananan ƙwari za su iya zuwa."
"Rufe mini baki bana wanke baki, amma har yau ban taɓa ciwon haƙori ba, ka kalli haƙorana ka san ba ni da ciwon haƙori." Ta ƙarashe maganar tare da wage musu baki haƙoranta suka bayyana.
Da sauri suka kauda fuskarsu, saboda ganin yadda haƙoran suka yi babu kyan gani, domin za su iya rantsuwar da abincin da ya maƙale tun na shekaru.
Komawa ta yi ta kwanta tana harararsa. Ta so ace za ta iya zama ta gyara musu zama, saboda tsaf sai ta yi maganin tsaftansu.
Jin abin da tace su suka daina mamakinta. Satan kallon ta suke yi. Wani irin gyatsa ta saki mai ƙarfi har sai da suka jiyu. A maimakon ta yi hamdala sai ta shafa cikinta ya ce,"Kwanta naman kaza da tuwon birni."
Sosai suke mamakin rayuwar da take yi. Ba su cika da mamaki ba sai da suka ji tana jan rago, domin har da gayya take yi, don su ga cewar ba za su iya ba su mayar da ita.
Munshari da take yi ya ƙara ƙular dasu, har suka fara tunanin dole su yi wa Mommy boren ba za su iya kwana da ita a ɗaki ɗaya ba.
Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka ɗauro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci suka kwanta suna karanto addu'a.
To Hajiya Jimmalo a birni ko ya zaman birni zai ci gaba? Ko kuma za ta yi nasarar a mayar da ita Damagaran?
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 17
*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*
*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*
*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*
*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*
*Iya adadin da kuke so muna turawa*
*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*08130902505*
Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka ɗauro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci, suka kwanta suna karanto addu'a.
Saboda canjin gurin kwanciya mai daɗi, sai ta yi baccin da ta ci bashi tun rasuwar Kaka Tani. Ba ta tashi ba har sai ƙarfe bakwai. Yaran gidan tun asuba suka tashi suka yi sallah, sannan suka yi karatun hadda. Bayan sun gama suka yi na boko, har suka gama suka kwanta, Jimmalo tana sharan bacci.
Mommy ta ninyar tashinta, amma tsoron rikicin ta ya sanya ta ƙyale ta, domin ta san ko ta tashi ba sallar za ta yi ba.
Ƙarfe bakwai ta buɗe idanunta, saboda alarm da Auta ya kunna ya ɗora mata kusa da kunni. Da sauri ta buɗe idanunta tana zare idanu. Babu salati ta zabga miƙa tana hamma. Ba tare da ta kulle bakin ba, sai ta miƙe tana zare ido tuna inda take.
Falo ta fito kai tsaye ba tare da ta yi sallah ba. Ganin babu kowa a falon, sai tibi da aka sanya karatun Alqur'ani suratul Tauba ƙira'ar Mishawi.
Jin motsi a kicin sai ta nufi kicin ɗin tana zare ido, tamkar makauniyar da ta warke daga makanta.
Mommy tana tsaye da Asibi mai aiki suna ƙoƙarin dama kunun gyada. Babu sallama sai dai suka ganta a tsaye tana soshe-soshe. Asibi har ta tsorata ta dafe ƙirjinta.
"Haba jimmmalo kyayi sallama kin ga kin tsorata ta." Mommy ta furta tana kallon ta.
"Gari ya waye ki mayar da ni Damagaran." Ta furta a maimakon ta ba ta amsa.
Mommy gabanta ne ya faɗi tuna alƙawarin da ta yi mata, domin ta ɗauka da gaske take yi. "Zan mayar dake amma ki je ki yi sallah, sannan ki yi brush da wanka. Na sanya Umma, ta haɗa miki kayanta, kafin a siyo mi.."
"Ni fa ba zan zauna ku cinye ni, kamar yadda kuka cinye Kakata ba, saboda aradu wannan dukiyar da kuke da shi mutane kuke cinye wa."
Murmushi Mommy ta yi, ganin yadda ta haƙiƙance kan gaskiyar maganarta."Ki je ki yi sallah lokaci yana wucewa." Ta furta mata daɗan tsawa.
Amma ko gezau ba ta yi ba ta ce,"A matar dani Damagaran don ba zan zauna anan ba."
"Shikenan, zan mayar da ke, amma yanzu ma sai kin yi wanka kin canza kaya."
Har ta buɗe baki za ta musu sai kuma ta juya tana gungunan.
"Hajiya, kamar zaginki take yi fa? Wannan yarinyar an yi mahaukaciyar ƙazama."
"Ya xan yi haka nan zan daure na canzata. Wallahi tun jiya da ta zo kaina ya fara ciwo, saboda ban san ta inda zan fara ba."
"Gaskiya ga shi ba ta da kunya kallon mutane take a tsaye."
"Hmmmmh! Hajiya ta haɗa ni da aiki."
"Babba ma kuwa, saboda wannan yarinyar canzata matsala ne." Asibi ta furta tana juya kunun gyadar a wuta.
Mommy cikin ɗaki ta koma don ta ci gaba da karatun da take yi. Xuciyarta cunkushe da tunanin ta inda za ta fara.
A maimakon ta yi wankan sai ta yi daka tsami. Ta lafka mai ɗaya daga cikin kayan Kaka Tani riga da zani ta ɗaura.
Sai kawai ta fashe da kuka ta rungume sauran kayan."Kaka Tani mai ya sa kika mutu kika barni?" Ta yi tambayar tana kuka.
Falo ta fito tana jin a zuciyarta dole su mayar da ita Damagaran, saboda zaman gidan shine zai ɗebe mata kewa ta ga kamar za ta dawo.
A lokacin da ta fito fili duk suna kan dinning. Daddy ne yake saukowa daga bene hanunnsa riƙe da carbi.
Ganinta sai suka zuba mata ido cikin mamaki. Da fari sun ɗauka ko mutuwar ya haukata ta, ganin shigar da ta yi, amma sai da ta ƙaraso ta kallo Mommy ta ce,"Na shirya a mayar da ni."
Umma, Auta da Nufaisah suka kwashe da dariya.
"Mommy, wannan wane irin kaya ta sanya?" Cewar Umma tana nuna ta.
"Ita kanta Mommy daurewa ta yi, saboda dariyar da take son cin ƙarfinta."
"Jimmalo, lafiyarki kuwa? Da gaske kike za ki rinƙa sanya wannan kayan?" Daddy ya yi mata tambayar cikin takaici.