Sashe 35
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kayan Kaka Tani ne, wanda su kawai suka rage mini na ke gani na ke jin daɗi. Daga yanzu su zan rinƙa sanyawa har ƙarshen rayuwata."
"Hakan ba zai faru ba, saboda mahaukaciya za a mayar dake, duk inda kike je da kayan nan dariya za a yi miki."
"A yi mini dariya, na fasa bakin mutane don ba ni da wasu kayan sai su." Ta ba wa Mommy amsa tana zare ido.
"Ba zai yiwu ki rinƙa sanya Waɗannan kayan ba, saboda za ki shiga makarantar boko da islamiya, kuma dole uniform za ki rinƙa sawa."
"Ni fa ba zan zauna da ku ba, dole a mayar da ni Damagaran." Ta furta tare da sakin ihu, ganin kamar wayo suke son yi mata.
"Za a mayar dake ki zo ki ci abinci."Mommy ta furta tana toshe kunninta.
"Ki dai na mata ƙarya Karimah, dole a gaya mata gaskiya, a yanzu ba ki da 'yan'uwan da suka wuce mu, kuma a nan za ki zauna tare da mu, don haka ki fuskanci rayuwar da za ki yi gaba. Kakarki ta mutu kuma duk wanda ya mutu ba zai dawo ba."
"Wayyo Allah! Ni ba zan zauna da ku ba. Amayar da ni ƙauye ku ba zan yi rayuwa da ku ba." Ta furta tare da fashewa da kuka.
Gabakiɗaya sai suka zuba mata idanu suna kallonta. Ganin ba za ta daina kukan ba, sai Daddy ya miƙe ya tsaya a gurinta. Damuwa ce sosai a fuskarsa, saboda gabakiɗaya ta hana su karyawa ta daɗi, sai kallonta suke yi cikin takaici, musamman Mommy da take ji kamar ta rufe ta da duka.
"Ya za mu yi da ita? Gaskiya kukanta yana damuna?" Cewar Mommy tana kallon Daddy.
"Ita ba yarinya ba ce dole ta zauna. Yanzu ina gama zan je makarantar su Umma na yi mata rigistration da kuma na islamiya har da hadda, dole in ta ga babu sauƙi ta haƙura."
"Za ta iya guduwa daga makaranta."
"Direba zai rinka kaisu kuma zan gargadi malaman." Ya ba ta amsa kamar ya ƙosa da maganar.
Jimmalo ganin sun shareta suna karyawa, sai ta ɗora hannu akanta ta ƙara fashewa da kuka ta yi ƙofar gida.
"Wayyo Allah! A mayar da ni Damagaran ba zan zauna a birni ba. Kaka Tani ki taso daga ƙabari ki tafi da ni." Kalaman da take furtawa kenan, cikin muryar kuka har ta isa bakin get. Zama ta yi ta ɗora hannu tana ihu.
Sun kasa cewa komai suka raka ta da idanu har ta fice.
Mommy ce ta leƙa ta hange ta a bakin get tana ta ihu. Dai ta dawo ta zauna xuciyarta na tafasa kamar ruwan zafin da yake cikin kwatami ana shirin saukewa mai jego.
Aliyu
Captain Aliyu a ranar da suka baro England za su dawo Nigeria, sai ya ji kewar gida ya kama shi. Ya so ya wuto, amma kan dole sai da suka je Barrack don sai da suka yi aiki. Kwana biyu ya yi, ya shirya zuwa Kaduna. Kasancewar da sassafe ya shirya, domin akwai ɗaurin auren da yake son zuwa, bayan haka yana son ya yi bacci kafin lokacin. Don haka ya yi wa Kaduna shigowar safiya.
A lokacin da ya fara hon, cikin mamaki Mommy da Daddy suka kalli juna.
"Kamar hon ɗin Ya Captain?" Cewar Nufaisah tare da miƙewa za ta leƙa.
"Ba kama bace shi ne, saboda mun yi waya da shi jiya. Ya sanar da ni da zarar sun gama aiki zai zo gida, kuma akwai ɗaurin auren abokinshi." Cewar Daddy.
Gaban Mommy ne ya faɗi, domin ba su san yadda za su kwashe da Jimmmalo ba, amma za ta san yadda za ta yi masa magana kar ya shiga sabgarta.
Murna suka fara yi daidai lokacin da motar ta shigo ciki.
"Wallahi Mommy Ya Captain ne." Auta ya furta tare da rugawa waje.
Aliyu Gwarzo zaki. Ya fito cikin shiga ta alfarma. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda gizna. An yi masa ɗinkin mai kyau riga da wando waɗanda suka ɗan kama shi kaɗan. Takalminsa agogonsa da kalar gold. Sai bakin glass da ya sanya wanda ya ƙara masa kyawu. Kasancewar sababbin kaya ne bai taɓa sanya su ba, sai yake ganin sun fi kowanne kayansa yi masa kyau, har da kakin da in ya sanya yake ji da tamkar wani sarki. Wani irin turare mai sanyin ƙamshi da daɗi ya fesa wanda ya cika motar nashi. Dama kun san mutumin da son ƙamshi, domin zai iya kashe ko nawa ne ya siya. Jinsa yake yana ɗaya daga cikin jerin mazan da suka amsa sunansu, saboda kwalliyar da ya yi yana ji da za a je gasar kyawu na maza, tabbas sai ya karɓo kambun. Shi kansa ya yi wa kansa kyawu domin jefe-jefi yake kallon kansa ta maganin motar har ya ƙaraso Zariya. Shi kansa yana ganin ya yi kyawu, ballantana ga 'yan matan da suke son namiji ɗan kwalisa kuma mai tashe da ƙuruciya da kuɗi da nera. Ya san cewa yau sai ya kasa hankalin ƙawayen amarya, don haka ya gama tsarawa ana ɗaura auren zai dawo gida, domin ba shi da lokacinsu. Jira yake kamar yadda yake classical ya samu wacce za su yi compatible. Nishadi sosai yake ji, sakamakon bikin abokinsa da zai halatta. Zuciyarsa ta fara kwaɗaita masa ya kamata ya yi aure, ganin duk abokanansa suna yi, sannan ya rabu da Lubaynah da ta zamar masa ƙarfen kafa. Lokaci ya yi da zo samu mace ta ƙwarai, wacce namiji bai taɓa riƙe mata hannu ba. Ya aura sannan ya killace ta a gidansa, su yi rayuwar aure su cikin so da ƙauna.
Buɗe motar ya yi yana ji da kansa da isa. Wayarsa ya ɗauki da jakarsa daidai lokacin da ƙanninsa suka rugo cikin tsananin farinciki.
Sai dai me, ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa, sakamakon kukan da ya ji mai kama da ma gardi. Da sauri ya waiwaya inda yake jin kukan cikin ɓacin rai. Kallonta ya yi cikin tsananin mamaki domin a tunaninsa ko fatalwa ce. Ko kaɗan bai yi tunanin ganinta a cikin gidan ba, domin tuni ya shafe babinta ta, tun ranar da Hajiya ta gaya mishi sun yi rabuwar rashin mutunci. Ko da suka yi waya da Hajiya ba ta gaya masa tana gidan ba.
"Wancan mahaukaciyar 'yar iskan fa?" Ya yi wa Nufaisah tambayar cikin tsananin tashin hankali.
"Ta dawo nan da zama Ya Capta.."
"What?!" Ya furta tare da cire gilashin idanunsa.
Kafin ta ba shi amsa cikin tsoro ganin rikicewar da ya yi, sai ya ji muryar Daddy yana faɗin,"Eh, Jimmalo ta dawo gidan nan da zama saboda kakarta ta mutu."
"Kuma Daddy, sai a rasa wanda zai ɗauki wannan mahaukaciyar sai mu? Wannan abin kunya ne tana rayuwa a gidan nan."
"Hajiya ta yi mini umurni da na kawo ta gida nan, kuma marainiya ce ba ta..."
"There's no way! Wannan mahaukaciyar za ta zauna a gidan nan." Ya furta yana harararta daidai lokacin da ta ƙara buɗe baki ta rushe da kuka.
"Ita kanta ba ta son zama da mu. Kaddara ce ta sanya ta shigowa cikinmu, kamar yadda ba mu da abin da za mu yi da ya wuce mu rayu da..."
"No daddy, na yi alƙawarin zan ba da ko nawa a kaita wani gida can. Ko gidan marayu ne, saboda ba zan iya zama da ita ba na tsane ta bana son ganinta, in har kuka sanya ta zauna a gidan nan zan iya kashe.."
"Kul! Karna ƙara ji. Karka ƙara maganar kisa saboda ba ta da gurin zama sai nan gidan, don haka ya zama dole ka sanya wa ranka haƙuri, ka ɗauketa a matsayin da ka bawa su Umma."
" I can't babu yadda za a yi, na haɗa matsayin masu hankali da mahakauci guri ɗaya." Ya furta cikin ɓacin rai tare da ɗaukar jakarsa, ya nufi cikin ɗakinsa a maimakon falon iyayensa.
Kallonsa suka yi cikin damuwa, ganin yadda yake huci kamar mesa.
"Saboda Aliyu na ji tsoro sosai da Hajiya ta ce anan za ta yi rayuwa, na san cewa dole za a samu matsala. Ya kamata ka fahimtar da Hajiya Jimmalo ta koma gidanta, saboda bana son a samu matsala ya karya musu yarinya watarana."
"Hajiya ita ma gudu ta take yi ba zata iya da ita ba. Ni kaina yarinyar nan tun da ta dawo gidan nan nake cikin damuwa. Dole zan yi magana da shi, sannan na san yadda zan yi ya ɗauke ta a matsayin ƙanwa. Zaman Jimmalo a gidan nan babu fashi." Jin abin da Daddy ya ce sai ta kalle shi tana girgiza kanta.
"Da kamar wuya hakan, saboda ka san yadda Aliyu yake in ya tsani abu."
Shiru suka yi suna kallonta da take ta ƙara sautin kukanta.
Jimmalo ganinsa sai ta zare idanunta. Duk da cewar ta tsorata, amma sai ta yi maza ta shanye tsoranta. Ganinsa sai ta ji daɗi sosai, domin dama ce ta samu da zata koma ƙauye, don haka ta ƙara sautin kukanta cikin zallar taɓara.
Captain kuwa cikin tsananin ɓacin rai ya shige cikin sashinsa. Buɗe falonsa ya yi ya shiga, sannan ya fara safa da marwa bayan ya ije jakarsa.
"Impossible! Ba zai taɓa yiwu ba yarinyar da na tsana ta zauna a gidan iyayena." Ya furta tare da dunƙule hannunsa ya naushi isa, sai kuma ya tsaya cak cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci guda ya nemi farincikin da ya zo da shi ya rasa. Turare ya ɗauka ya ƙara feshe jikinsa dashi, domin ganinta ya sanya shi har ya fara jin warin jikinta.
Ruwan faro ya ɗauka ya buɗe zai sha, sai kuma ya fasa ya yi jifa da gorar. Jakarsa ya laluba don ya ɗauki sigari, amma sai ya tuna inda yake. Da sauri ya mayar da zif ɗin jakar tare da wirgi da ita, tuna ko ya zo da ita bai isa ya sha ba.
"Ba zan taɓa zama da ita ba dole za ta bar gidan nan." Ya ce tare da kwanciya kan gadonsa yana mayar da numfashi.