← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 52

Sashe 40

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 20

*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*08130902505*

Ganin haka sai ta ci gaba da karatun, burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kawai ta yi ba tare da ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ma ta iya ba ballantana rubutu.

Wunin ranar ba za ta ce ta koyi komai ba, domin hankalin ta ba shi kan ta koyan, musamman turanci da suke yi wanda yafi ɓata mata rai da tsanar bokon sosai.

Ko da aka fita break, ba ta fita ba saboda kayan da ta sanya da rayuwar da ta tsinci kanta sai ta ji duk ta takura.

Umma tana son ta kawo mata abin break, amma ƙawayenta sun zura mata idanu so suke su gane da gaske 'yar uwarta ne.

Ganin haka sai ta faki idanunsu ta kawai Auta ya kai mata.

A lokacin da ya kawo mata kular da sauri ta karɓa domin yunwa take ji sosai. Kallonta yaran suke yi ganin yadda ta kai hannu za ta fi abinci ba tare da ta wanke hannu ba.

"Anty Safeeya, Anty ta ce ba a cin abinci ba tare da an wanke hannu ba, sannan ga cokali ki sanya ki ci."

Ije kular abincin ta yi tana kallon Nadiya da take tsaye a gefenta.

"Ke! Karya ki xan yi in har kika shiga gonata. A Kauyenmu da maza na ke karawa, don haka ban ga abin da zan samu a jikinki ba, domin ganin ki na ke kamar yanzu aka haife ki."

Jin abin da ta furta cikin zafi, sai ta matsa da sauri tana zare idanu. Jimmalo ta zabga tsaki ta ɗauki abincin ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Kafin ta gama cin abincin duk ta bata hijabinta.

"Uncle Yahaya, ka ga Safeeya ta ɓata kayanta." Mudassir ɗan ajinsu ya je ya gaya wa Uncle Yahaya, domin doka ce a makarantar duk wanda ya ci abinci sai an buge shi.

Cikin zafi ya isa gurin, ya yi mata bulalar da ya sanya ta miƙe za ta cakume shi. Da fari razana ya yi, amma kuma sai ya dake ya tsula mata bulalar iya ƙarfinsa.

Ihu ta saka tana sosa bayanta. "Oya mu je gurin Principal sam ba ki da kunya." Ya furta tare da kama hannunta yana janta.

Dukan da ya yi mata shi aka ƙara mata. Da fari zagi ta ƙunduma musu, jin hakan Principal ya sanya sajen ya yi mata dukan tsiya. Duk dauriyarta sai da ta koka ganin yadda ya fasa mata baya.

Kafin a tashi ta gama tsine musu, kuma ta rantse ba za ta ƙara zuwa makarantar ba.

Aliyu
Da ya koma gida Daddy faɗa ya yi mishi sosai."Cewa na yi ka kaita ayi mata rigista na islamiya da boko."

"Daddy, ba zan iya dawowa da ita a cikin motata ba."

"Ya zama dole ka san yadda za ka yi ka ɗauke ta a matsayin yar'uwa."

"Impossible dad, zan koma Abuja." Ya ce tare da miƙewa jin faɗan da yake masa.

Daddy haushi ya ji, ya haura sama Mommy ce ta kalle shi za ta yi magana ya riga ta."Please mommy don't say anything, zan wuce ki yi mini addu'a."

"Allah ya tsare." Ta furta ganin yana musu da su.

Yadda ta amsa sam bai yi masa daɗi ba, amma tafiyar ya fi saboda yana in suna rayuwa a gida ɗaya, watarana zai kashe ta. Ɗakinsa ya wuce ya ɗauki Jakarsa.

Zariya
Anty Amarya riƙe da jakarta mai ɗauke da kayan kwana biyu. Sun yi shiri tsaf ita da Hanifa da kuma Mufida. Dama sun shirya tafiyar za su yi wa Captain bazata. Tun da ya ce mata zai shigo Kaduna, sai ta shirya zuwa Kaduna, don ta yi masa kyakkyawar albishirin ta samo masa yarinya kalar wacce yake so.

Yarinya ce wacce ba za ta wuce shekaru sha bakwai ba. Hafizar Alqur'ani. Ita ta cinye gasar Alqur'ani na wannan shekara na ƙasa da aka yi.

Dalilin da har ta yi masa hanyarta. Mahaifiyarta ƙawar ƙanwar Mamanta ne da take zama a Suleja. Labarin yarinyar ta ji suna yi tana sha'awar tana da yaro ta aura masa, kasancewar maƙota suke.

Jin yadda take sha'awar tarbiyartarta, da kuma yadda ta fasalta yarinyar har ta gaya mata cewar burin yarinyar ta auri soja, duk da sanin wasu sojojin na su da natsuwa. Nan take ta yanke shawarar ta yi wa Aliyu maganarta, amma sai ya yi mata alƙawarin zai daina kula matan banza. Don haka take son su yi magana ta fahimta, kuma ba a cikin gidansu ba, don ka da wani ya ji abin da take son yi, ya zama silar da mutanen gidan za su ƙara tsanarta, musamman Hanifa da take ganin kamar kusancinta da Aliyu zai taimaka ta same shi.

Tun da Mufida ta ji za ta je Kaduna, sai hankalinta ya kwanta, ganin ta samu hanyar da za ta yi maganinta ba tare da wahala ba. Don haka ana gobe ta je aka yi mata lalli da gyaran kai. Ganin haka Hanifa ta cika da baƙinciki, domin ta san zuwan na ta ba ƙaramin cikas zai kawo mata ba.

Ba ta kira Aliyu ta gaya masa ba sai da suka kusa tasha. A lokacin da ta kira shi har ya shiga cikin motar da ya sanya jakarsa. Ganin kiran na ta sai ya fasa tuƙa motar ya ɗaga.

Sallama ya yi mata sannan ya ce,"Antyna, na yi shirin biyowa ta Zariya, amma saboda wata matsala ba zan zo..."

"Kwantar da hankalinka ka zo tasha ka ɗauke mu."

Jin abin da ta ce, sai ya cika da mamaki domin ba ta gaya masa za ta zo ba." Anty ina fatan ba yaran nan bane, suka sanyaki zuwa? Saboda wahalar da kansu suke yi. Gara ki gaya musu gaskiya su je su samu wadanda za su iya auren su, domin in har ni suke jira za su mutu babu aure."

Jin abin da ya ce, sai ta yi guntun murmushi tana kallon su. "Kwantar da hankalinka Aliyu. Na zo maka da kyakyawar albishir da zai sanya ka yi mini kyauta."

Jin abin da ta ce sai ya yi murmushi."Anty, an samu kalar matar da na ke so ne?"

"Daɗina da kai ka cika ƙosawa, ka yi maza ka zo tasha ina jiranka." Ta kashe wayar kafin ya ce wani abu.

Ganin ta kashe sai ya ije wayar, tare da kunna motar yana fatan Allah ya sa kalar matar da yake so ne ta samu. Ba tare da ɓata lokaci ba ya tafi zuwa tashar. A lokacin da ya isa suna tsaye suna jiran shi. Hon ya yi musu sannan suka fara tahowa zuwa gurinsa.

Kamar yadda gaban Hanifa ke dukan tara-tara haka na Mufida. Kowacce xuciyarta cike sonsa da ƙaunarsa. Burinta ya yi mata tarba na musamman, amma sai dai kamar kullum don ba ta canza zani ba.

Saboda girmamawa, fitowa ya yi daga motar ya karɓi jakarta. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce,"Gaskiya kin yi mini bazata kin san har na shiga mota zan koma Abuja?"

Mamaki sosai ta yi, domin ya ce mata kwana huɗu zai yi."Hala kiran gaggawa ka samu daga gurin aiki?"

"Anty gara kiran aiki da tashin hankalin da na samu a gida."

"Subuhanallahi! Lafiya?"

Yatsina bakinsa ya yi, daidai lokacin da ya sanya jakarta a bayan mota."Za mu yi magana, saboda in har zan yi maganar yanzu, wataƙila na kasa tarbarki da kyau."

"Komai dai ya yi zafi maganinsa Allah." Ta ce daidai lokacin da ta shiga gidan gaba.

Ba tare da ya ce mata komai ba ya kunna motar. Sai a lokacin suka samu ƙarfin iya gaishe shi a tare.

Ɗan waiwayo wa ya yi, ya watsa musu banzan kallo ya ce,"Kuna lafiya?"
Chapter 40 · 0% Book details