Sashe 28
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 14
"Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na ta budurcin?" Kin san Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta baya ƙasa za mu bi shi tun da ba shi da mutunci."
"Shikenan sai kin dawo."
"Yauwa kar ki damu ba zan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. "
"Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta.
Iyayenta sun ɗauki fushi sosai da ita, ganin haka hankalinta ya tashi sosai. Da ƙyar ta samu ta shawo kansu, bayan ta yi musu alƙawarin ba za ta ƙara kula shi ba, sannan za ta nemi wani ta yi aure sannan suka haƙura, amma har lokacin haushinta suke ji.
Captain tun yana sanya idanun za ta dawo, amma har ya ga sun kwashi sata bata dawo ba. Hankalinsa ya kwanta yana fatan ya yarda ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tafiya zuwa England ya kama shi hankalinsa kwance ya tafi.
Zariya
Mama Mufida zaune a gidan Anty Amina suna hira. Anty Amina ta waiwayo da take kwaɓa kullum ɗan-gauda ta ce,"Wai yanzu kina nufin wannan turaren bitazaizai da ta shafa bai kalle ta ba, mun yi asarar kuɗinmu kenan?"
"Hmmmmh! Ki bar ni da buhun takaici wallahi kallon banza ba ta samu daga gare shi ba, domin ta ce mini gara Hanifa da yake kin san kishiyar uwarta ta san yadda za ta shiga fita a cikin malamai, har kallon ta ya yi yana tambayarta karatu."
"Zai tambaya tun da yana zuwa an zuba masa a ruwa ya sha. Ni fa wannan Maryam ɗin tun da na ji Sama'ila zai aure ta, na san cewar sai ta gama da shi da iyalansa."
"Wallahi ta gama da shi har ita mamata Hanifa, saboda ba ki ga ladabi da take mata ba, kaf 'ya'yanta in har Maryam ta yi magana ya zauna, har da waɗanda suke gidan auren."
"Duk za ta iya wannan 'yar gidan malaman zauren? Har yanzu ba ki ga sanin sunan mahaifinta ba. Ita ma Maman Hanifah har da kwaɗayin ta sanya shi Aliyu, ya auri yarinyarta tun da kin ga ya shaƙu da ita so take ta haɗa aurensu, ba tare da sanin ko da ta haɗa ba itace da riba, domin haɗa auren amfaninta ne."
"Shi ya sanya tsani yarinyar nan, wallahi yadda na ke jin tsanarta, bana tunanin in Baban Mufida ya ƙara aure na tsani kishiyata kamar haka. Yarinya ƙarama sai kinibibin tsiya, kowa yanzu a gidan nan Anty Amarya dai."
"Iya makirci ne da kissa na mata, don ta zo daga baya ta mallake kowa a ciki, tun da bata haihuwa ai dole ta nemi hanyar da za ta mallake kowa ta juya yaranku."
"Ai ba zai yiwu ba kuwa in har ina da rai. Kin san Allah yadda kaf yarana babu wacce ta auri mai kuɗi kamar shi? To kuma babu yarinya da za ta samu mai kuɗi na zuba ido ayi auren ko da ace Mufida ba ta son shi, sai na san yadda na yi na hana auren, domin ina gani ba za a rinƙa mana iyayi da suruki mai kuɗi ba. "
"Ai gara ki miƙe wallahi in har Mufida ta same shi ta yi miji."
"Kin ga yanzu kuɗin da na ke juyawa na shinkafa na kwaso muje gurin Malamin nan, na fi son a yi abun cikin sauri domin kin san da zafi-zafi akan buga karfe."
"Yanzu kuwa domin ina ɗora tukunyar gaudar, kafin na shirya Karima sun dawo daga makaranta, sai na bar mata muje mu dawo tun da babu nisa. Ki kwantar da hankalinki Mufida bata da miji sai shi."
"Allah ya nuna mini haka, har na ga yadda zan shuka rashin mutunci a dangi. Kina ganin Anty Hafsa daga yarinyarta ta auri miji mai mota yana aikin gwamnati, sai iskanci duk aka zauna zancen suruki take yi, sai kace kanta aka fara auran mai mota."
"Mijin da ba ita ce ta farko ba mijin wata ta aura har take tutiya?"
"Za ta yi mana tun da yana basu abin duniya, kuma kin san ta itama da shige-shige ba zama za ta yi ba?"
"Haka ne kuwa ta shi mu tafi bari na ɗauko mayafina tun da ta dawo." Anty Amina ta furta bayan ta gama jera ɗan-gaudar a tukunya ta rufe.
Kasancewar babu nisa basu jima ba suka isa. Bayan sun yi mishi bayani sosai, ya shiga ciki ya yi musu rubutu da magunguna ya ba su.
Suna tafe suna hira Anty Amina ta kalle ta ce,"Kin dai ji abin da ya ce, sai ta kula yadda za ta yi amfani da su."
"In sha Allahu kin ga tun da suna shiri da ƙanwarsa Nufaisah, sai ta rinƙa tambayarta lokacin da zai zo. Yana zuwa sai ta je hutu gidansu, yadda za ta samu ta yi maganin, tun da ya ce dole wannan rubutun sai ya ci a abinci."
"Eh hakan ma ya yi shawara ma kyau. Allah dai ya sanya ayi a sa'a."
"Amin, bari na wuce gida kawai tun da samu abin da na zo nema."
"Na ɗauka za mu koma kici abinci Maman Mufida?"
"Gara na koma gida yanzu na san Mufida ta gama abinci."
"To shikenan Ubangiji ya bada sa'a."
Amsawa ta yi tana ƙoƙarin taran keke napep.
Cikin farinckin ta isa gida, ta yi sallama Anty Amarya ce zaune a tsakar gida tana gyara zoɓon da za ta dafa.
Amsawa ta yi tana mata sannu da zuwa. Wani irin tsuka ta saki ta wuce ciki ba tare da ta amsa ba. Kallo ta bita da shi tana mamakin kishin da take yi da ita, saboda kishiyarta suna zaman lafiya, amma Maman Mufida abin da take yi mata ko miji suka haɗa sai haka. Ci gaba ta yi da aikinta bakinta ɗauke da azkar domin tana kula da ibada, saboda ta san cewa tana da maƙiya sosai musamman ita.
Mufida, da take raba shinkafa da wake da mai da yaji da ta gama. Sallamar Mama ya sanya ta ɗago tana kallonta. "Sannu da dawowa Mama."
"Yauwa 'yar albarka maza ki gama ki shigo." Ta ƙarashe maganar tana washe baki tare da ije hijabinta kan igiya.
Ganin yadda take farinciki sai ta kasa ƙarashe rabon. Ba ta zuba nata da na Mama ta rufe tukunyar.
Shiga ciki ta yi ta zauna gefenta."Kina jina Mufida? Malamin yace ki natsu ki yi wannan aikin da kyau, domin ya tabbatar mana da in kika yi yadda yace Captain Aliyu sai yadda kika yi da shi, amma wannan rubutun dole sai kin zuba masa a abinci."
"Cikin abincin da zai ci, ina zan ganshi na zuba masa?"
"Dallah ja can kin cika tsoro. Kin san wane irin namiji kike son mallaka? Dole sai kin zama jaruma sosai. Abu mai sauki tambayi Nufaisah lokacin da zai zo, in ta gaya miki sai ki shirya zuwa Kaduna ki yi hutu, don kar a zarge ki ku tafi da Hanifa."
"Kuma haka ne Mama, domin na ji kamar Anty Amarya za ta je Kaduna, amma sai in ya zo."
"Shikenan, sai ki ce za ki bita kin ga ai ba za ta ce a a ba, tun da za ta da Hanifa."
"Amma ina jin tsoron yadda zan sanya maganin, kin san ko a gida abincin Mommy kawai ya ke ci?"
"Wannan kuma shawara ya rage wa mai shiga cikin rijiya, sai ki rinƙa abu kamar ba mace ba. Ke ko irin fim ɗin nan da ake kallo ake sumun dubara ai kyayi yi tunani. In kin kasa sanya iya abincinsa, ki sanya a cikin abinci kowa duka kin ga shi an yi don soyayar aure, sauran mutanen gidan sai su ƙaunace ki."
"To Mama, zan gwada duk yadda zan yi sai na sanya masa, domin ba zan iya haƙura da shi ba."
"Yauwa haka na ke son ji."
Damagaran
Jimmalo zaune a gaban Kaka Tani ta tasa ta kamar za ta yi kuka. Kallonta ta ƙara yi tare da ɗauko jiƙaƙƙen magani ta miƙa mata,"Don Allah Kaka Tani kisha maganin nan, kin ga tun jiya kika fara janta har yanzu jikin ya ki sauƙi."
"Na sha Jimmalo, sauƙin ne dai Allah ba kawo ba."
"To ki ƙara sha, yanzu zan je gurin Lado mau kyamis ko Audi ya haɗa mini maganin janta." Ta ce tana ƙoƙarin kai mata ruwan maganin baki.