← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 52

Sashe 3

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai ba ki da labarin Ya Captain zai zo ɗaurin auren nan ba, domin har sun kamo hanya. Na ji Baba Ɗanlami suna waya da Daddyn K.d, ya ce masa suna hanya, don haka yanzu na san sun kusa."

"Eh zai zo ɗaurin aure sai kuma aka yi me?"

Murmushi ta yi tare da kashe nata ido ta ci gaba da gyara kwallin da ta saka ta ce,"Shi ka ke yi wa wanna kwalliyar."

Wani uwar tsaki ta saki ta ce,"Amma iska na wahalar da mai kaya ƙara! Ke har yanzu Hanifah ba za ki cire Ya Captain a ranki ba? Wallahi tun ranar da ya wanka mini mari na yi zuciya na ce ko shi ne autan maza na haƙura da shi. Mutum sai wulaƙanci da girman kai sai kace shi kaɗai ne soja kyakyawa mai kuɗi? Ni fa na haƙura da shi, domin na san ko mutuwa zan yi ba zai aure ni ba."

"Saboda wulaƙancin da ya yi miki sai ki haƙura? Wallahi ina nan kan bakana, sai abin da ya turewa buzu naɗi. Idan yana taƙama da kyau ai ni ma ina da shi, sannnan ilmi shekarar ƙarshe na ke a digiri."

"Ki daina wahalar da kanki kawai ki haƙura da shi, saboda Ya Captain ƙila balarabiya zai aura. Yadda yake ji da kansa, ba na tunanin zai iya auren bakar fata."

"Wannan faɗan ki ne, amma ni ina jin zai aure ni."

Wata 'yar iskan dariya ta saki mai haɗe da shewa."Ashe kuwa za ki mutu ba ki yi aure ba."

Kafin ta amsa kyawawan 'yan mata su huɗu, kusan kansu ɗaya suka yi sallama suka shigo.

Kallon su ta yi ta ce,"Kuma duk kwalliyar kuka yi wa Ya Captain?"

"Ke dai ba kin sare da wuri ba, amma mu kam muna nan kam bakanmu. In sha Allahu sai ya auri wata a cikinmu. Ina fatan nine."

"Ku zauna kuna yaudarar kanku za ku mutu ba ku yi aure ba."

Anty Mariya ce ta shigo ciki tana jin hirar da suke yi. Murmushi ta yi saboda ta san duk a cikinsu babu wacce zai so. Ta san kalar macen da yake so, duk dacewar shi ba haka yake ba. Tasan zaɓinsa da rayuwar da yake so. Zata iya cewa yana gaya mata sirrinsa wanda iyeyensa ba su sani ba, domin ta san Aliyu da sirrin da yake ɓoyewa a rayuwarsa wanda ba ta fatan su sani, domin sanin zai iya kawo wargajewar farincikin rayuwarsu da kuma yardar da suka yi masa. Aliyu fuska biyu ne yana da wani hali, wanda take tunanin daga ita sai shi suka sani. Har yau tana fatan Ubangiji ya ci gaba da ɓiyo sirrin har ranar da zai daina. Ihu suke yi bayan hari domin duk cikinsu babu wacce take da criteria, da yake son wacce zai aura take da shi. Yana da wani zaɓi da buri ga matarsa, duk da cewar shi ba haka yake ba.

Zama ta yi tana kallon su, da suke ta hayaniya suna zuzuta kyawunsa kowacce tana fatan ace ita zai so.

"Ni wallahi na ƙasa su zo na ga shi, saboda ya daɗe bai zo family ba. Ko rasuwar da aka yi na Kaka Naninna. Daga Hajiya sai Mommy da Daddy suka zo."

"Ai lokacin baya ƙasar fa." Cewar Hanifah da ta gama kwalliya tana ɗaura ɗankwali.

"Yanzu ma baya ƙasar. Yana Yukrain. Har da shi aka zaɓa a cikin waɗanda za su kai wa Ƙasar Ukraine taimako."

Jikinsu ne ya yi sanyi, kamar za su yi kuka jin abin da ta ce.

"Kai innalillahi! Wallahi har da bashi na ci na sayi kaya don kawai na burge shi." Ummita tace tana kwance ɗaurin ɗankwalinta, da ta bata kusan rabin awa tana ɗaurawa.

"Aiko dai dai ku yi haƙuri domin zai yi wata biyu ko fiye."

Kamar za su yi kuka, haka suke kallonta jin abin da ta ce.

Murmushi ta yi musu ta miƙe ta fita ganin ya kira ta a waya. Tamkar ƙawarsa ya ɗauke ta, saboda sai ya gaya mata abu, ba tare da ya sanar wa abokinsa.

Masoya, wannan labarin da wani irin salo na musamman ya zo. Kar ku sare ku bibiyi labarin tare da yi mini xafafen comments domin akwai cakwakiyar gaske da ruɗani. Kun dai san comments na ku yake karfafa mini gwiya. Ku yi following channel, arewabook, da kuma Whatsapp ɗina.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiwasin abin da zai faru a gobenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, waɗanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sirrin da ya sanya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sirrin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina arewabook🙏🙏
https://www.arewabooks.com/chapter?id=686289d4e9cb75389b9d68c8. Check it out!

Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko.

Follow the channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 2

Jin Captain Aliyu ba zai zo bikin ba, gabakiɗaya jikinsu ya yi sanyi, domin kowaccen su ta ci burin ya zo ya ga kwalliyarta.

Da misalin sha biyu Hajiya, Daddyn K.d da Mommyn K.d har da Nufaisah, Umma da auta Farid suka iso cikin. Zariya.

Ƙofar gidan cike yake da mutane sosai a ciki da waje. Hajiya da ta fito daga cikin motar tana miƙa. Da sauri mutanen da suke zaune suka taho gurinta don kwasar gaisuwa.

Farar mace dattijuwa, wacce daga ganinta ka ga naira ya zauna, domin duk tsufan da ta yi, hakan bai ɓoye kyau da take da shi ba.

Tana sanye cikin riga da zani na atamfa, kasancewar mace wacce ta yi riƙo da shigarta na Hausawa.

Ɗaga gilas idanunta ta yi, cikin tsananin so da ƙaunar ɗanta, da kuma iyalansa suka ƙarasa inda suke.

Cikin mutunci take amsa gaisuwar na su, bayan sun gana gaisawa sannan suka shiga ciki.

Baba Ɗahiru wanda shi zai aurar da yarinyar ya bi ta suna tafiya."Hajiya, mun ga tsaƙo Ubangiji ya ɗaukaka ke da iyalanki. Sosai kun yi ƙoƙari har da soja, don ko jiya ya kira ni in akwai abin da ba a gama siye ba, ya turo kuɗi bayan abin alkhairin da ya yi."

"Ai wai Aliyu ai dama ban so ya zo bikin ba, ka san yanayin aikinsa, ni dama ko ba aikin ya tsare shi ba, gara da bai zo ba. Ya raba hali da wannan shegiyar ɓakar zuciyarsa."

"Soja ne dole ya yi zuciya, kuma baya haka kun manta halin mai sunan da ya gado? Yaya Aliyu har na haihu yana kai mini duka ina ɓata masa rai." Ya ƙarashe maganar yana dariya.

"Da wannan, amma kuma marigayi mijina ai zuciya bata hana shi aure ba, amma shi kuwa fa? Inda ya aminta da haɗin da na so na yi da yanzu matar ta haihu."

"Lokacin auren ne bai yi ba, kuma yadda yake da zafin zuciya bana son a yi masa auren dole. Mu bari ya zaɓi matarsa da kansa, saboda in har muka yi kuskuren masa auren dole mun cuci yarinyar. Soja ko shi ya ga mace yana so wallahi sai tayi haƙuri."

"Ni fa na tsame hannuna kan lamarin da ya je ya auri kaki. Ai duk abin da yake yi ɗaurin gindin ubansa ya samu. A lokacin dana ce ayi auren shi da Ameera ya ƙi, idan da ubansa ya yi masa dole ai zai karɓa."

"Zai yi lokaci ne Allah ya haɗa shi da mata ta gari."

Hajiya shiru ta yi ba ta amsa ba sai ƙuta da ta yi, domin sosai yake ba ta haushi.

Daddyn k.d shiru ya yi yana jin ta bai ce komai ba, domin ba ya son ya tanka ta raba masa abin faɗe ana taro, amma shi ya san dalilin da ya sanya shi bai aminta da auren ba. Sam ba ya son abin da zai ɓata zumuncin su. Ya san wane ne ɗansa da kuma in ya kafe ba ya son abu. Sam ba shi da matsala da rayuwarsa aure lokaci ne, kuma saboda zafin ransa dole ya tsaya ya nemi matar da za ta iya shanye duk halinsa. Jin daɗin da ɗaya da ba ya aikata abin da wasu sojojin suke yi. Yana alfahari dashi sosai, tun da ya shiga aikin soja bai taɓa ko shigar banza ba. Har yau yana alfaharin da ya riƙe alƙawarin da ya ɗaukar masa.

Ciki suka shiga, nan mutane suka taho gurinta cikin murna. Bayan an gaigaisa sannan Mommy ta shiga ciki ɗakin uwar bikin, Nufaisah kuma da Umma suka shiga cikin 'yan mata.

An yi taro cikin rufin asirin Allah, an kai amarya gidanta. Su Daddy sun dawo Kaduna lafiya.

Ƙauyen Damagaran.
Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu barsu suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar, sai su rinƙa kukan munafunci kamar su aka cuta?"

"To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai iya ba, sai a barsu da Allah."
Chapter 3 · 0% Book details