Sashe 20
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yadda ta yi, daga shi har Hajiya suka rakata da idanu. Wani wawan tsaki ya saki zai fice, kafin ya fita ta mayar masa da nata.
"Don Allah kar ka rinƙa biye wa wancan yarinyar, saboda ba ta da hankali. Ni ban taɓa ganin mace irin ta ba, wallahi Tani ta cuci rayuwarta yarinyar nan."
"Karki damu Hajiya, daga yau ba zan ƙara yarda na ƙara ganin ta ba, saboda na tsane ta bana ƙaunar na rinƙa ganinta."
"Allah ya saka da alkahiri hidimar biki da ka yi." Ta ce tare da kawar da zancen.
"Amin, ya ba su zaman lafiya." Hira suke yi har suka isa gaban motar sa.
Hajiya na tsaye ya shiga bayan ya yi mata sallama."Don Allah in ka je Zariya ka gaishe mini da su."
"Duk za su ji Hajiya." Ya ce tare da fara ƙoƙarin tuƙa motar. Da ya kunna sai ya lura ta yi ƙasa gaban motar.
Gabansa ne ya faɗi sosai da sauri ya kashe motar ya fito, yana son duba abin da ya faru, domin ya san motarsa lafiya take.
Hajiya kallonsa ta yi cikin damuwa, ganin yadda lokaci guda fuskarsa ta canza idanunsa suka kaɗa, saboda ganin aika-akar da ta yi masa, domin ya tabbata ita ce kawai za ta yi masa.
"Lafiya soja?" Ta yi masa tambayar da sauri.
Saboda zuciyar da ta tiƙe shi kasa magana ya yi, sai kawai ya nufin cikin gidan yana huci.
A ɗakin Jimmalo take rawa cikin farin ciki, domin abin da ta yi masa ta san sai ya kusa kashe kansa, saboda baƙinciki.
"Ina fatan ba wani abu kika ƙara yi masa ba? Kin ga ki fita harkar wannan mara imani..."Maganar ta maƙale mata sakamakon ganinsa ya shigo yana huci kamar mesa.
Kai tsaye inda take ya je, ba tare da ya kula da Kaka Tani da take masa magana ba. Wani irin wawan mari ya sakin mata, sannan kuma ya fara dukanta yana haurinta ta ko'ina. Saboda kafiya da taurin rai, ƙoƙarin ramawa take yi, kuma bakinta bai mutu ba, sai zagi take auna masa.
"Aliyu lafiyarka ɗaya kuwa don Allah ka daina dukanta." Cewar Hajiya tana riƙe shi, amma bai kula ba so yake sai ya ƙaryata.
"Zuwana birni ya zamar mini masifa! Hajiya in har ya kashe mini jika wallahi sai mun yi shari'a."
Ganin dukan da gaske yake mata kuma ya ƙi dainawa, sai kawai ta fashe masa da kuka sosai."Aliyu in har ni na haifi ubanka ka daina duka yariyar nan, domin zan iya masa baki."
Cak ya tsaya yana huci kamar mesa.Ganin haka ta fito da shi falo tana share hawaye.
"Na rantse ba zan yarda ba dole ki ɗauki mataki, kuma yau za mu bar gidan nan." Cewar Kaka Tani tana girgiza. Ita kuwa ko hawaye sai ɗura masa zagi take yi, tana jawo masa bala'i, amma kuma ta daku don ta ji jiki sosai.
"Hajiya ki fita daga rayuwarsu, saboda in har za su kasance dake zan daina zuwa inda kike, ko kuma watarana za a kulle ni nayi kisa.. Yarinyar nan tayoyin motana ta sace saboda ba ta da tarbiyya."
"Kai amma Jimmalo ba ta kyauta ba, na rasa yadda aka yi ta raina ka."
"Ok, goyon bayan jikan ki kike yi ko? Saboda ke kika haifi ubansa ba ki ga abin da ya yi mata ba?" Kaka Tani ta furta tana jijjiga.
"Tani ya kamata ki fuskanci gaskiya, ki gane irin tarbiyyar da kike mata babu kyau. Jimmmalo mace ce kuma uwa za ta zama nan gaba, in har baki canza ta kan tarbiyyar da kika bata ba, walllahi za ki yi dana sani."
"Dakata Hajiya bana son rashin tsoron Allah. Jiƙanki ya duke ta kuma ki goyi bayansa kina gaya mini jikata ba ta da tarbiyya?"
"Tana da shi ne? Ɗube ta tamkar jaka yarinyar nan ba ta da maraba da dabbobi, saboda wallahi dana zauna da ita gara na zauna da kare."
"Aliyu karka ƙara magana ba sa'arka bace."
Jin ya danganta Jimmalo da kare, sai ta fashe da kuka ta ce,"Innnali wa inna ilahir raju'un!" Dama kin ɗauko ni ƙauye, don ki wulaƙanta ni da jikata? Zumunci bai ce haka ba, saboda in da kin tuna zaman da iyayenmu suka yi, bai kamata ki yi mini wannan rashin mutuncin ba, amma babu komai yau zan bar gidan nan ba zan ƙara mintina ba. Kada ki ƙara tunanin kin san ni ko zuwa gurinmu, saboda don kina kawo mini abu ba zai taɓa sanyawa na yarda ki rinƙa zagin mini jika ba. Jimmalo ita kawai na ke gani na ji daɗi."
Hajiya sai ta rasa bakin magana, ganin yadda ta harzuƙa tana hawaye sosai. Jimmalo da take cikin ɗakinta jin kukan Kaka Tani, da sauri ta ɗauko gwafan da ta zo da shi ta fito.
"Waye ya taɓa mini ke yanzu na sakar mishi harbi?" Ta ce tare da take gwafar tana zare ido.
Ganin ta saita shi sai ya zabura zai yi kanta. Hankalin Hajiya ya tashi sosai, domin ta san in har ta ƙyale shi ba za a yi da kyau ba.
"Aliyu maza ka bar gidan nan." Ta furta da ƙarfi tana kallonsa.
"Hajiya ki barta na yi mata dukan da sai na gyara rayuwarta, domin wallahi tsaf zan iya kashe ta." Ya furta tare da kai mata hauri.
"Na ce ka fita za mu yi waya." Ganin yadda ta yi maganar sai ya fita daga gidan.
Mai gyara ya kira, sannan ya ɗauki motar da ake fita da Hajiya ya tafi gidansu. A mota kuwa ji yake kamar zai kashe kansa don baƙinciki. Ya so ace ta barshi ya karyata.
Da ya isa gida hon ya yi maigari ya buɗe masa. Daddy ne a tsaye da Mommy da suka fito za su anguwa. Ganinsa farinciki ya kama su sosai.
"Soja mazan fama." Cewar Daddy lokacin da ya ƙaraso, ya durƙusa da makullin mota a hannunsa.
"Ina wuni Daddy, da Mommy."
"Lafiya lau ya gurin aikin?" Suka haɗa baki a tare suka yi masa tambayar.
"Lafiya kau hutu na samu na ce bari na zo na yi kwana biyu."
"Allah ya yi maka albarka ya ƙara tsare mini kai."
"Amin, Daddy." Ya amsa yana miƙewa.
"Lafiya ka ganka da motar Hajiya? Ko ta jirgi ka zo soyayya ya tashi?" Ya yi masa tambaya da ya sanya shi murmushi da Mommy.
"Motata tana gidanta. Wannan yar iska mara kunyar yarinyar nan da muka je ƙauye ta fasa mini mota. Na gani a gidan Hajiya za ta yi mini rashin kunya na buge ta. Shi ne take ta yi mini faci."
Zare idanunta suka yi suna faɗin,"Jimmmalo, ba ta da kunya da hankali."
"Ni mamakin Hajiya na ke yi da take ganin kamar za ta shiryu. Ita tunanin yadda za ta yi ta kwace yarinyar take yi, don ta canza mata rayuwa."
"Wannan yarinyar momi ai ba za ta taɓa shiryuwa ba, kina ganin ta sam ba ta da hankali. Hajiya ko ta karɓe ta wahala za ta sha. Ga shi ta tsufa haka kawai ta sanya mata cuta."
"Ni ma abin da na yi tunani kenan, domin wanda yayi nisa baya jin kira. Ta ƙyale ta kawai, saboda duk wanda ya ɗauki yarinyar nan ya ɗaukarwa kansa jaraba. Ga ƙazanta ga rashin kunya da zagi kamar yar maguzawa."
"Daddy, ina zargin tana fitsarin kwance saboda wani irin xarni da karni na ke jin tana yi."
"Zai iya yiwuwa, domin yarinyar nan sakalta da sangarta ya yi mata yawa."
"Allah ya kyauta wallahi ina baƙincikin da ta fito a 'yar'uwarmu, saboda ƘIYAYYAR JINI na ke yi mata." Cewarsa ya miƙe.
"Ya za ka yi tun da Allah ya haɗa jinin." Cewar Daddy.
"Bari na shiga ciki, na yi wanka na shirya kafin Abdullahi Bakanike ya gyara mini motata. Yau zan shiga garin Zariya in sha Allahu."
"Gurin mutuniyar ta ka ko? anty Amarya." Cewar Daddy ya ce yana kallon sa.
"Eh amma zan je na gaishe da su Baba Ɗanlami na yi murnar biki."
"Yana da kyau zumunci abu ne mai kyau, duk dacewar na san dai dalilin zuwan ya karfafa don Anty Amarya."
"Haka ne Daddy kwana biyu ban je gurin ta ba."
"Ai shi da Anty Amarya ba a jin kansu. Ko ranar bikin ana ta yi mishi tsiya sai kare shi take yi. Yarinyar tana da hankali sosai, domin Ya Audi ya samu mace mai natsuwa da hankali.
"Gaskiya kin ga ai ta yi karatu sannan tana da tarbiya. Shi kansa yana yabonta. Na tabbata da ace tana da yarinya babba a yadda Aliyu yake mugun shiri da ita, zai iya auren yarta."
Kallon su ya yi yana murmushi domin zai iya ɗin. Tana da hankali da natsuwa. Kamar yayansa haka yake jin ta.
"Bari na shiga ciki ina Nufaisah, Umma da auta?"
"Umma, ta je ɗauko shi a makaranta." Cewar Mommy.
Cikin ɗakinsa ya shiga, ya ije jakar goyon da ya zo da shi, da kaya kala biyu suke ciki, sai turare da ɗan tarkacensa.
Ajiyar zuciya ya saki cikin ɓacin rai. Ya so ace Hajiya ta barshi ya cire mata haƙori.
Wanka ya shiga ya yi ta dirzan jikinsa, domin ganinta ya sanya shi ƙyamar kansa. Sai da ya ɓata lokaci gurin yin wankan, sannnan ya fito ya shirya cikin shigan manyan kaya ya sanya hula. Ya yi kyau sosai kamar ka sace shi ka gudu.
Wayarsa ya ɗauka don ya fito falo ya ci abinci. Nufaisah ce a falon tana shirya masa abinci, sai Adnan da yake falon yana kallon cartoon.
Ganinsa da sauri ya tashi ya rungume shi."Auta ya kake?"
"Lafiya lau Ya Captain, where is my promise?"
"Yana ɗakina ga makullin ɗakin kai da Nufaisah ku ɗauki tsarabarku."
"Thanks brother." Ya furta cikin tsannanin farinciki.
"Sannu da zuwa Ya Captain?" Cewar Nufaisah tana kallonsa.
"Yauwa ya kike ya karatu?"
"Alhamdulillah mun yi hutun semester za mu shiga two hundred level."
"Da kyau ayi karatu sosai ban da kula samari da ƙawaye."
"In sha Allahu ya Captain." Ta ce masa tana kallon sa.
Dinning ya wuce don ya ci abinci, amma sai kawai ya rinƙa tuno fuskarta da haƙoranta. Da sauri ya miƙe jin amai yana taso mishi. Mamaki yake yi yadda Hajiya ta iya surviving tana cikin gidan.