← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 29

Sashe 6

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nagode da shawarwarinki masu kyau qawata Allah yasaka miki da Alkhairi, kuma inshaa Allah zanyi yanda kikace".... Koda fito kai tsaye gida suka wuraren 2,tana Shiga gidan salla kurun tayi wata er Aikin gidan me suna Sha'awa tazo kiranta wai Inji mami,hijab kawai tazura tawuce side,gaida ta tayi sannan tace da ita

" jeki ki wanken toilet dina ki gyaran dakuna sannan kizo ki goge wannan parlor din sam Sha'awa bata iya komai ba" harta juya zata shige tace da ita

"Sarai kinsani ranar daga kimun gyaran daki aka nemi sarkar gwal dina aka rasa,ajiye hijabinki a nan kishiga a haka,banda munafurci arenaka acikin gida sannan kace karika yawo da hijabi,salon sata kawai" tana zubda kwallah tashige cikin dakin harta kammala kuka take,da sallamarta ta shigo parlor din,mutanen data ganine jikinta ya mace ,yaa Muhammad dakuma yaa kameel, durkusawa tayi ta gaidasu sannan tamike da zummar barin parlor din Muhammad sai kallonta yake yakula kuma kuka takeyi,kameel ne ya dakatar da ita

"Miss dimples zonan" tsayawa tayi ta durkusa murya na rawa tace "gani yaa kameel" kallonta yakumayi "me akai miki kike kuka ne?" Sadda kanta kasa tayi "Ba komai yaa kameel kaina ne yake ciwo" mami ce ta karbe zancen

"Aida kigaya mai gaskia wani kanki ne yake ciwo,kaga ranar fa daga yarinyar nan tamun gyaran daki aka sarkar gwal dina aka rasa,itafa zarah indai satane ajininta yake sam bata iya dauke idonta akan abin wani ko Yaya ne kuwa,kullum shiyasa take mana yawo da hijabi acikin gida sabida daga zaran ta wawura tazura ciki,tofa shine sabida nace tacire wannan hijabin kan tashigarmun daki take kuka,kaikuwa ba halin yin sata" kallonta yayi cike da mamaki sabida baisan wannan zancemba baitaba ji ance tana sata ba yace

"Mami sata kuma yaushe zahra ta taba yin sata acikin gidannan?" Aynah ce ta karbe zancen dacewa

"Laa yaa kameel baka saniba ai wlhy zahra kleptomania ce da ita,ranar anan sashin har Lipton tasata,abinda komai damuke dashi side namu suma ana ajiye musu a side nasu" harara ya wurgawa Aynah yace cikin fusata

"Karya kike mata wlhy,Zahra bata sata kudai binciki yan aikinku amma ba kanwata ba,tun tasowarta ba'a ce tana sataba sai yanzu? Wlhy nasan kage ake mata" Murmushi mami tayi tace

"Imma dai itace kanta tayiwa,ungo hijabinki zoki karb'a ,tana hada hanya taje ta karbi hijab dinta tabar parlor din cikin tsananin kuka wanda dukkansu sun jiyota wannan abin ba karamin bata rayuwar moh yayiba atake yaji ya kara tsanar Aynah da mahaifiyarta...

Mom nuaim
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

10
Garden taje ta fadi acikin korayen ciyayin dake malale awurin ta tsaki wani kuka mai tsuma zuciya kuka take tamkar ranta zaifita...side din kameel suka fito zasuje suka jiyo kukanta,kallon kameel moh yayi yace dashi

"Zanje wurin zahrah kajirani a daki" gyada mai kai kurun yayi kasancewar shima din a fusace yake sarai yasan sharri suke mata...kukanta take tana rero adu'ointa

"Ya Allah ka kawo mun dauki,Allah katallafi rayuwata Allah ka kareni daga Sharrin masu sharri, Allah kana kallo ya Allah kabimun haqqina...takuma fashewa da wani kukan me ban tausayi zaunawa yayi kusa da ita a hankali yakira sunanta

" Zahrah na" sarai taji shi amma bata dagoba sai tsagaita kukanta tayi,yakuma cewa

"Zahra na,dan Allah ki tashi magana zamuyi" tashi tayi zaune ta saka gefen hijabinta taci gaba da sharar kwallah,Lumshe manya manyan fararen idonshi yayi yace cikin murya mai ban tausayi

"Zahra na kidaina kuka,kinga nan?" Ya daura hannun shi Asaman kirjinshi ya furta "tafarfasa yakemun idan naga kina kuka,dan Allah ki daina lallai lokaci yayi dazan dauke ki daga gidannan karsu halla kamun ke" dago jajayen idonta tayi dasuka kumbura tace

"Yaa moh wlhy ka yarda dani karya sukemun,tun zuwana duniya abun wani be taba bani Sha'awa ba balanta na daukeshi ina zanje da wannan mummunan kazafin,yaune karo na farko dasuka tunkareni da wannan maganar nasan iyakar mutanen dasuka gayawa? Nasan iyakar mutanen dake kallona matsayin barauniya,na tabbatar idan Innah taji sai hawan jinin ta ya tashi" cikin kulawa ya janyo hannun ta yace da ita

"Ba wanda suka taba gayawa,nine suke so su saka Inji na tsaneki sabida haka suka kirani cewar mami na nemana kuma nazo ba wata kwakwarar magana sai gaisuwa da mukayi kisani ko danta data haifa da cikinta bai yarda yasan shiri ne kawai balanta na ni, cewa sukayi dani sun kiranine su bani hakuri akan karyar dakikayi na barin Waya a motana sabida na siya miki wani wai dama kinsaba baka kike,basuda labarin tun washe garin dana siya miki Waya naga motarki ashe me wankin motar acikin block compartment ya sakamun daya ganta,banmiki magana bane sabida already Kinyi wlcm back, so ki daina kuka sabida wanda akayi domin shi bekosan sunayiva,kuma kisani next time dazasuyi kokarin bata Wa zahra na suna kotune zata rabani dasu" Murmushi tamai dukda hawaye bai dena gangarowa daga idonta ba tace

"Yaa moh nagode daka yarda dani,kuma dan Allah kayi hakuri abinda ma" bata rai yai cikin wasa yace

"Bazan hakuraba sai kinmun alkawarin kin daina tsoron Aynah"

"Allah yaa moh zan daina namaka alkawari "

"Yauwa ya zancen samosa na,Nafa cinye wancen zobo nane kullum nakeshan Kofi daya shima yau ze kare gashi yayi dadi sosai" shagwabewa tayi dama zahra badai ruwan hawayeba tace cikin kukan shagwaba

"Nima bazan maka samosar da zobo ba saika dena wahalar dani" dariya yayi sosai cikin dariyar yace

"Nashiga uku menayi na wahalar dake cutynah" shagwabewa takumayi

"Toba kai bane ba,kake fushi dani kullum bana bacci har abinci ma bana iyaci sabida kana fushi dani" zaro ido yayi da wasa

"Da gaske bakya cin abinci sabida ina fushi dake cutyna?" Turo baki tayi tace

"Saina tasa abincin agaba nayita tunanin ka banasan ci"

"Lallai kuwa yaa moh bai kyauta,maza tashi muje nasiya miki kazar KFC ita kadai zata miki maganin yunwar kwanaki uku" maqe kafada tayi tace

"Ni bazanjeba Nima fushi nake" ware hannayenshi yayi ya daga kafadunshi alamar ko'a jikina yace

"Idan bakizo muntafiba kwana uku zanyi banci abinci ba,sabida haka ki zaba ko ki tashi ki shirya muje kokuma naje yajin aikin cin abinci tsaf zan daka barkono wlhy" Murmushi tayi tace

"Yi hakuri zani,bara na sauya kaya" "dadai zaifi miki yace cikin wasa...A hanya suka hadu da Aynah zasu Shiga mota,tace cikin tsawa

" Zahra zonan maza,gidan ubanwa zakije?" Dama zahran yauta shaqa bata taba fusata ba irin yau kannewa tayi ta tattaro masifar ta gashi dama indai bakar magana ne zahra an gwanance tace

"Me kuma na zagina kamar wata uwata,zani insiyo miki Lipton dinki dana sata mana,nida yaa moh" fusata tayi tayo kanta,,zata mareta,aikuwa Zahra tarike hannun tace

"Aunty Aynah idan Babba beji kunyar hawan jakiba ba abinda zai hana jaki ya nanashi da kasa,wlhy ban miki komaiba idan kika mareni Nima saina tsinka miki mari tunda naga abin naki haukae" tana kaiwa nan ta cillar da hannun,tazaga tashige motar abinta ta dare gidan gaba tayi fuska😎,haukace Wa Aynah tayi tashiga surfa ashar tna cewa "wlhy a kunnen mami saina fada mata komai banza karuwa" ba wanda ya kulata acikin su sukayiwa motar wuta suka bar harabar gidan...

Mom nuaim
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

*salam ina mai bawa dinbin masoyana hakuri akan rashin amsa dukkanin saqonninku,dan Allah Kuyi hakuri koda nake hawa message's sunyi yawa kuma bazan yiwa kowa reply ba,sannan kuma masu cewa na baku daga farko Kuyi hakuri bazan iya bin duka numbobin kuba kowa na bashi amma dan Allah idan nabaki kikaji wata na nema ki bata*

11
Da Murmushi ya mayarda dubanshi zuwa gareta yace

"That's my little cute,nafisanki da haka amma banasan naga kina tsoro saikace ba mace ba,idan kina haka idan me mata yazo neman aurenki sai naji tsoron bada ke ai" Dariya sosai tayi dajin wannan zancen ,shikam ma be taba ganinta tana wannan dariyar ba,sosai ta bashi sha'awa ,kallonshi tayi tace

"Yaa moh Allah kiyayeni da auren me mata,ninan kajira kaga mijin dazan aurah,kyakyawan saurayi ajin farko kuma bare taba yimun kishiyaba" mayadda hankalinshi yayi akan titi yace cikin dakakkiyar murya

"Bari muje gidansu budurwata taga babbar kanwata,ina mai tabbatar miki idan kika ganta saikin suma,yarinyar karshece wurin kyau" shiru tayi haka kurun bataji dadin maganar ba,dan waigowa yayi ya kalleta adaidai lokacin da yake parking harabar wurin yace da Murmushi dauke a fuskar sa

"Cutest zahra na,yadai kin bata rai?" Fuskar ta tamkar zatayi kuka tace

"Ba komai meka ganine?" Dan dariya yayi yace

"Kalli fuskar ta wai taji haushi nace budurwa ta,Toni wasa nake inada wata budurwa ne data wuceki?" Murmushin ta ta fadada tace

"Ni dama bance inayiba akai kasuwa"
"Kasuwar kenan ai zahra,Ba gashi harkin kwasaba,kinga banasan yanga idanfa bayaso kinga wata kyakyawar Yarinya yanzunnan zanje wurinta, turo baki tayi ta juya fuska tace cikin shagwaba

" Allah yaa Muhammad banaso" fitowa yayi daga motar yace

"Tun dake hawayen ki a ido suke ba wuya sun sauka,fito muje sarakan kishi" tana turo baki tace

"Allah ni ka dena banaso" koda aka kawo kazar da drink saita gagara ci,gani take tamkar da gaske yake yanada budurwar,sarai ya ganota,sai kallonta yayi yace

"Baby Zahrah, waikinsan ko yaa moh yana masifar sanki,Allah dazaki yadda da aurarki kawai zanyi" Banza tamishi,yakuma cewa

"Wannan kazar taficemun arai kwata kwata" kallonshi tai

"Mesa yafita aranka?"marairaicewa yayi abin tausayi yace

" Toba miss dimples bace bata sona,Ashe dama nikadai nake haukana ke bakimasan inayiba" Murmushi nta mai kara mata kyau tayi tace

"Ita da kanta tace dakai bata sanka? Wama zatace bakasan kyakyawan balarabe kamar ka?" Zaro ido yayi cikin murna yace

"Da gaske miss dimples kina sona?" Hannayenta ta saka duka biyu ta rufe fuskar tana dariya,kan wani yayi magana acikin su wayarta tafara ringin,mami ce ,cikin faduwar gaba ta kalleshi

"Ya moh Mami ce tsoro nakeji"

"Tsoron kuma kin fara ko,laifin me kikai ki daga mana" dagawa tayi tayi sallama

"Mintuna biyar nabaki wlhy kidawo cikin gidannan" ta kashe wayarta

"Yaa moh kaji mami wai mintuna biyar tabani indawo gida" Murmushi yayi
Chapter 6 · 0% Book details