← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma ai ita fully dimplelated kake kiranta ni kuwa dimples kuma nafison natan" dariya yayi har fararen haqoranshi suka bayyana sannan yace yana mai kallon su Ummie rilwan

"Kujifa wani rigima wai na zaran takeso,itafa both side na chicks nata lobawa suke koda batai dariya ba keko abinci takeci saikin gansu kefa? Idanma zaki dauki picture saikin karkata gefen da dimple din yake kina wani iyayi,sannan zakice nakira fully ace ina karya , AAA kidai tsaya a single dimple din ki yafiyemiki,koya kukace yanmata?" Dama ya khameel akwai barkwanci baya rabo da tsokana shisam idan ba tsokana yayi ba baya jin dadi ga fadar gaskia saidai idan zaka mutu ka mutu amma idan gaskia ce saiya gaya maka ita,mikewa tayi fuuuuu tana kuka sai dakin maminsu wai zata kai kara...

Mom Nu'aiym
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

03

Koda mahaifiyar Zara ta ganta a jike tasan Aynah ce tamata tamata wannan aikin Jan bakinta tayi ta tsuke dominko tasan zarah ba sanar mata gaskia zatayiba aranta tana masifar tausayawa yar tata a karkashin zuciyarta kuwa tana maijin zafin mahaifin zahra dabai gudu ya barta ba da bata tsinci kanta cikin irin wannan rayuwar ta tozarciba da wulakanci ba....zarah kuwa sauya kaya ta kuma yi tafice daga dakin zuwa garden acan ta dare kan lilo ta rufe idonta tana turawa a hankali a sannu take tsotsar alawar lollipop dake bakinta tana tunanin rayuwa,"sai yaushene zan samu yancin kaina? Sai yaushe zan daina fuskantar dozarci da wulakancin da Aynah kemun agaban mutane? Ada ina daukar ba komai bane tunda acikin gidane amma a yanzu na fahimci kowane lokaci zuciyana zai bugawa domin kuwa bazan lamunci tozarci a cikin skul ba,da inada iko dana janyo sauran shekara dayan daya ragewa Aunty Aynah a makarantar tayi ta kammala ta bani wuri konasha iska,ina level 1 amma kowa yagama sanina kasancewar agaban kowa tozartani ake" ahaka tayita zancen zuci tana saqe saqe aranta,shi kuwa mutuwar tsaye yayi ganin wannan kyakyawar halittar agabanshi aranshi yace wannan kuma wacece tunda nake zuwa anan gidan bantaba ganin taba a fili kuma sai cewa yayi

"Hasbunallahu Wa ni'imal wakeel,tsarki ya tabbatarwa maqagin Wanan santaleliyar yarinyar" itakamma batasan dashiba saiji tayi tamkar ammata tsaye aka koda tabude idonta idanunsu sukayi karo da juna da sauri ta sadda kanta kasa ta sauko daga Sama lilon ta zube kasa tace dashi

"Sannu ya Muhammad ina wuni"

"Lapia" ya amsa a takaice yana mamakin ina tasanshi ita kuwa da sauri tabar wurin kasancewar Aynah ta dade dayi mata gargadi a kanshi cewar karta kuskura tabari idonta da nashi su hadu,a lissafinta kuwa yanzu kusan watanni bakwai da dawowarshi kuma duk ranar juma'a saiyazo gidan amma basu taba haduwa ga daga ba sai yau,ita ta sanshi kuma tanajin sunanshi yaron Abokin daddynsu ne dan gidan senate president....kai tsaye juyawa yayi wurin sashen kameel dama can ya nufa ya Shiga palorn da sallamar shi suka gaisa sannan suka Shiga hirar duniya

"Kameel Wata Yarinya nagani hadaddiya a garden kasan Allah ko'a turai bantaba haduwa da yarinyar data kaita kyauba kaga dimples kuwa? Lollipop take tsotsa amma na rantse maka magana sukeyi,kuma abin mamaki saita gaidani kuma hartasan sunana" dariya kameel yayi yace

"Choo yau Allah ya nuna mun mutumina ya kamu a hannu wlhy kabi a hankali kanwatace gidannan take saika fara kamun kafa a wurina" Murmushi yae yashafi sumar kanshi sannan yace

"Ina duk fadin gidannan Aynah kadai ce mace"

"Yarda daddy ya haifaba amma ko miss dimples a gidannan aka haifeta ai,baka dai Santa bane kuma itama sunan daddy take amfani da and yanzu take base level one tana karantar pure English" shiru yadanyi kanya tabe baki yace Allah ya kyauta" kan wani yakuma magana saiga Aynah ta fado dakin Bako sallama a tsatsaye ta gaidasu sannan cikin karairaya ta mayarda dubanta zuwaga Mooh tace

"Tace yaa mooh Ashe kazo shine ba baka Shiga ciki mungaisa ba" wani kallo yamata na raini shisam ya raina tarbiyar yarinyar ya furta cikin murya a makale

"Dama su mami nake zuwa gaisarwa kuma kameel yasaba rakani kokin saba gani nashiga kaina tsaye" Murmushi tayi cikin Kawar da bacin ranta ta furta
"Muje na rakaka to" bayason ya bata kunya dolenshi ya mike yace da kameel

"Kasameni acan coz I'm not coming back here"

"Sure bro yanzu ba jimawa zanzo" suka fita atare ya kalleta da Wata muguwar Shiga ilahirin jikinta a bude yake ya furta

"Ya akayi kikasan nazo?" Murmushi tayi akaro na barkatai tace

"Ina zuwa zan Shiga mota naji kanshin turarenka saikuma naga bakuwar mota a waje tunda baka cikin gida nayi tunanin kana gun yaa kameel" gyada kai kawai yayi damashi bai fiya San surutu ba,a hanyarsu tashi ga main house sukaci karo da zarah,ta rabesu zata wuce Aynah ta kwallah mata tsawa

"Ke zarah zonan" da sauri jikinta na rawa ta karasa wurinta tace

"Gani Aunty Aynah"

"Dan uwarki ke baki iya gaisuwa ba ko bakya ganin mutanene?" Murya na rawa tace

"Dazunnan muka hadu a garden kuma mungaisa" wani mugun kallo ta wurga mata

"Garin ya kuka hadu a garden dan uwarki ?" Riki cewa tayi

"Nifa Aunty Aynah Allah zuwa kurun nayi gun lilo saimuka hadu kiyi hakuri"

"Kinsandai yanda mukayi dake ko? Kuma kinsan bana sauya hukunci wlhy saina wulakantaki banza jaka mara galihu" kukane ya kwacewa zarah ta juya da gudunta zuwa cikin bangarensu na yan aiki,yayinda Mooh yayi tsaye yana kallon wannan rashin tarbiyar da rashin sanin mutincin dan Adam,a kufule yace

"Me haka Aynah meta miki kuma? Bakyajin kunya kike irin wannan zagin kina mace wlhy kin bani kunya" yana gama fadar haka yajuya yabarta gun a tsaye......
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutiena zarah Bukar.

*Nasan nayi late amma amun afuwa,ina tayaki murnar zagayowar ranar haihuwar ki Meenah parrot Allah ya Albarkaci ratuwarki yasanya kikai shekaru dubu lolx😆 wishing you many more fruitful years ahead.
04
Ita kuwa ganin haka tabi bayan zarah,a dakin su ta sameta ta Shiga bako sallama,ninke kaya ta tarar tanayi ta wurga mata Wata harara sannan tace cikin isa

"Zara dan uwarki ya mukai dake?" Da sauri zaran ta dago ta kalleta ganin mahaifiyarta na wurin amma ba kunya ta zageta,kawai saita sadda kanta kasa batace da ita komai ba,

"Dan babarki badake nake magana ba?" A hankali ta kuma dagowa ta kalleta ido cikin ido ta furta

"Aunty Aynah kiyi hakuri,kinga Nifa banma taba ganin shi ba sai yau,yaudin ma it was a coincidence" cakumo wuyan rigarta tayi ta miqar da ita tsaye ta wanketa da kyakyawan mari sannan ta tura ta sanda ta fadi kasa

"Dan kaniyarki nizaki gayawa wani coincidence,ganganci kikai wlhy na Shiga huru Mina kuma zakisha mamaki na" tana gama fadar haka tayi waje a fusace...kallon nutsuwa mahaifiyarta ta mata sannan tace cikin sanyin murya

"Zahra menene kuma ya hadaki da Ayna'u yanzu kuma wanene kuke magana a kanshi?" Hawayen datake tarewa ne ya gangaro daga idonta yafara zarya saman lapiyayyen kuncinta

"Allah innah niba ruwana da wannan yaa Muhammad d'in,tun sanda nake gyarawa umminsu daki naji suna zancen wai yaron aminin daddy zai dawo daga America yafi shekaru bakwai acan,sannan dama yakan zo nan gidan tunkan yawuce shine suke tunanin idan yadawo zai rika zuwa musu,shine fa itada umminsu suka ce dani koda Sune suka sakani aiki wai ko daddy ne yasaka ni indai na ganshi kar inje wurin kar in kuskura har abada fuskana ya hadu da nashi,ni bansan ko wani mugun Abu ne a fuskana da ake gudu wasu su ganniba,kumafa shi bema sanniba nice nake yawan hangoshi idan yazo kuma nakanji suna fadar sunan shi yaa mooh,yau dinma ina garden yasameni a lilo kuma gaisawa kurun mukayi na wuce,yanzu kuma na kammala girki zan shigo nan muka hadu suna tare shine fa take fada wai naki ingaidashi shine nace da ita ai mun gaisa shine fa wai a ina? Taketa zagina tun a gabanshi nai taho wana shine ta biyoni" Murmushi Innah tayi sannan tace

"Ai wannan ba abin kuka bane ki barsu da halinsu sannan dan Allah wannan yaron ki guji duk inda zaku had'u ke idan ma kun had'u ki dauke kanki ma'ana kidaina nuna kinma ganshi balantana Ku gaisa,indai wannan Muhammad dinne juma'a kawai yake zuwa,saboda haka duk wani aiki dakike ranar juma'a na daukeshi akanki idan kin dawo makaranta da wuri kamar yau ki zauna anan shashin karki fita kokiyi karatu kokuma kiyi kallon ki tunda ba abinda kika rasa anan din" gydawa mahaifiyarta tata kai tayi sannan ta kwanta rub da ciki ta lumshe ido,sosai tabawa mahaifiyarta tausayi,tasani tun tasowar zarah take cikin kyara da tsangwama a hannun Aynah da mahaifi yarta,Haj Asabe ne kawai ke mata da sauqi sai ko daddy dake gani tamkar shine ya haifeta....

Koda Aynah tashiga gida kasa nutsuwa tayi sai zirga zirga takeyi so takeyi kawai ta wahaladda zarah can dabara ta fado mata da sauri ta fito daga side nasu zuwa nasu Zarah,bako sallama tafada ko kallon innah batayi ba balantana ayi zancen gaisuwa tace da Zara

"Zarah zo sako hijabinki aikenki zanyi gidansu khairi" ba musu ta dauko hijabin tace da mamanta "Innah zanje indawo" to kawai tace ta kawarda kanta domin kuwa tasan wannan aikar sam ba Alkhairi bace.

"Zuwa zakiyi gidansu khairi kice da ita nace tabaki dan kwalin kayana dana manta agidansu ranar yau dasu nakeso nayi amfani" kallon sararin zamaniya tayi yanda hadari ya hadu sannan kamar zatayi kuka tace

"Aunty Aynah Idi ne ze kaini ko lado?" Wani mugun kallo ta wurga mata sannan tace

"Ubanwa kika gani ciki Idi da ladon ina duk basa nan? Mtsww ungo kudin adaidaita maza kije ki dawo mintuna 30 na baki" mika hannu tayi tamkar batason karba ta karbi kudin sannan ta wuce tana mai rokon Allah yasa kar ruwa yamata duka domin kuwa zazzabi ne zai biyo baya mai zafi ga kuma tanada test ranar Monday... Bata wani sha wahala ba wurin samun abin hawa harta isa unguwar wuse zone 2,kallon dan adaidaitan tayi bayan tabiyashi tace dashi
Chapter 2 · 0% Book details