← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kizo muci mana nafisansa da zafinsa" marairaicewa tayi tace "Nifa na koshi" "koshi kaman ya danke fa nasiya kumama me kikaci?" Shiru tayi yace "maza zokici ko yanzunnan mu bata dake"
Sak kowa tayi tafara cin kifin tamkar zata kurma ihu,Koda suka kammala da gudunta ta ruga toilet,sosai tayi amai tamkar ba gobe,rike yake da ita harta kammala,heater ya kunna ya mata wanka sannan ya dawo da ita,shirin kwanciya sukayi ya rungume abarsa yana jijjigata tamkar wata jinjira sosai yakejin tausayi nta,gani yake tamkar sabida ya tilastatane yasanyata amai..."washe gari da suka tashi chips yamusu ordering da kuma beef kebab,sosai taci abincin,amma kuma warin tafarnuwar da ke cikin naman ya hanata sakat,hankalinta be kwanta ba sanda ta Harar da abincin duka,kusa kwanaki hudu kenan dukfa abinda zahra taci seta Harar,har yakai bata iyacin abincin,sosai moh ya tsorata dakanshi yamata pregnancy test yaga positive, kasa yadda yayi ya kwasheta zuwa asibiti mamakine yakamshi jin cewar watannin cikin uku ba sati daya meaning kenan tun saduwarsu ta farko cikin yashiga,sosai yayi murna daganan yakira momy,sanar mata yayi sanan yaroketa akan bayasan kowa ya sani,kuma ta gayawa su Innah yanajin kunya....sosai zahrah ke samun kulawa awurin moh abin har mamaki yake bata hatta wanka shine yake mata da kanshi.

Mom nuaiym
[9/20, 9:16 PM] billygaladanchi: 😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

33
Koda momy ta kira Innah usai ta sanar mata batayi mamaki ba,ta kula da hakan tun sanda sukaje gidanta,Murmushi tayi tace

"Au wainikam Haj Asabe baki kulaba tun ranar da mukaje gidanta? Ai sarai na kula,nazata boye boye take mana,Ashe itama bata saniba?" Cikin dariya momy tace "nadai kula da yawan kwanciyar ta kafin Ku wuce se kuma tadan abinci,Ashe jikana ke shirin zuwa" dariya sukayi daga nan sukayi wa juna sallamah...

Kwance zahrah take saman jikin moh tana narka shagwaba akan lallai saitasha ice cream

"Kinga zahrah bazeyi kina mura na dauki abu me ice ba nabaki,ke bakya tsoron taba lapiyan jikinki dana babynki?" Kara narkewa tayi tasaka kuka

"Allah ni yaa Muhammad ice cream kadai ne bashida karni,idan bashiba bazan ci komaiba" ganin yayita rarrashinta taki ya sanya ya daura mata kanta saman pillow ya juya mata baya, ganin haka yasanya ta saka masa kuka wiwi Banza ya mata hakan ya sanya ta tashi taje parlor ganinfa takusan 30 mnt zaune be zoba kuma ga yunwa yanaji ya sanya ta neje kitchen neman abinci, indomie ta dafa dayake tasu soaking ma kawai ya wadatar ta soya kwaya hudu,zuwa tayi parlor ta zauna ta cinyesu tatas,ta tashi ta nufi fridge ta dauko fresh milk da kullum shi take sha,ta kwankwada sannan ta mimmike akan kujera,bata dade da kwanciya ba ta ji zuciyarta na tashi,da gudu ta ruga wurin wash hand base dake wurin dining ta fara lailayo amai,dakyar ta samu ya tsagaita jinda tayi kanta na Sara mata yasanya taje ta dauki wani magani da taga moh yazo dashi yace mata na ciwon Kaine ta dauki kwaya biyu tasha,sannan ta rarrafe daki Koda tace baccinshi yake shara harda minshari, matsawa tayi kusa dashi ta kwanta,ba cimawa bacci yayi awon gaba da ita,canfa cikin dare taji mararta na murdawa a hankali,tashi tayi zaune ta kura ma marar tata ido,adu'a tayi sannan ta kwanta wasa wasa fa takasa hakura,can cikin baccin moh yaji tana tadashi mikewa yayi cikin bacci ya rungumota "zahrah na rokeki Ki dena zancen shan ice cream dinnan,bayanda za'ayi na dauki abinda nasan ze ciyar dake na baki kisha" yarfe hannayenta tayi duka biyu tace cikin murya me nuna alamar tanashan azaba

"Yaa moh marana da bayana kemun ciwo" saketa yayi gaje ya kunna fitilan dakin,ya dawo ya riketa "menene yasamu marar haka kuma?" Rike mai hannu tai sosai "yaa moh nasani wannan aman dana yine ya janyomun har maganin dakakesha na ciwon kai nasha kwaya biyu amma kan be denaba gashi marana ya kama" gwalo ido yayi waje yace

"Kina haukane waya sanar miki Masu ciki suna sha? Kumama ko ninan kwaya daya nake sha" rike hannun shi tayi sosai, tace dashi bara nace toilet nayi fitsari kaji" mikar da itan dazeyi yaga jini nabin kafafunta kara ya kwallah yace cikin rudu "Nashiga uku Fateemah ur bleeding fa" kallon kasanta tayi ta kwallah kara,gigicewa ya kwasheta zuwa asibiti, da da sauri suka karb'eta aka Hau kanta....wanan maganin daine yaso barar mata da ciki threatened abortion ne dole aka barta on bedrest abinka da bature na Kusan four month scanning nasu ya nuna musu yarane fiye da biyu acikin cikinta (lol Ummee Kay wannan ne fatan Ki dama anbaki) murna awurin moh ba'a magana da haka ya sanya yayi waya yasaka aka mata differing na session nata a skul,taci gaba da rainon cikinta cikeda kulawa a hospital...

*Bayan wata hudu*

Bayanda ba'ayi da daddy ba akan ya bari zahra ta haihu a London yaki,acewar sa dolene ta dawo wurin danginta, Muhammad dama dayayi watanni biyu acan Ummie ta matsa dole ya dawo Nigeria kuma ba wanda yasan zahra Nada ciki,daga sucan London se momy da daddy,da kanshi yaje London kwananshi shida suka juyo a tare,shi sanda yaga cikin zahra ma wai ace watanninshi bakwai abinma tsoro ya bashi sosai dakyar take daga kafa,dukda kasancewar tayi bulbul tayi fari kal alamar Hutu hakan be sanya ka kasa lura cewar a wahale take da cikin nan ba,jirgima cewa sukayi ya kai 9 month bazasu dauketa ba dakyar suka dauko ta,ya sanar wa momy isowarsu kuma dama can ya roketa akan zasu sauka gidanta su ci abinci kasancewar Aynah nada shigar ciki batada lapia bazata iyaba tace,hakan kuwa akayi suna dawowa kai tsaye gidanta suka nufa...mamaki ne ya Ummie ganin zahra da ciki,ga wani mugun faduwar gaba daya sameta ganin cikinan ko'a mafarki batayi tsammanin hakan ba,kana ganin yanda take yake idan kasanta kasan cewar ba'a hayyacinta take ba sam,

"Au Babana dama zahran cikine da ita shine baka sanarmun ba,har yayi tsufa haka,watanninshi nawa ne?" Kallon ta yayi cikeda jin kunya yace "watanninshi bakwai Ummie harya dan gota ma" shiru Ummie tayi tana ayyanah kenan zahra ko kwakwaran sati biyu ba tayiba tasamu ciki?" Ganin kar ayi wani tunanin yasanya ta sassaita nutsuwar ta tafara fada

"Amma lallai Muhammad karaina mutane Wato banida muhimmancin dazaka sanarmun matarka nada ciki haryayi tsufa haka?" Sosa kai yahau bata hakuri dakyar ta hakura daganan kuma tafara ina zan saka da zahra,har mamaki abin ya Masu matuka,se gamma suka nufi gidansu, kai tsaye par dinsu suka nufa zahra ta tsala wanka ta saka karamar riga ta nufi kitchen acewar ta samosa zatayi idan ba shi tayiba da matsala shikadaine abincin da zataci ta koshi gata da mugun cin tsiya,tana daga kitchen tajiyo muryar Aynah

"Ina juyar gidannan,bakida aiki se cin tsiya da gantsara katon kashi Kizo Ki gani,ta Allah bataki ba ko yanzu kuwa ga ciki ajikina" mamakin kalamanta ne ya fito da Muhammad daga dakin kasa yayi daidai da fitowar zahra ma daga kitchen, dama ko tayi alkawarin bazata kuma bari Aynah taci zarafinta ba dama ta riketa da mugun kazafin data mata,kallon ta tayi kasa da sama batare data gantaba tana kallon bangaren Muhammad ,tace "Baiwar Allah lapiya kika shigomin gida ba sallama kuma kina mun hargowa" juyowa Aynah tayi a fusace ganin zahrah da ciki yasanya tayi turus tana Kallonta ta kasa magana, zuwa zahra tayi tawuce ta taje ta zauna ta dan kishin gida cike da isa tace

"Aynah ban shirya dawowa gidannan domin na tayaki jida matsalarki ba,kisani banida lokacin ki kuma nan gidan ba juya,idan ma ita kikazo yadawa magana Ki kama kanki domin bazan lamunta ba sabida ni gidana ba juya" kasa magana Aynah tayi domin sam an tabbatar mata zahra bazata taba haihuwaba shiyasa bata kawowa kanta ganin hakan ba,Muhammad ne yazo gab da zahra ya sunkuyo daidai fuskarta ya sanya hannu ya dago fuskarta yace "Baby cute ya mukayi dake,ban sanar miki ba'a kula kare idan yana haushi ba? Shine zesa yayi yunkurin cizonka ai,beside banasan kikoya babyna rigima tunkan yazo duniya" Murmushi tayi tasakala hannunta awuyanshi tace dashi cikin rada "Kayi hakuri na dena" tsaki Aynah taja "Dadin abin kanwata shegiya tayi cikin narigata kuma wlhy ko kinaso ko bakya so a gidannan sai kinga kwaina" Banza sukayi mata tagaji da jinininta tafice cikin kunan rai tana mamakin yanda akayi zahra tasamu ciki.

*Bayan wata biyu*

Sosai cikin Zahra yakama yayi wani irin kato, bakaramin tsoro da tausayi zata bakaba idan kaga tsininshi dakyar take tafiya,zaune suke itada moh ta dage se cin kaida kafa takeyi na kaza,dariyarta yakeyi sosai "Haba cute yanzu a dage adafa kaza wai kizauna kina cin kai da kafa tsabar rashin sani dad'i" kallonshi tayi zatayi magana sai sallamar safiyyah taji yar aikin Aynah,durkusa wa tayi tace "Yaa Muhammad Aunty Aynah batada lapia sosai" zabura yayi yace muje na dubata" jiki na rawa ya kwasheta zuwa asibiti,Koda suka isa cikin yarigada ya gama fita,Dr Jamal kuwa kallon moh yayi yace

"Muhammad a gaskia dawuyane idan matarka zata kara conceiving ba,sabida maganin data sha na zubar da ciki ya taba mahaifarta Koda ta dauki cikin bazata iya rikewa ba" nisawa yayi yace "Dr kanta tayiwa nidai fatana Allah ya sauki zahrah lapiaya"

*Bayan kwana biyu*

Sak kowa zahrah keyi dakyar daga matattakalar kofar gidanta,driver ne ze kaita ANC tunda safe,ganin kawai tayi aynah tayo kanta iya karfinta,"narantse da Allah baki isa ki haife wannan cikinba bayan kin kassaramun tawa mahaifar" kan zahrah tayi wani yunkurin tuni ta hankadota ta fadi a kife take jini ya balle mata,gashi moh bayanan,ta dare bayanta tahau dukanta driver ne ya rugo domin ya ceceta...

Mom nuaiym ce
[9/21, 8:41 PM] billygaladanchi: 😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

34

Dagowa ta wanke driver din da wani lapiyayyan mari "kai dan ubanka ina ruwanka da sha'anina,dahar zakayi matsayin da zaka tabani" a fusace ya kalleta
Chapter 24 · 0% Book details