← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dinnan na fahimci bakisan mutunciba wlhy,angaya miki neman halal haukane da zaki taka kowa yanda kikeso,sabida nidinnn sakaraine sena kyaleki ki hallaka baiwar Allah kina ganin mace da tsohon ciki haka kimata wanan tsabar rashin imani,wlhy kika kuma tabata sedai na kare a prison dukan tsiya zan miki" ja tayi da baya ganin da gaske yake ya kwallawa yar aikin zahra kira,ita ta tayashi dagata suka kaita mota,national hospital suka nufa da ita inda take ANC Koda suka isa tana bleeding batamasan inda kanta yakeba,sanda suka karbeta sannan Aminu driver ya kira moh,kai tsaye ya sanar masa meya faru da zahra,a rude moh ya kamo hanya,sanin da akai masa a asibitin sabida yakanzo yamusu aiki yasanya besha wahala ba wurin Shiga wurin ta,Dr Zainab dake duba zahrah ya kalla hankali atashe yace

"Dr Zainab dan Allah sanar dani menene matsalar?" Sosai ya bata tausayi tace cikin raunin murya "Look Dr Muhammad Bafa wani abin bane ba,kurun buguwa ne ya sanya take bleeding, se kuma labor daya taso b4 Edd nata,amma ba matsala bane ba kuma kasani coz dama gobe ne Edd dinta" kallon zahra yayi daketa faman yarfe hannaye cikin tsananin azaba,yace "Dr Zainab ki duba mana how many cm take plss" juyawa tayi taduba sannan tace "5 cm Dr I'm sure she will soon deliver plss dnt worry my self much" nisawa yayi yaje ya rike hannunta,kafin mintuna arba'in zahra ta soma pushing iya karfinta,batare da wata wahala ba,ta sunkuco yaranta har uku maza biyu mace daya,ganinfa tana pushing yasanya moh da kanshi ya duba,kwallawa Dr Zainab kira yayi dataje tana takan yaran tabaiwa nurse's yaran tazo da kugu

"Dr Zainab this is unbelievable another baby is coming" karaso wa tayi ta saka hannunta kallonshi tayi tace "seriously Dr Muhammad, bt the servix is too thick still" Kallonta yace ta matsa Koda ya duba hakanne kuwa,kallonta yayi yace

"Dr zee zahra zatasha wahala fa,Nima naji hakan sam bazan iya tsayawa ba tausayinta nakeji,bara naje waje" harya juya ta riko hannunshi ta kura mai ido kurun batayi magana ba da wowa yayi ya dada rike hannun cikin dakiya yace

"Zahra na plss hold your self together trust me u can make it" Murmushi karfin hali tamasa tace "yaa moh please stay still I can feel that the baby is on the way too" kan yayi magana ta kankameshi numfashi daya tayi ta kuma wuntsilo yarta daya amma tafi kowa kanka nta acikin jariran kuma jinjirar batayi kukaba ganin anta dukanta taqi kokawa yasanya akayi da ita ICBU domin bata taimakon gaggawa atake aka daura mata oxygen lokaci daya kuwa ta cancara kara,murna awurin moh ba'a magana,momy kuwa tarasa wa zata fara dauka acikin jariran tsabar mamaki bata zata zahra zata haifi yara har huduba kai ko twins bata zata zata haifaba,dukta wani rikice,dama Innah usai sun iso tun jiya waya kurun tamusu inda kowa mamaki yake.(gareku readers nasan zakuce karya nake wai nace an haifa yara hudu to haka salon labarin yake,kuma Ku sani haka Allah ke ikon shi yanda yaso). Zahra kam ba kanta domin tun anan Dr Zainab ta kula mahaifar ta tayi rauni,takuma sanar da mijinta cewar lallai a dauki mata sabida mahaifar tasha wuya,kunnen moh su fareedah sai ihu suke suna daukar hotuna da yaran guda uku kasancewa r daya nakan oxygen suna famar posting a social media....Aynah na zaune ba abinda tafi bukatar ji irin asanar mata mutuwar zahrah tare da cikinta,amma har azahar shiru kakeji tana nan zaune tana saqe saqe taji alamar shigowar message a wayarta da sauri ta dauko moh ne,ga abinda ya rubuta

"Aynah ta Allah ba takiba,zahra ta sauka lapia and for ur information yara har hudu biyu maza biyu mata" dafe kirji tayi ta kwallah kara,karyane wlhy karya yake yace wai zahra ta haifi yara har hudu" sai haukanta take ita kadai,a rude ta zari key na motar tayi gidan su ta sanar wa maminta wannan mugun labarin.

Sanda su cute suka kwana asibiti washe gari aka sallamosu,kai tsaye gidanta aka wuce da ita,wannan tirjewar moh ne shi a dole yaranshi baze yadda su mai nisaba,zahra dakyar ake tafiya ansha stitches, gida momy ta wuce akan zata hado kayan gyaran nono da na sha'anin biki,itada yan aikin ta ne kawai sai Muhammad, yara biyu sai ihun yunwa suke zahra wai ita bazata iya fito da nononta ba kunya takeji,abu fa kamar wasa sanda Muhammad ya daka mata tsawa yazo ya zuge zip dama na gabane ya Ciro nonon,rikon yaro ma batasan yazatyiba dakyar sukayita shirme ita dashi dakyar suka samu yaran suka sha,kuma gashi ba yawan ruwan nono,dan kanshi yaje ya lalubo madarar yara aka Shiga basu,matan abin mamaki sak Zahra sukayo yayinda maza ke matukar kamada moh dukkansu, Momyn moh munkasa gane kanta amma azahiri bata farin cikin wannan haihuwar yake kurun takeyi...kallon zahra moh yayi yana rungume da jarirai biyu maza ya kwantar dasu sannan ya lalubo hannunta "Thank you so very much fateemah,thanks for giving the light of my life,na dinga faranta miki kenan har karshen rayuwarmu,kuma bazan dena wa Allah godiya ba har na koma agareshi" murmushin dai kurun tamasa,ta langwabe kai cikeda shagwaba tace

"Yaa Muhammad dan Allah kace da momy su dena sakani yin wannan sit bath din,karkaso kaji zafin dake akwai kuma bakaga tafasasshen ruwan dasuke mun wanka dashi ba" matsowa yayi yaja mata kuncinta daya tadanyi kara

"Neman lapia nki ake bakya ganin kinada stitches da yawa,ni baxan hanasu gasa kiba,gwara ki warke da yawa nafara missing Matana" maqe kafada tayi "Allah nikam yaa Muhammad Bazan karaba" dariya yayi yabar mata dakin...

*Ranar suna*

Sosai aka wulakanta dala a wannan bikin yara sukaci matan dayar Aisha( sunan momy taci) sai dayar kuma maryama (sunan mahaifiyar moh) mazan kuwa Abdurrahman da Abdurrahim,kowa hankalinshi na wurin taron sunan,lokacin da akazo daukar hotone hankula suka tashi domin kuwa karamar jaririyar wacce taci sunan momy Wato Aisha da aka sakayawa suna Lana an nemeta an rasa,abufa kamar wasa annemi yar mutane an rasa har karfe goman dare,gashi duk a cikin yadan zahrah tafi Santa sai kuka take tamkar zatayi hauka....

Mom nuaim
[9/23, 5:58 PM] billygaladanchi: 😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

Wannan shafin na sadaukar dashi ne gareki sweetest in-law Ummie rilwan Allah ya nuna mana ranar auren ki da bro Bilyameen ranar akwai Ghana dance hhhhhh....

35

Zahrah fa duk ta rikice yan biki duksun fashe kowa da abinda yake tofawa,tashin hankalin zahra ya karu ne ganin fa ba labarin yarta har gashi Tara ta gota,kuka sosai takeyi,ba karamun San lana takeyi ba,rungume take ajikin moh tana sauke ajiyar zuciya kasancewar tasha kuka,a hankali yake patting bayanta yana Shafa gashin kanta,shi kanshi a rude yake,dagowa tayi cikin kuka tace

"Yaa Muhammad wlhy Nina San Aynah ce,dan Allah muje wlhy ko rokar ta zanyi I will even go down on my kneels just so she could help and bring back my baby" kura mata ido yayi yace

"Baby cute plss mana,wlhy zarki bashida kyau ki kwantar da hankalinki inshaa Allah zamu ganta ne"

"Haba yaa Muhammad yaushe ne idonka ze bude,yaushene kunnuwanka zasu fara sauraran zantukan makiyanka karara,matar da taso kashe ni itace zakace wai ba ita bace? Wanene maqiyinka ko nawa aduk fadin duniyar nan banda Aina? Wlhy bazan yadda ba" daga nan takuma rushewa da kuka ta fada jikinshi....wasa wasa fa har washe gari ba Lana ba labarinta zahrah dukda tayi kumburin ciki lokaci daya ta zabge,yan sanda har gida sukazo bincikensu suka gama suka wuce,Aynah kuwa sai murna take aranta tace saura karashen yaran a kwashe su muga karshen iyayi...

*Bayan kwana biyu*

Shafa'u ce me zaman da jariran ta kwallah wa zahrah kira "Aunty zahrah Kizo da sauri ga Lana a parlor" garin sauri har hada hanya take Koda sukazo suka tarar yar tana kallon sama ta kakafe ido a jikinta wata farar takarda ce,da sauri zahra ta rungume yar tana kuka ta karbe takardar tafara karanta wa kamar haka

*wannan saqone zuwa gareka moh,kacuceni da yawa kuma bazan yafe maka ba,kasani naso hallaka wannan yar sainayi tunanin me jinjirar nan tamun,kuma na tsinci kaina da kasa cutar da ita,ina kaunar yarinyar ka saka aranka,kuma kasani abinda kamun bazan yafe ba har abada* kanta ne ya daure tace aranta bazan yanke hukunci ba na kira wannan da mace ko namiji,amma koma waye akwai wani al'amari Babba a tsakaninshi da moh,nidai Alhamdulillah tunda 'yata ta dawo gareni".kowa yayi farin cikin jin andawo da baby,saidai Muhammad yakasa gane ko waye me wannan saqon dakuma yanda akayi hakan ta kasance koma dai menene ya barwa Allah.

*Bayan wata shida*

Masu Aiki biyu ke kula da yaran kasancewar,zahra na zuwa makaranta,zuwa yanzu zahra ta samu sassauci awurin mahaifiyar Muhammad sosai ba kadan,riritata takeyi tamkar kurjin gwiwa,bataso abinda ya shafi zahran,matsala daya suke fuskanta shine lina,sam yarinyar ta dawo sai kace yar aljanu,bata bacci tun daga ranar da aka dawo da ita bayan an sace ta,haka kuma bata taba yin kuka ba,sai uban shan farce kullum dan yatsanta na'a bakinta tana tsotso idanun kuwa kakkafe kasu farare tas,sannan kuma bata karbar nonon zahra,batashan madara kuma tafi dukkan yaran girma, komai Nisan dare lina Aisha ido biyu take kuma a kakkafe idon suke,moh ya kaita asibitoci ba iyaka an shaida masa lapiyan ta kalau,dukkanin yaran suna wasa da dariya amma ina sam sai kace gunki,gashi moh da zahra sun fi kaunar ta fiya da sauran yaran musamman zahrah,wasu lokutan cikin dare sai zahra ta farka taga yarinyar a zaune hannu a baki tana wangala dariya,amma daga zaran ta tabata sai Yarinya tasha mur kuma abin mamaki hararar ta takeyi,Kokuwa tarikajin surutai a kusa da yar,kamar dai wata aljana,dakewa kawai take tana yin adu'ointa na tsari,dukkanin yaran basa shan nonon dare madara suke sha, kuma ba'a wurinta suke kwana ba,amma sam banda Lana Aisha,bata zama bakuma kuka takeyi ba kawai dai sunce abubuwan ban mamaki yar keyi,da wannan tarokesu su rufa mata asiri subar maganar iya su....
Chapter 25 · 0% Book details