← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sarai nasan zancen zahran sedai ni bashi bane ya kawoni,bazan bari auren Muhammad ya lalata mun harkar siyasa ba dole yar manya ze aura kuma me usuli"

"Yallabai aiko zahra 'yata ce kuma tanada usulinta tunda ita yakeso abashi aurenta kawai" fusata senate president yayi yace

"Kaga shayau naga alama so kake ka mayar dani yaro karami,kasani kobayan raina ban lamun cewa Muhammad auren shegiyaba kuma wlhy kaji na rantse idan baka yadda da aurenan ba saina lalata siyasarka,takarar nan daka fito ko tsaida kai bazan bari ayiba" da sauri daddy ya dago ya kalleshi yace murya na rawa

"Subhanallah yallabai tsakanina dakai aiba wannan dandai auren yarana sai munyi arguing sekace zaku yankatane,na amince muku ko yanzu kukeso a daura auren" Murmushi n mugunta senate present yayi sannan yace

"Zaka yankamun sadaki yanzunnan inbiya shedar anbada auren tabbas tare da alkawarin za'ayi auren komai rintsi sannan kuma nanda wata daya" ba musu ya amince aka biya sadaki naira dubu dari biyar sannan sukai sallama.

  Yaune ranar da aka sallamoh zahrah kamar yadda yau aka bada auren Aynah ga moh,sosai Muhammad kejin faduwar gaba,a daddafe ya rakosu gida ya wuce gidansu,gashi kuma bincike ya nuna zuciyar zahra ta tabu wanda akace aguji bacin ranta,donkuwa abu kalilan ze haifar mata da  bugawar zuciya wanda sai mutuwa.... Mikewa tsaye momy tayi dafe da kirji tana hawaye tace

"A gaskia daddy baka kyautaba so kake na rasa 'yata daya daya tilo kajifa abinda liikitoci sukaci yanzu idan zahra taji me kake tunanin ze faru da ita?"

"Kiyi hakuri Haj Asabe Nima sabida ba yanda zanyine wannan shine tsarin Allah adua kawai zakiyi Allah yazaba mata mafi alkhairi" tana kuka tashige dakinta...

  Murna awurin Aynah ba'a maganar Koda taji wannan batu,part nasu zahra ta wuce bata nan kai tsaye sashin momy ta wuce tashige sashin zahrah, a kwance ta taradda ita tace tana dariya

"Banso kokadan ba'@ zuraki ramin da aka haqa domin keba,farin Cikina daya daya kasance bakin cikin aurena daza'ayi damoh nanda Wata daya ya isa ya karasaki wlhy dama na sanar miki nice agaba,kuma Ki sani jiya jiyanna aka kawota sadaqina da moh,idan ma baki yaddaba nanda Wata daya INDA RANKI KYASHA KALLO" momyce ta daka mata tsawa da gudu tabar sashin...murya na rawa tace da momy

"Mony abinda Aynah ta fada da gaske take" dafa kafadarta tayi tace

"Zahra na Ki daurewa zuciyarki Ki yarda wannan shine tsarin Allah Kici gaba da addu'a Allah yamikk zabi na alkhairi" runtse idonta tayi wasu zafafan hawaye suka Shiga zarya a kuncinta...

  Zaune Muhammad yake durkushe agaban Abbi dinshi da Ummie,Abbi yayi gyaran murya yace

"Muhammad yau dakaina naje na neman maka auren Aynah yar Gidan Muhammad shayau kuma nabiya sadaqi naira dubu dari biyar hade da tsaida raina nanda Wata daya kacal" da sauri ya dago ya kalleshi yace

"Abbi Aynah ko zahra?" Ummie ce ta cafe da cewa

"Narantse maka da girman Allah ban yarje maka kara zuwa wurin wannan zahran ba,kuma ko Waya ka kuma kitanta Allah ya isa,sannan idan baka auri Aynah ba bani bakai har abada.

Mom nuaim ce

[9/11, 9:18 PM] Billy Galadanchi: 😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

   23

Dagowa Abbi yayi ya kalleta yace cikin sigar rarrashi

"Dan Allah D janye wannan Allah ya Isar,Muhammad dinkine fa Baban nai,sarai kuma kinsan halin yaran zamani,kedai tunda ya miki wannan biyayyar kibarshi yaji da daya" nisawa tayi tace

"D muddin ba rabashi mukayi da wannan yarinyar na baze taba hakura da iyaba,sam baze iyaba,nina ga haukan dayayi fa"

"Duk da haka D Ki sassauta masa,yanzu kinga auren nan daza'ayi masa dole ne ya rungumi matarsa ya huta" kallonsu yayi yana hawaye yace

"Abby,Ummie dan Allah karkumin haka,wlhy bazan iya hakura da zahra ba" sosai Ummie tasha mur tace

"Na yarda da zancen cewa ba Allah ya isa ko tsinuwa akan zahra tsakanina dakai amma wlhy Muhammad kaji na rantse kuma Nayi kiran sunanka kai tsaye wlhy ko bayan raina ba Wata kaddarar ba ka furta da bakinka bazaka auri Aynah ba ban yafe makaba duniya da lahira,sannan kuma lallai ne kana zuwa zance awurinta,kar labari ya sameni wai baka zuwa" kura mata ido yayi kan yace

"Allah ya sanya shine mafi Alkhairi garemu baki daya" sannan ya mike yamusu sallama yabar gidan zuciyar shi na tafarfasa....

   Da yamma ya fito cikin Shiga ta Alfarma,kai bakace yana cikin matsananciyar damuwa,sanye ajikinshi T-shirt ce fara qal sai bakin wandon jeans da agogo da takalmi da madibi duka bakake sai sheqi yake yana tashin kamshi shida kanshi yasan ya hadu ba karya, Hadaddiyar motar shi yashige baqa wuluk sannan ya biya ya siyawa zahra kayayyaki na ban mamaki na makulashe sannan ya wuce gidansu kai tsaye,parking yayi a parking space sannan ya fito da ledojin kai tsaye part din momy ya nufa kasancewar yasan zahrah nacan,a hanya ya hadu da Aynah ko Kallonta beba,ita kuwa tasha gabanshi tana wani yauki tana far da ido

"Toni ya moh haka zaka rabeni ka wuce ko gaisawa bazaka bari miyiba?" Kura mata ido kurun yayi sabida a yanda yakejin tsanarta ko magana ma baso yake ya mata ba" ganin yayi shiru tawani narke da shagwabe

"Yaa moh dan Allah kamun magana mana,Karfa ka manta nan da Wata daya zan zamo matarka,idan bamu fahimci juna yanzu ba se yaushe kakeso mu fahimci juna" dukda beso kulata ba amma wannan maganar ta aure da tayi ta mugun kular da shi,ya kalleta a wulakance yace

"Aynah Kisani Kinyi nasarar aurena dazakiyi amma Ki sani wlhy keda farin ciki a gidana har abada,sena gasa miki aya a hannu sena nuna miki kuskuren dakika tafka na Shiga rayuwata sena tabbatar miki dacewar Muhammad ba kalar kibane,wlhy Aynah namiki alkawarin se Kinyi dana sanin zuwanki duniya,se Kinyi dana sanin sanina dakikayi arayuwar Ki har kika auren sena nuna miki cewar nidinnan cikakken namijine kuma namijin duniya,sekin gwammacewa kida da karafi,Banza mara Aji me kwadayin abin duniya,narantse da Allah idan baki janye na wuce ba sena wankeki da mari" ba shiri ta matsa tana mamakin kalamanshi,aranta tace nahango iya gaskiyarshi a kwayar idonshi amma yanda nakeso Ummie rilwan tasan bata finiba wlhy Nima me kudin zan aura dolene sena aureshi kota halin Yaya ne wlhy.....

    Momy ya tarar a parlour KALLO daya ta mishi ya bata tausayi tace da me aikinta mariya Ki kaishi parlor din Sama kuma kitayashi da kaya sannan kuma Ki sanarwa zahrah da zuwanshi" godiya yamata yabi bayan yar aikin zuwa saman...Koda ta fito daka ganta kasan bata cikin nutsuwa ga idonta ya mata jajir alamomi sun nuna taci kuka ma'ishi,ga fuskar ma abinka da farar fata ta kumbura tayi pink,kujerar daya zaune ta zauna akai kasancewar 2 sitter ce,tace cikin dishashiyar murya

"Ina wuni yaa moh" kura mata ido yayi yanaso ya fahimci wani abu game da ita,sosai yakeso ya boye mata maganar shi da Aynah saboda condition nata,yakuma fahimci tamkar da abinda ke damunta, amaimakon ya amsa gaisuwarta seya wayance ya janyo Leda ya Ciro mata ice cream daya siyo mata strawberry and blackcurrant flavor  her favorite yace
"Baby zahra ungo alkawarin mu,yau nacika miki kinji" kura masa ido tayi bata karba ba,ya kalleta shima

"Ungo mana ko bashi kokesoba,kinga banasan rigima yau nasiyo miki komai ma har samosa ma coz nasan bakida lapiya kwana biyu bakici ba" ya janyo Leda fito da snacks din ya miko mata,nanma kura mai idon taci gaba dayi batai magana ba,a hargitse yace

"Cute lapiya dai? Kodai wani laipin namiki ban saniba,ehn cute dina?" Nanma Banza tamai kurun dai tafara hawaye zuwa wannan lokacin,sosai fa Muhammad ya rude,tsoron sa daya kaddai zahrah taji zancen neman aurenshi da Aynah yace cikin rikick

"Nashiga uku zahra na kuka kuma,dan Allah kiyi hakuri gayamun menene?" Cikin sheshekar kuka tace

"Yaa Muhammad wai dagaske Aynah da momy sukace wai...wai an kawo aadakinka da ita kuma aure nanda.....sai kawai kuka ya kwace mata me karfi,Kifa kanta tayi saman cinyarshi taci gaba da kukan iya karfinta,har momy dake parlor din kasa tanajiyota kasa zama momy tayi tabar part din gaba daya zuwa part din daddy....abinda yake gudun tasani dari gada ta sani,iya tausayi tabashi tausayi,kasa hanata kukan yayi sanda tayi me isarta tafi mintuna talatin tana kukan dan kanta tayi shiru takuma daga kan nata daga kan cinyarshi ta sake  kuramai idon nata dasuka kara rikida suka kuma kumbura sosai,kunyarata ma yakeji gawani tausayin Kansu dayake ji sosai janyo hannunta yayi yace cikin sigar rarrashi

" zahrah kinsan bakida lapiya ko? Sarai kinsan condition da Dr ya bayar akan ciwonki ko?dan Allah Ki nutsu muyi magana dalla dallah" gyada mai kai tayi tasa mayafinta ta share kwallah daya zubo mata

"Cute Kisani dukkanin abinda yafaru damu mukaddari ne daga Allah Ki sawa zuciyarki hakan shine mafi alkhairi, wlhy banida  masaniyar faduwar hakan sai Daren jiya,fin karfi na akayi ba yadda zanyi...daganan ya kwashe komai ya gaya mata,ya kara dacewar

" cute wlhy Ki kaga ban aure kiba mutuwa na yi Kokuwa tun dama can Allah be kaddara cewar kedinnan matata bace,dan Allah dan Annabi kiyi hakuri wlhy cute ina sanki,ban kaunar ganinki cikin wannan halin Allah ne shaidana" ba shiri tafada jikinshi tasaka wani sabon kukan dakyar ta tsagaita tace dashi bayan ta dago

"Wlhy yaa moh karubuta ka ajiye duk ranar da aka daura aurenka da Aynah ba daniba wannan ranar itace ranar mutuwata,na rantse maka da Allah aduniyar nan kishin danake akanka yafi San danake maka yawa,wannan ya tabbatar min dacewar zallar kishi shine kauna ta zahiri,yaa moh nan" ta nuna masa zuciyarta da hannu "Nanne yakemun wani azababben zafi zafin da bana tunanin ze daina sai ranar daka zamto miji agareni,radadin dana tabbatar ze zama ajalina duk ranar da aka daura aurenka da wata baniba,lallai mutuwa ce kadai zata rabani da wutar dake dad'a ruruwa a girjina idan har ba auramun kai sukayi ba,kaicona da mutuwa bata wuce daniba sanda Nayi dogon suma,watakil dabazan fuskanci wannan mummunan ranar ba me cike da bakin ciki" janyota yayi sosai yanzukam ma hawayen yakeyi yace murya na rawa

"Ya kike kokarin kara rudani my life,plss Ki daina ambaton mutuwarnan,wlhy nasan bazaki mutu ki barni ba,dan Allah zahra kiyi hakuri,indai Allah ya yarda kedinnan matatace kidaina zancen mutuwarnan" kwace jikinta tayi tace
Chapter 15 · 0% Book details