← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mlm dan Allah ko zaka jirani kamayar dani kaga garin akwai hadari kuma sako kawai zan karbo nafito" shiru yadanyi kanya ce gaskia baiwar Allah sauri nakeyi akwai yaran danake daukowa daga islamiyyah kuma lokaci ya wuce sabida shida ta gota kiyi hakuri" ya wuce abin haushin ma koda ta karasa me gadin ke sanar mata dukkanin mutanen gidan sunje Kaduna bayan juma'a kuma sai Sunday zasu dawo,ta tabbatar Aynah tana sane ta mata wannan amma ba komai akwai Allah

Tafiya take amma tarasa abin hawa gashi akwai jayawa tsakanin wuse da maitama tama rasa ina zata saka ranta sannan saiga iska ta taso gadan gadan kankace me wannan am fara tsuga ruwa babu kama hannun yaro rakubewa tayi ajikin wani icce har ruwan yadan tsagaita amma kam ta daku da wannan ruwan gashi har lokacin ruwan be tsayaba yadai rage karfi ne kawai sannan kuma ga magrib tama gota, a hankali take tafiya tana sharar kwallah iska tana kadawa ga ruwa na sauka a hankali sosai take jin sanyi sai rawar sanyi take ga har lokacin ba alamar abin hawa kaiko mutane ma babu a wurin....

A hankali yake tukin kasancewar har yanzu ruwan be tsayaba gashi dama idanun tunna haihuwar shine sai a slow,ya hangota tana rangaji iska sai faman kadata yakeyi sam bazai taba manta wannan fuskar ba yarinyar da aka sanar mai sunanta zarah, da sauri yayi parking ya janyo umbrella ya fito ya nufota ganin wurinta ya nufa yasanya ta kara sauri a tsorace ita bata gane ko waye ba,kara sauri yayi yasha gabanta sannan ya janye lemar daga kanshi zuwa kanta yace

"Zahra lapia dai daga ina kike haka?" Dukda kasancewar sanda suka gaisa lapia kadai yace da ita hakan bai hanata gane muryar shiba da saurinta ta dago ta kalleshi tazube akasa

"Sannu yaa Mooh ina wuni?" Dama moh badai zuciya ba cikin fusata yace

"Me haka dan Allah zahra? Bakisan ciwon kanki bane danla mike maza muje mota" ta tsorata dashi sosai jiki na rawa tace

"Yaa dan Allah karufan asiri Aunty Aynah zata kasheni idan taji cewar nashiga motarka dan San manzon Allah katafi kuma karkace da ita mun hadu" sororo ya tsaya yana kallonta kan yace cikin sanyin murya

"Saidai idan kene da kanki zaki sanr mata mun hadu nifa a gate kawai zan ajiyeki bakya tsoron ki hadu da shashashan gari saisu miki wata illar kinga garin shiru" girgiza kanta tayi tace

"Yaa Muhammad na rokeka daka tafi abinka nasan halin Aunty Aynah tunda ta aikeni dole saita tsaya jirana a gate" durkusawa yayi shima yace cikin sigar rarrashi

"Dan Allah zahra kizo na saukeki gida daganan zuwa maitama ko'a mota saika yi mintuna ashirin bazan iya barinki a nan ba,kalli fa rawar sanyi ma kike" shiru tayi,batada niyyar motsawa shimadin sai yayi yanda tayi yace

"Plss mana zahra dan Allah fa" yafada tamkar zeyi kuka,mikewa tayi ta nufi motar shima yabi bayanta....

Mom Nu'aiym
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

*Allahu Akbar yan uwa Muna barar adu'ar ku,yaune muka samu labarin rasuwar mahaifiyar daya daga cikin writers namu wato feedoh deedoh,Muna rokon duk wanda ya karanta wannan shafin ya taimaka ya mata kulhuwallahu kafa goma sha daya,don neman rahamar Allah agareta,Muna rokon Allah yakai haske kabarinta yakuma bawa iyalanta damu hakurin jure rashin ta*

05

Da sauri ya kashe AC din ya kalleta cikin kulawa ya furta,sannu kinji Zahra ki saki jikinki ba abinda zai faru indai akan Aynah, tokuma Aynah haifana tayi dazatace bazanga wanda nakeso nagani ba? Beside me ma dalilinta na wannan shirmen?" Banza tamishi kawai taci gaba da rawar sanyinta domin kuwa kasancewar ta AS (carrier) yasanya koya akayi ruwa ko sanyi koda batashiga ruwanba saitayi ciwon gabobi wanda har zazzabi yake sakata,jin tayi shiru yasanya ya kalleta takasa koda motsi sai lumshe ido takeyi har cikin kasusuwanta take jin sanyi mai tattare da wani azaba na ratsa ta,hannu yakai yajanye hannunta data dora a kai ta kwallah wata kara

"" Nashiga ukku wayyo Innah hannuna zai karye " rikicewa moh yayi yace cikin Rudy

"Subhanallah hannun ki yana miki ciwo ne?" Amaimakon tabashi ansa sai dada rikicewa tayi

"Yaa moh kakaini wurin Innah na sanyi nakeji sosai dan Allah ka kaini wurin Innah" rasa ma mezeyi yayi da sauri ya tashi motar yayi hanyar metama ita kuwa sai rawar dari take tana kiran Innah, sharara gudu yake tamkar zai tashi Sama lokaci zuwa lokaci yakan maida dubanshi zuwa gareta yana mata sannu,cikin mintuna bakwai ya isa kofar gidansu har lokacin batasan inda zata saka kantaba ,zagowa yayi ya bude mata yace
"fito kishiga ciki sannu kinji" dakyar ta dago ido ta kalleshi cikin murya me nuna alamar awahalce take tace

"Yaa moh bazan iya tashi ba ka taimaka ka kiramun Innah ta dagani" shiyama rasa mezaice,kawai janyo wayarshi yayi yakira kameel,yana dagawa yace

"Kameel zo get din gidanku da sauri plss da matsala Babba" batare da kameel yace komai ba yayi hanyar waje yana karasowa yace dashi

"Motarka ta tsaya ne?" Marairaice fuska yayi tamkar wani karamin yaro yace

"Zarah ce kameel" matsowa yayi dafda motar yace

"Wace zarar kuma menene?" Cikin rashin fahimta ya furta hakan

"Zarar gidan nan mana haduwa nayi da ita a hanyar wuse ruwa ya mata duka sai rangaji take,dakyar ma ta yadda ta biyoni wai dimples zata kashetane idan taganmu tare nikome hakan yake nufi oho,tun ahanya take kukan Innan ta wai jikinta namata ciwo bazata iya tashi ba" wurinta kameel yayi da gudu yana fadin

"Aiko Yaya ruwa ya daki zarah saitayi wannan ciwon,kasanfa Carrier ce kuma suna shan wahalar sanyi sosai kasusuwansu ke ciwo iya ciwo,amma nayi mamakin metajeyi wuse,zarah bata fita kuma da yammanan naganta agida" gyaran tsayuwa moh yayi yace dashi

"A yanda tace dani Aynah ce ta aiketa" kallonta yayi sai murqususu take yace

"Aynah kuma? Ina ta aikeki da yammah haka ina daddy ma ya hanaki fita saida driver?"

"Yaa kameel ka kiramun Innah mutuwa zanyi kuma sanyi nakeji" da sauri ya sungumeta yayi ciki shima ya rufe motar yabisu abaya,a bangaren innar ta sallama sukayi tazo dasauri ta bude kofar parlor din tana ganin yarta tafara kuka tace

"Nashiga uku ni ummulkhairi dama nasan a Rina wlhy,meya sameta kamilu?" Karasawa sukayi ciki dukkansu da sauri ta dauko flask ta juye tafasasshen ruwa ta dauko towel tafara kasa mata gabobi shiru dukkansu sai ihunta duk sanda aka tausa wurin dake mata azaba,dauke kanshi yai daga dubansu yana jin zafin datakeji har cikin ranshi a haka a haka suka samu tayi bacci mamar ta kunna room heater,sannan ta mayarda dubanta zuwaga kameel

"Sannu kameelu nikuwa meya faru?"

"Innah Muhammad ne wai ya hadu da ita a hanyar wuse ruwa yamata duka shine ya kawota gida,metajeyi Canne?"

"Ayna'u ce ta aiketa gidansu kawarta khairi, bansan kome ta aiketa yiba dai,bayan tafita dai nakirata tace can zataje amma yanzu nayita kiranta bata dagaba" mamaki karara a fuskar shi ya furta gidansu khairi kuma? Yinme bayan basa gari" da sauri ya janyo wayar yayi kiranta yace tasameshi shashen su zarah,bako sallama ta shigo,tasha mamakin ganin moh amma saita kawarda mamakinta ta riqe kugunta tace taunar cingam dake bakinta

"Yaa kameel gani" atake yasha mur

"Agabana naji kuna sallama da khairiyyah kan cewar zasuje kaduna,kuma Muna tare kukayi Waya bayan magrib dinnan akan cewar sun sauka lapia,gayamun mekuma kika aiketa yi agidan da yammannn kina ganin hadari tsabar rainin hankali kuma kinsani sarai ko ruwa ake tana daki sabida condition nata,mesa kekam kika takura yarinyar nan meta tsare miki?" Wani ware ido tayi tace cikin mamaki

"Zaran ce tace daku Nina aiketa? Allah ni karya take mun tun rana rabona da ita" Innah ce tace

"Ayna'u kiji tsoron Allah ina nan zaune kikace ta dakko hijabinta zaki aiketa"

"Kinga Innah karki wani daurewa karya gindi agabanki na aiketa nida natuna basanan aicewa tabarshi tadaije yawonta data saba shine zakimun karya"

Tasss kakeji kameel ya wanketa da mari

"Innar ce take miki karya? Tsabar ba kunya a idonki sannan kuma itadin kike mayarwa magana?" Dafe wurin tayi tabar dakin tana kuka wai zataje tagayawa umminsu Innah ta fara hadata da yayanta" girgiza kanshi yayi cikin jin haushin kalar tarbiyar da mahaifiyar su tayiwa Aynah yayinda suka bawa inna hakuri suka bar gidan.....

Moh kuwa kasa bacci yayi ranar ya rasa dalilin daya sanya yarinyar ta tsaya Mae arai yakuma fahimci sudin bakowa bane agidan,atake yaji ya tsani Ganin Aynah yanda ta rufe ido ta gayawa babbar mace kamar wannan bakar magana....aranshi ya kudiri abubuwa da dama...

Mom Nuaiym
[9/11, 8:58 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

*Ina godiya da dimbin kaunar dakuka nunawa littafina tin farko Allah yabar kauna #Bazan barkuba#*

06

Koda ta farka,ta danji sauqi mahaifiyarta ce a kusa da ita,kallonta tayi cikin tausayawa

"Sannu Zahra na kinji sauki?" Cikin karfin hali tace

"naji sauki Innah hannuna kawai ne bana iya dagawa har yanzu"

"Sannu zahrah idan nagasa miki shi kuma kikasha magani zakiga kinji sauki kinji ?" Gyada mata kai tayi cikin barwa

*washe gari*

Dukda kasancewar ka'idarshi ne baya fita saida yamma weekends saiya tsinci kanshi da kasa hakurin jin yanda yarinyar ta kwana, daga wayarshi yayi yakira kameel

"Kameel yajikin zahra?" Ya tambaya kameel na daga wayar,mika kameel yayi yayi salati sannan yace

"Nifa tun jiya ban komaba amma inaga taji sauqi ai" guntun tsaki yaja yace

"Amma bakada kirki kaifa ka gayamun kanwar kace da Aynah ce haka zaka mata?"

"Bro yanz fa shabiyun rana, Allah tunda nayi asba nake bacci idan nayi breakfast na kimtsa zanjene dole" datse kiran kawai yayi azuwan sauyaji daga gareshi amma shiru har yamma be kiraba wannan ne yasanya ya figi motarshi....

A parking lot din gidan yayi parking yafito cike da yanga sai tashin kamshi yakeyi a gogon hannun shi a wurgawa kallo yaga 5mnt after 5 kai tsaye bangaren dasuka kaita jiya ya nufa ya isa da Sallamarshi ya tsaya a kofar parlor din,gabanta yayi mummunan faduwa jin muryarshi sannan cikin rudu ta amsa sallamarshi janyo hijabinta tayi ta saka sanan tamai iso,har kasa ta duka ta gaidashi ya amsa da kayataccen Murmushi dake a fuskar shi
Chapter 3 · 0% Book details