← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 29

Sashe 13

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sir daka hakura ruwannan ya tsagaita sosai yake hadeda iska,na tabbatar bazakaga hanya ba idan kace tuki zakayi" juyowa yayi ga kaleta sannan ya nemi wuri a daya daga cikin kujerun dake reception din ya zauna,sam baya cikin nutsuwar shi...

"Malm kozaka paka ne kan ruwan nan ya rage Kifa tamkar iskar nan zata kifar damu" gyaran zamanshi yayi yace

"Cewa akayi dake yanzu za'a dena ruwan ko iskar,ai gwara mu karasa tukunna" shiru tayi tsoro na kara shigarta kara rungumo Jakarta tayi Bata ankaraba taji iskar ta kara karfi,ga ruwan sai data karfi yake shima,sosai ta rikice kantace wani abin,ji tayi Wata motar tazo tayi musu ibar karan mahaukaciya,basu tsaya ako inaba saida suka maki wani dutse,zahra kuwa atake ta some.....tamkar an tsikareshi haka Yaji ya mike yayi hanyar waje kuma,Luba kallonshi tayi takuma cewa

"Sir iskar da ruwan dad'a karfi sukeyifa?" Ko Kallonta beyiba yayi Sa'a kuwa ruwan ya tsagaita,da sauri ya shige motarshi ya tasheta,tafiya yake a hankali yana kallon gefen hanya kozai ganta,can davara ta fado masa ya janyo wayarshi ya kirata,ringing daya kuwa aka daga,ga mamakinshi muryar wani yaji,yace

"Plss me wayar fa?"

"Yallabai me wayrfa gasunan sunyi accident a hanyar metama gada ta farko,yanzu haka ana shirin kaisu National hospital ne" gigicewa yae

"Kace zahra na wai kake nufi,karkuje Ku kirani zanzo ina ma hanya" a jaka da Rabi ya Debi motar Allah ne kadai ya kaishi lapiya.....da gudu ya ruga wurinta ya tallafota yaga Bata motsi bare numfashi...jijjigata ya shigayi yayinda tsirarrun mutanen dake wurin ke bashi shawarar kaita asibiti kasancewar Bata numfashi sam....kwasarsu yayi har me adaidaitan ya yi asibitinshi dasu,kasancewar yana taba ko Wanne fanni na doctors ya sanya ya ce ze dubata da kamshi,dukkuwa dayake yafi kwarewa a fannin kashi. Me adaidaitan kuwa wani friend nashi Dr Jamal dake aiki a asibitin aka kaiwa shi a emergency domin ya dubashi....iya bincike yayi Amma kanshi ya daure kasancewar ba wani rauni ajikinta ko karaya kaiko goge wa bata yiba Amma sam she's unconscious, yana tsoro indai ba Internal bleeding bane....ganin ya saka tsoro ya sanya yafice domin kiran Dr Jamal,sannan ya zaro Waya yakira momy ya sanar mata meke faruwa....kallon juna sukayi shida Dr Jamal, Dr Jamal yace dashi

"Dr moh I'm sorry to say we lost the patient, he was already gone even before u arrived here"  hawayene ya gangaro wa moh yace

"Jamal zoka tayani duba zahra na moh,tare suka samu accident wlhy,nakasa gane komai,batada targade ko karaya but batama numfashi..." Subhanallah moh muje maza mu duba ta...

Sun hadu da momy ya gayamata komai sannan saiya koma gun zahra,Dr Jamal yafi 1 hour akanta Amma bata farfadoba atake suka daura mata oxygen tafara numfashi Amma sam alamomi sun nuna da babbar matsala,chances na surviving are very low,and above that tsabar tsoro da firgici ya haifar mata da mummunan bugawar zuciya....kallon kallon suke shida Jamal,yayinda Jamal ya rike kafadarshi

"Muhammad kai doctor ne kuma sarai kasan abinda wannan wannan bugun zuciyar nata dake tafiya tamkar bayasonyi ke nufi and kasan  ma'anar wannan numfashin dake yawo tamkar ana hura kunne,ni da kai ba abinda zamu iyayi sabida kuwa tsakani da Allah jijiyar dake  harba jini a zuciyarta zuwa kwalwarta tayi weak so chances na survival are more than low sedai kawai mu zubawa sarautar Allah ido"kura masa ido Muhammad yayi sabida harga Allah baya gane me yake nufi,sam ya zama kurma a rude yake,janyoshi yayi sukabar dakin  momy ta tare su,batare da koma Dr Jamal ya fayyace mata halin da ake ciki,Waya tawa daddy ta tsanar masa komai,Allah yasanya ya iso Abj yace da ita gashinan zuwa asibitin....

Gaba moh ya saka su daddy da kuka tamkar karamun yaro,sai hakuri suke bashi suna cewa yamata adua,sai kamar suna ingizashi har su Mamie da Aynah da Innan duk suna wurin ...ganin dayayi Jamal ze koma wurinta yasanya ya bishi da sauri,Koda suka Shiga numfashinta yana yi kasa sosai har Injin din yafara kara alamun daukewar numfashi atare sukayi kanta,ba yanda basuiba su ceci ranta Amma ga alama shirin Allah ya zarce nasu,kokarin danna mata kirji suke Amma sunaji suna gani yarinyar Allah ya karbi a barsa,disbelievingly moh ya kalli Jamal yace

"Jamal is she gone too?" Girgiza kanshi yayi yana tausayawa friend nashi tun bayan rasuwar farida moh bai kuma samun yarinyar dayakeso ba kamarta and above all a hannunshi ta rasu itama,dafa kafadarshi yayi yace

"Muhammad ya muka iya da tsarin Allah akanta,lokacinta yarigada yacika dan Allah full urself together my man,karkace zaka mana yanda Kayi alokacin Fareeda plss....." Sulalewa yayi ya fadi gun a sume! gigice Jamal ya kwasheshi zuwa wani gadon ya dubashi ya zare ox din ya daura mishi sannan ya fito gwiwa a sace ya kalli daddy yaje yayi kiranshi gefe yace dashi

"I'm sorry to say sir we lost her too" innalillah wa inna ilaihirraji'un itace kalmar da daddy ya furta,sannan ya janye glass dake manne a idonshi ya share kwallah sannan yaje da su momy

"Haj Asabe saidai hakuri Allah yayiwa yarki faduwa,dan Allah Ku dauki dangana domin kuwa hakan shine tsarin Allah akanta" kunsan mata har Aynah da rashin mutuncinta da kamai sanda tayi kuka,kowa mutuwar  zahran ta girgizashi haka akaje aka kwasheta zuwa gida moh bemasaniba,daganan mahaifiyarta da kanta tamata wanka,aka dunguma da ita makwancinta na har abada....

To jama'a nasan dayawa bazakuji dadi ba,karku manta Shifa ubangiji hikimomin shi da yawa suke,kuma tabbas namuku alqawarin happy ending, dukda haka Masu shawara ko karafi,sa iya ajiye saqonnan su ta inbox kamar haka
07084161619
Mom nuaiym ce
[9/11, 9:18 PM] Billy Galadanchi: *😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.
Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

21

    Sosai mutane suka girgiza da mutuwar zahra,jeddah kuwa sumanta biyu, bayan kammala wanka aka fito da gawar domin amata sallah akaita makwancinta daddy kawai ake jira domin ko shima ya kasa fitowa sosai jikinshi ya mutu  da wannan mutuwar takai tsaye......bude idonshi yayi a hankali ya saukesu akan Ummie dake tsaye kanshi tana sharar kwalla, a hankali ya janyo hannunta wanda yasa ta maida hankalinta zuwa gareshi,yace cikin kuka

"Ummie na mafarki nake zahra na bata mutu bako?,dan Allah kice dani mafarki nake Ummie na wlhy idan ba zahra Nima zuciyana bugawa zatayi na mutu" cikin tausa yawa ta kalli dan nata tace

"Muhammad bazan maka karyba,Allah ya karbi ran zahra a yanzu haka danake maka wannan maganar har anmata wanka ana shirin kaita makwancinta" zabura yayi yamike tana rikeshi haka ya cisgeta yabar dakin,lalubar key nashi yayi ya fashe da gudu sai gidansu.....cinci rindon mutanen daya ganine ya tabbatar masa cewar zahran ta mutu har abada.....gwiwa a sace yae cikin Gidan baya ma ganin inda yake jefa kafarshi yana kaiwa harabar yaga gawarta nanma mutane sai alwala suke,da gudu yae kanta ya rirrike makarar yashiga sambatu

"Wlhy ni kubedemun zahra na,zahra bata mutuba wlhy Ku taimakamun Ku cireta daga wannan farin kyallen" daukacin mutanen dake wurin yabasu tausayi duk kuwa dayake basusan yanda yake da ita ba,daddy ne ya dafa kafadarsa yace dashi

"Muhammad dan Allah be a man and full your self together, baka ganin mutanene ka daure ka mata adua kuma kamata bankwana yanzu zamu mata sallah,nabaka mintuna biyar kama zahra addua da bankwana kazo ka daura alwala mu sallachankalina  kallon daddy kurun yayi ya kurawa gawar ido yakasa cewa komai,can kuma kamar an tsikareshi ya kwallah kira

"Daddy wlhy Kuzo zahra na motsi na rantse da Allah suma tayi,dan San manzan Allah Ku cireta daga wannan abin tae numfashi da kyau" kokarin kwance likkafanin yashigayi yayinda mutane sukawo kanshi suna salallami,daddy ne ya ce da mutanen

"Yaronnan rudewa ne yayi,maza Ku nemomum kameel"

"Wlhy daddy da hankalina,zokaima ka duba dakyau zahrah na tana motsi,Ku agazamun na kaita asibiti,numfashinta har yanzu yananan" daga nan kameel yazo shida friend dinshi ,daddy yace

"Kameel lallai Ku hakura da sallar nan,kaga Muhammad badaidai yakeba,maza kuje Ku kulleshi a daki har sai bayan mun kawarda zahrah,kar azo ai gawa biyu kaji" kara birkicewa Muhammad yayi yashiga hauka,"wlhy da hankalina ni karku karasamun ita dan Allah" Ahaka fa yanaji yana gani suka kamashi ta karfin tuwo zuwa part din kameel,suka kuma garkameshi aciki.....ihun duniya yayi Amma basu saurareshiba....sallaceta akayi sannan aka kinki mi gawar da cincirindon mutanen zuwa maka barta...

Tsakani da Allah fa Muhammad yaga zahrah tana motsi,wanna yasanya wani karfin tuwo yazo masa ya balla kofar yafito,kai tsaye,Jamal yawa waya,ko gaisawa basuiba yace

"Jamal na rantse maka da Allah zahra tana motsi na gani da idona,Amma sunqi su yarda se cewa sukai wai bana cikin hayyacina,dakyar na balla kofar daki na fito,ko naje bazasu aminta daniba ka taimakamun muje dakai ka duba ta da kanka" gyaran murya yayi yace dashi

"Ina wurin yanzu haka,gashi ma ana shirin sakata arami,idan har ka tabbatar kaga tana motsin karka zo bani muntuna biyu zanwa daddy magana ya bari na dubata,zance dashi nine da kaina naga tana motsin idan kazo bazasu yadda ba,just stay dere I will get bck to yhu as soon as possible" daga nan sukai salla,ya paka gefen titi yana tunani sam ba nutsuwar a tattare dashi, ayanda yakeji koda sun binne ta saiya tonata sabida shikam tabbas ya hango tana motsi da numfashi da kyar kuma yasan bawai gizo bane....

  "Ranka ya dade dazakumin uzuri dana duba gawar nan,sainaga tamkar tana motsi" juyowa daddy yai ya kalli Jamal

"Dr Jamal koda dogon sumane tunda ruwa ya taba jikinta yakamata ta farfado,tunda kukaga dan Allah Ku hakura mana" kallon daddy shima yace

"Yallabai da akwai cases sosai irin haka fa,karka zo ka kashe yarinyarka da hannunka,da akwai wacce ta Kusan awanni goma sha hudu kuma anmata wankan har an sakata a rami,amma ta farka....wlhy naga yarinyar nan tana motsi dan Allah kabarni indubata" nisawa daddy yayi sannan yabawa mutane hakuri yace adubatan....zare likkafanin fuskarta yayi sannan ya yane na kirjinta,kallon farko daya mata ya gane tana numfashi amma kasa kasa,hannushi yakai gun hancinta ya kuma tabbatar tana numfashin,pause dinta ya taba yaji yagane bugun zuciyar ne not stable above all Koda take araye she's unconscious.... Hannunshi duka biyu yakai ya danna kirjinta sosai ya dago a take tayi picking wanda kowa dake wurin ya kula da hakan kabbara wurin ya dauka yayinda shikuwa ya kinkimeta yana fadin
Chapter 13 · 0% Book details