← Book details Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Inda Ranka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lallai Muhammad nasani kai yarone me kirki saidae ka sani banji dadi ba sam da abin ya kasance haka,mahaifiyarka taci zarafina sa yawa duk da yake nasani zugota akayi,abu daya yamun zafi bansan ina wannan batancin dasuka Wa zahra na zai tsaya ba sabida haka nagode da kuka zo kuma na hakura ha wuce ni dama ban rike kowaba,amma kasani narigada na gama yanke hukunci akan zaman ka da Zara,ko Waya ka daina kiranta domin kuwa na hanata daukar wayarka,karkayi tsammanin wani abin nake nufi,ko daya wlhy kawai dai ina kariyar mutum cin mune" har Muhammad ya manta rabonda yae kuka amma ya kasa tsayarda hawaye nsa

"Innah dansan manzan Allah ki rufa mini asiri wlhy rabani da zahra tamkar rabani da rayuwa nane,sam bazan iya hakura da itaba,daga zaran daddy na ya dawo komai ze daidai ta" kura masa ido tayi nayan dakiku sannan tace

"Muhammad kayi hakuri, sosai nakeda hakuri da Kawar dakai amma sam bana jurar wulakanci, hal daya nawa mara kyau shine bana sauya hukuncina,lallai ne saikun fita harkar juna,MUTUNCI daya zan muku shine nabaku dama kuyiwa juna sallama shima din kameel Kaine shaidana mintuna 15 kawai na basu" daganan ta mike tabar part din gaba daya,shima kameel ficewa yayi,sosai suka bashi tausayi

Sumadin mikewa sukayi atare kamar sun hada baki,takowa yayi ya nufota ya kama hannunta duka biyu,suka kura Wa juna ido na kusan mintuna uku,kuka tafara mai,ya girgiza mata kai alamar ta daina sannan yace
"Cute please karki saka na kasa sukuni mana,idan na barki kina kukan nan bazan iya komai ba arayuwa,dan Allah ki daina kinji cute na" zare hannunta na hagu tayi ta daurashi saman kirjinta cikin muryan kuka tace

"Yaa Muhammad nan nakejin zafi,mutuwa zanyi idan suka rabani dakai,basuda labarin tun farkon ganina dakai kake raina,basuda labarin Kaine farin cikina ur my other half, babuni idan har baka,yaa moh ka taimakeni dan Allah" hannu ya saka ya to she mata baki yace

"Ya isa my cute,kiyi hakuri kan daddy na yadawo,namiki alkawarin komai zai daidaita" cikin daga murya tace

"Yaa moh har yaushe? Har yaushe daddynka zai dawo harsai yaushe zan daina jin rad'ad'i da zagin da zuciyana kemun,bakada labarin kan wannan lokacin na mutu da bakin cikin rashin ka?"  Sosai ta bashi tausayi,datasan me yake ji data hakura da nata fitinar,kara matsowa yayi daf da ita yace

"Cutest Zahra na plss kiyi hakuri,daddyn bazai dadeba kinji" uban kuka ta Rosa har bata San sanda ta daura kanta saman kafadar shiba,kasa koda motsi yayi,dakyar yaja hannun sa yashiga bubbuga bayanta a hankali,a haka kameel yashigo yasamesu,gyaran murya yayi wanda zahra bata Masan yazo ba yace

"Moh saura  2mnt fa,karku kara bata ranta" dagota yayi ya rike kafadunta yace cikin dauriya shima din jiyake tamkar yae kuka,baya so ne ya karyar mata da zuciya

"Cute I'm so sorry there is nothing I  can do to ease ur fine now,but I promise u zan share miki bakin cikin nan ba jimawa" gefen dan kwalinta ta saka ta share kwallah daya zubo mata tace

"Yaa moh I love you so very much,and it pains me alot now dat I'm loosing u for good"

"Please don't say such my queen ur not loosing me,not even for a single second,I'm urs and urs alone for ever,please be strong my cutest zahra" tana hawaye tana Murmushi tace

"I will my king,I'm surely gonna miss yhu" kasa hakura yayi ya hugging nata

"I will miss u more my queen" ya rada mata a hankali ya saketa ya juya,a hankali ta kira sunan shi ya juyo kawai ya kalleta bai karaso ba,da gudu ta ruga ta fada jikinshi,tasaka wani kukan,janta yayi ya ajiye saman kujera yafita da sauri hawayen dayake kokarin tarewa suka gangaro,aikuwa dasuka koma dakin kameel kuka ya saka yace dashi

"Kameel zahra macece anya zata iya jurar wannan abin kuwa,tun kafin naje turai karo nabiyu nayi alkawarin idan macen aurenaba bazan kuma rike koda hannun maceba amma nakasa controlling gani nake tamkar idan ban hugging nata ba,bazaji sassauciba,ga yarinyar da kamun kai,itama so take ta kwanta ajikina tayita kukan nan,hakanne kawai zai bata sassauci,shiyasa ta rungumeni,ban mata adalciba idan nasabar mata da hakan,alamomi sun nuna bazamu rayu atare ba,kamar yanda ban mata adalciba dana hanata karasa kukanta asaman jikinaba,sam nasan haramcin yin hakan shiyasa na hanata,mesa  nakejin haushin kaina yanzu". Rike hannunshi kameel yayi ya dafa kafadar shi

" moh ai kayi abu mai kyau,barin abu sabida sanin haramcinsa shine daidai,so kasamu  lada,daga zarar daddy yadawo namaka Alkawarin zan sanar masa komai,kuma yanda yakejin zahra bazai kiba kuma innah bata ketare maganar sa"...

Mom nuaim ce

Dan Allah acikin kwanakinnan arage rike Waya a dinga hadawa da inada,akwai falala sosai.
[9/11, 9:18 PM] Billy Galadanchi: 😳INDA RANKA....kasha kallo😳*

Billy galadanchi

Wattpad @68Billygaladanchi

®HASKE WRITERS ASSO.

Sadaukar ga cutyna zarah Bukar.

18

Dukkanin byannin da lecturer din nasu keyi fiye da awa daya bata tsinci komai,sam hankalinta baya wurin gashi jiddah batazo school ba itakuwa ta bar phone nata agida bata San mesa batazo,Sosai hankalin young lecturer din nasu ke kanta,sarai ya kula yau bata cikin walwala,sanin daya mata sosai take bada gudummawa acikin,wannan dalilin ne ya sanya ya daga murya yace

"Zahrah Muhammad shayau,meet me in my office now" daganan ya kwashi takardunshi ya bar lecture hall din,tashi tai jiki ba kwari tabi bayan shi,yan class nasu ma yasun fahimci batajin dadi,sabida yau batayi participating a class dinba amma,alhali itace gwana....

Da salla ta tura kofar office din ta Shiga,ansata yayi hankalinshi nakan takardun dake hannun shi,shigowa tayi bayan bata izini ta tsaya sannan ta russuna ta gaidashi, daga cikin madubin dake manne a manyan idonshi ya dan dako ya kalleta yace

"Lapia lau,have a sit" zama tayi jiki ba kwari ta sadda kanta kasa,tafi mintuna biyar kan ya ajiye takardun hannunshi ya mayarda hankalin shi zuwa gare ta yace cikin murya dabata tabajin yayi amfani da ita ba a class

"M shayau menene yake damunki yau sam baki participating a class ba" dagowa tayi ta kalleshi cikin rau nanniyar murya tace

"Ba komai sir,kawai yau banajin dadine" kishingida yae a saman kujerar sa yace cikeda yanga

"Sarai nasan bakyajin dadi,dalilin kenan daya sanya nakesan sanin musabbin rashin jin dadin naki" sosai tasha mamakin Sir mujeeb sam shi baya Shiga shirgin student,shiba magana bane dashi amma sosai yakeda tsare gida siyisa ake shakkar shi sosai,ko sanda ya kirata ta hango tausayin ta a fuskokin jama'a da dama class din, dakyar ta dago tace

"Sir Allah kaina ne yakemun ciwo" kura mata ido yayi harta tsargu,sannan yace cikin kasala

"Look Zahra,na tabbatar kina da wani damuwa,so tari nikan kula cewar kina cikin damuwa,amma yau dinnan yafi na kullum,samsam banajin dadin ganinki cikin damuwa,kinga gaf kuke da fara exams pls koma menene kiyi hakuri,kinada san karatu yasa kike matukar birgeni" wasa tashiga yi da yan yatsunta kantace

"Zan kiyaye inshaa Allah nagode sosai sir" dagowa yayi daga kishingidar da yayi,atake ya yalwanta fuskarshi da kayataccen murmushin yace

"Tunda daganan zaki nunamun kin rage damuwa" dagowa tayi sukayi ido biyu tace

"Sir" murmushin shi ya fadada yace "Saikin yi Murmushi zakibar nan office din,kinmaji na gaya miki" murmushin ne ya kubuce mata,taji mamakin sauyawarshi lokaci daya" tamike tace

"Sir na gode sosai zan wuce" lokaci daya ya murtuke fuska yace

"Wanene ya baki izinin tafiya, maza ki zauna labari zaki bani" komawa tayi ta zauna a takure,sosai takejin nauyin sa,maganar shice ta katse mata tunanin ta

"Hmm zahra ina jinki" dagowa tayi idonta hjiki yayi raurau tamkar zatai kuka,shagwaba kuwa sana'artace har bata Masan tanayiba sabida ya zame mata jiki

"Sir please lemme go" kallonta yayi yanda tayi maganar a shagwabe tamkar zatae kuka yace

"Why should I?" Kara langabe kai tayi tace murya na rawa

"Sir dan Allah faa" sosai ta karkace ta ware da imaninsa,datasan yanayin maganar ta kasalar data saukar mai data rufamai asiri ta daina,kishingida ya kumayi yana Murmushi yace

"Yauwa zanmafijin dadin sauraren kukanki tunda kuka zaki mun a amaimakon labari Bismillah ina saurarenki" rausayar da kanta tayi tace

"Kayi hakuri sir,its just that I'm not comfortable @ all"

"Ok then leave" kallonshi tayi ga alama beji dadin maganar taba tace

"Kayi hakuri sir ba wani abu nake nufiba fa" mikewa yayi yace

"Nima I mean nothing, its better u leave since ur not comfortable" bataga alamar wasaba yasa tamike tamai godiya ko kallonta beyiba ta fice" A kokarin ta na fita daga office din taci karo da Aynah kallonta tayi kasa da Sama tace

"Hoo karuwancin yakaiki bin diddigin dakin malamai?" Batace da ita kalaba tayi gaba abinta,Binta tayi baya tace

"Ke badake nake maganaba" juyowa tayi tace

"Aynah please lemme be mana,mekuma namiki yanzu?"

"Bakimun komai ba Haj laifin ki daya da kike kokarin takara dani acikin makarantar nan,yanzu saikin gayan uwarwa tace kisaka irin atamfar danake da ita Karin ace muna sharing a banza" hararota zahra tayi

"Sabida bakece kika siyamun ba malamai"

"Amma ai dabazata kike rawa sabida akarkashin ubana kike" murmushin yake zahra tayi tace

"Alhamdulillah tunda bake ne kike siyamun ba,kinga Aynah wlhy ki rabu dani,yau dinnan ni kadai nasan me nakeji" tafa hannu tayi tace

"Dolene kiji abu mana,an raba ki da wanda kike tatsa,yanzu ba kudin kati,kuma wlhy wannan motar saina rabaki da ita,daddy na zuwa zaki ganene,ninan nafi karfin inhau mota yar aikin gidanmu tahau,banzaye dangin mayu matsafa kawai" juyawa kawai zahra tayi ,suka saka dariya itada kawayenta......isarta gidan keda wuya ta taradda momy ta iso aikuwa da,gudu tayi shashinta,sosai sukayi murnar ganin juna sedai sam momy bataji dadin ganin hannu da fuskar da a kumbure ba,koda ta bukaci sanin meya samu zahrah,zagewa tayi ta sanar mata komai,har hukuncin Innah akan zamanta moh,mikewa momy tayi tace muje sashin Innan taki....

"Sosai naji zafin wannan abin dakikamun usaina,ai kamata yayi ace kijira dawowana,kasancewar nice mahaifiyar zahra bansaniba kodaga baya kika kwace kyautar dakika mun" dagowa innah tayi tace

"Haba Asabe? Wane irin magana ne wannan, nifa sam ba haka nake nufi ba,abinda suka munne banji dadiba sam,kuma tun farko sanda na gargadeta" nisawa momy tayi
Chapter 11 · 0% Book details