← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 38

Sashe 9

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" zanje nakwanta akwai abunda kakeso,? yafada cikin tsare gd, papa nima zanyi bacci kusa dakai, kamar zai daukeshi sekuma yafasa, yajawo hanun dan nasa yasauko daga kujeran , ahankali yake dingisa kafar hasuka isa bedroom, kwantar dashi yayi shima ya kwanta, domin yasamawa kansa saukin bacin randa yakeji, allah yagani kwata kwata bayaso Nisha ta kusanci aheel, gaba daya ransa baci yake inya gansu tare, gashi allah yayi dansa mai bala'in wayo da surutu allah kadae yasan mai yake gayamata insuna tare, gaba daya bakin aheel ba ba control, maida kallonsa yayi ga aheel daya tsura masa ido yana kallonsa, yaron magana yakesonyi but ganin mahaifinsa fiskarshi babu annuri yasa shi yin shuru, shikuwa AJEEMAL kallonda aheel yake masane yasa yace,

" bazakayi baccin bane kake kallona, lumshe ido aheel yayi daga bisani papansa yaja musu blanket yarufasu,
Nisha kuwa tana shiga part dinsu tasamu ita suke jira dan haka tasamu gu tazauna sukashiga fara cin abincin suna dan hiransu cikin nishadi, bayan la'asar salma tafara kokarin shirn tafiya gd, nan fareeda tasanar da ita wani birthday party dazasuje nawata friend dinsu , dan haka ta tsaya sutafi tare daga bisani sesu sauketa agd, haka kuwa akayi nan suka shiga shiri cikin riga da wando saman kuwa suka daura bakar riga, itama Nisha hakan suka sata tayi, fareeda taimata light makeup tafito tas da ita tayi kyau sosai, salma se kallonsu take yanda sukayi kyau dasu musamman Nisha kamar ba itaba, da itama kamar zatasa duguwar riganda reeda taba sekuma tafasa because seta nunawa ummynta, part din Hajiya suka nufa domin mata sallama, a parlour suka sameta zaune tanacin abincin da Nisha tazo ta ajiye mata, binso tayi da kallo daya bayan daya tana kare musu kallo, yan matan daddy sunyi kyau sosai, too wannan kwalliyarfa se ina, waje suka samu suka zauna suna kallonta , ina tambayar ku se ina, sun kuyar da kai nisha tayi tana jiran taji mai zasuce, cikin susa kai reeda tace

" am gdnsu fauziyya zamu yau take birthday, ba ranar munfada miki zatayi birthday ba ko kin mantane, aa ban saniba amma kusantu dazu kunfita da safe , AJMAL yanajin fitarku agdn nan haka yazo yasamene yana fadin fitarku yayi yawa kuncika yawo duk inda kukace zaku ninake barinku su ammi basusan shiga da fitar kuba, to kunga atakaice dai ninake daure muku gindi kenan ko,? to tunkafin ku saka ranku afitar nan gwara ku hakuri shi zaifi dan nasan zaku iya gamuwa dashi, kuma ba wanda zaije yayi mitar seni gwara ahakura da kitarnan kawai, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa daga bisani fadeela tace,

" amma ko fauzee bazataji dadiba fareeda tace gskykam tafada tana kallon Hajj mama, kuma ae fitanda mukayi dazu ammi ne ta turo da kudi tace muje muyiwa Nisha shopping, to komade mainene kukirata kubata hakuri baza kusami zuwaba , kai bazai yiyuba shi waya takura masa haka damu zai takuramu reeda tafada tareda mikewa tsaye, cikin hanzari hajja mma tace,

" to rashin kunya zakimin, ko zaki ketare abunda tacene iyye, sbd kin isa ko shakararriya, jitayi kamar tayi kuka because sunsa ransu zuwa party nan, part dinsu tanufa suma suka rufa mata baya, yau murna ya komaciki, gaba dayansu samun waje sukayi suka zauna bawanda ya iya cewa da dan uwansa kala, salma kadan yarage dariya ta kubcemata, yanda take kallonsu fadeela bakinsu kamar zai taba bango, jin ana kokarin bude geat fareeda tamike cikin hanzari yayi labuleh window tana lekawa, AJEEMAL ne yafito hand dinsa cikin na aheel suka shiga mota mai gadi yamude masa geat yafita, wani wawan tsalle reeda tabuga cikeda murna tace,

" kaikuzu mutafi yanzu ya AJEEMAL yafita, part din Hajiya suka koma suka sanar da ita yayansu yafita hutawa dan Allah suma tabarsu suje su shakata, ganin yanda suka damu da fitar yasa ta kyalesu, da sharadin lallai su dawo kafin dawowarsa in har yadawo yafahimci basa nan tofa ba ruwanta, dan sunfita sanin koshi waye kuma sunsan halinsa, cin yanayi na murna da nisha di sukace inshallah allahu ma zai dawo ya tarar dasu agd, nan suka mata sallama sukayi gaba, tafiya suke suna hiransu cikeda nishadi, tsayawa sukayi daidai wani katon plaza suka shiga suka siya mata wani birthday cake mai hawa uku cake din yayi kyau sosai gwanin shaawa, suka hada mata da wani turare na kwali mekyau da kamshi ga kuma tsada, suka shige mata dashi,
koda suka iso wajen sukayi parking motarsu a compound din wajan, tundaga arian wajan kakejin sautin kifa natashi koda suka karisa shiga Hall din, salma da Nisha suke karewa wajan kallo wajan ba karamin haduwa yayiba kaikace biki ake, ganin su farida da fauzee tayi yasa tayi kansu da gudu ta rungume su, ta mikawa salma da Nisha hand suka gaisa, ga fara'a ga kyau yarinyar balaifi, aina dauka baza kuzuba danaga time yaja da harnayi fushi, fauzee tafada tana kallonsu, kema kinsan ba abunda zai hanamu zuwa ae suka fada suna dariya, waje ta sama musu suka zauna daga bisani suka mika mata gift dinda suka taho mata dashi cikin murna da farin ciki ta karba tana fadin,

" thanks, kowani table ankewaye da kayan ciye ciye da makulashe, mazansu da matansu se shashewa ake ganin haka yasa fadeela da reeda suka mike suka shiga cikin yan rawar because yawanci classmates dinsune awajan, can Nisha taji bazata iya jure zama wajanba, ga wasu maza da suka zuba musu ido suna kallonsu musamman Nisha, ganin haka yasa Nisha tamike tana kokarin fita , yanaga kin mike salma tafada tana kallon Nisha, nagaji da zaman nan dinne ga kuma karan balonda yake fashewa, jirani nima salma tafada tareda rufa mata baya, su reeda kam basuma kula da fitansuba, hankalinsu yayi gaba, waje suka samu daga gefen Hall din suka zauna, suna ganin masu shiga da fita na wajan , ke dama inaso na tambayeki dama haka ya AJEEMAL din nasu yake, mekike ganin Nisha ta tambaya, yanada miskilanci kuma masifaffene, dariya Nisha ta tintsire da dariya tana fadin,

" gsky baki fahimce shiba mutumne da yatsa akasa masa abaki bazai cizaba, yanda kikasan kurmafa haka yake gsky banaje yacika surutu bama balle masifa dakikace, baeshida miskilanci de, amma de bansan mekika ganiba kikace hakan, to nide abunda idona yagani kenan kuma yayi agabana nagani, domin dazu danazo ban samekuba kunfita muna zaune da Hajiya yashigo yana surfa bala'in, wai ina kukaje, wlh mutumin nan kamar bazai amsaba nina daukama bai jinibane ashe yaji se masifa yake nida farkoma na dauka ko baban sune amma yanda nagansu zankada zankadan yan mata nace kai wannan bai kai ya haifesuba, allah seda nayi nadamar gaisheshi, dariya Nisha tashigayi tana fadin,

"tab waneshi ya haifi kamar wadan nan, boy dinsa daya aheel shima daya yakare dashi, nimade shinagani ganin masifar tayi yawane shiyasa nayi tunanin hakan salma tafada tareda sake fadin,

" ke tashi mukoma ciki kar su nememu surasa, mtswww wlh banason komawa cikin nan bare barensu yayi yawa Nisha tafara tana tsuke baki, daurewa zakiyi ae munkusa tafiya salma tafadi, harsun tashi zasu shiga me idonta rahila da wani matashin saurayi sunfito daga mota suna kokarin shiga cikin hotel din, idonta tarufe takuma budewa da sauri tareda murza idon da kyau tana binsu da kallo, salma ce ta dan bugeta kadan tana fadin,

" ke lafiyanki kuwa meye hakan,? kinta bin bayin allah da kallo kinsansune dakike kallonsu hk, ke nasanta mummyn aheel cefa dawani sekuma tayi shiru ko ba ita bace kam Nisha ke tambayan kanta, to mema zai kawota nan ita da take gun aiki, inga kamane ko nasaba gani, gsky kam kinsaba gani kam dan banga mezai kawo matar aure nanba, to meye ma naki aciki in itace mutafi muyi abunda ke gabanmu salma ta Fadi, tabbas abun yabawa Nisha mamaki dama ace batasan rahila bace se ace kama tagani ko kuskusne ganine, dan haka bawani batun kama itance,.

"kukuma mekukeyi anan munata nemanku aciki, please kudawo ciki fareeda tafada tareda juyawa, rufa mata baya Nisha da salma sumayi suka shiga ciki, , anci ansha yanda yakamata anyi rawa sosae gari yarufa magarib ya gabato kai, yanda suke ciki bawanda zaiyi tunanin magrib yayi, kowa dake wajan seda fauziyya ta taimasa kyauta mai kauri daga bisani akashiga watsewa, fituwar su fareeda keda wuya, sukaga gari yayi duhu, lokacin fadeela takalli agogon hanunta karfe 6:45 , ga miss call din hajja mma kaca kaca, nan suka shiga mota suka nufi hanyar gd , seda suka suke salma agd sukayi sallama, sannan suka wuce suma, reeda ta dannawa mai gadi hon, yabude musu suka shigo, tundaga nisa suka hango motar yayansu, dan haka sukayi parking motar suka fito, kota kan Hajiya basuyiba suka wuce part dinsu asukwane, kowannesu ahankali atashe banda Nisha da ahankali ta akwance yake, dan haka tanufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah abunta, ganin haka yasa suma suka tashi sukayiyo alwalan sukayi sallah, bayan idar wansu kowa yasamu gu yazauna , kowannesu da abunda yake sakawa cikin ranshi, tunda suke basu taba kai dare awani wajeba se yau, duk fitanda suke arayuwar su, da zaran yamma tayi zasu nemi hanyar gd, sede infita yakama na family to shine ahankalinsu kwance, gashi yau sanadin fauziyya sunyi dare,

Nisha kam yau gaba daya abun kallo su reeda suka dawo mata, duk yanda suke da surutu amma yau shiru kamar basuba, ko wacce se zare ido take kamar tayi karya, jin ana turo door yasa suka kurawa kofar ido a tunanin su Hajiya kokuma yayansu, ganin Barka ce yasasu sauke wani goron numfashi, kufito kuci abinci anshirya komai baba Barka tafadi, dukansu bamaijin yunwa, dan ba karamin ciye ciye sukayiba awajan partyn, duk da nisha bawani cin abu tayi sosaeba, itama ba yunwar atareda ita, nan suka sanar mata ba maijin yunwa acikinsu ma'ana yau baza sufito cin abinci ba, bata tambayi daliliba tajuya tafita daga dakin, itama Hajj mama cewa tayi takai takai mata nata bangaran ta, sunayi Isha kowa tanemigu ta kwanta yau bawani Hira, juyi suka dingayi dake suka samu bacci ya daukesu, da suba Nisha ne ta tashesu sukayi sallah daganan suka nemi guri suka kwanta, Nisha kuwa seda ta dan taba karatun Qur'an data saba, sannan ta kuma ta kwanta itama,
Chapter 9 · 0% Book details