← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 38

Sashe 27

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

seda suka iso filin gdn indasu muhaiseen sukayi parking, goggo rabi ta bude kofar motar gdn baya ta kutsa nabilah wacce hawaye suka suma wanke fiskar ta, ammi hajja mama reeda fadeela se allah ya kiyaye sukeyi tareda musu fatan alkairi, banda Nisha dake gefen hajja mama tayi rau da ido kamar mai shirin kuka,

Shima gdn baya inda nabilah tashiga kamal yashige ,"

Allah ya tsare yakiyaye kakula dakanka kakula da kanwarka sosai please daddy yafadi yana dafa shoulder din kamal,"

Inshallah Daddy kamal yafadi yana yar murmushi daga haka Daddy ya rufo musu kofar motar nan su mb suka shige gaba muhaiseen shine me driving ,

Nan mai gadi yabude musu geat daga nan muhaiseen yayiwa motar key suka fice, seda sukaga ficewarsu aharaban gdn gaba daya hakan yabawa su daddy daman dugumzuma su koma parlour inda suka fito,

kowannensu jiki amace abun ba dadi , haka kowa yanemigu yazauna sukayi shiru nadan wani lokaci, daga bisani Daddy yasuma kokarin mikewa, harya fara nufa upstairs se shigowar su heelah tareda mom dinta hajiya jumana, hanunta dauke da na aheel kamar wayanda aka jefo daga sama,

ganin haka yasa daddy jiyuwa ya koma yazauna inda ya tashi suna ganin isowar su, aheel cikin hanzari da dauki ya zame hanunsa daga na kakar tashi da gudu yanufi inda yaga Nisha zaune ya fada saman cinyar Nisha tareda washe baki, yana fadin,"

Aunty!

rungumeshi nisha tayi cikin farin da daukin ganin shi , "

ba shakka hajiya jumana tafadi tana tabe baki yayinda take kallon aheel da Nisha yanda suka wani rungumi juna, gefe takalli heelah wacce itama idanta ke kansu ,

seda suka karisa tsakiyar parlourn heelah da mom dinta suka nemigu suka zauna, suna bin yan parlourn da kallo wanda suma idansu akansu yake, cike da mamakin ganin su,

hajiya jumana atsatsaye ta daga musu gaisuwa suka amsa ba yabo ba ballasa, itakuwa heelah baki tatura gaba bata daniyar gaishesu jin mom dinta ta zungudeta yasa tabude baki ta daga musu gaisuwa ciki ciki suka amsa,

hakama su reeda da Nisha suka gaisheda mom ta amsa nasu reeda amma nisha ko kallo bata ishi hajiya heelah ba,

"Lapia kuwa,? Daddy yafadi yana kallon su

" Eh lapia yar kenan magana nake tafe dashi ko nace kara na kawo, hajiya jumana tafadi atakaice, ""

kara! daddy ya furta ahankali, se kuma ya kalli su fadeela ya basu umarnin su tashi sushiga ciki, nan suka mike dukansu suka nufi bedroom tareda aheel duka,

"Kara kuma karan wa kenan hajja mama ta tambaya,

rabi! dalili nakeso tabani na kama diyata taita duka kamar jaka, saboda kawai fada ya hadasu da waccen yarinyar Nisha take ko waye, rabi bata tsaya taji kan zanceba tayi kan heelah da duka ,

kunganta tanan tun jiya zazzabi mai zafi yarufeta tayiyo gd ba wanda ya damu da damuwarta balle yasa me yasameta,"

Subhanallah anan gdn kum wannan abun ya faru, ammi ta tambay

cike da yamutsa fiska hajiya jumana tace ,"

Aina kike tunanin hakan zata faru inba anan dinba, ranar da ake shirye shirye tafiya dinner hakan tafaru dalili daya hana heelah zuwa partyn kenan sbd rashin kyautawa da kunya tata cikin friend dinta, anuna mata kasawarta, angwada mata bare ta fita mutunci,

parlourn ne yadau shiru kaman ba mutane cikinsu mamaki hajiya jumana da maganganunta ya gama basu mamaki,

Daddy ne yamaida kallonsa ga rabi wacce tayi tsuri tana kallon heelah da mom dinta da irin karai rayinda suka zo dashi,"

Rabi kinji abunda hajiya tazo dashi daddy yafadi,"

Naji sede amma sun fadi sun zuciyarsu ne indan zasu fadi yanda zancen yake heelah ce batada gsky nikuma amatsayina na babba nayi hukunci yanda ya dace, "

Oh hakama zakice mun fadi sun zuciyarmu to shikenan nida kaina zanyiwa tufkar hanci dama nazo nafadane dan kusani but tunda kun sani shikenan, hajiya jumana tana gama fadin haka tasuma kokarin jan hanun heelah, ,"

Dakata mana yakuna abu sekace wasu kananan yara kutsaya abin abun abun asunnu mana, daddy yafadi yana kokarin dakatar da hajiya jumana daga kokarin tashin da take, "

kin kawo karanki munji mun gamsu muna baki hakuri bisa kuskuren da ya faru, hakan bazata sake kasance waba,

kuma batun rahilah ta koma dakinta tazauna duk abunda yake damunta za amata magani anan, batun bata da lafiya ta koma gd duk bai tasuba, "

Mijintafa baya nan kuma ko sanar da ita baiyiba balle tasan time din da zai dawo , ya barta ita kadai ba waya ba komai se bautar dansa datake ko time din zuwa aiki yanzu batadashi , baisan wani hali suke ciki ba wayarsa akashe,

dan haka kubarni zan kula da abuna agdna har ta warke ta kuma haiyacinta idan da yiyuwar da wowa seta dawo ai ga danku shikam nasan yafi kaunar zama anan, dama nan din yafi dacewa dashi, nabarku lapia,

daga haka suka mike suka fice, baki bude daddy yabi bayan matar dan uwan nasa da kallo daga bisani ya jin jina kai tareda sunnar da kai kasa

Nanfa daki yasake daukan shiru, jiki asanyaye daddy yatashi ya haura sama, yabarsu ammi saune suna jimami, ba wanda yacewa da dan uwansa kala,

jim kadan hajiya tamike tanufi hanyar fita goggo rabi ma sidi sidi ta tamike tabi bayan hajiya, ganin haka yasa ammi tashi itama jiki ba kwari tabi bayan mijinta,

Yaufa zama sam bata kare da dadiba kamar yanda aka saba, aheel yanacan bedroom dinsu Nisha yanata zuba musu surutunsa da yasaba baisan su mummynsa sun tafi sun barshiba, su kuma sun biyeshe da shirmensa basu san wainar da aka gama tuyawaba ,

rayuwa tacigaba musu kamar yanda suka saba cikin farin ciki da annashuwa Nisha da kanta tashiga da wai niya da aheel cinsa shansa duk ita ke kula dashi, domin ammi tasanar dasu heelah batada lapia tana gun mom dinta ke kula da ita shiyasa tabar aheel anan, jin hakan ba karamin dadi yayiwa Nisha ba dan tanaso yaron sosai kuma tana son kasan cewa dashi

shiyasa ta dau ragamar kula dashi tare suke kwana su tashi ta shiryashi cikin uniform tarakashi har mota drive yakaishi

aban garan hajiya kuwa takasa mancewa da abunda uwar heelah tazo tayi , na maganganu na rashin da'a dacewa da samarwa karya wajan zama. ,

gaba daya abunda tazo tayi yabata mamaki batasan tsaurin idon jumana ya kai hakaba , ba inda diyarta ta barota, ashe gurin uwarta take koyan wasu halayi da da'biu gaba daya tagama shagwabasu da lalata tarbiyarso da sunan wani so,

Itade hajiya tun daren ranar tagaba yanke hukunci kuma very soon zata zartar dashi kuma dole akarba huncin da tayanke ko anaso ko ba aso tunda kowa kasa yake da ita🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴

Story and writing by oum amreesh

(Khaleeseart Raeeys)

Page 31

Bayan yanke hukunci na hajiya take ta dau waya ta dannawa abban heelah kira tasanar dashi tana bukatar ganinsa nan yasheda mata baya gari but inshallah allah in ya dawo zaizo dajin haka hajja mama ta katse wayar tasa ido rana da lokacin zuwansa,

Ranar alhamis da dare bayan sun kammala dinner yau ba dan wani dugun hira sosai kowa yanufi ma kwancinsa ,

goggo rabi da hajiya suna zaune parlour suna jiran dawowan su Daddy da abban heelah domin sun sanar da hajiya suna tafe tare,

ba dadewa motarsu ta kunno kai cikin gdn mai gadi yabude musu geat suka shigo, sunayin parking direct part din hajja mama suka nufa,

haka su daddy suka shigo cikin parlourn daya nabin daya suka nemigu daga gefe suka zauna,

nan suka shiga gaisawa da hajiya daga bisani sukayi shiru dan jin meys makasudin ganinsu da hajiya takesonyi , "

Modi wai meya yake faruwa agdn kane, hajiya ta fadi tana tambayar abban heelah, baki na bari yasuma maganaa,"

Haj.. hajiya mai kuma yafaru,?

Magana nake akan matarka da heelah naga kamar yanzu sundauko wata da bi' a narashin ta ido,"

Hajiya gwara kiyiwa yaya modi bayani yanda zai gane ba se anbita wani dugun turanciba, bari nina kura masa jawabin abunda ya wakana bayanshi, goggo rabi ta karbi maganar,

Heelah da mahaifiyarta bakaga iban albarka da rashin kunya da sukazo suakayi agdn nan ba agaban hajiya,

Nan goggo rabi ta labarta masa abunda yafaru wanda jin hakan ba karamin mamaki yayiba, duk da yasan halin jumana sarai za ta aikata ,

Shiru yayi kansa kasa yakasa cewa komai, se tsinkayar muryar hajiya yayi dacewa,"

Ni baruwana da rashin kunyar da sukazo suakayi duk wanda yayi na gari dan kansa, tunda tace yarta baza tazauna tayi zaman aure kamar yanda kowa yakeyiba ba matsala gari da yawa maye bazaici kansaba,

duk lokacin da taji zata iya dawowa dakinta yana nan yana jiranta , amma kafin nan akwai hukunci dana zartar hajja mama tafadi tana kallonsu,"

hukunci kuma hajiya? wani irin hukunci?"

Gobe in allah ya kaimu bayan sallah jumma'a ina bukatan adaura auran MODIBBO da yarinyar nan Nisha"

Hajiya aure kuma? please kar ayi gaggawar yanke wannan hukunci mana, idan baki manceba ko auran MODIBBO na fari bawai da amincewar sa bane kekika bukataci ahadasu muka hadasu yanzu kuma ake shirin kakaba masa wani,.. daddy yafadi cike da damuwa ,"

Nasani idan yanzu kowa bayida bukatar hakan ni inaso, kamar yanda nabukaci nabaya akayi to wannan ma haka nake bukatar akullashi ,

dan haka bana bukatar shawarin kowa umarni nake baku ba shawaraba, koshi MODIBBO danake shirin kara masa auran bai isa ya kaucewa magana taba ,

naso agabana za adaura auran ina gani amma kasancewa ana bukatan shaidu shiyasa nabarshi zuwa gobe, dan haka indan allah ya bamu tsawon rai zuwa gobe ashafa fatiha,

Daga Daddy har abban heelah shiru sukayi suna jinjina maganar hajiya ammade wannan hukunci data yanke da tsauri yake, to amma uwarsuce ba yanda suka iya basu isa sukaucewa maganar taba,

Goggo rabi kuwa se washe baki take ranta kal zuciyarta fes ba karamin jin dadi hakan tayiba"

To kutashi kutafi dare yayi se allah yakaimu goben, hajiya tafadi, jiki asanyaye suka mike suka fice ,

Daga waje suka tsaya sukayi sallama abban heelah yashiga motarshi mai gadi yabude masa yafice, daddy nagani tafiyar dan uwan nasa shima ya kutsa kai cikin parlourn haurawa yayi sama cikin bedroom dinsu,
Chapter 27 · 0% Book details