← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani dugun kwafa heelah tasaki bata da time dinda zata bata dan anjima kadan operation zataskhiga dan haka taciza lips dinta takalli nisha takuma hararanta kafin tashige fuuuu tafice daga parlourn tana sunbatu , nisha bin bayan heelah tayi da kallo hartafice daga parlourn kallon da heelah tayi mata tana ciza lips yasa taji gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya , "

To amma ita haka aiki rayuwa mutum da mijinshi sam bawata damuwa ko nuna kulawa yanzu haka ko breakfas batayiba bare wani kimtse kimtse na dakin fitarma dazatayi daga ita har mijin bawanda ya kulawani haka tasakai tafice ,uhm allah ya kyauta aheel da papanshi suna ganin takansu ga wanga diya, sam nisha ta mace da inda take se surutai take cikin zuci tajuyawa ajmal baya tashiga tunani ,

bata ankareba seji tayi ana zuba mata ruwan zafi bisa gefen wuyanta harcikin rigarta, wani ihu nisha tasake tayi baya ahanzarce ta dafe gefen wuyan nata tana kallon ajmal dake tsaye da cup din coffee ahanunshi yana hararanta ya hade gira, allah ya taimaka ruwan bawani zafi yasuma hucewa daba hakaba dase dan buzunta ,nisha kallonshi take tana zare ido nan da nan maganar KB yafadu mata ✍🏼🦚🦚IG AJEEMAL🦚🦚

Story and writing by oum amreesh❤️
Khaleeseart Raeeys💦💦💦
Page 4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣
______________🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹✍🏼
Gudu take sosai tamkar maishirin barin gari , bata tsagaita da tafiyarba harseda ta iso daidai wani dan kareriyar hotel tanufi compound din hotel din daidai parking space tayi parking, ko tsayawa daukan handbag batayiba wayarta kawai tazaro tabude morfin kofa tafito cikin hanzari tanufi cikin hotel din,

dedai door din wani bedroom tatsaya tashiga yin knocking ahankali , bugu daya zuwa biyu akabude , dan leko face dinshi yayi kadan yana kokarin fadin,"

Wa,,ye,, ganin heelah dayayi tsaye bakin door yasa yagimtse baki yashiga sakin wata iriyan murmushi ta marasa gaskiya still yakasa bata hanya tawuce, wani kallo heelah tawurga masa ganin yana tsaye baibata hayaba balle yamata iso, "
Yadai katsaya bakin door bakada niyar min cemin nashigo , kodai baka gane wayece a gabanka bane , murmushi yakumayi yana dan sosa head yana fadin ,"

Nagane mana come in , ya dan silale jiki yamatsa , cikin hanzari heelah tura kofar tayi daniyan shiga cikin, sekuma ta tsaya cak tana fadin ,"

Ya ilahi mai zangani haka? faruk ! wacece wannan yariyar kuma? heelah tafadi tana nuna wata yar matashiyar budurwa dake zaune bisa kujeran dakin tana sanye cikin t-shirt da dan wando iya gwaiwa , saman kanta tayi kitson atach har gadon baya , ga wasu uwar farata tsaro tsaro kallo daya zakamata kagane bata inda suka hada dan gantaka da musulunci alamade ba musulmabace , tana zaune tana danna phone dinta kallo daya tayiwa heelah da tashigo bata kuma sake daga ido takalleta nabiyuba tacigaba da harkan gabanta,"

Nayi maka tambaya kayi shiru bakace komaiba , who are she? kuma zaman metake anan, heelah takuma tambaya karu nabiyu tana tinkaran faruk Wanda yasunnar dakai kasa yana sanye cikin gajeran wando se yar vest , "

friend dinace tawajan aiki ziyara takawomin bana fadamiki kwana biyu banajin dadiba shine tazu tagaisheni dajiki, am,,am,"

Wait ya ishene haka , cemata tadauki komatsanta tafice daga nan kaikade nakeda bukatan gani, heelah tafadi yayinda taja gefe ta tsaya ta harde hand dinta saman chest dinta tana kallonshi , shiru faruk yayi baice komaiba kuma baiyi niyar aikata abunda heelah ta umurceshi dashiba , "

Ko bazaka iya sallamar gimbiyar takabane ninaje nasaita ta ahanya inuna mata bakin door, heelah tafadi tana hararo faruk sidi didi faruk ya wuce yanufi wannan budurwar yasunkuya daidai ita yashiga yimata rada kamar munafiki , meyace mata se allah daga bisani yanufi bedroom ba jimawa yafito hanusa dauke da makudan kudade ya taho yamikawa wannan budurwa , takarba tasanya cikin jakarta tadauki mayafi tadaura samankanta tareda rataye Jakarta tadauki hanyar fita ,

seda budurwar ta tsaya suka kalli juna kowanne ya harari dan uwansa daga bisani budurwan tasamu daman fita taja kofar da karfi tarufe, "

Hmm cin amanar dakasa gaba kenan kana tunanin asirinka bazai taunuba wataran , heelah tafadi gamida gyara tsayuwa tana kallon faruk dayanemi guri yazauna yana kallonta,

tsam yamike yanufi inda take cikin yanayi na magiya yashiga fadin ,"

Sweet mekike kokarin fadine wlh ba abunda kike tunani bane kinsan bayanda za ayi naci amanarki kamar yanda kike zargi tayama zan iya hada soyayyarki da wata macen kema kesan abune mai wuya agareni yafadi yana kokarin rungumarta , cikin sauri tamatsa baya tana fadin, "
Hmm faruk kenan kaifa namijine , ko kamanta takenku cewa namiji ba dan goyu bane to dan meyasa zan yarda da wadan nan zan tukan naku, bari kaji niba long talk nazo muyi dakaiba, dan numfasawa tayi sannan tamatsa daga inda faruk yake tanufi kujeran da yatashi tazauna kafin tacigaba da fadin ,"

ni dakai mundau tsawan lokaci muna tare tun before nayi aure still harnayi auran bamurabu ba muncigaba da kasancewa tare , ina baka kulawa da soyayya da lokacina wanda ko mijina da Dana da aikina ban bawaba, amma karshe cin amanace zata biyu bayan kyautatawar da namaka,

nasan abaya banida madubi naso dakauna danake dubawa face kai tun muna school a England bayan kammala warmu Allah baiyi zamucigaba da soyayya dakaiba , harna dawo gd nayi aure, sebayan aurena kafin allah yayi haduwata dakai har muka kulla wata soyayya sabowa wacce ko tunanin aurena banyiba nasaki jiki dakai namance da aure dake kaina ,

To amma yanzu na dawo haiyyacina , dagowa heelah tayi takalli faruk tana fadin, "

Gaskiya bazan boye makaba , ina kaunar mijina da dana kuma duk abunda zai kawomin cikas atsakanina dashi zan iya dakileshi , ina nufin akwai wani gibi dana bari atsakanin aurena banyi tunani akwai mecikeshiba, amma saboda sakaci irin nawa da rashin kula wata tana kokarin cikemin batareda na ankaraba, cikin katsaita da magana faruk yamatso daga inda yake ya tsuguna saman carpet tareda daura tafukan hand dinsa saman thigh din heelah yana fadin,"

Sweet waimeye kikeson fadine ban gane inda maganganunki yadosaba, mikewa heelah tayi tana fadin, "

ba lallai kaganeba faruk amma inaso kasani as from today na dakile duk wata mu amala tsakanina dakai zamudaina haduwa , banki mugaisa iya phone ba ya wadatar gaisuwarma intayi yawa tsan iya jigineta, "

Awani dalili zaki dakile mana jin dadi rana tsaka kodan kingani da wata shine kikeso kiyanke wannan danyan hukunci haka, faruk ya tambaya gamida mikewa tsaye yana kallonta "

Hmm kusan hakane because dama can inaso nasanar dakai haka to yanzu da time yayi nazodaide inda akazo gaban cin amanata , wlh tunda naganka tareda wata nake sakejin banason sake wata mu amala dakai , zanje nacigaba da kula da mijina da dana kamar yadda kowacce matar aure keyi nabakar lapia, heelah nagama fadin haka tajuya daniyar fita,"

Hhhhh yariya kenan wayace miki in akashiga bari saukin fita gareshi, ballema bariki irin nawa ba afita hakanan , karki mantafa kema cin amanata kikayi kinsan muna soyayya dake but kika zagaya kikaje kikayi aure ba tareda saninaba se labari naji amma duk namance dahakan nadawo muka daura inda aka tsaya ahakama nina nemuki kekinma banta da babina, amma wai nikike kallon idona kikefadin zaki koma gun mijinki zaki rabu dani,

mai mijin naki yafini dashi idanma ace kyau yafini da matsayi da kudi ninasan baifini zama namijibat , nasan saboda gazawarsa yasa kika amince dani kike bibiyata, ko kin mantane , nan kikezuwa da yunwarki mijinki baya kula dake bayida time dinki, nan kike zuwa ninake ciyar dake bawata gazawa kitashi kiyi godiya kitafi, wani dariya yafashe dashi kafin yacigaba da fadin ,"

Yanzu zaki koma kicigaba da zama da yar uwar takine , dan wannan mijin naki dashi da mace marabansu kadanne , gwarama ke wani lokacin kina nuna mazantakan kikwaci hakkin ki awajansa , wani lokacinma baya ahankalinsa wayo kike masa, ince ahaka kuke lallaba rayuwar harkuka haifi dan naki dakikeji dashi,

hmm tode idan wannan rayuwarne muna nan zakidawo kitarar dani , dan kyau ko kudi ko wani mukami bashi bane, kanuna kai namijine shine magana faruk yafadi yana wani kakkashe idanu , yana shafa suman habansa yana dariya,

heelah tacika tab da takaicin magan ganun faruk da dawani abun agefe seta dauka tarutsa masa kai dashi , yanzu mijinta yake duka da wanga kalamai haryake kokarin kirashi da mace ,hmm lallai kuwa da yasan waye IG da wadan nan zantukan basuyi saurin fitowa daga bakinsaba, kyauda matsayi kawai yasani baisan sauran zancenba, inbanda rashin kulawa da IG dayake mata maima zaisa tayi kokarin zuwaga wannan mutumin haryake jifanta da wadan nan zantukan girgiza kai heelah kawai tayi because tarasa abincewa, nan tajuya tayi ficewarta tabar faruk awajan yanata dariyar asara,

parking space tanufa tashiga motarta taye mata key tafice daga cikin hotel din tadauki hanyar gida, gudu take sosai tana tafe tana zuba tsaki tana mai takaicin faruk a rayuwarta, bawani bata lokaci hanya ta kawota gida tashiga yiwa mai gadi hon , cikin hanzari maigadi yatasu yabude mata geat takutso da motar cikin filin gidan ko dai daita parking batayiba tafito tanufi side dinta,

Tana shiga ta yada handbang dinta saman sofa itama zubewa tayi tazauna Tana tunani iri da kala cikin ranta, tadau tsawon lokaci tana zaune agun daga bisani tamike tahaura sama tanufi bedroom dinta,

*****neesha*************

aban garansu nisha kuwa, shopping din kayan abinci sukajeyi komai da komai nabukata ajmal yasa aka dankarashi cikin moyarsa daga bisani sauka sake daukan hanya, atunanin nisha hanyar gida yakamata sukama sekuma taga yama hanyar wani wajan daban, tafiya suke cikeda nitsuwa ajmal yakunna sautin Qur'an cikin mota sa yana saurara yana kumabi ahankali,

gaba daya nisha jitayi ta tsorita inakuma ajmal zaikaiso , dan haka seta kasa hakuri tadago kai kadan tadubeshe cikin barin baki tace, "

in,,na,,kuma zamuje? hankali kwance ajmal yajiyu yakalleta kafin yace,"

gidan da ake seda kan mutane abunda yace kenan yamaida hankalinsa ga tukin dayake, hadiye miyu nisha tayi tazubawa sarautar Allah ido dagani inda zasu, sunyi tafiya sosai kafin hanya takawosu wata anguwa gurin shiru yake kaikace bamasu rayuwa cikin arean daidai wani gida dan madaidaici maikyaun gaske ajmal ya tsaya yashigayin hon,
Chapter 36 · 0% Book details