← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 38

Sashe 15

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ma tanufi bedroom dinta, Nisha tana shiga bedroom din toilet tanufa tayi alwala tafito tayi sallah , bayan idar wanta kamar kullum tashiga yiwa umma da abbanta addu'a da fatan alkhari,

tana kammala tamike tareda samun guri daga bakin gadon tazauna yunwa takeji sosae because tunsafe rabonta da tasawa cikinta wani abu kuma bata san cin abinci ita kade, tasaba ci tareda su fadeela, dan haka tazauna zaman jiransu,

jin hon din mota tashigo haraban gdn yasa Nisha mikewa, tanufi window domin lekawa taga waye, ganin cewa su fareeda suka dawo tasaki wani murmushi jin dadi, Allah kadai yasan miss dinsu datayi agdn yau,

nan takoma tazauna tana jiran shigowar su, ba adadeba sekasu sunshigo kamar yanda aka jefosu daya nabin daya,

washewa Nisha baki suka shiga yi yayinda suke karisa shigowa, reeda ce tasuma magana tana cewa," sannu da gd sis da alamar yau gdn nan bai miki nice ba, fareeda ne takarbi maganar dacewa,"

inafa zai mata dadi bama nan tafara cike da zulaya, don't worry kinkusa dena missing kema yayinda tamike saman bed tana sauke gajiya,

I'm feeling hungry wlh reeda ta fada tana shafa cikinta, nima yunwan nakeji fadeela tafada tareda mikewa tana kallon Nisha daketa faman zuba musu murmushi,

Ke kinci abincinne ko bakijin yunwane , aa dama kunake jira banajin dadinci nikadai, alright bari naje na kawo mana abincin, fadeela tafada yayinda tanufi hanyar waje,

tana zuwa kitchen tasamu baba Barka ta tsaka da aiki, ganin fadeela ne yasa ta tsagaita da aikin datake, tashiga washe fadeela baki tana fadin," yan matan daddy andawo, " wlh baba Barka kuma gashi yau mun dawo da yunwa,

shine nace bari nazo na daukar mana abincin, lah ae ai dakin koma abunki yanzun nan zan kawo muku, a no karki damu, bari nadauka dakaina, tana fadin haka takai hanu ta dauki food flas din abincin tareda plate din abinci, tafita tareda komawa bedroom dinsu, tana shiga ta baje musu kayan abincin saman capet,

nan ta tadauki plate tashiga saka musu abincin nan suka sakko daga bed din suka suma cin abincin, sunci suna dan hiransu , seda suka kammala Nisha da reeda suka shiga tattara kayan da sukayi amfani dasu suka maida kitchen,

bikin kml yanata kara matsuwa yau saura 2 weeks, yau gd yayi baban bakowa Hajiya rabi,

kamar kullum dasuka saba banyan gama breakfast dinsu sukan dawo parlour suzauna su dan taba hira, ammi yau bata fita office ba kasan cewa weekend ne ba aiki, Hajiya sesu fadeela, Nisha yau bata jin dadi maranta naciyo saka makon bakunta na wata,

ammi ta bata magani tasha sannan tasheda mata da ta kwanta tayi baccin ta tahuta, hira suke sosae cikin nisha di, jin sallmar da ake yasa suka zubawa kofar parlourn ido dan ganin mai shigowa,

gaggo rabice kanwar dadinsu ketafe hanunta dake da jakarta, cikin shirinta mekyau fiskarta ta dauke da murmushi yayinda take karisuwa ciki, bayanta dauke da mai gadi yana tafe da akwatin kayanta,

su fadeela ne suka tashi dasuri sukayi kanta suna fadin," oyo oyo gaggo sannu da zuwa, cikin farin ciki ta rungume yayan nata tana fadin," my daughter's kune kuka kara girma haka masha allah ashe nakusa na auradda yayan nawa mekukeci haka gaba daya kun dawo wasu broilers daku, tafada cikeda zulaya tana dariya,

cikin sunnar da kai alamar kunya suka shiga yimata dariya tareda kokarin karbar jakar hanunta, karisuwa tayi kusa da Hajj mama tazauna tana sakar musu murmushi,

Mutan kd irin wannan zuwan bazata haka, ammi tafadi tana kama haba, dariya goggo rabi tayi tana fadin," wlh kuwa dama cewa nayi zuwan bazata zan muku, Daddy ne kadai yasan da zuwana shima kuma na kwabeshi nace kar ya sanar daku,

carab Hajj mama takarbi zancen da cewa," a lallai kin sham macemu, ina mutumin nawa shima kwana biyu shiru kamar baya nan ku leko mutane bayayi,

dariya goggo rabi tayi tana fadin," muhaiseem wai , shifa Hajiya tafadi, yana uganda, yakusa dawowa ae shima zai zo bikin kml goggo, hmm Allah yasa nasan halin mutumin da kalula,

dariya sukayi daga bisani ammi tace," Allah yasa hutun da yawa akazo amana, dan kema kin dade rabunki danan,

kede bari ae yanzu se kungaji da ganin, dan har bayan auran kamal ina nan kusuda uwata dan tayi kewanta so much, tafada tareda kwanciya shouldern Hajj mama,

dariya sukayi Hajj mama nafadin," kede rabi bansan yaushe zaki girmaba har yanzu wani abu kike kamar yarinya , yo ba dole ba yar uwatan Hajiya guda ammi ta fada na dariya, ato nima shi nagani goggo rabi tafadi tana wani sake nukewa,

lah namance bamu gaisaba natsaya surutu tafadi tana dariya, nan tashiga gaishesu suka amsa cikin fara'a da muna suna tambayar ta ya hanya tace alhmdllh,

nan suka cigaba da hiransu cikin raha da nishadi, kiran sallan azaharne ya dakatar dasu daga hiran, daga bisani goggo rabi takalli su fareeda tace,yayan nan muje kutayani daukan kayana mukai dakin Hajiya, yo kaji matar nan ga dakuna da yawa agdn nan bazaki bari nasa baba Barka ta gyara miki inda kikeso kishigaba fadar ammi tana kallon, rabi ,

aa nikam yau ina kusa da Hajiya ta dakinta zan sauka because nayi kewarta, tafa tana kallo Hajj mama tana dariya,

shikenan to autar Hajiya se kudau kayan ku isa mata dashi, ammi tafadi yayinda take kallon su reeda, nan suka dauki akwatin kasan cewa akwatin biyun suka raba kowa yadauki dada suka fita, yayinda rabi da Hajiya suka rufa musu baya, banda ammi da ta nufi kitchen dan duba halin da baba Barka take ciki,

tana zuwa tasamu baba Barka takammala komai, nan ta tayata suka jera komai inda ya dace, daga bisani ammi tanufi bedroom dinta sallah, tana shiga tayi alwala tayi sallah tanufo kasa,

direct bedroom dinsu Nisha tanufa domin dubata taga awani hali takeciki, tana zuwa tasameta kwance tana bacci da almun baccin nata yayi nisa sosae, dafa koshinta tayi wanda yayi sanyi qlau da alamar zazzabin da takeji ya sauka, ganin tana zufa yasa ta dauki remote din AC ta kuna mata takuma rage fawanshi kadan, ahankali sanyi mai dadi dasa kwanciyar hankali ya lullube dakin nan taja mata kofar tafito,

akokarinta nafita su fadeela suka kunno kai zasu nufi bedroom dinsu, kukuma fa ammi ta tambaya, sallah zamuyi sukaba amsa atakaice, to kadde kutashi yarinyar nan , to shikenan karki damu baza mu tashe miki babynkiba suka cikin zolaya suna dariya suka she dakin nasu,

ammi ban garan Hajiya tanufa tasanar dasu abinci ya kammala sufito suyi lunch, rabi tashiga wanka bari inta kammala se mutafi gaba daya Hajj mama tafadi , okay ammi tace tareda da neman guri tazauna sukashiga hiransu,

bada wani bata lokaciba goggo rabi tafito cikin wani shiri maikyau shin riga da siket na atamfa tamata kyau kamar su yakara fito da dan uwanta wato daddy , rabi duguwar ce fara mai diri maikyau ga manyan idanu kasan cewa ba inda taba mamanta wato Hajiya,

duk da ta manyanta ga wanda bai santaba in aka fadi she karunta bai ce tayi wannan shekaruba, murmushi yasakar musu yayinda take karisuwa tazauna,

dama ke muke jiran fitowar ki, the food is ready, ammi tafadi yayinda take kokarin mikewa daga zaman datayi, suma mikewa sukayi tareda rufawa ammi baya suka wuce babban parlourn, domin cin abincin,

suna zuwa suka tarar da su fareeda suna zaune a dining table din suna jiransu, lallai fa har kun rigamu zuwa da alama yunwace takoroku, goggo rabi tafadi tana dariya, suma dariyan su fadeela suka kayi batareda sunce komai ba,

dukansu zama sukayi suka suma cin abincin sunci suna dan hiransu har suka kammala, nan rabi take tambayar Daddy a tunanin ta yau weekend ba aiki, ammi ta sheda mata yafita dan yasanar da ita yana da tattaunawa da wasu abokan hurdansu, but kafin dare zai iya da wowa,

yinin ranar bakaramin dadi yamusuba because goggo rabi tasamu kawo musu ziyara , kasan cewa rabi tana da barkwanci bata da matsala kokadan shiyasa suke kaunar zama da ita,

aban garan Nisha kuwa tayi bacci sosae yanda yakamata itace batasamu farkawaba se kusan goshin magarib, bude ido tayi amma takasa mutsawa ta tashi gaba daya jikinta amace yake, rinza ido tayi kamar wacce takoma bacci amma azahiri idonta biyu,

hanunta nakan maranta dayake dan murda mata da because dama dan baccin da tayine yasa tadan rage jin zogin, ta dauke dugun lokaci ahaka tana kwance idonta narufe, harsu fadeela suka shigo sukayi sallah suka sake fita duk akunneta tana jinsu ,

ganin kwanciyar kamar shike kara mata radidin datakeji yasa tamike har wani jiri jiri takeji, gaba daya tagama laushi, ahankali tasuma cire kayan jikinta, tareda samun towel ta daura tanufi toilet, wanka tayi sosae, daga bisani tafito tanemi kaya tasa,

ahankali ta taddafa tanufo parlourn ganin shiru ba alamar kowa aciki yasa tanufi inda tan suka saba zuwa, akokarinta nabarin parlourn, taci garo da AJEEMAL dake kokarin shigowa parlourn , kallon kallo sukashigayi, yana kallonta tana kallonsa da rinannun idanuwanta da suka canza launi,

dan jabaya yayi kadan yana sake dubanta kadan kamar wacce yau yataba ganinta, ita kuwa jiki se bari yake ganin irin kallon da papan aheel ke mata wacce itama batasan wani irin kallo bane wannan,

," follow me abunda yace kenan yafara kokarin juyawa, ganin batayi mutsiba yasa yajuya tareda cilla mata wani irin harara," ko bakiji abunda nace bane yafada cikin wata irin murya, " naji Nisha tace bakinta nabari, juyawa yayi itama tarufa masa baya,

tafiya take ahankali yayinda takejin zuciyar ta kamar zata faso heat dinta, tsabar tsoro,

part disa yanufa yatura kofar yashiga, nan ya tsaya tsakiyar parlourn yana jiran shigowar ta,

Nisha kuwa tsawa tayi a kofar parlourn takasa shigowa, tsoronta mai zai fada mata, "baza kishigo bane, nisha ta tsinkayi murya AJEEMAL yana tambayar ta, shigowa tayi ahankali tareda sake bude kofar dakyau because in abun yatashi naguduwa ne basetasha wahalar bude kofar ba, sede tafita da gudu, close the door and seat down here, yanuna mata saman capet, yana tsaye yana kallonta tamatsu ahankali ta tsuguna inda yanuna mata jikinta se bari yake kanta na sukuye kamar wacce ta aikata ba dai ba,
Chapter 15 · 0% Book details