← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 38

Sashe 19

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

seda aka kammala wa matar sannan tamike tasanya mayafinta tareda ciru kudi ajakar tamikawa matar tana fadin," to Aunty sofy gashi nagode nibari nawuce still hankalinta nakan Nisha,

okay Hajiya zulai nine da godiya se anjima kigaida gd Aunty sofyn tafadi, to gd yaji daganan hajiyar tajuya tafice,

bada wani bata lokaciba aka samu daman farayiwa su fadeela, emergency abunka da kwararro basu wani jima sosai shagon salon din ba, nan da nan aka kammala komai,

gyaran kai da kunshin da aka musu yayi kyau sosai especially Nisha yanda kunshin hanunta dana kafarta sukayi mata kyau kai kace itace maryan,

bugu da kari yanda gyaran gashin nan yayi kyau yasake black dashi se wani walwali yake yana daukan eyes,

ita kanta kallon kanta take tacikin mirror tana sakin murmushi yanda gashin kanta yasake kyau dashi ya zubu har bayanta kamar wata kyakykyawar ba india,

hasali ita kanta matar shagon tayaba da kyan yarinyar dakuma sumar da Allah yamata,

haka su fareeda suka komai yayi yaji allhamdullah because suma ba bayaba wajan kyau da halittar gashi, amma de sirrin kyau irin na Nisha abun ba acewa komai say masha Allah,

Fareeda ne ta dannawa kamal kira, ganin ya dauka nan yashiga sanar fashi sun kammala, nan yace mata gashi nan zuwa, jin haka yasa suka zauna zaman jiransa,

ba a wani dade ba sega motar kamal ya iso, inda yaderesu dazu nan yayi parking yana jiran fitowar su,

jin alamar isuwarsa , yasa suka mike reeda tabude handback dinta tazaro kudi ta sallami matar, daga bisani suka mata sallama suka wuce,

Inda yayi parking suka nufa tareda shigewa motar , daganan kamal yayiwa motar key suka dau hanyar gd,

sannu hankali har allah yanufa suka iso, kamal ya danna hon mai gadi yabude masa geat yashigo yanufi compound din gdn yayi parking daga bisani suka fito, fadeela kikawomin food part dina quickly kamal yafadi tareda kokarin maida kofar motar yarufe,

to fadeela tafadi, daga bisani baki dayansu suka nufi sashin su ko takan su Hajiya basuyiba direct parlour suka nufa suka nemigu suka zauna kowa yashiga maida ajiyar zuciya,

reeda ne tamike tanufi kitchen, tana zuwa tasamu baba Barka tana tsaka da aikace aikacen da tasaba, ganin reeda yasa ta tsagaita da abunda yake tashiga fadin," yayan daddy kundawo, eh wlh yanzun nan shigowar mu reeda tafadi yayinda take tambayar abinci, ayya to bari nazu na hada muka abincin ku koh , barka tafadi, okay reeda tace tafara kokarin barin gurin,

cikin hanzari barka tace," yauwa dazu bayan fitanku telan nan yazo yakawo dinki nakarba nakai muku bedroom,

reeda bata jira barka takarisa maganar taba tajuya dasauri takoma parlour tasanar dasu fadeela dinkinsu ya iso,

daga fadeela har Nisha bayan reeda suka nufa suka shiga bedroom din, saman bed suka hangi ledan kayan, nan suka karisa shiga tareda haurawa saman bed din suka shiga dai dai da kayan ledar,

wani tsadeden Court less ne purple color mai kyan gaske da daukan ido da alama dinkin da zasu sane nawajan dinner da za ayi gobe,

gown ce duguwa kala 3 iri daya anyi masa tsadeden dinki yayi kyau sosai, haka sauran dinkuna da zasusa abikin suma sunyi kyau sosai ,

nan suka shiga shiga gwadawa suna kallon junansu, farin ciki far zuciyoyinsu, musamman Nisha da tamatsu gobe tayi taganta cikin wannan gown din,

wannan ranar sun wani cikin farinciki sun kosa gobe tayi jisuke kamar sujawuta, dan ko makaratarsu sundau hutu se angama bikin kml, because bikine dasuke ji dashi,

washe gari kankame gd ALH ABUBAKAR MODIBBO BATURE yacika da yan uwa da abokan arziki kama daga kawayan ammi matan abokan daddy, friend dinsu fadeela yan school dinsu su fauzee da sauransu , gakuma salma kawar Nisha,

yau aikin gdn yafi karfin barka ita kadae, hakan yasa tasa akara yawan ma aikatan, tundaga iman restaurant aka debo mai aikata domin girke girken gdn, c

ciye ciye da tande tande gdn a magana abun se wanda yagani,

yamma lis, ango kamal da abokansa acan gdn masaukin bakin Daddy, can suka ya dazango suma anyi musu ordern abinci iri iri da abunsha,

kamal nazaune yana kwance saman gado idonsa nakallon sama, kamar mai nazarin wani abu, jin saukan duka saman ciyarsa yasa yamike zaune yana kallon abokin nashi yana fadin," meye haka kamal yafadi yana hararo abokin nasa, oh sorry my man naga kamar baka sense dinkane but tundazu naketa magana naji shiro baka amsaniba, abokin yafadi, so what happened

dan wani guntun tsaki kamal yana fadin," nothing kawai kamal yafadi yana kokarin mikewa, yazakace bakomai bayan face din ka yanuna akwai alamar problem,

yaufa ranar nishadine indan kasan akwai wani matsa gwara ka amshi wannan karage zafi kar dan karkaje wajan dinner nan ba walwala afiskanka but today kai angone, abokin yafadi tareda mikewa yana miko masa shishan hanunsa, "

karbi kadanja nan da nan duk wata damuwar ka zai yaye kaji kwakwalwar tayi fine,

wani bazan harara ya kamal yawatso masa yana Fadi," kaide har abada bazakayi hankaliba kb abuda kamal yafadi kenan yasa kai yafice yabar dakin,

mtsww banza daga naganka cikin damuwa insun tai makonka shine kake kokarin fada min baka, bakomai kaje can damuwar ta kasheka, kb yafadi tareda bajewa saman bed yana cigaba da zukar abarsa ,

can parlourn kamal yanufa infa wasu abukan nasa suke shakatawa, zama yayi kusa da wani friend dinsa yanata faman sake wani abun tsaki,

kai kuma fa tsakin mai kake abokin ya tambaya, " wani guntun tsaki yasake saki yana fadin," kb mana suyake lalle sena koma ruwa, ranar aurena ma bai banniba"

, hmm nasani ai mai hali baya fasa hali ko ainane kakyaleshi da shirmensa yanzu katashi kaje kaahiga wanka kashirya, kasan time se gudu yake bajiranmu zaiyiba, ga aiyuka agabanmu, kasan amarya tafadi kar amusu african time,

mikewa yayi, tareda komawa bedroom din, koda komawa ya tarar da kebi na baje yana cigaba da aikin da yabarsa yanayi,

girgiza kai yayi tareda shigewa toilet yana mai jin haushin kb duk da cewa dan uwansane but haushinsa yakeji because shine ummul aba isin damuwar da yake ciki yanzu,

aban garan su, Nisha kuwa , tundaga parlour kakejin muryoyinsu da shewansu suna kyakyatawa da kawansu ,

yau Nisha kamar ba itaba ta zage se tadi ake, because gata ga salma kawarta anan ne salma ke basu labarin bikinta saura 1 month tana gaiyatarsu ,

Murna gun nisha ba a magana ganin bikin babban kawarta yakusa, dan yanda takeji dabikin salmanta ko nata iyaka kenan, yanda nisha tasake take surfa surutu, bakaramin mamaki yabawa su fadeela ba,

basuyi tsammanin haka Nisha takeda baki da surutu ba,

kawansu reeda ba girman kai sunzage se fira suke dasu nisha da salma kamar sunsansu musamman Nisha da labarin ta ya gabama isa garesu wajansu reeda, sun kuma sheda masu irin kaunar dasuke mata kamar ciki daya suka fito, kullum surutun su a school Nishan su,

se guraren magrib su Nisha suka nufi toilet yin wanka tareda alwala daya bayan daya, daga bisani masu yin sallah sukatashi sukayi haramar alwala sukayi sallah wayanda suke fashi suna zaune suna danna wayoyinsu,

bayan ko yakammal ibadarsa yakuma yazauna, ganin haka yasa reeda tamike tafice, akokarinta nafita taci karo da wacce suka kira domin tazu tamusu makeup, tareda mai tai maka mata agefenta tana rike da makeup kit a hanunta, nan tace musu sukarisa bari taje ta dawo,

jin haka yasa suka sakai suka nufi cikin bedroom din, ita kuwa reeda kitchen tanufa tayiwa barka magana kai musu abun tabawa bedroom dinsu, nan baba Barka tasheda mata yanzu kowa, daga bisani reeda tajuya takoma ciki,

koda shigowar ta tasamu har anfarayiwa fadeela, nan itama tazauna dayar tashiga mata, Nisha kama tana daga zaune saman bed suna hira da salma,

seda aka kammala wa fadeela, daga bisani Nisha tasakko aka shiga yimata, basu wani bata lokaciba abunka da kwararro nan danan aka kammala musu duka,

fadeela ne tadauki kayanta tashige toilet domin tasa, because, dakin da mutane bazai yiyu su canza kayansuba,

ganin haka yasa reeda taja hanun Nisha suka nufi wani dakin domin canza kayansu suma, kuda isarsu dakin reeda ta dauki nata kayan tayi toilet din cikin bedroom ne domin bawa Nisha daman shiryawa itama,

nan itama tashiga sari gan koda mamakinta dake kayan yashige , hakan nanufin takara gibane ko me, duk dacewa shima telan bawai ya gwada taba bane ganinta kawai yayi,

kasan cewarsa kwararre shiyasa bai nemi gwadataba, gown din yadan matseta kadan, gaba daya shef dinta ya bayyana masha Allah,

fareeda ne tafito idonta yasauka kan Nisha datayi tsaye tana kallon gown din jikinta, wow masha allah Nisha tsinkayi muryan reeda, dagowa Nisha tayi tana kallon reeda data tsaya tana kallonta,

reeda matsowa tayi tana fadin," kai my lovely kiga yanda gown dinnan ta mashi jikinki kuwa gsky tamiki kyau sosai,

murmushi nisha tayi tana Fadin," nagode kema tamiki kyau ai, murmusawa reeda tayi tareda fadin," okay muje aima dauri musamu mudanyi picture kafin motarcin dinner su suma zuwa,

ahankali Nisha take daga kafa, because yanda takejin kayan ya matseta dan haka setakeji kamar tsirara take, dan gaba daya a tsarge take ita damuwartama karya barke mata cikin mutane aji kunya,

tundaga shigowar su nisha yan dakin suketa wow wow nikuwa nace,( baku suma wowba sema an kammala kwaliyar,)

nan akashiga rangada musu dauri, kowacce da kallan daurinta, sunfito sunyi kyau dasu kai kace yan ukune masha allah, gaba daya sae suka zama abun kallo, gani yanda suka fito sukayi kyau dasu kamar wasu taurari,

kuwa phone dinsa yadauka yashiga daukar su a photo, suna cikin daukar hutun ammi tashigo tana sanye cikin kayaceccen shirnta mai kyau da ban shaawa sewani walwali take uwar angoba ,

masha allah abinda ammi tafadi kenan sanda idonta yasauka kan kyawawan taurarin yayanta 3 , ganinta da su fadeela sukayi yasa sukayi kanta suna daga salfi,

seda tajira sungama daukan photon nasu daga bisani ammi taja hanun Nisha suna kokarin barin dakin, ganin haka yasa su reeda fadin ," ammi ina kuma zakuje muna pictures , babu yanzun nan zata dawo,

Ammi na fadin haka taja nisha suka fita, upstairs ammi tanufa da Nisha, direct parlourn Daddy suka nufa yanda manyan bakinta suke,
Chapter 19 · 0% Book details