← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 38

Sashe 25

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daukeso daga nan asasu cikin mota, cikin hanzari inspector Ahmad tareda doctor fu'ad suka suma tattara su kb baba mai gadi ya taimaka musu suka kutsasu cikin motar kamar yadda IG ya bukata,

Shima AJMAL din bin bayansu yasuma kokarin yi sekuma ya tsaya yana kallon saman capet inda aka daukesu kamal, hankali ya sunkoya, yasa hanu yadauki wani hadden zuben azurfa, mai kyalkyali da ban shaawa, kallon zuben yashigayi sosae daga bisani yadan sake wata murmushi wacce nima bansan tameye bace, sannan yamike tsaye tareda sanya zuben cikin aljuhu yanufi hanyar fita,

Jikin motar ya taddasu doctor fu'ad suna jiransa tareda maigadi daga gefe, seda ya kariso indasuke yakalli baba mai gadi yana fadin,"

agyara parlourn nan yayi excels arufe shi abunda yafadi kawai yasakai cikin motar yayi mata key, mai gadi dajin haka yanufi geat yabude musu suka fice
*****Nisha***************
Aban garan Nisha kuwa tunda tabar gurinsu kamal tawatsa da gudu tafice daga gdn, bata zame ko inaba sae gd gab goshin magarib, tundaga nesa ta sallami mai adaidaita tundaga kofar gdn ta tsaya tashiga goge hawayen dake face dinta, gaba daya fiskar yayi jawur dashi, seda tagama kimtsa face din ta, daga bisani takutsa kai cikin gdn, koda shiganta ciki bakowa umma bata ciki da alama tana bedroom dibta, cikin sanda tasuma tafi domin shiga dakinta, "

Seyanzu,? Nisha taji muryan umma wacce fitowar ta kenan daga daki , hanzarce Nisha tajiyu tana kallon umma cikin sanyin murya tace," eh seyanzu munata fira da salma ban ankaraba ashe magarib tayi, Nisha tafadi tana tsili tsili da ido, "

To seki samu kiyi sallah kizo ga abinci najiranki, to kawai Nisha tace tanu daki dasauri, umma de bin bayan Nisha tayi da kallo ganin yanda gaba daya fiskar ta tasauya bayacce tasaniba, kamar akwai wani abunda ke damunta, shiru umma tayi kamar mai nazarin wani abu daga bisani tajuya tanufi kitchen,

Nisha tana shiga daki toilet tanufa tazauna tayi kuka mai isarta tashare hawaye tayi alwala tafito, nan tashin fida sallayan tayi sallah tana idarwa tabarke da wani sabon kuka gaba daya abun ya faru yakuma dawo mata,

itakam tashiga uku ina zatakai hakin daukan rai har mutum2 wannan wace kallar kaddarace ta fada mata, lokaci daya akasi ya giftawa rayuwarta, sukuma meye dalilin su nashiga rayuwarta harsuke kokarin rushe mata gobenta, ?tana tsaka da sheshshekar kukan taji muryan umma,"

Subhanallah meyafaru meyasame ki kike kuka, ,? umma ta tambaya lokacinda ta karisu tasun kuya kusa da Nisha tana tambayar ba asin kukanta, cike da wayancewa Nisha tafada jikin umma tareda sakin wani kukan tana fadin,"

Umma ina matukar kewar abbana inason sashi cikin idona, inason sani wani hali yakeciki, Nisha tafadi nan da nan taji kukan ya hadu mata biyu, kukan kisan kai da kukan rashin abba, ba Nisha ba hatta ita kanta umma jitayi gabobinta sunyi sanyi zuciyar ta tayi wani irin rauni hawaye nasonyi zarya saman face dinta, kamar ta tayata suyi kukan tare but bazata jure ganin diyarta cikin wannan halinba, dan haka tamatse nata kwalan ta dago nisha tana fadin,"

Ya isa haka karki damu abbanki yana cikin kushin lapia kina misha fatan alkhari da addu'a a duk inda yake allah ya karkatu hankalisa gd, yanzu kitashi muje kici abinci umma tafadi tana mikar da Nisha tsaye suka fice daga dakin,

kwana2 da faruwan hakan amma sam Nisha takasa mancewa da abunda yafaru, koda yaushe jira take bincike yayi bincike taji sallaman yan sanda sunzo tafiya da ita, tana zaune tayi jugum adaki tana tunane tunane tajiyu sallama daga bakin door ana kokarin shigowa,

salma ce tafe taja ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Nisha dake kallonta da rinannun idanuwanta, cikin hanzari salma takarisa gadon nisha ganin yanda face din ta yakoma da alamar damuwa,

salma nazama ta dafo shoulder Nisha tana kokarin magana setaga Nisha tafada cinyarta tasake wani kuka mara sauti kasa kasa,"

salma nashiga ukuna na aikata abunda ya dameni, nayi abunda bazan yafewa kainaba

dagota salma tayi tana kallon tasuma tambayar ta,"

Lafiyanki mekike? fada haka keko wani laifine kika aikata kiketa wadannan zantukan, ? dago ido Nisha tayi tana fadin,"

Kisa nayi mutum harbiyu nan Nisha tazaiyanawa salma tun farkon wakanan lamarin har karshe , yanzu tunani na sun mutu ko suna raye allah masani Nisha tafadi cikin kuka mai tsuma rai,"

suna raiye basu mutuba kamar yanda kike expecting "

how kinsan abunda yafaru ne,? Nisha tafadi hanzarce tana zazzare ido,"

Eh but naga wautanki cikin lamarin kuma banyi tsammanin akwai wani sabon lamari da zaishigo rayuwarki kibuyeminba, ko danki bukaci idea daga gareni amatsayina na kawarki kuma aminiya wacce zamu kashe mubinne tare ba wanda yaji balle yasani why,?

salma tafadi tana kallon Nisha datayi mata zuru da ido cike da mamakin magan ganuta takasa cewa wani abu, kinyi shiru inata surutu bakice komai ba salma tasake fadi still idonta bakan Nisha ,"

Please bani labarin taya kikasan wannan abun yafaru, Nisha tafadi asukwane, ,"

dan gyara zama salma tayi tana fadin," inba ki manceba mb friend din kamalne , kuma wannan abun da yafaru kanshi nazo muyi magana, shine makasudin zuwana gdnan,

Nisha share hawayen face din ta tayi hade da gyara zama tana sauraron salma da abunda zatace,"

Mb baya gari baisan mai akecikiba, yakirani yakuma sanar dani abunda yafaru, yasheda min tun bayan faruwan lamarin kamal yakirashi cikin tashin hankali da damuwa yakura masa jawabin abunda ya wakana ,

Ba damuwarsa illan dakika masaba, damuwar shi baisan mai ya aikata agarekiba fatan shi Allah yasa ba abunda yashiga tsakaninku ,

duk wannan abubuwan da suka faru babu laifin kamal, wannan duk shirin kb ne, yayi duk yanda zaiyi dan yacutar dake ta dalilin magan ganu mara dadi da kuma marinshi da kikayi

🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh
( Khaleeseart Raeeys)

Free book 🤗

Godiya mai tarin yawa gamasoya abun alfahari ina alfa hari daku koda yaushe 🤝

Page28

Kamal yayi iyaka kokarinsa wajan ganin ya tare duk wata hanya da hakan zai kasance

ganin haka yasa kb yayi amfani da kamal wajan cutar dake ta hanyar zuba masa abu cikin abunsha batare da saninsaba duk abunda kikaga yafaru time din kamal baisan da kasan cewarsaba,

dan nunfasawa salma tayi kafin tacigaba da fadin," allah sarki yanzu suna can suna amsar magani kamal duk ya gama daburcewa cikin wannan lamari da ya afku, kwata kwata baida masaniyar abunda dan uwansa ke shiryawa,

gaskiya kb takadarine hmm Allah ya kyauta yacigaba da karemu daga sharrin masu sharri,"

amin Nisha tafurta asanyaye, salma duban Nisha takumayi wacce tayi kalar tausayi se kuma tamai da idonta ga phone dinta dake gefen cinyarta tadauka tareda kai hand tadauki dan ma daidaicin phone din nisha,

wani number salma tashiga jerawa Nisha cikin phone dinta sannan tamikawa Nisha wayar tana fadin,"

gashi wannan numbern dakike gani nasanya miki cikin phone numbern kamal ne shiya bukaci da abaki because yace inda akwai wani issue daga gareki you can call him dan haka ki barshi cikin wayarki tana gama fadin haka tamike tana fadin,"

To nikam bari nawuce sena jiki tafadi tareda shigewa gaba itama Nisha mikewa tayi tarufa mata baya suka fice, kishingide umma take saman kujera wacce tun shigowar salma gurin ta sameta, ganin fitowarsu yasa umma ta mike tana fadin," har anfito

"Eh umma salma tafadi tana washe baki yayinda Nisha ke biye da ita,

" To kigaida gd kice ina gaida ummyn taki,

"Zataji inshallah daga haka sukayi sallama nisha itama daga bakin parlourn sukayi sallama tajiyu ta dawo kusa da umma tareda yin matashi da cinyarta tana sauke ajiyar zuciya ahankali jitake zuciyarta fes,.

dan shafo suman kan Nisha umma tayi tana fadin,"

Ina zuben da abbanki yasemikine kwana 2 ban ganshi ayazunkiba kin gaji dashine ko yardashi kikayi awani guri dan nasanki da shiririta wani lokacin,

rass nisha taji kirjinta yabuga nan ta sulale tamike daga kwanciyar tashiga kallon yatsun hand dinta sam ko batayi da zuben baya hanuntaba se yanzu da umma ta ankaradda ita "

to ina zuben yashiga kuma ina nayaddashi? Nisha tashiga tambayar kanta cikin zuci, ganin umma ta tsareta da ido yasa Nisha kirkiro murmushi tashiga sosa keya tana fadin,"

Nima bansan wani lungun yashigaba tunda natashi abacci ban kalleahiba maybe ya yashiga wani gurin kinsan dama bai kama yatsun hand dina sosaiba, amma dai zan dubashi bata jira taji mai umma zatace ba tawuce fuuu tayi daki tabar umma awajan,

tundaga wannan lokacin nisha ke neman zuben ta dan zubene mai matukar mahimmanci agareta zuben da abba ya bata lokacin da yasa kafa yabar gdn bai sake waiwayan suba,

batan zuben ba karamin taba zuciyarta yayiba duk lokacin da take tare da zuben jitake tamkar da abba take tare, gashi yau tawayi gari babu shi atare da ita bata kumasan inda taya dashiba,

aban garan kamal kuwa kullum tsumayin kiran Nisha yake dan atuna ninshi kiranta agareshi tamkar tayafeshini komai ya wuce,

ita kuwa Nisha tun time din da salma tasanya number kamal cikin phone dinta batayi tunanin kiraba bata kuma ji alamar zata kiraba har se lokacin da umma ta kwanta rashin lapia sannan tasamu daman kiranshi nanma ba yanda ta iya batada kuma wani zabi because tasan yana da arzikin da zai iya taimaka musu , awannan yanayi Nisha ta dangana ga kamal wanda lokacin sukayi ido biyu da nabilah wacce ta daura mata karan tsana duk da batasan dalilin zuwan Nisha wajan kamal,

Atakaicede wannan shine labarin abubuwan da suka faru abaya***********

Parlourn ne yadau shiru tamkar bakowa, kama daga su fadeela muhaiseen da sukejin abun da yafaru abaya da kuma abunda kb ya aikata, kowa da abunda yake sakawa cikin zuci,

Nabilah kanta kasa tagagara daga kai gaba daya kunyan Nisha da tausayinta sungama mamaye kwanyarta, ta kaicin abunda dan uwanta kb yayi yagama bata mamaki duk da tasan ba bakon al amari bane agareshi komai akace yayi babu makawa zai aikata, suna tsaka da wannan alhinin sukajiyo sallama ana kokarin shigowa,

dagowa sukayi sukayi dukansu suka tsurawa kofar door din ido dan ganin mai shigowa, goggo rabi ne tafe tana sanyi cikin lullube fiskarta cike da fara' a ta kariso tsakiyar parlourn tanabin kowannensu da kallo daga bisani ta tsaida idonta kan nabilah dake ta matsar kwalla, "
Chapter 25 · 0% Book details