← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 38

Sashe 7

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"lallai baki yabude sauki yasamu, washewa sukayi da dariya dukansu nanfa hira ya farke aka cigaba da tadi, tadi suke sosae wanda sundau tsawon lokaci suna yinsa , yanzu kam Nisha ta dan sake sosae anyi firan da ita, hajja mma data fahimci hakan ba karamin dadi tajiba, Hajiya bata wani dadi sosae ba wajan hiran ta mike taimusu seda safe domin kuwa bakaramin gajiya tayiba zaman asibiti ga ba bacci mai Dadi, gakuma dawainiyar aheel, sallama sukayi ta tafi tayi kwanciyarta, ba adadeba fareeda ma tamike saka makon wayanta dake ringing itama seda safe taimusu ta tafi, sunyi tadi sosai da fadeela sewajan karfe 10:30 lokacin bacci yafara cinye idon fadeela itama mikewa tayi tana fadin,

" Nisha kitashi muje mukwanta wlh bacci nakeji sosae, aheel baiyi bacci ba karmutafi mubarshi shikadai, rabu dashi papanshi zezo ya daukeshi ae ,

" aa kije kawai zan biyoki dan nima banajin baccin yanzu zamu danyi hira kadan, murmushi fadeela tayi tana fadin,

"naga kamar zama da aheel yana miki Dadi koh,

"hmm zaki gajima inde yaron nane surutain sama kadae ya isheki,

"aa nikam bawani isata dazaiyi, alright se kinshigo to, tafada tareda juyawa tafita, maida kallonta ga aheel tayi da ya tsura mata ido dan bayason ta tafi tabarshi,

"Aunty zanyi fitsari kikaini toilet , taimaka mishi tayi takaishi yayi fitsarin, ta dawo dashi tagyara masa kwanciyar tamasa matashi da cinyarta, suka cigaba da hirarsu wajen karfe 11: lokacin sunyi laushi daga shi har Nishan, domin kuwa bacci yafara cinye idon su, tuni aheel yasuma baccinsa nanfa itama tafara gyan gyadawa,

Motarsace ta kunno kai gdn , jin hon yasa mai gadi yaye geat din gdn, nan ya tako motar ya kariso haraban gdn yayinda yayi parking, mitowa yayi yayi da mai gadi yakarisu da hanzari yana mai kwasan gaisuwa, amsawa yayi tareda tafiya yakarisa ga part dinsa , nan yatura kofar yashiga back din hanusa yacillar kan kujeran, direct bedroom dinshi yanufa kokarin cire kayan jikinsa yasuma yi seda yacire yarege daga shi se dan short dress daga bisani ya dauke lallausan towel dinsa yanufi toilet, wanka yashiga yi sosae dan yau ba karamin gajiya yayiba , fitowa yayi jikinsa daure da towel iya gwiwa, kallon inda mai yake bai kalleba because wani kasala yakeji gakuma gajiya gaba daya yagama yin laushi, jallabiyarsa yazura tareda fitowa yanufi kitchen tareda hadu coffee yasamu gu daga dining yasamu waje yazauna yana sha, seda ya kammala yamike ya koma bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa, kashe wutan dakin yayi tareda kwanciya saman bed din hade da janyo blanket yarufu, wayarsace tayi kara hakan yabashi daman lalubu phone din dan yaga waye meshirin shiga hakinsa acikin night haka, dago phone din yayi yana kallon screen din wayan , matarsace raheela ke tafaman kiransa komai zatace masa oho, wani tsaki yaja da kamar bai daukaba sekuma ya daga batareda yace komai ba,

" hey my baby yau nayi dare sosae gashi but ina ta missing dinka gakuma wani accident din da aka kawo yanzu, so bazan samu dawowa ba se zuwa tommorow, baijira takarisa maganar ba yakatse wayar tareda cillata gefe namaijan tsaki,

" stupid dama yau kika saba kwana hospital koba wani issue zakice akwai meye problem dina da hakan yafada tareda sake lullube jikinsa hade da rufe ido yana maida numfashi slowly, firgit yatashi yazauna se yanzu ya tunada aheel, gaba daya gajiya tasa ya mata dashi, da sauri yatashi yanufi hanyar waje, bangaran Hajiya yanufa tareda murda handle din kofar yajita abude take yakutsa kai, dauke da sallama, turus yayi yayinda yakarisa shigowa ciki, binsu yayi da kallo duk sunyi bacci Nisha ma baccin barawo yasaceta, kan aheel na cinyar ta , itakuwa ta jingina bayanta da jikin kujera, tanata sheka bacci, haunsu cikin najuna, Nisha tareke hanunshi gam, wani abu yaji yatukare masa makoshi , gaba daya haushin yarinyar yagama kamashi , datasan haushita dayakeji bata fara gigin kusantu dansaba, matsawa yayi ahankali yafara kokarin jan hanun aheel tareda cire hanunsa acikin na Nisha,

cikin bacci Nisha taji aheel na kokarin zare hanunsa hakan yasa takara rike hanun gam , kamar wani zai kwaceshi, gaba daya jiyayi ransa yafara bacci gani irin rikon da tayiwa dansa, hunsa yasa akan na Nisha yana yamutsa fiska, daya hanun kuma ana aheel yana kokarin raba han nayensu, jin tarike gam yasa afusace yafincike da karfi wanda yasa aheel mutsawa yana fadin,

" ah. Aunty hanuna yafada cikin nan nauyan bacci, yacigaba da bacci yana surutai, itakuwa jin aheel ya janya hanunsa yasa tasake jayo hanunsa ta rungume akirji, waro ido yayi yana bin hanusa da takamu takai kirji tanamai cigaba da baccinta, nanfa yafara kokarin jaye hanunsa jin haka yasa Nisha kokarin bude ido dayan hanunta tasa tana murza idonta, karfa idonta ya sauka akansa dake kokarin kwace hanusa daga nata kyansa ta zubawa ido wanda ta gagara dauke idon akansa, lumshe ido tayi tabude still tana rike da hand dinsa taki sakewa, ,

" hey madam samu dama kisakarmin hand na dauki dana yafada tareda hade gira, cikin hanzari takalli hand dinshi da tarike Gam sakuma tasake dasauri tana fadin,

" I'm sorry ta fad'i tareda mikewa tsaye , kauda kai yayi tareda daukan aheel yadaurashi saman shoulder dinsa suka nufi part dinsu, bayansa tabi da kallo jikinta se mazari yake sekace wanda taga wani dodo, cikin hantsari tabi bayanshi ta nufi bangaran su itama, tana shiga ta samu su fareeda duk sunyi nisa da bacci itama samun waje tayi takwanta dan idonta tuni yamata nauyi,**********

washe gari da asuba suka tashi sukayi sallah su farida suka koma bacci abunsu, qur'an Nisha ta dauka tasuma karatu kasa kasa take gudun karta shiga hakkinsu suna bacci ta dade tana karatu daga bisani ta dakata, addu'a tashigayi wa mahaifanta ita kanta sannan tashafa takoma tayi kwanciyar ta,

,sewajan karfe9:40 Nisha tafarka ganin babu kowa ita kade aka bari tanata sharar baccinta hakan yasa ta sakko daga bed din ahankali takarisa sakkowa, itama waje tanufa a parlour ta iskesu suna zaune, ahankali takarisa inda hajja mma take hadeda gaisheta amsawa tayi cike da fara'a tana fadin ,

"anishatu harkin koshi da baccinne tafada tareda kokarin dagata daga durkusawan datayi , cikin tsukuna fareeda tace,

" oh mubaza akulamuba hajja mma kawai aka sani, bude baki tayi daniyar magana nanfa hajja mma tace da ala kyalesu zumuje muci abinci ke muke jira daman tafada tareda jan hanun Nisha suka nufi dining table, time din baba Barka takammala komai ta ajiye inda yadace, fareeda ne ta bude abincin tashiga zubamusu, seda ta zubawa ko sannan ta koma tazauna domin fara ci, kuwa yashiga cin nasa banda Nisha datasa plate agaba tana juya spoon, tanason sake sa aheel aidonta, hajja mma duk tana duk tana kallon abunda take, yade nisha tunanin mekike,? cikin hanzari Nisha tadagu tana fadin,

" bakomai tana fadan haka tashiga tsikaran abincin tana ci, wayan fareeda ne yayi kara ta dauka cikin hanzari ganin mekiran , karawa tayi akunne tareda fadin,

" hello ammi ina kwana, daga daya ban garan ammi ta amsa da lapia, ya gd yasu Hajiya, qlu suke sede gd ba dadi muna miss dinki gsky fareeda tafada cike da shagwaba, fisge wayar fadeela tayi takara akunne tana fadin,

" ammi yaushe zaku dawo , ina daddy ,? kibashi wayan , daddyn ku baya kusa don't worry nanda 2 days zamu dawo, ammi tafa cikin sigan lallashi, yau to kuyi suri kidawo kiga new baby girl da muka miki fareeda ne ta kwace wayar dacewa,

" kuma ammi so beautiful inkika ganta zakiyi happy, ammi batayi mamakin maganar suba domin ta dade da jin labarin gurin Hajiya daga ita har Daddy sunsan zancen, to shikenan se mundawo din, daga Nisha har hajja mma kallonsu suke suna murmushi, sunyi fira sosai da amminsu daga bisani sukayi sallama yakatse wayar farin ciki fal zuciyoyinsu, suna kammala cin abincin suka koma cikin parlourn suka cigaba da firansu, sundau time suna hirarn daga bisani hajja mma takatse kiran dacewa,

" kun fasa fita shopping dine ko se rana tayi? cikin hanzari fadeela tace,"lah mun mance fira tayi dadi, lallai kam hira tayi dadi kutashi muje mushirya mutafi cewar fareeda duk suka mike, ganin ba alamar mikewar nisha yasa reeda taja hanunta tana fadin,

" dake zamu ae tashi mutafi tafada tareda jan hanunta izuwa ciki, hajja mma kam kallo kawai tabi bayansu dashi tareda mikewa tanufi bangaran ta , ba adadeba suka fito cikin shirinsu mekyau but koda suka fito basu tararda hajja mma a parlourn ba, hakan yasa suka bi bayanta domin yimata sallama, Nisha kam bata samu daman bin bayansuba daga waje tatsaya tana bin part din dataga AJEEMAL ya nufa da aheel tana karewa benen kallo , juyawa tayi danufin shiga part din Hajiya jin muryan aheel yasata dakatawa, da sauri ta daga kai takalli inda take jiyo muryan aheel, daga saman benan yake kwala mata Kira, Aunty see me yafada yayinda yake dago mata hanu yana dariya, washe masa baki tashigayi yayinda take daga masa nata hand din, daga sama take jiyoshi yana fadin,
Chapter 7 · 0% Book details