← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 38

Sashe 11

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" kabita kukoma inda kukafito sena dawo, abunda yace kenan yasa kai yafice tareda shigewa mota yafita, cikin sanyin jiki Nisha tariko hanun aheel nanfa yaro yanuke tareda yin rau rau da ido yana shirin kuka,

" ni yaunwa nakeji nan taga ya zame hanusa daga nata ya dingisa cikin daki, bai dadeba yafito hanunsa daukeda cheeseburger yana ci nan ya mika mata haunu tajashi suka fita, zuwa yanzu gd ya dumame da kamshin abinci kota ina, nanda nan suka kammala komai suka jereshi a dining table , daga bisani suka tattara izuwa part din Hajiya nan suka baje kolinsu na hira, nan sukaita hiransu har gorin goshin magarib, motar AJEEMAL ne yakunno kai mai gadi yabude masa geat, jin ana kokarin bude geat ne ya tabbatar musu dacewa su ammi sun isu, nan suka fito tareda watsawa aguje kamar wasu babies suka nufi motar,

AJEEMAL nayin parking suka karisu suna washe baki, reeda ne tabude kofar baya ammi ta fito fiskarta daukeda murmushi, nan sukayi kanta tareda rungume cikin kewa da murna, Daddy ne yafito daga gdn gaba shima suka shiga rungumarsa suna fadin sunyi kewarsa tareda karban karamin jakar hanunsa, okay nikam ba wanda yayi Miss dinako shiyasa ba akalli inda nakebama, juyowa sukayi cikin hanzari suna fadin,

" lah ya kamal ashe kaima kadawo, aa mantani akayi acan yafada yana tura musu baki, nan suka nufushi suna dariya tareda rungumarsa, suna jan hanunsa, to nikam kukyaleni karku yadani, sewani jana kukeyi, dariya sukayi gaba dayansu tareda karisawa parlourn mai gadi na biye dasu da suran ma aikatan gdn dauke da sauran kayansu, suna zuwa parlourn suka dire kayan tareda karamusu bangaji sukafi, su reeda suka dauki jakan kayan suka karisa musu dashi bedroom dinsu, farin ciki fal zuciyoyinsu, AJEEMAL kama tunda yadiresu yanufi part dinsa yayi alwala yanufi masallaci,

haka kamal ko wanka bai tsaya yiba shima alwalan yayi yafito, yana fitowa yayi karo Daddy shima zaitafi, nan yanufa masa baya suka wuce, aban garan ammi kuwa wanka tashiga yi sosae daga bisani tayi alwala tafito, kaya mara nauyi tanema tasa tadauki hijabi ta tada sallah, bayan ta idar tayi kasa parlourn shiru bakowa nan tafito tanufi parlourn hajja mma tasan baza arasasu canba, tunkafin ta katisa shiga takejin sautin muryoyinsu, dan haka takarisa tareda tura door din tashi dauke da sallama abakinta, kallo tabisu dashi yayinda suketa hiransu, suna ganin shigowar ta su fadeela sukatashi tareda nufuta suna fadin," ammi Miss u so much wlh, da bakwa nan gd ba Dadi, gd yakoma shiru, oh dama da muke nan mukesa gd yayi hayaniya koh ,? Ammi tafadi, dariya sukayi reeda tace," ammi bafa haka muke nufiba, hakane mn, tukunna ma kunyi sallahne da kuka zauna kuna hiranan, eh munyi dazunan muka idar , okay ammi tace yayinda yamaida kallonta ga nisha da aheel yayi matashi da cinyarta yana bacci, mazawa tayi kusa da ita tayi tazauna,

cikin hanzari Nisha sannu da Hajiya tafada tareda kokarin tazame aheel daga cinyarta, ganin haka yasa ammi tayi saurin cewa," zauna abinki, tafada yayinda take kallon Nisha, sunkuyar da kai nisha tayi tana fadin," ya hanya andawo lapia, lapia kalau alhmdllh, ya gdn I hope yana mike dadi, kuma ba matsalan komai , eh Hajiya , karna sake jin Hajiya nan call me ammi kamar yanda kikaji su fadeela suna kirana, kema yatace yar ta gaban goshima tabada tana dafa shoulder dinta, dariya su reeda suka shigayi jin abinda amminsu tafada nisha ta gaban goshine, cikin wasa ammi ta hararo su reeda dake dariya tacigaba da hira da Nisha tana fadin," kisake jikinki damu nan gdnkune, to Nisha tace tana sunkuyar dakai tana murmushi, yadae ina Hajj mama ne banji mutsintaba, ammi ta fada tana kallon reeda, dazunan tashiga bedroom sallah tode haryanzu bata fito. .,

batakaiga karisa maganar ba, Hajj mama tafito fiska dauke da fara'a tana fadin," ah mutanan US har hutun yakare , tafada yayinda take kokarin samun waje tazauna" wlh fa hutu yakare ni harna gaji da kasarma ammi tafadi, yo ae dama duk wanda yabar gd tofa gd yabarshi Hajiya tafada gami da dariya, gsky kam nan ammi tashiga gaida Hajiya, seda suka gama gaisuwan, Hajj mama tace," to kingafa new babynki, tafada tana nuna Nisha, eh naganta har mun gaisa ae, ," ayya ina mai gidana koshi bai shirya dawowa kun barshi acan dan naga yafi kaunar can abunsa, aa tare mukazu inaga yana masallaci da daddynsa , nasan yana dawowa ke zai fara nema kinsan mutumin naki ae, dariya Hajiya tayi tana fadin," eh wannan haka yake nafi kowa sanin kayana, dariya sukayi duka tareda cigaba da hirarsu, nan ammi take basu labarin irin kayanda sukayi order na bikin kamal da nabeela, su fadeela murna biki zai tashi agdnsu za ayi bikinda ba ayiba baya, dan ko bikin AJEEMAL baiyi wani gagaramin bikiba, dan haka zasu rama abunda basuyi abayaba suyishi yanzu, ana kiran isha kowa yawatse yanufi yin sallah, Hajj mama takuma bedroom sallah, haka ammi ma tanufi bangaran ta dan yin nata ibadar,

su fadeela da Nisha suka rufa mata baya hanunta dauke da aheel gudun kar abarshi shikadai suka nufi nasu dakin, kwantar dashi tayi saman bed tanufiyin alwala tayi sallah, su fareeda suna idarwa suka nufi parlour yau rawar kai se abunda yakaro ammi tadawo, zama sukayi a parlourn suna jiran sakko won ammin, Daddy ne yashigo bayansa dauke da AJEEMAL tareda kamal, shigowar su gwanin shaawa, cikin happy suka isa gareshe suna masa welcome, yayi daidai da sakkowan ammi fiskarta daukeda murmushi, tana bin yayanta damijinta da kallo gwanin burgewa tana mutukar alfahari da wannan family nata gaku wani garin da allah yabasu Nisha, karisowa tayi gunsu ahankali dauke da murmushi nan nata, tana fadin,

" gwara da kuka shigo yanzu dan yunwa nakeji gaba daya bana gane kaina, dama kekam gwanar jin yunwace Daddy yafada cike da tsokana tareda karisawa dining suma suka rufa masa baya suna dariya, waje suka samu suka zauna banda AJEEMAL da kamal dasuke tsaye ammi ne ta kallesu tana fadin,

" kufa dakuke tsaye kuzauna muci abincin mana, kamal ne yafara magana yanacewa, ni banjin cin abinci for now because ni wankama nakeson nayi, gaba daya agajiye nake, kallon reeda yayi yana fadin,

" please in kin kammala ki kawomin nawa bedroom dina, to tace masa daga bisani yajuya yafita, kaikumafa Daddy yafada yana kallon AJEEMAL dake tsaye yakama kugu kazu muci abincin mana, a no akoshe nake, yafada can kasa, wul wul ga ido yayi yana su yatambayi aheel amma yasan bazai wuce suna tareda waccan yarinyar ba tunda bai ganshi a parlourn ba , guntun tsaki yaja ahankali tareda sakai yafice daga parlourn, bayanshi sukabi dakallo kawa tareda cigaba da cin abincin su, ammine tadan bugi reeda abayanta,ashhh ammi meyafaru mekuma nayi, saboda mun dawo har kun mata da kanwar taku koh,? to maza kutsaida cin abincin nan kuje kukirata tazo taci abinci, cikin hanzari fadeela ta tashi reeda tabi bayanta,

zaune suka sameta cinyarta dauke da kan aheel tana shafa kansa, reedane ta karisu tareda dauke kan aheel daga cinyarta takwantar dashi gefe tareda jan hanunta Nisha batareda tace mata komaiba suka fito parlour, seda takaita har dining ta zaunar da ita tana fadin," to ammi ga shalelen babyn taki, ganin Daddy da Nisha tayine yasa tazame wa ta gaisheshi, cikin fara'a ya amsawar tata , yana fadin," ina kika shiga kowa ya halarci wajan cin abinci amma banda ke, kefa ba bakowa bace, as from now dazaran time din cin abincin yayi to naganki awajan, kuma duk abunda kikaga wani yayi agdn matukar mai kyaune kema kiyishi, duk abunda kikeso ko kike bukata gani ga madam kitambaya batareda shakka ko tsoroba, muma iyayenkine kinjiko, cikin sanyi murya nisha tace,"to inshallah, to baza kici abincin fadin ammi yayinda ta dire mata plate din abinci gabanta, nan sukaci gaba da cin abinci suna hira cikin raha da nishadi, Nisha taci abinci sosae kuma ta sake dasu sosae ,

seda suka kammala suka dawo parlourn suka cigaba da hirarsu, yayinda Barka tazu ta kwashe abubuwan da akayi amfani dasu tayi kitchen, nikam kaje gurin Hajiya kuwa,? Ammi ke tambayan Daddy," eh na leka mun gaisa dawowana daga masallaci muka biya, okay to ae shikenan, wayan fadeela ne yayi kara taduba screen din wayan taga kamal ne ke Kira, cikin sauri tamike tana fadin," oh my God, na manta daya kammala yace nakawo mishi abinci, cikin hanzari ta tashi tanufi kitchen domin hada masa abinci," hira yayi dadi kin manta da batunsa zaku hadu ae ammi tafadi tana dariya , Nisha kam tunda fadeela ta furta sunan kamal gabanta yafadi, kwata kwata tamanta dame irin sunansama, ya ilahi wannan wani irin rayuwace, mutumin da yabata makudan kudi dan ta cece rayuwar mahaifiyar ta, shine tayi saurin matawa dashi haka, se yanzu yafado mata ko daran da umma zata rasu taga miss call dinsa, still tasake ganin kiransa bayan zuwanta gdn nan , kin karbi kudinsa kin kuma manta dashi balle kisan duniyar dayake, nashiga uku tafadi afili wanda ita kanta batasan maganar yafitoba,

cikin hanzari tasa hanu tarufe bakinta tanabin yan parlourn da kallo, jin yarda ta tashi azaburene yasa duk suka nufota suna tambayar lapiya, yanda taga sundamu suna tambayar ta yasa tace," bakomai jinayi gabana yafadi, ammine tajawota jikinta tana fadin," ba nashiga uku zakiceba, idan kinji irin haka nan gaba cewa zakiyi ina'lilla hi wa inna ilahi raju'un, bana shiga ukuna kinjiko, gyada mata kai tayi, to maza kije ki kwanta kuma kiyi addu'a kafin kwantan kinjiko, cikin sanyin jiki Nisha tace,"to, tareda juyawa tayi daki , gaba daya suka bita da kallon tausayawa, daga ammi har Daddy ba wanda Nisha bata kwanta masa araiba, duk da dama Nisha yarinyace mai shiga zuci, ga hankali da nitsuwa, tana shiga daki tafada saman bed kusa da aheel, hanu tasa ta lalubo yar karamar phone dinta, tabinciko numbern kamal tayi dealing koda takira tajita switch off takira yakai sau uku but abu daya ake mai maita mata, ritsa ido tayi cikin zuciyarta tana fadin,
Chapter 11 · 0% Book details