← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

oh haryanzu kukan bai kare bane goggo rabi tafadi tareda matsawa kusa da ita ta dagota tamikar da ita tsaye tana fadin,"

Kukan nan ya isa haka, kukuwa duk taronku nan arasa mai lallashita, barinma kai kamal kana kusa da ita kanaji tanata asarar hawayenta, to kutasu muje Daddy ya dawo yana nemanku a parlourn sa, tana gama fadin haka ta tusa nabilah agaba kamal da mb tareda muhaiseen suka rufa musu baya jiki amace kamar wayanda aka zarewa laka,

reeda fadeela Nisha anrasa mai kwakwaran mutsi acikinsu, Nisha hawayen idonta tanema tarasa sotake tayi kuka ko abunda takeji cikin zuciyarta zai ragu but hawayen yaki zuwa balle kukan yabiyo baya, "

kutashi mutafi muje mukwanta , reeda tayi magana cikin karfin hali yayinda tamike taja hanun fadeela da Nisha suka fice ,

parlourn bakowa duk sun hauwa sama parlourn Daddy hakan yabasu daman shige bed room dinsu domin shirin bacci, seda kowannensu ya kimatsa yayi night dressed daga bisani sukanemi guri suka kwanta, amma sam bacci yaki zuwa se kwafa suke suna tsake in fadeela tayi se reeda takarba itama se juyi suke sun kasa bacci gaba daya haushin kb yagama cikasu jisuke inama ace zasu ganshi yanzu se sun hadu sunmasa dukan da se yagagara tashi, duk da sunsan sangarcewa irin tashi mom dinsa tagama san gartashi but basusan abun yakai hakaba yana kokarin lalata yayan wadan su da kuma son daura yayansu kan turban da bai daceba,

Nisha shiru tayi ta lumshe ido kamar mai bacci duk tanajin yanda su reeda suke juyi sun kasa bacci saboda damuwar dan uwansu,

itama bacci yaki daukarta gaba daya tausayin kamal da kaunarsa suna taba zuciyarta , kwata kwata batasan da kaunar da kamal yake mataba se yau da labari yasa tasani , to amma yanzu haryanzu yanajin sonta cikin zuciyarsa kamar yadda yafadi abaya ko kuwa yashafeta cikin heart dinsa yanzu Nisha tashiga tambayar kanta

🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh ❤️

(Khaleeseart Raeeys)

Free book 🤗 to all my lovely fans

Page29_30

Duk da tasan abaya tasawa zuciyarta babu wani tunanin akan so ko soyayya cikin rayuwarta amma ko yanzu kamal ya gabatar da kaunarsa agareta zata amince dashi batare da wani jayayyaba,

saide yanzu tasan hakan ba mai kasan cewa bane because yanzu yana da mata kuma tasan sonda nabilah keyiwa kamal akwana atashi zai manta da wani sonta da yatabayi gashi yanzu zuwa gobema wata kila basa kasar se yanda tayi dashi,

da wadannan tunane tunanen bacci barawo yayi awun gaba da ita suma su fadeela tuni bacci yacinye idanunsu,

Abangaransu kamal da nabilah sun tattara parlourn Daddy nasiha tayi nisa ammi hajja mama goggo rabi gefe muhaiseen da mb kowa yana tofa albarkacin bakinsa, daga karshe daddy yakalli kamal yana fadin,"

gobe tafiyar taku ko an daga?

dan dagowa kamal yayi yana kallon daddy nasu fiska bayabo ba fallasa yace,"

No tomorrow inshallah, because akwai wani wasa da zamuyi cikin satin,

haba mutumin basusan kai sabon ango bane yau aka daura maka aure ba daga kafane muhaiseen yafadi yana kallon kamal cike da zolaya, ,"

ba daga kafa malam su ina ruwansu yaje yabuga wasa kawai shine magana mb yafadi yana dariya,

dariyarsu muhaiseen suka shiga masa suna tsukanarshi shikuwa kamal kallonsu yake yana hararansu yana cizon lips, "

to allah de yaba da saa yakuma baku zaman lapia yasa albarka cikin auran ku, muyiwa annabi salati,

daga nan aka shiga rufe zama da addu'a daga bisani kowa yamike yanufi turakarsa, goggo rabi da kanta tamaida nabilah dakinta inda tadauketa dazu,

Kamal kuwa suna waje yaraka abokinsa mb tareda muhaiseen dan shima ba agdnsu yasaukaba hotel yakama dan ba wani dadewa zaiyiba bikin kamalne yakawoshi yanada aiyuka da yawa agabanshi, seda yarakosu kowannensu yashiga mota mai gadi ya bude musu geat suka fice sannan kamal yajuya yanufi part dinsa,

yana shiga a parlour ya tarar da nabilah bisa kujera ta takure seda ya iso tsakiyar parlourn yakallita yana fadin,"

kitashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah, dan dago kai tayi ta kalleshi time din har ya juya baya yanufi toilet din dake parlourn danufin alwala ganin haka yasa nabilah mikewa jiki bakwari tanufi cikin bedroom, direct tayi toilet tayiyo alwala ta dauko musu sallaya tayiyo parlour ,

atsaye tasameshi yana gyara hannun rigarshi da ya tattare wajan alwala,tana karisowa tashin fida masa sallayan daga bisani tayi baya ta shin fida nata, nan yashige gaba suka tada sallah,

bayan sun idar sun dan dade awajan suna addu'a daga bisani suka mike nabilah ta ninke sallayan tamayar bedroom ta dawo ta zauna, "

ba zama zayiba kitashi kidauko wancan ledar kamal yafadi yana kallon nabilah yana mata nuni da ido inda ledar take , ahankali tamike tanufi dining table inda ta hago ledar ta dauka daga bisani tadawo ta ajiye saman table din parlourn ta nemigu tazauna, "

kibude kici mna kamal yafadi yanadaga kishingide daga saman sofa yana latsa wayar hanunsa, "

Kai kumafa,? Nabilah ta tambaya tana kallonsa

" Akoshe nake abunda kawai yace kenan yaci gaba da abunda ke gabansa, shiru nabilah tayi tana kallonsa daga bisani ta dauke kai daga kansa tasauke kan ledar tashiga budeta, ledodine guda biyu aka sasu cikin leda daya shiyasa tun daukowa datayi taji ledar da nauyi,

chicken roasted fish se pack din irish guda biyu daya ledar kuma yoghurt kayan shaye shaye na drinks d
tareda kayan marmari bada wani bata lokaciba tasuma ci dan kuwa yunwane atare da ita,

tana tsaka daci tsulum taga ya mike yana kokarin nufa bedroom ,"

indan kin kammala kishigo ciki

to nabilah tafadi baki na fari, daga haka yajuya yashige ciki,

tana kammala wa kamar yanda ya umarceta ta tashi tanufi toilet ta wanko hand dinta tare da bakinta sannan tanufi bedroom din

akwance tasameshi time din harya sauya kayan jikinsa zuwa farar jallabiya face dinsa na kallon sama ya lullube jikinsa da blanket idonsa alumshe kamar mai bacci, tsayawa tayi kikam kamar wacce aka dasa agun tana kallonsa, "

kinemi gu kiwanta mana kintsaya, kamal yafadi yana kallon ta, ahankali tamatso jikin gadon tasuma kokarin hawa,"

Waited! kamal yafadi yana kallon kayan jikin nabilah wani tsadeden les mai nauyi ga kuma lullube bisa kanta, "

zaki iya bacci da wannan dress din jikin kin,? cikin fiskar tausayi nabilah ta kalleshi tareda gyada masa kai alamar" eh

okay kamal yafadi tareda gyara kwanciya itama tarabe daga gefe ta kwanta ta rintsa ido daga ita harshi ba wanda ya iya rintsawa se juyi da kyar suka samu bacci ya daukesu

Guraren asuba aka suma kiran assalatu wanda ya doki kunnuwan nabilah wanda yasa tamike tazauna gaba daya baccin rabi da rabi tayishi because kayan jikinta duk sun isheta, gefe kuwa tamaida kallonta ga kamal dake kwance yana bacci hankalin kwance dan shi ko kiran sallahn dama can yayansa ajmal shike zuwa yatashisa sallah asuba ko daddy in ka rasa 1 tofa ranar amakare za ayita,

tashi tayi tanufi toilet tayi alwala nan tasamu ta sauya kayan jikinta zuwa mara nauyi yar gown mai lushi tasamu tasa daga bisani tayi gadon dumin tashin kamal,

tana zuwa kusa dashi tashiga tashinsa ,nan yabude ido tasanar dashi dayatashi yayi sallah nan ya mike ya saukko daga gadon yanufi toilet tana ganin shigarsa ta shin fida sallahya tasuma gabatar da sallahnta,

yana fitowa yasa kai yafice yana fitowa sukaci karo da daddy shima yafito da niyar fita masallaci, nan kamal ya rufa masa baya suka wuce,

nabilah na idar da sallah ta haye gado ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa,

shima kamal yana dawowa daga masallaci yanufo bedroom din yasamu nabilah tayi rashe rashe tana bacci da alamar baccin yayi nisa, dan jinjina kaiyayi yana kuma kare mata kallo seda ya kalleta sosae daga bisani ya lumshe ido yabude sannan yasakai yafice daga dakin ya koma parlour kan sofa ya kwanta ya lumshe ido yanata kwancewa da sakawa cikin ransa,

karfe 10 nasafe ahali daya antattara gurin cin abinci anaci ana raha ana kuma tadi, kamar yanda suka saba dazaran sun kammala breakfast za adawo parlour acigaba da fira , yauma hantake , Nisha na kusa da hajiyanta farida da reeda suna kusa da daddy sun sanyashi tsakiya se goggo rabi da ammi suna daga gefe cikin farin ciki da annashuwa, sallaman su kamal da nabilah yasa suka dan dakata suna kallon shigowar su,

Kamal na gaba nabilah nabiye dashi tareda try din breakfast da ammi tasa baba barka ta kai musu, ammine ta kwadawa barka kira baba barka na fitowa ammi ta umarceta da ta amshi try din hanun nabilah, nan barka ta amsa tanufi kitchen dashi, hakan yabawa su kamal daman karisawa cikin parlour kamal daga gefe saman carpet yasamu guri yazauna haka itama nabilah kai sunkuye nan suka shiga gaisawa dasu daddy seda suka gama gaisawa kamal ya dan dago ya saci kallon Nisha datayi lamuda ita uwar son jiki tasanya kanta saman shoulder din hajiya kamar wata mara lapia gaba daya ya sakan kance da kallon Nisha wacce zuciyarta ke bata kamal na kallonta but sam takasa daga ido takalleshi because hawaye zai iya ziyarta idanunta,

nabilah duk tana lura da kallon da kamal ke yiwa Nisha ban sauran yan parlourn da hankalinsu ke kan hira,

Nabilah ba kallon kamal , kamal kuwa idonsa na kan Nisha duk da nabilah ta lura Nisha batasan da kallon da kamal ke mataba, gaba daya setaji zuciyarta na mata suya because nabilah tanada zafin kishi sosai musamman akan kamal
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴

Story and writing by oum amreesh
(Khaleeseart Raeeys)

Free book 🤗

Page29_30

Jitayi tamkar tasa kuka ganin abunda idanuwanta ke kallah, shigowar su mb da muhaiseen yasa duk ilahirin hankulansu ya dawo garesu,

Nan su mb suka shiga gaisawa dasu daddy, daga bisani muhaiseen yakalli kamal yana fadin,"

My man muje ko,

jiki ba kwari kamal yamike ganin haka yasa nabilah mikewa itama, daga bisani Daddy da dukanin mutanen parlourn suka tashi domin yiwasu kamal rakiya,
Chapter 26 · 0% Book details