← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 38

Sashe 24

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke Nisha yadai umma ta tambaya, cikin hanzari da kirkiro murmushi nisha tace,"

bakomai tareda barin parlourn tanufi bedroom, umma de bayan Nisha tayi da kallon gami da karisawa kitchen din dan ganin maike tafiya, umma na zuwa ta tararda komai Nisha ta kammala se dan wasu aiyuka da bata samu daman karisawaba,

hakan yasa umma tashiga jarisa aikace aikacen, nisha kuwa tana shiga daki ta tazauna tana tunanin iri iri, shigowar sako wayarta yasa cikin sanyin jiki tadau wayar tashiga dubawa, address aka turo mata hakan yasa tashega wasi wasi, because allah ya gani bazata iya daukar kafa taje gurin Wani saurayiba, wannan ma ai se duniya ta tsine mata,

Kuma umma bazata yafe mataba, saurayi yazo guntama bazata lamunci hakaba balle kuma ita tadau kafa taje,

ta wani fannin kuma tsoro take kar akawo mata gawar sauri kamar yanda mutumin dazu ya sheda mata , dan haka gwara ita taje ayi mai yiyuwa tayiwa tufkar hanci,

tashi tayi tashiga kimtsa jikinta, tareda sauya kaya ta nemi hijab tasaka tareda nufo parlour cikin sauri yayi daidai da fitowar umma daga kitchen,"

Ina kuma kike saurin fita kije,? umma ta tambaya tana kallon Nisha dake ta fidda ido, "

Gdnsu salma zani because na kwana 2 banje naduba jikintaba,"

to adawo lapia ki gaishesu abunda umma kawai tace nisha tasa kai tafice,

tunda tafito take ta tafiya tareda tunanin wannan saurayi da ya tacewa rayuwarta haryake tunanin salwantar da rayuwarsa akanta, inko harda gskne shiko wani irin sone haka,?

Nisha tafiya tayi sosai seda tabar arean anguwar tahau titi, sannan ta tsaya ta tsaida mai daidaita tanuna masa address inda zai kaita daga bisani tashiga suka dau hanyar tafiya,

bada wani bata lokaciba haya ta kawosu, daidai jikin gdn mai adaidaita ya dire Nisha, daga nan ta sallameshi tasakai dan ma daidaicin gdn, tura kofar tayi tashiga kirjinta se dukan uku uku yake,

Koda isuwarta cikin compound din gdn bakowa gurin shiru yake, to nan din gdnsune ko ina,? but bata ga mutane cikinsaba, ga kofar parlourn abude yake nisha ke tambayar kanta,

jitayi tsoro yagama mamayeta kamar tajuya takoma because taji gaba daya bata yarda da gdnba, jin shiru datayi ba alamar kowa, maybe ma yan yankan kaine ko kidnapping, soke kokarin wasa da hankalinta da sunan soyayyarta na kokarin ilata Wani,

har tajuya zata fice daga gdn wayarta tayi kara, kamar bazata dagaba sekuma ta dauka tareda karawa akunne,"

Na hangoki ta window but naga kamar kokari kike kikoma please ki kariso bawan allahn nan ya ganki ko zai kuma cikin hankalinsa kafin musamu mukaishi hospital,

daga cikin phone din takejin ana ambato sunanta, daga gefe da wace irin raunan niyar murya, ana neman agajinta hakan ya tabbatar mata akwai matsala kuma akwai kamshin gsky alamarin

dan haka takarisa takutsa kai cikin parlourn bakinta dauke da sallama, ga mamakinta parlourn ma shiru yake ba kowa nan ta tsaya tana dan wul wul ga ido tana karisawa tsakiyar parlourn, jin an murda handle din kofa ana kokarin fitowa daga bedroom din yasa ta kurawa kofar ido dan ganin mai fitowa,

turos tayi tana binshi da kallo tana dan gwalo ido, kamal ne yafito daga dakin yana sanye cikin t shirt da gajeran wando, yayi kyau dashi, tsayawa yayi yana kallonta shima da mamakin mai ya kawo yarinyar gdn ,

Rintsa ido yakumayi atunanin shi ko gizo tafara masa, kara bude idon yayi dakyau because yanda yaji sunyi masa Wani nauyi , tabbas itacede ba wataba tayi tsaye kamar sakaguwa, ta gagara motsi daga inda take,

dawata kasa lalliyar murya kamar wanda yasha wani abu kamal yakira sunan ta yana fadin," Nisha kece ,? mekuma ya kawoki nan,? yajero mata tambaya yana mai kokarin karisuwa ciki parlourn,

ita kuwa nisha jin tambayar da kamal ke mata yasa ya tabbatar mata wani ke kokarin rena mata hankali ko kuma shida kansa yake kokarin zargata, dan haka kafin ya kariso tsakiyar parlourn Nisha tayi baya da sauri tana kokarin barin parlourn,

kirif taga anja kofar anrufe daga waje, Nisha kamar ta tsula fitsari awajan aikin tsoro da kidima, nan tasuma bugun kofar da karfi tana fadin," waye agurin please kabudemin natafi gdnmu, dan Allah , tafada cikin sigan kuka, kamar daga sama taji murya daga waje ana fadin,"

Rashin kunyarki ya kwaceki yaude kinshigo hanu yau zanyi maganin rashin kunyarki, ashema bakida wayo harna iya zargaki yau gaki amakomata, bake har Zaki iya daukan hanu kimari wanda bakisan waye shiba, zakiyi bayani

makwat kakeji Nisha ta hade wani yawu, tareda sakin handle din kofar da tarike tamaida kallonta ga kamal dake tsaye yana rike da head dinsa yana rinrintsa ido tareda girgiza kai,

Nanfa ya tsulale kasa, jiyayi kansa yayi nauyi kafafuwan sa sun gagara daukansa, jiyayi kamar ba aduniyar yake bama, Nisha na ganin haka tayi kansa da sauri tareda tsuguna wa , kusa da kansa tana tambayar sa wanda baimasan tanayiba, "

Kai lapiya kuwa mai kakeyi haka,? please katashi ga budemin kofa natafi gdnmu wajan ummana, tafadi cikin sheshshekar kuka, ganin babu alamar zai tashi yasa tasuma kokarin mikewa tsaye, carab taji yarike hand dinta,

Kallonsa tayi dashima kallonta yake da idonsa dasuka canza launi zuwa jaaa, ganin haka yasa tasuma kwace hanunta, jin yarike hanunta gam still yana kwance saman capet bayida niyan tashi,

baki takai da niyar cizonsa but kafin tayi yunkuri ya jawota saman jikinsa, ya rungume ta tsam, waro ido Nisha tayi because jitayi wani irin yarrr tsoro da firgici yasa tashiga kiciniyar kwace kanta da karfi tana bugun kirjinsa,

shima cikin zafin nama ya yunkura tareda yin kasa da Nisha shikuwa yakuma sama,"

Innalillahi wa'inailaihi raju'un hasbunallahu wani'imal wakil, abunda Nisha tafadi kenan tareda sakin wani ihu tana neman agaji,

Kb daga waje yajiyo ihunta nan da nan yasake wani ihun dadi hankali tareda rawar murna yana sakin wasu wakoki ," yaude yayi magani mara kunya buri yacika,

dan tsa gaitawa yayi da rawan jin shiru yasa yamatsa kusa da kofar yayi kusan minti 10 daga bisani ya dan murda handle din kofar yashiga lekawa ahankali, " inna lillahi wa'inailaihi raju'un kb yafadi tareda kara bude kofar da sauri, kamal ya hango kwance saman carpet kamar macecce keyarsa se fidda jini yake,

gefe kuwa kwalban da sukasha drinks dazu acikine afashe awatse agurin ," subhanallah kb yafadi atsorace tareda karisawa cikin parlourn kusa da kamal dake kwance ya tsuguna yana kallon sa, fusace kb yamike yana fadin,"

Where are you yau zakici ubanki kashemin dan uwa kikayi,? yafadi yana kama kugu, yana dan wul wul ga ido yaga daga ina zata fito, yana tsaka da surutain sa, Nisha ta fito daga bayan labulen da tabuye dama taci alwashin bazata tafiba seta illatashi shima,

yana cikin surutun nasa yaji saukan kwalba akeyarsa shima, bai fadiba seda yajiyu sukayi ido 2 da Nisha yana rike da kansa dake kokarin zubda jini, yasuma kokarin magana nisha ta hankada kirjinsa da karfi yafadi sumamme,

da sauri Nisha tayasar da rabin kwalbar dake hanunta takalli kamal dake kwance gefe takalli kb nan da nan tafashe da kuka tayi waje da kudu

Mai gadi dake zaune awaje saka makon dazu shiharta yatafi zagawa shiyasa baiga shigartaba se fita,

Mai gadin ganin yarinya tafito da gudu hakan yasa yamike atsorace yanufi cikin gdn, yana karisawa parlourn ya kamal da kb kwance cikin jini kamar mataccu, ,"inna lillahi wa'inailaihi raju'un mai gadi yafadi ya rude tareda ciru yar karamar phone daga aljuhu yashiga kiran wata number ringing daya biyu aka dauka, mai gadi nayin sallma yashiga zaiyanu abunda idonsa yagani da abunda yafaru, cikin tsoro da faduwar gaba baba mai gadi baikaiga karisa maganar ba yaji ankatse wayar,
.
ganin haka yasa yamai da wayar aljuhu yaja ya tsaya daga gefe yana kallon su kb dasuke kwance, bada wani bata lokaciba baba mai gadi yaji wani irin gawurceccen hon cikin hanzari ya karisa geat din tareda budewa,

Kyakykyawar mota black mai daukar hankali ta danno kai cikin gdn , tsakiyar compound din gdn akayi parking mai gadi yazo da sauri yabude masa murfin kofar motar yafito,

Masha Allah kyakykyawar namiji dirarre dan matashi maijin kanshi, dan gaye son kowa kin wanda yarasa , yana sanye cikin black suit face dinsa sanye da bakin glass gwanin burgewa da shaawa kamar kasaceshi kagudu,

IG AJEEMAL kenan tareda abokinsa inspector Ahmad gefe kuwa doctor fu'ad AJMAL na gaba suna binshi abaya shima baba mai gadi na biye dasu,

Seda suka shiga tsakiyar parlourn suka tsaya, IG kallo daya yayiwa parlourn daga bisani yakalli kamal yakoma yakalli kb, daga nan yakoma nisa dasu ya nemi kujera yazauna yana kuma kallon gurin su kamal inda suke kwance,"

Baba come here IG yafadi yana kallon baba tareda masa hanu alamar yazu, jikin baba mai gadi har kerma yake ya karisa kusa dashi tareda dukawa saboda yaji mai zai Fadi,

Khaleeseart Raeys ✍️

08105565439
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Daga ALKALAMIN khaleeseart Raeys ✍️

Free book 🥰

Page 26_27

IG seda yakarewa baba mai gadi da kallo daga bisani yashiga fadin,

What happened? meyafaru da wadannan,,? jikina kyarma mai gadi yasuma cewa,"

Yallaboi kamar yadda kace ina lura dashiga da fitan yaran nan agdn nan, yau ansamu akasi domin kuwa wata yarinya ce tasaci jiki tashigo ta aikata wannan ta asar

Kaikana ina har akashigo akayi wannan danyar aikin,? anyama macece ta aikata wannan aikan haka?, inspector Ahmad yafadi tareda tare baba mai gadi da maganar yana kuma kallon sa,

Shima AJMAL din kallon mai gadin yake yanason jin karin bayani, "

Tabbas macece yarinya karama tana sanye cikin hijabi lokacin da tashiga na dan zaga bayine dataga bakowa wajan shine tasidado tashigo, se fitanta nagani.. bai kaiga karisa maganar ba, sukaga IG yamike daga zamar dayayi yakalli doctor fu'ad yana fadin,"

Check them,

doctor fu'ad kamar jira yake dama, nan da nan yashiga checking dinsu, ya kuma tabbatar wa da IG suna da rai, "

dan matsowa yayi kusa da doctor fu'ad tareda karewa su kamal kallon da kwalbar dake watse saman capet wanda akayi amfani dashi wajan lahantasu, hankali yafurta,"
Chapter 24 · 0% Book details