← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 38

Sashe 29

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganinayi bata da lapiya tana gdnsu batajin dadin jikinta, tunda allah yayi dawowarka lapiya yakamata kaje gdnsu heelah kaji lapiyarta koba komai zataji dadin hakan"

Okay ajmal yafadi yayinda ya kammala breakfast ya koma yajin gina bayansa da jikin sofa"

Please kadaure kaje kaji lapiyar matarka ammi tafadi tana dafa shoulder dinshi tareda mikewa ta tattare kayan break dinda ta kawo masa tasuma kokarin fita,

bakin door taci karoda aheel dayashigo dagudu wanda yaji labarin dawowan papansa wajansu reedah, cikin watsawa aguje yayi kan papansa cike da murna yana fadin"

Oyoyo papa nayi missing dinka sosae papa kadawo jiya amma baka nemeniba inata kewarka yafadi cike da shagwaba yana nukewa, "

I'm so sorry jiya nadawo nagaji sosai kuma Nasan time din Kayi bacci shiyasa ajmal yafadi yana dan murmushi yayinda yasake hugging din dan nasa cike da kauna yana dan shafa bayanshi,"

Papa mummy bata sona guduwa tayi tabarni, Aunty nisha ita takemin wanka tashiryani har school take rakani abaki take bani abinci kuma tare muke bacci ba kamar mummy ba

Nibazan sake zama kusa da mummy ba Aunty nisha tafi sona nima inasonta kusa da ita zan dinga zama baruwana da mummy.....mukut aheel ya hadiye maganar ganin yanda papanshi yabishi dawani kallo wanda yasa aheel yashiga mis mis da ido,

sam ajmal baya kaunar aheel yadinga kawo masa zancen yarinyar nan da yake kira da Aunty, zame aheel yayi daga jikinsa ya zaunar dashi gefe,

tsam yamike yanufi hanyar bedroom dinshi jima kadan yafito cikin shiri mai kyau farin shadda gezina tsadadda, yasanya hula shigar tayi matukar kawata kyansa duk dacewa shiyamusu kyau basu suka masaba,

aheel naganin papansa yafito cikin shiri da alamar fita zaiyi hakan yasa aheel mikewa daga zaune yayi gun papansa da gudu yakama hand dinsa yana tambayarsa"

Papa where are you going please zan bika yafadi tareda shigewa jikinsa,"

gurin mummy nka zanje, cikeda washe baki aheel yasuma fadin,"

Please zanbika muje tare , "

No bakace baruwanka da mummy ba kafison Auntynka alright kaje gurinta kazauna sena dawo ajmal yafadi tareda zamewa yasuma tafiya seda yafito haryaje jikin mota yajuyu yasauke idonsa kan aheel dake tafe bayanshi yana matsar kwallah

tabbas yaso sutafi tare domin yaga mummynsa amma ya riga ya bata masa rai da surutun dayaitayi dazu rai adan bace ajmal ya kalli aheel ya na fadin"

stop crying and do what I said , nan da nan aheel yafashe da kuka yawatsa dagudu yayi part dinsu ammi, ajmal yana ganin shigar aheel shima yashige mota yamata key mai gadi yabude masa geat yafice,

sannu🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴

Story and writing by oum amreesh❤
Khaleeseart Raeeys

Free book😘

Page37

sannu ahankali yake tafi har allah yasa yadangana ga gdnsu heelah , nan ya danna hon maigadi yafito yaleko dan ganin wake danna hon ganin ajmal cikin kyakykyawan motarshi yasa mai gadi yashiga rawanjiki tareda washe baki yabude masa get yashigo,

nan ajmal yadangana parking space yayi parking yafito, mai gadi tamkar zai masa sujjada wajan gaisuwa,"

Yallabai sannu dazuwa ,"

Yauwa sannu ya aikin "

Alhamdulillah bari nasanarwa gdn zuwanka mai gadi yafadi , gyada kai ajmal akwai yayi nan mai gadi yasuma sauri haryana tuntube, Yana isa parlourn ya suma sallama yanajin an amsa masa yakutsa kai yashiga,

hajiya balkisu mahaifiyar nabilah nazaune bisa kujera tana kallon tv remote bisa hand dinta mai gadi yazube saman carpet yana fadin,"

Hajiya sannu da hutawa , cike da sakin fiska hajia balkisu ta amasa masa da yauwa sannude ya akayi,"

baban aheel ne yazo yana waje , gyara zama hajia balkisu tayi tana fadin,"

Haba kaikuwa shine zaka barshi awaje maza tashi kamasa iso yashigo , cikin sauri mai gadi yafita yanufi inda ajmal yake jikin motarsa yana danna wayarsa,"

Yallaboi waika karisu ciki! Ajmal dagowa yayi yakalli mai gadi batareda yace komaiba mai gadi nakokarin komawa bakin aikinsa seji yayi ajmal ya jefa masa kudi cikin aljuhunsa , cikin murna da farin cikin mai gadi ya kalli ajmal yana fadin,"

Nagode duk da dama ba yau yasaba masa Kyautar kudiba matukar yazo gdn nan seya masa alkhairi, ajmal bai saurari godiyar da mai gadi yake masaba ya kunna kai cikin parlourn bakinsa dauke da sallama ,

Mikewa hajia balki tayi ta tareshi cikin farinciki , karisuwa yayi yadurkusa yasuma gaisheta seda suka gaisa daga bisani ya gyara zama bisa kujera itakuwa hajia balki tanufi kitchen domin hadu masa abubuwan tabawa , seda hajiya balki tagama hadu abunsha dana tabawa takalli hajjo mai aikinsu wacce take tsaka da aiki, tace,"

Hajjo dan dakata da aikin nan haka ki haura sama kiyiwa umman heelah magana heelah tayi bako mijinta papan aheel yazo cikin sanyin murya mai aikin tace to ,

Tare suka fito daga kitchen din hajjo tahaura sama dan isar da sako itako hajia balki takarisa da inda ajmal yake ta dere masa try din da takawo masa bisa tablet tana fadin,"

Bismillah kafara da wannan kafin heelah tasakko na aiki hajjo ta kirawota, gyada mata kai yayi yana fadin,"

Bakomai tareda cigaba da danna wayarsa,

hajia jumana tana kwance kata faran gadonta tana latsa wayarta jin nocking bakin door dinta yasa mikewa tazauna cikin daga murya tasuma fadin"

Wayene kam yake kokarin damuna haka da nocking, cikin rawar murya hajjo tace"

Nice dama hajiyace tace tanazo nasanar miki baban aheel ne yazo hajjo tafadi daga Bakin door batareda tashigoba, jin haka yasa mom din heelah tazamo daga bed tanufo kofar tareda budewa, seda takarewa hajjo kallo ta tabe baki sannan tace,"

Anji keje anazuwa , cikin hanzari hajjo tajuya da sauri ta sauka Kasa, wani murmushi mom din heelah tasaki kafin ta dangana ga bedroom din heelah , azaune tasamu heelah gaban mirror jikinta sanye da towel tana latsa wayarta tana zuba uban murmushi, da alamar bata ankara da shigowar mom cikin bedroom dintaba,

ahanzarce mom din heelah takarisa kusa da heelah tareda fizge wayar hanunta tana fadin"

yanxuke tsabar sha shanci wanka kikayi but kinkasa sanya sitira ajikinki kinzau kinata chat din banza to kitashi kinyi bako, cikin tura baki heelah tace"

Mom bako kuma? nibawanda nagaiyata koyace zaizo gurina"

To papan aheel ne yazo dan gdnku sekitashi kiyi haraman sa kaya, tsulum heelah tamike dadi kamar me papan aheel yazo cikin hanzari tayi wardrobe tasuma lalubar kaya, "

kiyi shiri mai kyau wanda zaidau hankali karki manta kisanya humranda kawata habiba tabani nakawo miki kishafa duk wani lungu da sako dan humran na dakyau zaki bani labari, mom tafadi hartajuya zata fice nan tajuyu takalli heelah tana fadin,"

Karfa kimanta bakida lapia karki zage dayawa,"

Oh mom nasani kije kawai heelah tafadi cikeda kosawa, tobari naje kihanzarta maza mom tana gama fadin haka tajuya tafiata daga bedroom din tanufi downstairs,

Ahankali mom din heelah take saukowa harta kariso cikin parlourn murmushi dauke afiskarta but ganin hajia balki yasa ta murtuke face tamkar ba itake murmushi dazuba,

karisuwa tayi tazauna ko kallon inda hajia balki take bata kalla ba, ajmal dan zamewa yayi daga kujeran yasuma gaisheta, seda suka gaisa yake tambayar ya jikin heelah
nan tashaida masa jiki da sauki amma saukin ba haushe , because indare yayinema zazzabi ke rufeta baya mata da wasa,

hajia balki duk tanajin karyanda mom din heelah ke shirgawa because ita tasan bawani rashin lapiya tunda rashin lapiyar baya hanta fita yawo inda takeso hmm allah ya kyauta tafadi cikin zuciyarta, yayinda tazora ido da kunnuwa tana sauraron karairayin mom din heelah ba kunya ba tsoron allah tsabar son zuciya ,

shigowar heelah parlourn yasa mom ta tsagaita da surutun da take shikanshi sauraronta yake bawai hankalinsa yana kanta bane dan ko cewa akayi ya maimaita abunda take fadi yayi karya ya iya maimaitawa,

Karisawa heelah tayi tazauna tana rarraba ido atsakani,"

Yauwa kin kariso tundazu kinbar mutum yanata jira komai kike adakin oho mom tafadi tana kallon, itade heelah shiru tayi batace komaiba domin sun hanata rawan gaban hantsi ganin haka yasa mom tamike tana fadin,"

Uhm bari mutashi mubaku waje , malama semubawa ma aurata waje zasu gana mom tafadi tana kallon hajia balki tana wani harare harare, tabe baki umman nabilah tayi daga bisani tamike tanufi kitchen, domin yau itace da office ganin haka yasa mom din heelah itama tamike tahaura sama,

heelah naganin sun watse daga parlourn hakan yabata daman mikewa daga inda take tanufi sofan da ajmal yake zaune kansa kasa yana latsa waya,

sam bai ankaraba sejin heelah yayi bisa cinyarshi nan ya dago suka hada eyes nan tasakar masa murmushi tareda yin hugging dinshi,

kokarin tureta daga jikinsa yasoyi but yakasa because wani fitinanne turare da tasanya wanda yahanashi yin hakan ahankali yaji tana rada masa akunne,"

i miss you so much my lovely kayi matukar ladaftar da zuciyata na tsawan wasu kwanaki tana fadin haka tayiyu kasa da lips dinta tana kokarin kissing dinshi, cikin hanzari taji ajmal yatureta gefe tareda mikewa tsaye yana kallonta, yana fadin"

Sorry sauri nake akwa inda nakeda bukatan zuwa banason bata time, lapiyarki nazo naji bye , yana fadin haka yajuya yafice nan yashiga motarsa mai gadi naganin fitowarsa yashiga mota yabude masa get tareda daga masa hanu ajmal yafice,

heelah shiru tayi da mamakin tureta dayayi dukda ba sabon abu bane wani lokacin haka yake yaita tureta kamar ba namijiba wani time din kuma yanajinta tana kissing dinshi tareda tabashi yanda takeso bazaice mata kalaba wani lokacin ma har biyeta yake, to kode turarenda tasane bai masaba, inba hakaba kodan kewarsa da tayi yakamata ya saurareta,

Nan heelah tashiga shun shuna humran jikinta ko zataji wani aibu amma sam bawata aibu maybe halinne ya motsa kawai
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴

Story by oum amreesh❤
(Khaleeseart Raeeys)

Page38

Mikewa tayi fiska ba annuri tanufi upstairs Tana surutai,
______Nisha____________
karfe 9:30 nadare bayan kammala dinner kamar kullum kowa ya halarci turakarsa, Nisha na kwance bisa gado Tana kallo cikin wayarta se aheel dake kwance gefenta daya gama rikecinsa har bacci ya daukeshi duk da bacci yaci idonta sosai amma takasa ajiye kallon da take takwanta ,

gefenta reeda ce zaune Tana amsa waya da alamar habibintane akan layi , se fadeelah dake baje saman carpet tana karatun exam dan tuni suka suma jarabawa da alamar tayi nisa cikin karatun, kowanne da aikin da yakeyi
Chapter 29 · 0% Book details