← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan idarwansu harsun hai saman gado zasucigaba da firan kenan ammi tashigo fiska cike da fara'a , ganin ammi da sukayi yasa dukansu suka shigayiwa ammi smile , ahankali ammi takariso kusa da bed din tazauna tana kallon nisha da itama kallon ammin take cike da farin ciki, "

Oyoyo ammi su fadeelah suka fadi yayinda sukkinsan kanta suka rungumeta suna dariya , "

Ku da allah ku kyaleni seyanzu kukasan da ina gdn ko nemana ai bakuyiba da nadawo ammi tafadi tana hararo su reeda dasuka tura baki gaba sun shagwabe fiska suna fadin ,"

Ai bamusan kindawo bane ammi kinsan mumuke fara miki welcome"

Uhm kukajiyo ni kubani guri wajan kyakykyawar yata nazo, ammi tafadi tana kallon nisha da tasunnar dakai tana satan kallonsu fadeelah tana murmushi , "

Tashi muje muyi dinner kinjiko ammi tafadi tareda jan hanun nisha suka mike ,"

Mukumafa ammi? Reeda ta tambaya cike da niman magana ,"

Inzaku iya kwa iya biyomu ammi tafadi tana tabe baki, daga nisha har su fadeelah dariya suka fashe dashe suka nufo parlour,

a parlour suka yada zango indasu hajia da goggo rabi suke zaune, suma gurin suka samu suka zauna fareeda nakusa da goggo rabi reeda kuma kusa da hajia yayinda nisha ke makale kusa da ammi , "

Oh yaukam yar taki wuni zubur tana hutawa abinta ko duk gajiyan aikinne yasake bacci haka ko lekomu bakiyiba , goggo rabi ta tambaya tana kallon nisha da tamakalewa ammi ,"

Aiki kuma ?waye yasa kyakykyawar yata aiki ya wahalarmin da ita, ,"

Waye kuwa banda shalelen danki MODIBBO da neman magana , hajia tacabe maganar tana murmusawa, ,"

yau kuma shida kanshi ,? Ammi ta tambaya,

Kwarai kuwa harda turowa ayi kiranta kamar abun arziki , goggo rabi tafadi,"

Alhamdulillah MODIBBo yafarajin magana tasan hakan yanada nasaba da magana da nasihunda tamasaba, ammi ke magana cikin zuci , azakiri kuwa kallon nisha tayi datake tazuba murmushi , gefe kuwa takalli su fadeelah da reeda daketa kallon juna suna maganar kurame ,"

Incede lapiar ku qalau ? Ammi ta tambaya tana kallon su fadeelah, "

Lapia qalau ammi suna kuma kallon junansu , ammi batakai ga karisa maganarba , Barka tazo tasanar dasu komai yazama ready , "

To ai seku tashi muje yannema hajia tafadi tana yar dariya tana kallonsu reeda, gaba dayansu dariya suka sake sannan suka nufi dining suka suma gudanar da dinner cike da farinciki da annashuwa , suna cin abincin suna fira , harsuka kammala dinner, daga inda suke basu motsaba suka cigaba da firansu cikin raha, nan goggo rabi take shaida musu tafiyarta gobe zata dagashi because se antsaida sa ranan wadannan yaran fadeelah da reeda domin acewarta bataki adaura auran yanzu suyi gaba da matar danta wato mahaiseen , amma komai na bukatan shiri da lokaci domin ita dayar wato fadeelah bawai sun gama fiskantan juna da samarinta bane , kaf cikin samarinta nawanda ta tsayar madubin da zata duba matsayin abokin rayuwa, domin ita hankalinta ya karkata kan babban likitansu kuma aboki ga yayansu wato doctor fu' ad hadaddan matashin nan maisaukin kai da barkwanci , abunda yake yasake burgeta dashi kenan ,

bayida girman kai kwata kwata ga son dariya da wasa kullum face dinshi dauke da fa' a , kusan kowani lokaci da hotonsa take kumalo because duk safiya inta tashi seta kalli kyakykyawar pic dinsa tashafa face dinshi tacikin screen din wayar ,

wani time din inkewarshi yamata yawa tanason sashi cikin idanunta seta kirkiro rashin lapia dan kawai taganstaganshi, amma koda yazo haka zai gama dubata ya bincikata amma bawani abunda ke damunta sannu ahankali doctor fu' ud yagane salon iyashege irin fadeelah na rashin lapia da take daurawa kanta,

dan haka daga zaran annemeshi fadeelah ba lapia dazaran yazo ya dubata ya tabbatar bawani problem seya dauko allura yace zaimata yasanta datsoron allura itako tana ganin haka zata zura dagu tayi toilet bazata fitoba seta tabbatar yatafi,

tunda tafahimci tsorata da allura dayakeyi yasa tadena kwanciyar , setunani kodayaushe da addu'an allah ya maidu da hankalinsa gareta ya farajin abunda takeji gamedashi,

washe gari da asuba bayan su nisha sunyi sallahn jikinta fadeelah da reeda suka koma bacci dan yau bacci yaga takansa kasancewa sunsamu hutun school yau bacci se abunda yaturewa buzu nadi se anga farkawansu , nisha kuwa bata komaba se karatun Qur'an datadan tsayayi, ahankali take karatun gudun kartashiga hakinsu , segurin 6 sannan ta dakata da karatun , tashiga toilet ta sheka wankanta tafito takimtsa jikinta tanemi yar duguwar gown da dan karamin mayafi ta daura bisa kanta tanufi hanyar parlour,

direct kitchen tanufa ta tarar bakowa aciki , hakan yasa tayi hanyar dakin baba barka tana zuwa tabude kofar ahankali tashiga lekawa , akwance tasamu barka sesake gwarti take kwar kwar bacci harda minshari , murmushi nisha tayi gami da kada kai tamaida kofar tarufe , takoma kitchen,

nan da nan nisha tashiga dawainiyar hada girki kala kala , tadafa wannan ta sauke wannan seda takusan kammala komai barka tashigo tana hamma gami da murza idano tana kallon nisha kitchen duk ya kacame da kamshi girki, "

yau naga takaina da wanga diya , mekikeyi hakan nan barka ta tambaya tana kama haba, dariya nisha tasaki tana fadin,"

Aiyukan nake dan ragemiki dan naga kamar agajiye kike baccinki yayi nauyi dan har dakin nashiga inata tashinki amma naga baki tashiba shiyasa nace bari nafara rage aiyukan kafin kizo,"

uhm wlh kekam murane da ciyon kai yadan matsamin to tunda nasha magani kuma shikenan dan ko sallahn asubama amakare nayi bakiga bisa sallaya naketa gyan gyadawaba, barka tafadi yayinda tasuma tayata da aikin, "

Masha allah yau kitchen yayi bakowa , me ake dafa mana ne , sukajiyo muryan ammi tafado kitchen din kamar daga sama, tana sanye cikin shirin fita office, "

Barka da safiya ammi antashi lapia, atare nisha da barka suka dagawa ammi gaisuwa nisha se washe baki , ammi amsa musu tayi cikin fara' tana mai karisowa kitchen din,"

Maizamusamu mubawa cikinmune nida Daddynku kafin muwuce ammi ke magana yayinda takalli nisha tana yan bude bude , "

Ammi kije kizauna yanzun nan zan kawo miki nisha tafadi cikin zumudi ,"

to shikenan bari naje inajira, ammi nagama fadin haka tajuya tafice tana murmushi , ba bata lokaci nisha tashirya abinci cikin tray, tafice dashi , dinning tanufa ta tadda ammi da Daddy suna zaune bisa kujera suna dan kuskus , motsin isowar nisha gurin yasa suka dago kai suna kallonta suna murmushi, "

Daughter yau hardake cikin kitchen kina wahalar dakanki ko, Daddy ke fadi yana murmushinsu na dattawa murmushi kawai nisha tayi tareda dagawa Daddy gaisuwa "

Daddy antashi lapia, amsa mata gaisuwan yayi yana mai tambayan me aka kawo musu , nan da nan nisha tashiga bude abincin kamshin abincin ya cikawa su ammi da Daddy hancinansu , "

Masha allah allah yasa yanda kamshin abincinnan ketashi yacika mana hanci haka zamuji dadinshi abakinmu ammi tafadi yayinda tasuma zuba musu abincin , nisha se zuba murmushi take kamar gunar auduga, nan tajuya ta koma kitchen din, tadauko wani hadadden flaks da cups ta dawo dinning tundaga isowata gurin ta fahimci delicious din da ta hada ya tashi kansu ganin yanda sukeci suna kada kai ,

Ajiye cups din tayi sannan ta dauki flaks tashiga tsiyayamusu special kunun madara mai matukar dadi da bada shaawa ta dire musu cups din gabansu tana murmushi, kallon juna Daddy da ammi sukayi kafin suka kai hanu suka dauki cup din suka kaibaki, ammi seda tayi rabin kofi kafin tasauke cup kasa shikuwa Daddy seda yaga kwal uwar daka , kafin yasauke nashi kofin ,"

Masha allah daughter allah ya albarkaceki , Daddy yafadi yana shafa cikinsa alamar koshi, "

Ameen! Nisha ta amsa tana sunar dakai, "

Ammade zakikaiwa yayanku wannan delicious din nasan zaiji dadinta ,ammi tafadi tana kallon nisha, cikeda murmushi nisha tace ,"

Eh zainkai mishi ammi , dama yau nisha daniyar burgeshi ta tashi , domin shima da NASA special din agefe data tanada masa, "

Uhm dan nakinma da ba gwaninta ake masaba Daddy yafadi yana tabe baki , "

Ai halinka ya dauko ammi tafadi tana dan yamutsafisa ,"

Ah nikam rabani bahaka nakeba kema shaidace tashi mutafi daddy yafadi yana murmushi tareda mikewa itama ammi murmushin take tamike sukayiwa nisha sallama suka fice , haba data jikin nisha seyayi sanyi jin abunda daddy yafadi ba ayiwa papan aheel gwanita gaba kidaya setaji tasare, tattare kayan abincin dasu ammi sukayi amfani dashi tayi tamaidasu kitchen,

Dawowa parlour tayi tazauna natsawun wasu lokuta, tana dan tunane tunane, guraren 9 nisha tamike tanufi kitchen ta dauka tray din abincin da zata kaiwa ajmal tanufi hanyar waje, sannu ahankali nisha ta dangana ga side din ajmal, security dake gefe yana ganinta dauke da tray din abinci yayi saurin bude mata kofar parlourn yana mata sannu, "

Thanks tace misha kafin tashige yamaida kofar yarufe , daga nisa tahangeshi saga dining area yana zaune bisa kujeran table din yana sanyi da wando short black iya gwaiwa se white shirt ya minmike kafa fuwa yana latsa waya yana rike da cup din coffen yanashaa , yanajin motsin shigowarta ya gyara zamansa yana maicigaba da latsawar tasa,

Ahankali nisha takariso kusa ta ajiye traydin abincin tasuma gaisheshi , maimakon ya amsa mata sai yatsareta da tambaya,"

Meya hanaki kawomin dinner jiya in the nights? batakaga bashi amsaba nisha ta hangi heelah jikin cikin dressing nazuwa aiki yanayin shigar yayi matukar amsar jikinta tayi kyau sosai ganin nisha tsaye tareda papan aheel sun zuba mata ido suna kallonta yasa takarisa sakkowa ahankali tana kuma kare musu kallo itama,

Ajmal kwaida kaiyayi yamaida idonsa kan wayarsa yacigaba da abunda yake , heelah da nisha kallon kallo sukashiga yiwa junansu nisha tasunnar dakai kasa kirjinta sai bugu yake , kwata kwata batayi zammanin ganin heelah ba tayi zaman tana can wajan aikin nata ,

heelah kallon traydin dake gaban ajmal tayi sannan takai kallonta ga ajmal din daya hade gira yabata fiska babu alamar wasa ko sakin fiska atare dashi, kallonta takuma kaiwa ga nisha wacce ido suka fito waje sezaresu take ,
Chapter 35 · 0% Book details