← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 38

Sashe 13

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gimtse fiska fareeda tayi tana kallon kakar tasu , jin dariya kasa kasa yasa taimada kallonta ga fadeela dake dariya kasa kasa cikin hanzari reeda takalli Hajj mama tana fadin,"

wlh Hajiya kiyiwa fadeela magana dariya fa takemin, ato gulmarki taja miki Hajiya tafadi,

nan fadeela tasake bushewa da dariya , pillow reeda ta dauka tabugawa fadeela, itama fadeela tadauka tajefa mata, Hajiya kam kallon su take tana dariya,

Aban garan Nisha kuwa tunda tayi breakfast bata zauna adakinba takoma tayi kwanciyar ta
Daga daki takejin hayaniyarsu amma takasa fitowa, saboda kanta dake dan sara mata,

Shigowar aheel ne yasata dole ta tashi tazauna ta saurari shirmensu da yasaba, Aunty gobe Monday zan koma school zakirakani koh Muje kiga school dinmu, school dinmu yanada kyau sosai, Ai nataba baki labarin koh ,

Eh kataba bani lbr yana da kyau nisha tafadi, yau zamuje tare koh , eh tace masa dan yau kwata kwata batajin yanayin surutu,

muryan aheel taji yana sake fadin," yau mummyna tana gd bata fitaba, baki taba ganin mummyna ba koh, nataba mana , cikin zaro ido yana fadin," a ina to, ? murmushi tasakar masa tace," lokacin da kake kwance asibiti,

lah ashe kintaba ganinta yafada yana washe baki, murmushi tamasa batareda tace komaiba, su fareeda dane suka shigo yayinda suka gama hiransu kowa yakama nashi guri, yauwa aku sarkin surutu yana nan yana miki surutun nasa da yasaba koh, fadeela tafa yayinda suke karisuwa ,

kallonsu nisha tayi tana fadin,"har kungama firan , eh mungama anyi bake, cikin sauke numfashi Nisha tace,"to yazanyi naso fitowa ayi hiran dani amma ciyo kan nan ya matsamin , oh sorry kinsha magani kuwa, fareeda ta tambaya," aa base nashaba nasuma jin sauki, aheel ne yazame daga bed din yana fadin," Aunty zanje gurin papana zan dawo anjima , to kawai tace tareda bin bayansa da kallo har yafita,

Wani dugun numfashi tasauke tareda maida kallonta gasu fadeela da suka kwanta suna danna phones dinsu, ahankali tazame daga gadon tanufi hanyar fita, domin kuwa ta gaji da kwanciyar, parlour tanufa tanemi kujera daga gefe ta zauna tvn parlourn akunne yake dan haka tashiga kurawa tv ido,amma hakalin ta kwata kwata baya wajan , da alamar ta lula wani dunyar tunani,

Kamal ne yashigo parlourn hand dinsa daukeda hairbrush yana taje kansa, idonsa ne yasauka kan Nisha dake zaune takurawa tv ido, da alama batama sanda shigowar sa ba,

ahankali yamatsa tsakiyar parlourn yana karewa Nisha kallo da mamaki, kallonta kawai yake bakinsa tagagara furta komai,

ita kuwa jin kamar ana tsaye kanta yasa ta daga idonta kadan, dantaga waye, daram gabanta yafadi kamal tagani tsaye kanta yana kallonta,

azabure tamike tayi baya tana kallon shi cikin zare ido, shima haryanzu kallonta yake," NEESHA kece,?:kml yafadi yana sake dubanta da kyau, ita kuwa baki se bari yake takasa cewa komai, hakan yasa tajuya tareda watsawa da gudu tayi daki,

shikuwa baki bude yake binta da kallo harta shige dakin, abun yayi matukar bashi mamaki meye Nisha taxoyi gdnsu, to kodae gizo tamasa,

kaiwan nan ba gizo bane tabbas nisha ce yabawa kansa amsa, yana cikin wannan tunanin ya tsinkayi muryan ammi dacewa,"

kai kumafa seyanzu, hanzarce ya kalli ammin tasu cikin sosa kai yana fadin," eh wlh , wani irin bacci kake haka, kayi break kuwa ammi ta tambaya, eh nayi Barka takaimin seda nayi ma nakoma baccin, okay to ae shikenan ammi tafada tareda take kokarin juyawa tayi kitchen, cikin hanzari kml yace,"

am bakowa mukayine, cikin tsareshi da ido tace," bakowa kuma aina ammi ta tambaya, eh yanzu naga tashiga bedroom dinsu fadeela, murmushi ammi tayi tana fadin," kodae Nisha kagani,?

Eh to ina ganin ita dince kamal yabata amsa,
baku taba haduba se yau kenan, eh kawai kml yace yayinda yake kallonta yanaso karin bayani, okay yanzu ina dan saurine in nasamu time zan maka explain daga baya kajiko, okay yace batareda yasake cewa komaiba, nan ammi tajuya tashiga kitchen abunta, ganin haka shima yajuya yafita daga parlourn,

Nisha kuwa tunda tashiga daki tanemigu ta kwanta, lokacin ta tarar su reeda duk sunyi bacci, nan ta nitsa kanta cikin pillow tana jin zuciyar ta yanda yake mata dukan uku uku, yanzu ta tabbatar da zarginta dama shine ya kml dinda su fadeela suke fadi, atunanin ta wani kamal dine da ban ashe kamal din da tasanine,

tundaga wannan lokaci Nisha tasumu sara daga sungama breakfast sun koma parlour Hira zata zame tayi daki tayi zamanta because kunyar hada ido da kamal takeji,

dukansu sun lura da hakan atunaninsu rashin sabu dasune wanda kuwa ba haka bane,

haduwa da kamal ne bata sonyi, wani lokaci ahar tunani take akan wace irin kaddarace ta kawota gdnsu kml

inama bata biyusu Hajiya ba tayi wani wajan daban, duniya da fadi ae bazata rasa wajan fakewa ba,

aban garan kml kuwa tunda idanunsa sukayi tuzali dana Nisha yakeson sake ganinta but hakan yakasa samuwa because duk wani hanyar dazaisa su hadu Nisha ta tusheshi ko haraba gdn ta daina fita, balle yazuba ido wajan shiga da fitar ta,

Abunda yasani shine zasu hadu komai daran dadewa tunda gd daya suke dole wani dalili zai hadasu,

yau hutun so fareeda na makaranta yakare komai ya dawo mata sabo kewa yasake dawo mata, domin kuwa su reeda sun koma makaranta,
dama hutu suke yanzu kuma hutu yakare,

shima kuma aheel mutumin ta yakuma school kuma wuni yake acan, gaba kidaya abokan surutun nata basa nan gd yakoma shiru, hatta itama ammin tana zuwa office, dan haka intaji kewan yamata yawa, seta tattara takoma sashin Hajiya tazauna suita hiransu, har yamma kafin su fadeela sudawo,

bikin kml da nabeela se karatuwa yake yau bai wace saura month ba, gd se shirye shiryen biki ake kaikace next week ne bikin, su fadeela har ankai dinki na event din bikin, duk da kamal yasheda musu shiba wani bidi'a zaiyi a bikinba,

atunanin shi wannan bawani bikin da za'ayi wani shagali bane because bikin bawani shiga heat dinsa yayi harcan ba,

nishane kwance bisa gado yayinda idonta ke kallon sama kamar mai nazarin wani abu, phone dinta ne yashiga ringing akwai kamar jira take akirata dama, salmace kan laye, hanunta har bari yake wajan dagawa,

Karawa tayi akunne ta tareda yin sallma, salma bata amsa sallamar taba tashiga watso mata tambaya, " wai nikam qlu kike kuwa, salma tafadi,cikin hanzari Nisha tace," mekika gani meyafaru,? tafada yayinda take kokarin gyara zama, ✍️

Bansan meyake damunkiba, tunda nabar gdnku baki sake daukar waya ki kiraniba, kuma kince zakizo gd shima kuma kin gagara, shine nace bari nakira naji har rayuwa tai miki dadinda zaki manta dani koh,

jikin Nisha ne yayi sanyi dan tasan bata kyauta ba , gaba daya tarasa meke damunta, cikin sanyin murya nisha tace,"

Nama rasa bakin magana amma kiyi hakuri nasan ban keutaba, ke kwata ce kuma aminiyata aduniyar nan banida kawar datakaiki, hasalima in inada wata damuwa nakanzo nasanar dake ko ummata wani damuta bata sani kamar da ke kika sani , salma yanxu haka ina cikin damuwa amma maganar bazaiyiyu awayaba, gashi gdn nan ba afita daga gd se mkrnt, kwata kwata ba afita salma,

naji ba afita amma yanzu dole kisamu hanyar fita domin kuwa ankawo kayan lefena, salma tafada tana tura baki duk da Nisha ba ganinta takeba,

cikin farin ciki nisha ta wantsalo daga gadon tahau rawar murna kaikace ita aka kawo kayan, daga bisani tadan dakata da rawan tana fadin," amma kuma shine baki sanar daniba kafin akawo kayan,

dama nazuba miki idone inga ko zaki kirani, amma baki kiraba kirkinki yayi kadan, gashi nina damu dake nakiraki, kuma na sanar dake, yanxu de sena jiki kuma ina zuba ido, to kawai Nisha tace daga bisani suka kayi sallama, salma takatse wayan, zama nisha tayi abakin gadon tareda zamewa ta kwanta farin ciki fal zuciyar ta, jitake kamar ta bace ta tafi gdnsu salma,

aheel ne yashigo dagudu dakin tareda hawa bed yafada jikin nisha Yana washe baki yana fadin," Aunty

ta tsorata sosae ganin bata san da shigowar shiba, cikin tsoro tana zaro ido ta dago aheel tana fadin," amma kai wannan yaro koh tafada tareda jan kumatun sa , gabani tsorofa,

washe mata baki yayi yana fadin, "Aunty wai tsorita kikayi, eh mn, waima mai ya hanaka zuwa school yau, Nisha ke tambayan sa,

lah yaufa weekend kin manta ba school , oh haka na manta , suna cikin hiran tasu su fareeda suka shigo daya nabin daya, suka karisu suka zauna, hanun fadeela dauke da chocolate suna sha, fadeela ne ta ajiyewa Nisha ledar acinyarta tana fadin," ga chocolate kisha, nan sha ta bude ledar tadauki daya tabare tasuma sha har wani lumshe ido take aikin dadi, nisha na kaunar chocolate sosai,

Nan Nisha takalli aheel dake kallonta shima tana fadin," kaima kadauka kasha mana, nan yakai hanu zai dauka reeda tabuge hanunsa tana fadin," mai zakayi, Aunty nima sha zanyi yafada tareda marairaice fiska, fadeela ne ta amshi maganar da cewa" saboda kaine mai bakin kwadayi koh,? to muma ya kml ne yasammana kaima kaje yabaka yanadashi dayawa,

cikin hanzari aheel kuwa yazame daga bed din yana fadin," nima bari naje yabani, yafada tareda yin waje dagudu,

Da kinbarshi muma ba iya shanyewa zamuyiba, Nisha tafada tana kallon su reeda, ke kyaleshi yaje zamu iya shanyewa tunda muka dibo, Nisha bata kuma cewa komaiba sukaci gaba da hirarsu, wunin yau kam yamata dadi sosae because abokan hiran suna nan,

sede damuwarta dayane shine sanar da ammi batun fita, dan haka da batun takwana aranta,

Washe gari da suba suka tashi sukayi wanka tareda alwala suka yi sallah kamar yanda suka saba, su fareeda suka suma shirye shiryen tafiya skull domin kuwa 7 a mkrnt yake musu, dan haka basu tsaya wani dugun breakfast ba coffee kawai sukasha suka wuce,

nisha kuwa tana kammala karatun Qur'an da tasaba ta koma takwanta, batayi wani wacci mai tsayiba sbd atunanin ta ammi 10 ma baya mata a gd,

wajan 8:45 Nisha tasamu daman farkawa, dan haka ta sakko daga gadon tanufi hanyar parlour takoyi sa'a can dining ta hangi ammi na break dan haka tasamu daman karisawa dan su gaisa,
Chapter 13 · 0% Book details