← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 38

Sashe 28

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a zaune ya tadda ammi gaban mirror tana shafa mai, ganin shigowar sa yasa ammi mikewa tashiga masa sannu da dawowa, "

Yauwa ya amsa tareda neman bakin gado yazauna yana dan dafo goshinsa,"

Bari naje nashirya maka dinner,"

Ah no da kinbarshima, akushe nake, daga fadin haka ya mike saman bed din face dinsa na kallon sama,

cike da nitsuwa ammi ta matso kusa da bed din gefe tanzauna, tana tambayar shi,"

Allah yasade lapia naganka kamar cikin damuwa, bayida niyar fada mata halinda ake ciki, but amma ba amfanin boyewar tunda dole zata sani koshi bai sanar da itaba, "

Hajiya tanaso ta kunno wutar da bazata iya kashetaba, daddy yafadi cikin damuwa"

What do you mean ammi ta tambaya adan tsorace , "

aure takeso ahada tsakanin MODIBBO da waccen yarinyar Nisha,"

What aure? kuma da Nisha? Because of what ammi tafadi akideme ,"

Yes aure, nasan bazai wuce dan magan ganuda mom din raheelah tazo tayi bane maybe abun ya bata mata rai shiyasa take kokarin yanke wannan hukuncin, "

Kana nufin MODIBBO bai san da wannan hadinba to ya za ayi kenan, amma ta tambaya "

Muzubawa sarautar allah ido hajiyar data hadasu da kanta zata musu bayanin dagashi har ita yarinyar mude ta bukaci daura auransu gobe inshallah, Daddy yafadi, "

Allah ya zabar da abunda yafi zama alkairi fadar ammi, "

Ameen

yaude gaba daya suna cikin zulumi akan wannan alamari mai zaije ya dawo?

taya MODIBBO zaizo ya riski wannan lamari aure da yarinyar da baisan waye itaba, su kansu basu da cikekken labari ko masaniya akan rayuwarta , sude susan yarinyar batada kowa hakan yasa hajiya ta janyo yarinyar jikinta takuma bukaci zamanta agdn

yau kuma kwatsan ta bukaci ta hada auran yarinyar tare da jikanta,🌴🌴 IG AJEEMAL, 🌴🌴

Story and writing by oum amreesh ❤️
(Khaleeseart Raeeys)

Whatapp number
08105545639

Face book account
Khaleeseart Abdullahi Bello,

Free book 🤗

Page 32_33

Washe gari hajiya na sashinta cikin parlour saman sallaya bayan gudanar da sallah jumma'a, tana lazumi, gefe goggo
rabi saman kujera bayan idar da nata sallah tashi amfani da wayar hanunta,

Shigowar su daddy bayansa dauke da abban su heelah hannayansu dauke da goro da minti suka taho suka direwa hajja mama gabanta face dinsu ba yabo ba fallasa,"

Hajiya ga goron daurin auran jikanki MODIBBO masha allah yaude andaura aure kamar yanda kika umurta yau MODIBBO yazama mijin mata biyu, daddy yafadi yana dan murmushi,"

Masha allah alhamdulilla allah ya muku albarka, allah yasanya alkairi cikin auran, hajiya tafadi cike da murna da farin ciki

Ameen! Suka amsa dukansu goggo rabi kamar ta taka rawa haka takeji aikin dadi, "

Daddy mikewa sukayi sallama sukayi wa hajiya kan zasu wuce nan tashiga sambada musu albarka daga bisani suka sakai suka fice daga parlourn suka shiga mota mai gadi yabude musu geat suka tafi ,

Nisha ne tafito daga part dinsu wacce zama shiru yasa tafito tanufi parlourn hajja mama,

da sallama abakinta ta turo kofar tashigo parlourn hajja mama da goggo rabi suna bisa kujera gabansu dauke da goro tareda sweet

haka kawaii taji gabanta ya dan fadi wanda batasan kuma mai dalilin hakan ba, fiskansu dauke da murmushi Nisha ta kariso ahankali kamar wacce aka zarewa laka tazo tazauna gefe dasu, "

Surkarmu ya akayi yau yan makarnta sunmiki yaji goggo rabi tafadi cike da zolaya kamar yanda tasaba, "

Jinayi zama shirun ba dadi shiyasa na gudunan, nisha tafadi adan shagwabe,

Hhhhh shiyasa nace daga kinga kiwa yadameki kiyiyo nan gaki ga rabi zatai tamiki surutu tana zuba kamar fanfon da yabaci, hajja mama ta fadi tana yar dariya, suma su nisha da goggo rabi dariyan suke rabi tana fadin,"

Hajiya nice suruna kamar fanfon da yabaci tafadi tana harba sweet da tabude takai bakinta, "

Eh mana narasa ina kika koyi surutu haka koda yake shima mijin naki gwanin surutunne, se allah yabaku da wanda magana ma bawani damunsa yayiba hajja mama tafadi, dariya rabi tayi tana fadin"

hajiya kenan nan daga bisani rabi ta dibi sweet din datake sha ta dan kawa nisha,"

Karbi kisha muji dadin hira mubar hajiya da goro, dariya suka sake titsirewa dashi Nisha ba tunanin komai aranta takarbi sweet tasuma shaa suka cigaba da firansu

washe gari da dare bayan sun kammala dinner sunyi firan dare sunkare, kowa yanufi bedroom dinsa ,

ammi na zaune saman sofa zaman jiran dawowan daddy kamar yanda tasaba, tun wunin jiya da tasamu labarin daura auran MODIBBO da nisha haka kawai taji zuciyarta yakasa kwanciya,

Sometimes tana try din number ajmal setaji baya shiga kuma bai taba kiraba tunda yasa kafa ya tafi yauma haka taji tasake gwada kira ko zata dace,

Yaude tayi sa'a wayar tashiga ringing daya zuwa biyu ya dauka, ammi baki har na bari wajan fadin,"

MODIBBO ina kashiga haka phone dinka baya shiga, murya can kasa taji yana kiran sunanta"

Ammi! What happened, ina gd

Gd kuma ? Ammi ta tambaya ,"

Yes ina parlour ajmal yafadi, kashe wayar ammi tayi tanufo down fitowa tayi daga part dinsu tanufi sashin IG

Tana zuwa ta murda handle din kofar tashiga, bakowa a parlourn se dan kayan tarkacen da IG yayi order na kayan ciye ciye da yagama ci yabarsu awajan, direct bedroom dinsa tanufa da tayi tunanin yana can,
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴

Story and writing by oum amreesh

Free book 🤗

Page 34

Ba takai ga karisawa bedroom din ta hangoshi yana kokarin saukowa daga upstairs yana sanye cikin night dresses,

tsagaitawa tayi tana jiran sakkowar shi , yana isowa ya tsaya agaban ammin tasu yana fadin,"

Yadai what happened? Ammi jan hanunsa tayi suka karisa suka zauna bisa kujera daga bisani tasuma fadin'

MODIBBO lapia kuwa ya naganka wani sukuf dakai what's wrong with you? Ammi tafadi tana dan shafo gefen face dinsa, "

No things mekika gani? ya tambaya"

MODIBBO naga kadan fada kalli eyes dinka duk yanayinka ya canza baka da lapia ne? "

I'm feeling fine kawai kajiyace inaso nayi bacci na huta ajmal yafadi akasalance, "

Are you sure bakomai, ammi takuma tambaya tana kallon dan nata cike da kauna da nuna kulawa,

Gyada mata kai yayi alamar eh hakan yasa ammi nunfasawa sannan tace,"

Okay ka kwanta kahuta naga dare yayi sosae but gobe inshallah akwai magana da nakeso muyi very important ammi ta karishe zancen da mikewa"

Okay kawai IG yace yana dan lum lumshe ido , nan ammi tai masa seda safe ta kama hanya tafice daga parlourn,

Yana ganin fitar ammi shima yamike asukwane yanufi bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa,

Washe gari da asuba assalatu akunnen ajmal ya sauka amma kasala ta hanashi mutsi balle yamike gaba daya jikinsa amace yake bacci bata ishi idonsa ba,
.
yanajin yanda ake nocking na door but yakasa tashi daddy jin shiru ajmal baiyi mutsiba yasa daddy bude kofar yashigo

Kwance yasami ajmal kamar wani baby ya takure guri guda yana rungume da pillow tsam akirjinsa, lallausan kashinsa duk ya hargitse saman face dinsa, Daddy kada kai yayi yana murmushi cikin natsuwa ya karisa saman bed din ajmal,

Daddy hanu yasa ahankali yajanye pillow da ajmal yarunguma , ajmal jin anrage masa jin dadi anrabashi da tattausan pillow nsa yasashi bude ido ahankali tar yabude ido akan daddy dake zaune tsakiyar katafaran bed dinsa yana sakar masa murmushi,"

Wake up mana yaufa kayi late daddy yafadi , lum lumshe ido IG yashiga yi tareda tashi zaune ya zame daga bed din yanufi toilet dan gabar da alwala yafito

Daddy naganin fitowarsa yamike yayi gaba ajmal ya rufa masa baya jiki amace, suna dawowa daga masallaci IG yakuma kwanciya dan cigaba da baccinsa,

dasafe bayan kammala breakfast dinsu ammi da hajiya, ammi takoma kitchen takuma hado wani zazzafen break din, tajera a try tasuma kokarin fita daga parlourn,"

Ikon allah kekuma ina zakikai wannan breakfast din hka, hajiya ke tambayan ammi, budan bakin ammi keda wuya daddy ya tari maganar dacewa"

MODIBBO zata kaiwa kinsan ya dawo jiya, "

Ikon allah shikuma ba' a sanin tafiyar sa da dawowarsa fadar goggo rabi tana kallon hajiya datayi zuruu, takasa cewa komai,

Murmushi Daddy kawai yake yana kallon hajiya da idonta da suka fito waje, tuni ammi tayi nisa part din ajmal, tana zuwa ta tura kofar tashiga,

azaune tasameshi saman kujera yana sanye cikin shiri mai kyau t shirt and black jeans yayi kya dashi yayi ordern break ya tusa agaba yana kokarin ci,

cikin saurin ammi ta karisa bisa table din dake gaban sa tature abinci da ajmal yayi order ta ajiye nata girkin tana fadin,"

Please as from today bana bukatar sake ganin wannan abincin kantin, kaifa babban mutumne ba girman ka bane cin abincin kanti, ammi tafadi tana kokarin zama kusa dashi yayinda take kokarin zuba masa abinci,"

Nasan rashin mai dafa maka yasa kake sayowa kuma kai nasan bakason yar aiki to ai gwara nina kashe duk wani uzurina nadafa maka kaci because nasan kayi missing girkina kuma nasan yanzu inkaci zakaji dadinsa sosai ,

zazzafan pepper soup tatura masa gabansa gefe ga arish and bugar tareda zazzafan coffee ,

Ajmal ba musu gskyne yayi missing special food na amminsu tun bayan aurensa da heelah , yayi aure but bai taba sanin dan danun girkin matarsaba because ba abunda ta iya na girki, se fita office da kwanciyar bed,

Ko kimtsa daki batayi se idan sun fita office dukansu aturo baba barka ta share musu dakin ta kimtsa duk da bawani baci yakeba, saboda ba cika zama sukayiba,

Ahankali ajmal ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa nan ya dauki spoon ya dibi rumun soup din yakai baki yana lum lumshe ido, ammi inde gurin girkine ba a magana,

Taji dadi sosai ganin yanda yasaki jiki yana diban girkin data kawo masa, "

Kayi waya da matar ka kuwa, ? ammi ta tambaya asukwane,"

Meyasa zamuyi waya ajmal ya watsu tambayar sa yayinda yakai bugar bakinsa hankali kwance yake maganar, sosai ammi take bin ajmal da kallon jin amsar da yabata, "

🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴

Story and writing by oum amreesh❤

(Khaleeseart Raeeys)

Free book😍

Page35_36
Chapter 28 · 0% Book details