← Book details Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Ig Ajeemal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

se wajan karfe 10:30 , Barka tazu ta tashesu tasanar dasu ana jiransu a parlour, wanke bakinsu sukayi sannan suka fito, angama shirya komai kan table Hajj mama zaune harta fara cin abincin ta, karisowa dining din sukayi suka shiga daga mata gaisuwa bata kallesuba tamaida kallonta ga nisha tareda amsa nata gaisuwan, ganin haka yasa suka sake gaisheta karo nabiyu , murya can ciki ta amsa musu, sannan suka nemigu suka zauna tareda diban abinci suka suma ci, suna tsaka daci, AJEEMAL ya kunno parlourn hade da sallama jikinsa sanye da kana nan kaya wayanda suka amshi jikinsa , abunka da kyakykyawar namiji sede ace shiyayiwa kayan kyau, hand dinsa daukeda na aheel, fiska ba yabo ba fallasa, ya nemigu daga parlourn yazauna remote ya dauka ya kunawa aheel cartoon amma sam aheel hankalisa baya gun, yana kan Auntyn sa se washe mata baki yake yana kokarin tashi yaje gunta ganin yanda papansa yarike hand dinsa gam yasa yakalli papan nashi , koda yaga hankalisa nakan wayarshi yasa shi dole yakura yakoma ya zauna,

Nisha duk tana ganin abunda AJEEMAL keyi wato bayason aheel yazu gunta shiyasa ya hanashi tashi, su reeda kam tunda yayansu yashigo suka dakata da cin abincin kirjinsu se dukan uku uku yake, Hajj mama mikewa tayi tareda riko hand din nisha suka nufo parlour, ganin Hajiya ta tasu yasashi zamewa daga zamar da yake still yana rikeda hanun aheel, gaisheta yayi ta amsa da fara'a tareda neman guri tazauna, shima kujeran ya koma tazauna yashiga latsa wayarsa , Nisha kamar bazata gaishe shiba, sekuma tace,

" ina kwana, shima shiri yayi kamar baijiba, sekuma yace lapia, tareda maida kansa ga wayarsa, jin muryan aheel yakira sunan Auntyn sa yasashi AJEEMAL saurin kallonsa sekuma yamaida kallonsa ga Nisha da tamikowa aheel ahannu alamar yazu, ganin Hajiya na kallonsu yasa AJEEMAL yasaki hand din aheel fiska murtuke yakebin aheel da kallo ganin irin tacinsa dashi da Auntyn tasa dayake Fadi, ahankali aheel ya dingisa yakarisa gun Nisha tareda fadawa cinyarta yana dari itama Nisha dariyar take tana fadin,

" my baby yakake, I'm fine aheel yafada yana washe baki, duk akunne AJEEMAL surutun dasuke, aunty shine bakizo kika karamu wasanba koh baruwana dake aheel yafada yana shagwabe fiska, daram taji kirjinta yabuga ba ita kadaiba hattasu reeda dake zaune haryanzu sun kasa tashi daga wajan dasuke,kaikace ba kowa awajan, ko mutsi basayi, se yanzu AJEEMAL ya dago yamaida kallonsa ga su fadeela daga inda suke zaune yana fadin," yau kunfi karfin zuwa kugaishenine toni bari nazo nagaisheku yafa yana kokarin mikewa, cin hanzari harsuna gwaral , cikin rawan jiki suka karisu tareda zubewa saman capet suna gaishe shi, cin sake fiska ya amsa musu yana murmushi, nan hajja mma da AJEEMAL suka buge da fira wanda yasa su fareeda tunanin komai yawuce, fadeela "

go and call me Barka AJEEMAL yafadi, okay kawai tace tanufi gun baba Barka dan kiranta, ba adadeba suka taho tare, seda suka gaisa da barka daga bisani yasheda mata cewa yau yana bukatar tahuta kartayi aikin komai gdn nan, girki ko shara kowani wanke wanke tabarwasu reeda ,zasuyi komai in akwa wajen datake da bukatan tafiya zata iya zuwa, tansan halin AJEEMAL niya fadi magana baya canzawa kuma ba atamka masa , dan haka batayi musuba tajuya tatafi, amma gsky ba karamin mugunta yashirya musuba, suma kansu da jikinsu yasaba da wahala ya suke karewa da aikin gdn, balle su yaran gdn da basusan komaiba se hutawa da kwanciyar gado,

gaba daya parlourn yadau shiru hajja mma da Nisha kallon su fareeda suke da tausayawa, sukuwa ido raurau kamar masu shirin yin kuka, wannan wani rin punishment yayansu kesunyi musu, am sekutashi kuje tabaku wani aikin kufara kafun naje nadawo,

"I think yau su Daddy zasu dawo yafada yana kallon Hajiya, eh yau sukace suna hanya, alright bunda yace kenan yamaida kallonsa gasu reeda yana fadin," so kunga yau seku farantawa ammi rai da special cook nasan zatayi happy sosai, zanfita naje nasiyo wadansu kayan abincin seku hada akai, yafada tareda mikewa yana murmushi, kallo sukabi bayansa dashi, tareda mikewa suka nufi hanyar kitchen kamar yanda ya umarcesu, Hajiya ce tabisu da kallo tana fadin,

" lallai kam za aci girki mai dadi agdn nan yo inbanda abun AJEEMAL mesu fareeda suka sani agirki banda indomie wayan nan kam se Barka tasa musu hanu dole, inba hakaba shirmensu kawai zasuyi zanga ya zakuyi inkunje gdn maza jenku ae bakowane yakecin abinci yar aikiba irin yayanku, bakaramin mamaki nisha tayiba jin basu iya girkiba, muryan Hajiya taji tana fadin," nikam bari naje bedroom nadan mike zuwa anjima tafada tareda mikewa, tafiya zakiyi aheel yafada yana kallon Hajj mama, eh zanje nadan kwanta kadan ga Auntynka katayata Hira, kozamuje can din Hajiya tafada tana kallon Nisha, aa zamu zauna anan karmuje mudameki da yawa, dariya Hajiya tayi tana fadin,

" to shikenan bari naje tana fadin haka tajuya tafita, ganin haka yasa Nisha takalli aheel tace

," jirani bari nazo tafada tareda gyara masa zama akujeran, kitchen tabisu fadeela, tundaga shigowar ta , tasan lallai kitchen yayi baki, Barka tsaye akansu tana dariya tana kallonsu, kaida kaga yanda suke aikin kasan babu alamar sabo a taredasu, daga bakin door din kitchen Nisha tatsaya tana kallon su gaba daya yanda suke wanke wanke ba tsari, gaba daya guri ya hargitse, ga fiska babu annuri, ko wacce baki kamar zai taba bango, kai yayan nan, kukawo nan natayaku gaba daya kun bata jikinku kubarshi kawai zanyi cewar Barka, amma sam basu kalataba balle sumatsa yanda ta bukata, juyawa nisha tayi takoma parlourn gaba daya sun bata dariya da tausayi, nan ta zauna kusa da aheel suka cigaba da tadibsu, yana bata labarin school dinsu papa yace ranar Monday zai cigaba da zuwa school tunda yaji sauki, se wajan azahar suka fito daga kitchen din sukayi iya abunda zasu iya suka barwa Barka sauran, suna fitowa suka nufi dakinsu gaba daya sunyi laushi,

seda suka gyara dakin nasu suka share tas mai yayi need sannan suka fi suka haura sama dakin ammi dana, ganin aheel yayi bacci yasa Nisha tazameshi daga cinyarta ta gyara masa kwanciyar, daga bisani tanufi inda taga su fareeda sukayi, nan ta tayasu suka share suka goge ko ina duk dacewa dakin bawani faci yayiba, suka kuna turaren wuta mai bala'in kamshi da kama daki, nada nan gd yadau kamshi, haka suka shiga bangaran Daddy shima suka gyara shi need suna kammala wa suka nufi dakinsu sukayi wanka tareda alwala sukayi sallah, gada nan suka nemi gu suka kwanta dansu sake gajiya, Nisha kuwa tana gama shiryawa tanufi parlour ganin tabar aheel shikade yana bacci, zama tayi tasake masa matashi da cinyarta tana kallon kyakykyawar fiskar shi yayinda yake bacci, lumshe ido tayi tana sakawa da kuncewa cikin zuciyar ta, nan kuma tabude idon ta saukeshi an aheel dake kwance cinyarta, hawaye ne , yashiga wanke fiskarta, ta tuna lokacinda take kwance cinyar umman ta, itama lokacin da suke tareda umma bata rabuwa da cinyarta, kullum insuna zaune se yakasance kan Nisha a cinyar umma,

" oo rayuwa kenan allah kajikan ummana, allah ka kai haske kabarinki, yaushe zansake samun farinciki irin wanda nake acikin mahaifana, ya Allah na rokeka ka baiyanamin ma haifina, iduk inda yake kasa yana cikin koshin lapia, ubangiji ka karkatu hankalisa gareni, ahankali tasa hanu tashare hawayenta, hadeda maida kanta jikin kujera,gd yayi tsit kamar ba kowa su reeda sun dade da bacci banda Nisha datakasa rintsawa ta zauna ta tsunduma kogin tunani,

Motar AJEEMAL ne yakunno kai cikin gdn, mai gadi yabude masa geat, yashigo yayi parking, yafito tareda kiran mai gadin cikin rawar jiki maigadi yakariso yana fadin

," ah yallabo sannu da zuwa, yauwa sannu AJEEMAL yafada tareda mika masa ledojin hanusa yana fadin yakai ciki, yana fadin haka yajuya yanufi part dinsa, nan mai gadi yanufi parlourn da aikenda aka bashi, nisha yatar a parlourn yamika mata yace inji yallaboi AJEEMAL, nan ta amshi sakon tai kitchen dashi ta direwa Barka, tanufi bedroom ta tasu su fareeda daga bacci ta fada musu sakon yayansu ya ISO, seda sukayi sallahn la'asar daga bisani suka nufi kitchen suka suma aiki ba kama kafar yaro, duk abunda suka san da Daddy da ammi naso shi suka daura, Barka basa musu hanu tana nuna musu yanda zasuyi, karsu tafka shirme, duk da nisha itakam ba bayaba, wajan girki, dan lokacinda suke gda da umma ita take komai bata barin umma tayi ko hanyar kitchen sede tazama yar kallo kawai, dan haka ta zage sosai wajan nuna musu nata bajintar,

aheel ne yatashi daga bacci ya dingisu kitchen inda yake jin muryan su , Nisha naganin shi tazame hanunta daga abunda take tanufi gurinsa tana fadin,

" baby katashine, gyada masa kai yayi yana tambayar papansa bai dawoba, ya dawo muje nakaika tafada tareda jan hanunsa suka fito daga kitchen din, har part dinsu tarakashi tareda murda handle din kofar lokacin AJEEMAL yake kokarin fitowa shima cikin wani shirin mai kyau da alamar fita zai sakeyi, Nisha tsawa tayi tana kallon kyakykyawar fiskar hade da lumshi ido tana shakar daddan kamshin turarensa mai wayar mancewa dan ko zama yayi agu yatashi se ka kwana 2 kina jin kamshin wannan turaren, hankali take sakebin kamshin jikinsa tareda matsuwa ahankali, sake baki yayi yana kallonta ganin yanda ta lumshe ido tana matsushi, baya yayi da sauri yana fadin ,

" ke lapiyarki meye hakan yafada cikin da ga murya ya na mai hade gira yana kallonta arazane tabude ido se yanzu nutsuwarta ya dawo gaba daya ta rude jin tsawar da ya buga mata, shikansa aheel seda yatsorata yanda yaji papan shi, ya dagawa Auntyn sa murya, bin mahaifin nashi yayi da kallo tareda matsawa kusa shi yana fadin," papa ina zakaje nima zan bika yafada yana jan hand dinsa, ✍️ .

Page 11, cikin bacin rai ya kalli nisha sekuma yamaida kallonsa ga aheel yace,

" zanje nadauko su Daddy daga airport ne yanzu zanje nadawo, sekuma ya daga kai tareda hararota Nisha da ke kokarin fita daga parlourn wanda kanshin turaransa yajawota ciki, cikin kaushin murya yace

," ke tsaya, cak tsaya tana kallonshi jin mai zaifada seta ga yamaida idonsa ga aheel yana fadin,
Chapter 10 · 0% Book details