← Book details Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rai dai Rahama ke dai bari in auri Felisha zaku sha mamaki nifa ku
e zanta turowa ina siyan gidaje wallahi sabida ko ta sakeni na fita da fitata dan ba mutunci bane dasu akwai wani abokina da yake Auren Baturiya wallahi da muke hira yake fa
a mun kullum a cikin fa
a suke da kai
ararshi kotu, muna kan wayarma ta fisge saida taji muryata shine ta sauke ajjiyar zuchiya"
Dariya muka tuntsire dashi dukkanmu
Bana Uzairu zuchiyata yayi abun kai har nera dubu biyar ya bayar ni kuma na bada dubu ashirin Rahama ta saka kai ta tafi.

Saida nayi sallah kana na rarrabe tsarabar dana kawo lokacin Maigogul ya fito yana falon yana waya da Hajiyarshi sai kashe murya yake yi yadda kuka san tsohuwar karuwa.

Har su Layuza saida na musu tsarabarsu nasa Aisha ta kai musu, sai ga Raliya ta hauro godiya.

Ni dai ina yin sallar la'asar na sake kaya na fito shar dani tare da tsarabar su Mardiyya da Baba Malam.

Har zuwa wannan lokacin Rakiya bata dawo ba su Aisha suna Kitchen zasu
aura abinci.

Dubu biyar na basu nace a siyo kaza
atuwa a fasheta a cikin jallof
in.

Maigogul ya tusani gaba sai gamu a
ofar gidansu Babangida almajirai cike anata karatu Baba Malam na zaune akan kujerarshi ya hangomu mun nufoshi.

"Sabuwa Maigogul kune a tafe?

Lallai yau ina da manyan ba
i.

Kai magajin malam shiga zaure na uku ka shinfi
a mana keso maza"
Ai kuwa sai Malam ya mi
e yayi gaba muka bishi har zaure na uku.

Ins hango zuwanmu gidan na farko lokacin ina
auke da cikin mardiyya a wannan zauren muka zauna.

Rayuwa kayan Allah komai mai wucewane ada inna doso zaurukan gidannan sai inji tashin hankali dan nasan dole in shiga in tarar da
iban albarka da rashin mutunci iri _iri daga Malama Babba.

Amman yau gani a gaban Baba Malam hankali kwance.

Bayan mun gaisa sai nayi shiru shi kuma Maigogul sai ya zayyanama malam Halin da nake ciki.

Ya
aura da cewa.

"Ni da naso in mata kiranyen aljanu ma.

To amma wallahi na tuba kawalcinma bana yi sam sa'ar da taci kenan wallahi Malam,
itama Sabuwan nasan ba zata bani ha
in kai ba shi yasa ma.

"Ashsha banji da
i ba.

Ha
a zama da irin she
anun matannan akwai ha
ari sosai.

Amman babu komai zan mata rubutu gobe Babangida da yaran sai su kawo mata, ki dinga sha kina shafe jikinki in sha Allahu babu abinda zata miki yayi tasiri.

Sannan ni da su Aminu zamu yi sauka mu miki adda'a sosai.

Ai maganar turen aljanu shirkace Maogogul na kuma ji da
i sosai da kace ka tuba.

Abinda ya kamata shine mai zai hana da kai da iyalai ku shiga makarantar magidanta ku yi karatu abubuwan zasu kuma sau
i sosai "
Maigogil yace.

"Dake ina da iyali kasan acan Kano Dutse shigowa nake yi duk sati in koma.

Su dai sai su shiga makarantar.

Baba Malam izifi talatin cib akwaishi a kaina kuma na iya ba
i aikine dai dashi ba'ayi kuma babu sanin fassara bare mutum yasan ma'anar"
arashe yana wannan dariyar ta ba
in ciki.

"To ai ta kwana a gidan sau
i in sau
aya zaka zauna a aji, ko majalisin karatu zaka
aru sosai.

A Kano ga manyan malamai suna karatuttuka da littattafai in kana so sai in ha
aka da gadon
aya ko Dr Sani rijiyar lemo ka dinga zuwa majilisi kana sauraren karatu.

Kuma in ka shigo Dutsen ma zaka iya shigowa tamu makarantar a hakan ka dinga
aukar darasi da tuban zaifi tafiya da kyau yadda za'a bautama Allah bil ha
"To shikenan zan dinga zuwa makarantar in na shigo.

Suma su kayi nayi zan musu tayi in suna so ai sai su dinga zuwa wallahi mun gode Baba malam sosai"
"Maigogul ina abokinka Cicib?

"
Dariya suka yi du su biyun ni kuma nayi murmushi.

"Ki soma shiga ciki Sabuwa ku gaisa da
arama sai ki fito mu shiga makaranta kiga yaran naki"
To shikenan.

Ga tsaraba na kawo maka"
Na ajjiye ledar na shiga cikin gidan da tsarabar yara dana Malama
arama.

Tayi mamakin ganina sosai kuma da fara'a sosai muka gaisa na bata tata tsarabar na fito.

Bisa jagorancin Baba Malam muka shiga makarantar anata
aukan darasi
ofar ajin su Mardiyya muka tsaya, tana tsaye tana koyarwa abun sha'awa tana hangomu ta fito da sauri ta rugun
ume maigogul sunata dariya.
ar nema" Cewar Maigogul, murmushi Malam yayi yana kallon mardiyya.

Malama da A
a'u suna aji suka hangomu ai da gudu suka iso inda muke.

Duk muka
unguma zuwa ofishin Aminu
Yana zaune yana ba wata matar Aure littafin arba'una hadith muka shigo
Baki ya rufe ga murmushi ga hawaye a fuskarshi.

"Ja'iri
araso mana"
Cewar Maigogul yana wannan dai dariya da kuka santa
arasowa yayi ya ri
e hannuna.

"Ummi kece kika zo mana.

Yaushe kika dawo?"
Shafar kanshi nayi.

Nice Aminu ya karatu?

"
Murmushi yayi ya dubi
annenshi suma suna cike da farin ciki.

"Adda dama kinsan Ummi zata zo shine baki fa
a mana ba?

"
Mardiyya tace da Aminu.

"Bata fa
amun ba nima ganinta kawai nayi"
Ofishin Baba Malam muka shiga acan mukayi hirarmu na basu tsarabarsu na
irgo ku
i na basu nace su sai wani Abun.

"Ummi bikin Adda amman dake za'ayi komai ko dan Allah?

"
Dani za'ayi A
a'u zan zo tun saura kwana biyu soma bikin in sha Allah"
Ai sai farin ciki ya lullu
esu.

Baba malam yana kan teburinshi yana rubutamun addu'o'i a jikin takadda da zamu tafi ya mi
o mun.

Nan mukai sallama dasu muka tafi akan gobe yara zasu kawo mun rubutun.

Muna hanya Alhaji ya korawoni mun jima sosai muna waya.

Mun isa gida mun tarar kayi nayi ta dawo suna ta cin abinci dake magriba har tayi lokacin
Saida nayi sallah nazo muka gaisa da kayi nayi.

Su madamcy kuwa har lokacin suna asibiti Gaza ma yazo yana can asibitin tare dasu.

Da daddare ma mun kai kusan minti talatin muna waya da Alhaji kafin ya kashe wayarshi yace ga Hajiya nan ta hauro sama.

Kuma Maigogul ya sanar dashi gobe zan karashi Abuja wajen Iyalan Amininshi ya amince mun inje.

Ajjiyar zuchiya na sauke
Ai kuwa washegari asussuba ni da maigogul da Uzairu zuchiyata muka fito da zummar nufar Abuja.

"Wai maigogul me akeyi to a Abujan da zaka kwashi yara ku tafi.

Ke Lolo wai meke faruwane nace miki?

Ka mayar da
an cikin ka abokan yawonka ko ina dan masifa kuna tare wannan dai abu da zafi yake"
Babu komai Rakiya ai yau zamu dawo"
Tsaki tayi tace.

"Allah ya tsare in kun so ma daga can ku wuce Kano ai Allah yana ganin irin zaluncin da maigogul yake yi mana.

Ku kuma bamu bane a gabanku barinma Uzairu zuchiyata sallamammen banza.

"
Maigogul zaiyi magana nace.

Dan Allah maigogul kayi shiru.

Rakiya dan Allah ki dinga sanyaya ranki.

Wallahi ba wani abun muke
ullawa ba kawai gidan wata zamuje su rakiya kawai zasu yi mun"
"Au ta hu
u kuka samo mishi?

Ai kuwa na rantse miki da Allah in ya
aro wani Auren duniya zan shige uban kowa ya huta."
Wallahi dukkanmu saida muka dara
"Rakiya kenan makirar mace.

Allah ya shiryeki mu sai mun dawo.

Kuma yau zamu dawo sai ki shirya tarbata ai kamar yadda Hajiya Balataba take mun ta soya kaji da basmati tana jirana.

Ke kuwa koda na fa
a miki ina hanya bai hanaki zaran buhu ba."
Motarshi ya ja Sama ya bu
e mana get muka fice.

Sai a hanya muka dakata mukai sallah muka naushi hanya awanmu bakwai tafiya yankin Azaba.

"Bani takaddar adireshin in gani, dan babu inda ban sani ba a garin Abuja.

"
Jakata na zaro na ciro takaddar na nuna mishi ya ri
e baki.

"Wuu anguwar manyan kenan.

To ki kirata kafin muje a sakar mana kare"
Uzairu zuchiyata da yake ta waya ai sai dariya.

"Wallahi akwai gidan da muka ta
a kai wasu mata anan Abuja ashe karene mai gadin gidan.

Muna tura get karennan ya taso mana gudun kilomita nawa kunsan muka yi?

Cicib dai har takalmi da
ankwalinshi sai da ya yar.

Munci wuya"
Munyi dariya kamar zamu mutu Uzairu zuchiyata fa
i yake.

"Wayyo cikina zan mutu.
yal
yal
yal
yal"
Mun jima muna dariya wallahi, baza ku gane ba ina mugun son ahalina koba komai za'ayi dariya ayi raha.

Kiran Aisha nayi ringin biyu kuwa ta
auka da sallamarta.

Gabatar mata da kaina nayi sannan nayi mata bayanin gani a Abuja ma inaso inzo gidanta.

Ai kuwa ko a muryarta ta nuna jin da
inta sosai ta sake yi mun kwatance duk da nace mata Maman yasmin ta bani adireshinta.

Cikin minti arba'in sai gamu a
ofar gidanta.

Waya nayi mata tasa maigadi ya bu
e mana get muka shiga ciki.

Tana tsaye da
aton cikinta a gaba fara kyakkyawar mace mai gashi sosai.

Da fara'arta ta
araso.

"Ahh har da su Baba kuke.

Sannunku da zuwa.

Baba mu shiga ciki maraba"
Tare duk muka
unguma zuwa falon gidan wanda yaci ku
i daidai gwargwado.

Zama muka yi aka sake dasa sabuwar gaisuwa kafin kuma falon yayi shiru.

Mai aikice ta shigo da kular abinci da komai a
aton faranti ta ajjiye a gabanmu tare da gaishemu cike da ladabi duk da dattijuwace.
ewa tayi da
yar tace.

"Bari in baku waje kuci abinci ko"
Ta saka kai ta bi wata
ofar.

Abincin na zuba mana jalof
in kuskus ne da soyayyen kaza na cikin jajjagen yaji sai lemukan sha.

Maigogul na soma zuba ma, ni da Uzairu zuchiyata kuma na zuba mana tare ni dai duk hankalina ma baya jikina wallahi komai ma dauriya da
arfin hali nake yi.

Abincin kanshi loma uku kawai nayi na ajjiye lokalin nayi shiru ina sauraren yadda gabana ke ta aikin dokawa.

"Lolo mu kam zamu je mu dawo kafin ki gama abinda ya kawoki zan le
a abokaina.

Duk abinda ya kamata kuma ya dace ki sani kada ki mance ki nutsu ki tambayeta da kyau.

Taso muje Uzzy"
Sallama sukaimun suka wuce.
Chapter 8 · 0% Book details