← Book details Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 28

Sashe 6

Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar kullum muna asibiti tun safe da Hajiya ta warke gaskiya kuma likitocin sun tabbatar mana da hakan.

Ta matsa mu koma gida, duk da shima aiki na najeriya yana jiranshi sai waye waye yake yi da mutane.

Wayar Alhaji na kar
a na fita, dama nakanyi hakan ba dan komai ba sai don in basu waje su tattauna zantukansu na mata da miji.

Lambar wayar Labbai na soma kira ai kuwa tana
agawa na jiyo muryar Maman Shafa da Cicib anata gabzawa.

Cicib sai tattafa hannaye yake yi yana zage zage.

"Hmm Kina dai ji ko Sabuwa?

Ni sai nake ganin Aure kamar bai kar
emu bane.

Tun jiya ake ruwan bala'i a cikin gidannan Maman Shafa mitsiyaciya ta hana kowa sa
at.

Jiyan saida na kwa
e muka daku har Shafa saida naima shegen duka wallahi kafin fa suka shiga taitayinsu."
To wai duk wannan akan menene Labbai?

"
"Akan taga ina yin mangya
a ana siye, ina yin
uli
uli, masu kilishi ma Cicib na kai musu tunkuza suna siye shine take tunanin shi ya bani jarin kinji fa musabbabin wannan rigimar da aketa faman yi ta
i ci ta
i cinyewa"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.

Allah shi kyauta ke dai ki kula da sana'arki kawai.

Ya Adama ta saro kayan kuwa?

"
Na tambayeta dan mu kawar da wancan zancan.

"Ta saro kaya harta koma.

Wallahi ko da muka yi waya jiya tace anata siye, kuma Hajiya Balaraba ta
ara mata jari kuma ita ta ha
ata da mai aikinta ta rakata kasuwa"
Wani farin cikine ya lullu
eni har ajjiyar zuchiya saida na sauke tsabar jin da
i nace da'ita.

Saura su Aisha da su Rahama so nake suyi Aure tukunna.

Yanzu dai in sha Allah gida zan dinga wadatawa da komai tunda Alhaji Zaidu yace zai dinga siya musu hatsi ni sai in dinga basu na cefane kinga yawo in sha Allah ya
are in duka sukai Aure sai in basu jari ko wacce ta kafa kanta itama shikenan"
Mun jima muna hira kafin na kira gidan nanma aka saka a bayyane mukaita gaisawa harda su Hauwa dasu Raliya da magazin da Sama duk saida muka gaisa.

Sama ya ro
eni jari zai zuba furobishon a shagon waje na
ofar gida na mishi al
awarin zuwa
arshen wata.

Su Magazin kuma nace su
ara ha
uri shi Magazin zan tuntu
a ko Alhaji Zaidu ko Hajiya Balaraba in za'a sama mishi aiki dan su ka basu ku
i kayi aikin banza ba jarin da zasu wani ja
arshe ma su cinye a shaye_ shaye.

Ina gama waya dasu na kira Maigogul nanma mun jima muna waya ina kashewa na kira wayar Mardiyya duk muka gaggaisa da yaran sai naji sanyi a zuchiyata.

Na jima a zaune inata waya kafin daga bisani na koma ciki a nanne Alhaji yake sanar mun zamu koma gida Najeriya nan da jibi.

Mun shiga dashi kasuwa mun yo tsaraba sosai gaskiya.

Mun je gidansu Maman Yasmin mun musu sallama ta
auki lambar
anwarta da adireshinta ta bani a takadda, nima na
auki lambata na bata a takadda.

Ranar talata jirginmu ya dira a kano da daddare misalin
arfe bakwai na safe.

A mugun gajiye na shige
arayina, ga gidan cike da
an uwan Hajiya harda
awayenta, ni kuma babu nawa ko
aya.

Ko dana gaishesu sai wani mele bakinsu suke yi ni kuwa nayi shigewata ciki.

Sai naga halamun kamar an shigar mun
aki tabbas ni dai nasan ba'a bu
e ba bar sib
ina ba.

Tsayawa nayi a gaban sib
in sai naga kamar dai ba'a
auki komai ba amman ya zamemun dole gobe gobe in duba in tabbatar komai nawa yana nan.
aki na fa
a na saki ruwan
umi a jikina idanuna a lumshe inata tunane tunane.

Bayan na fito na nemi yadi mai sau
i na saka na shiga Kitchen na ha
a tea na
ebi cincin na dawo falo.

Zan zauna kenan naji ana buga
arayina nasan ba Alhaji bane.

Turyan turyan naje na bu
awayen Hajiyane bisa jagorancin Naja'atu ai kun tuno ta mai saka rigar bacci.

Da fara'a na tarbesu na juya suka shigo duk suka zazzauna muka sake sabuwar gaisuwa.

"Sannu da
ari Hajiya Munubiyace dama tasa muzo muyi miki godiya bisa jinyarta da kika jajirce kika yi, angode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma ha
e kawunanku"
Cewar Hajiya Mansa kenan Amiyar ita Hajiya.

Ayya ai babu komai abunda yayi Hajiya tabbas shi yayi ni mun riga mun zama
aya"
Nan dai sukai mun sallama suka fita.

Ni wallahi dana gama shan shayi na nayi isha sai nabi lafiyar gado.

Wajajen goman dare naji shigowar Alhaji Zaidu.

A bakin gado ya zauna yana mun murmushi.

"Lallai Wazirat ke baccinki kika yi ma kin mance kece da kwana ne?

Kin barni a sama inata juyi?"
Murmushi nayi nace.

Ai na zaci Hajiya ke da kai tunda ni kaga tare mukaita kwana acan ko?"
Fuskata ya shafa yace.

"To ita kam Hajiya ta ha
iyi magunguna tayi baccinta tace a soma rabon kwana daga kanki kiyi kwana biyu itama tayi kwana biyu"
Jawoshi nayi ya fa
o jikina dan yadda nake jin gajiya bana jin zan iya haurawa sama.

Ai kuwa a
akina ya kwana, mun sha soyayya sosai na lura Alhaji bashi da wasa ta fannin mu'amala bil ha
i yake yi mun.

In nayi
orafi sai yace bana isarshi ne ai shi yasa.

Washegari dai da asuba daya fice na tashi nayi mana abun kari mai sau
i dankalin turawa da
wai na soya sai shayi mai kayan
amshi kawai.

A samanshi na jera mishi komai na kunna buna na zuba turaren wuta, na jirashi ya shigo muka karya a gurguje yace.

"Muna da aiki a ofice da yawa fa.

Amman yau ki zauna
an Rano sun yi mun waya zasu zo uhm"
To shikenan nagode, dan Allah da daddare inka dawo...

"
Bakina ya rufe da nashi mun
au lokaci a haka kafin ya sakeni.

"Ba sai kin fa
a ba zamu je wajen Alhaji Baba. gobe in Allah ya kaimu sai muje Dutse mu kaima su Mama tsarabarsu"
Ai saina
ameshi gam.

Sai kuwa daya samu nutsuwa dani kafin yayi wanka ya ca
a ado ya fita.

Ni kuma na koma
arayina na shiga binciken sib
ina saida na fito da komai na sake jerawa.
ankwalin jar atampatane ban gani ba sama da
asa.

Kuma ko ana jibi zamu tafi tabbas naga
ankwalin.

Ai take hankalina ya tashi ainun.

Na gama mayar da komai kenan na jiyo dirin motar
an Rano ko dana le
a Bus guda suka ciko yaran mata da dattijai.

Kaya na sake daga cikin kayan da na tafi dasu dan wallahi kayan sib
in duka sai naji ni bamma yadda dasu ba.

Fita nayi na samesu a
arayin Hajiya anata gaisawa.

"Amarya sannu zo ga waje
ar albarka"
Cewar Yaya Tani kenan.

Gefenta data nuna mun naje na zauna aka gaggaisa suna ta jinjinamun bisa
arina.

Hajiya na
ara basu labarin
arin da nayi.

Kamar minti talatin da zuwansu na dubi Zarah nace.

Zarah muje mu
aura sanwa ko?

"
Yaya Tani tace.

"Hauwa aikin me take yi da ke sai kin
aura girki.

Baki da
ar aikine ke a
angaren naki?

"
Murmushi kawai nayi Hajiya tayi carab tace.

"Kema kya fa
a har sau biyu na nemo mata masu aiki wallahi wai ita bata so dole na ha
ura Alhaji kuma yace tunda bata so a barta"
Shiru Yaya Tani tayi can tace.

"Ai ba'a haka ita ya kamata ace ta nemo
ar aikinta da kanta ai bawai kishiya ce zata nemo mata ba.

Ko ni nan bazan yadda da hakan ba, ko
iyata bazan yadda ayi mata haka ba.

Sabuwa ya kamata ko matar Babanki kima magana ta nema miki mai aiki ta
an dinga rage miki aiki.

Amman abinda zamu ci Hauwa zata sarrafa mana tunda zuwan na Hajiyane kuma a
arayinta muka yada zango kada ki damu"
Hajiya dariyar ya
e kawai take yi.

Tare da maganganun data tabbatar ta kare kanta sabida gudun zargi.

Na fahimci kamar Yaya Tani bata shiri da Hajiyane, ko kuma macace mai fa
a da bata son wargi.

Duk da haka saida na
aura farfesun kaza guda uku suke nan a firjin cikin awa guda ta dahu dake kajin gidan gonane na juyo musu a
atuwar kula na kawo musu.

Ai kuwa sunji da
i sosai.

Wuni sukayi ko da zasu tafi na
ebo sabulai da man Shafawa nace akaima Goggo amfana, ina da ragowar farfesun naman kai na cika kula dashi nace akai mata.

Bamu sake ha
uwa da Hajiya ba har saida Alhaji ya dawo, yaci Abinci ya shirya da zamu je duba su Maigogul ne muka je falonta na duba jikin nata tana zaune tana shan fura.

"Bari ina zuwa ko?

"
Ta mi
e ta shiga ciki, sai gata da leda fara ta mi
o mun wai in ba Uzairu zuchiyata.

Godiya nayi mata, na fita na
an basu waje ko zasu yi magana.

Ya kai kamar minti goma haka ya fito ya sameni muka wuce, muna tafe muna hira har muka isa gidan.

A falo muka tarar dasu suna cin abinci Uzairu zuchiyata dai baya ciki.

Maigogul da sauri ya mi
e ya nufo mu sai murmushi nake yi mishi.

"Lolona ashe kuna hanya, dafa nace gobe in zan wuce Dutse zan biyo ta gidan naku mu gaisa ashe kuna hanya Alhaji Zaidu?

"
Hannu ya mi
a mishi suka gaisa da girmamawa sosai.

Sannan muka zube a
asan kafet ga tsaraba ni
i ni
Mun jima sosai a gidan kafin daga bisani mukai musu sallama suka rakomu har bakin mota.

Muma gobe zamu shiga Dutsen in sha Allah"
Baki Maigogul ya washe yace.

"Allahu Akbar to ai shikenan tazo gidan sau
i saimu tafi a jere, goben zan biyo ta gidan naku sai mu wuce daga nan"
Ni dai banso yace haka ba, amman tunda Alhaji ya amsa yana iya dole na ha
ura a hakan.

Ko da muka dawo Hajiya ta rufe
arayinta sama muka haye muka raya darenmu da farin ciki.
Chapter 6 · 0% Book details