Sashe 8
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yi tunanin zasu rungume juna, sabanin haka hannu ta mika mishi suka gaisa hade da fadin, bayan ya dauki Ramlah
"lale marhababika da bangon gida, kowa ya yi kewarka, Alhamdulillahi da ka iso lafiya jarumina"
Murmushi dauke a fuskarshi ya mayar mata da amsa
"Na yi kewarku sosai uwargidana ke da yara, na yi farin ciki da na same ku lafiya"
Na yi tsaye sororo da kaya a hannu, ina kallon yadda suke fadawa juna yanayin da suka shiga da ba sa tare
Kamar ma sun manta ina gurin, dalilin da ya sa kenan na mika hannu na karbi Ramla, don sai wangale min baki take yi, hade da daga hannuwa alamun tana son in dauketa.
Haka nan nake son yarinyar, ina jin kamar 'yata ta cikina haka nake jin kaunarta.
Gaba ya zauna shi da matarsa, yayin da ni da yara muka zauna a baya.
Ita ce ke tukin cikin kwarewa, yayin da suke ta hirarsu cikin nishadi, da alama sun manta da ni, don kuwa ko sau daya ma basu saka ni a hirar ba, ni ma kuma ban shiga ba.
Ni da yara kawai muke tamu hirar.
Bayan mun iso gida, na nuna mata tsarabarta da aka ba ni in kawo mata, ni kuma na dauki tawa na yi sashena.
Hade da ajiyar zuciya na zauna, kan kujerar, kaina ma har ya fara ciwo, saboda tsananin kishi.
Kwankwasa kofar ne ya sa na mike da sauri, na yi zaton Abbansu Khalil ne.
"Ga shi in ji Aunty a kawo miki." Wata yarinya bakuwar fuska ta fada, shekarunta ba za su wuce sha uku, zuwa sha hudu ba.
"Na gode." Na fada hade da mika hannu na karbi babban tiren.
Tuwon semo ne da miyar egusi da ta sha kifi da ganda, ga ganyen ugu, gaskiya a ido ma kawai akwai burgewa bare a baki.
Sosai na saki jiki na ci tuwon, na sha ruwa.
Sannan na mike na shiga kakkabe dakina saboda kurar da ya yi
Har sha biyun dare na kasa bacci, zuciyata saka min abubuwa marasa dadi kawai take yi
Tana hango min Abbansu Khalil da Maman Khalil cikin jin dadin da baya misultuwa.
"Mtswwww!" Na ja siririn tsaki, hade da mikewa zaune, ni dai yanzu da za a ce in koma budurwa, to gaskiya zan zabi auran miji mara mata, na yadda wata ta biyo bayana, amma dai ni in zo a farko.
Yanzu da ace ni ce farko, da ba ruwana wata ce zan bari cikin kalubale.
Yanzu ga shi tun da muka dawo ban kara ganinshi ba, ko a waya ma bai kira ni ba. Na so kiranshi, amma kuma ina tsoron kar ta ga kamar na shiga huruminta
"Kai jama'a! Kai da mijinka, amma kira a waya ma ya zama damuwa." na yi maganar tare da mikewa na shiga toilet don rage marata
Wasa-wasa ban yi bacci ba sai biyu saura, shi ma cike da mafarkai kala-kala.
Dalilin da ya sa kenan na tashi da matsanancin ciwon kai, har tashin zuciya nake ji.
Da kyar na dafa indomie da tea na sha, na koma na kwanta.
Cikin bacci na ji ana jan kafata.
Da alamun yanayin bacci na bude I danuwana hade da dorasu a kan fuskarshi.
Sanye yake ciki yadi ruwan kasa mai laushi, dinkin manyan mutane, ga kamshinshi da na matarsa na fita a jikinsa.
Haushi yake ba ni sosai, ko kunya tun jiya yana manne da matarsa, ko leko ni ya kasa yi sai yanzu karfe sha daya na safe. Mayar da idona na yi hade da lumshesu, ina jin wani daci a zuciyata.
"Amaryata, ya gajiyarki, fatan kin tashi lafiya?" Ya yi maganar daidai yana zama saitin kaina.
"Ban tashi ba, ya dameka ne? Ba dai ka dawo wajen babbar masoyiyarka ba?" na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma ban ce komai ba.
Bargon ya yaye hade da kwantar da fuskarshi a kan kirjina "Ba kya ji ne?"
"Ina ji, na tashi lafiya" Na yi maganar tare da kokarin ture sa.
"Jikinki zafi"
"Eh bana jin dadi ne tun jiya"
"Ban sani ba, sannu, kin samu magani ne?"
"Eh na sha paracetamol"
"Sannu to, gajiyar hanya ce kawai, na so leko ki jiya ai, ni ma na gaji ki yi hakuri"
"Amma gajiyar ai ba ta hanaka hawa gado ba" na kuma yin maganar a zuciyata
Amma a fili na ce "Ba komai."
"Zan je wurin aiki"
"Allah ya kiyaye hanya"
"Amin" ya fada a lokacin da yake kokarin tashi.
Sai da ya sumbaceni a wuya da hannuna sannan ya ja min kofar ya fice.
Na sauke ajiyar zuciya mai sauti
Allah ya sani ina son mijina, ina kuma son kasancewa da shi a ko wane lokaci
Amma kuma ba damar hakan, ya zama ma kamar ƴarmin ake yi.
Wunin ranar dai haka na yi shi da zazzabi, komai karfin hali kawai nake yi.
Maman Khalil kam har daki ta zo, ta kawo min tsarabar da aka ce in kawo mata, ni ma na kai mata tawa tsarabar.
Jin tsoron abin da zai faru da dare ne ya sa na kira Abbansu Khalil a kan ya taho min da maganin zazzabi.
Tun da ya shigo nake jiran ya kawo min maganin amma shiru, ga kuma zazzabin ya kara tsananta.
Har karfe goma bai shigo ba, ni kuma na ki kiransa.
Paracetamol na kuma sha na kwanta
Tun da na zo duniya, ban taba jin matsanancin zazzabi irin wanda na ji a daren nan ba , ban taba tunanin za a wayi gari da ni ba.
Kuma a daren ne na fi yin nadamar auran mijin wata, da mijna ne ni kadai, da ko mutuwa zan yi, zan mutu ne a hannunshi, amma wannan kam sai dai da safe su zo su samu gawata.
Jiya ma ko leke bai lekoni ba, bare a yi batun magani.
Hade da sallama ya turo kofar, kamshinsa ya daki hancina sai na ji zan yi amai.
"Morning Dear!" Ya fada a lokacin da yake matsa kafafuna.
Bakina cike yake da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji, hakan ya sa na yunkura, na mike zuwa toilet din bedroom nawa ba tare da na yi magana ba.
Bi na ya yi kamar bindi, har na zubar da yawun na koma cikin dakin hade da zama gefen gado.
"Har yanzu jikin ne?" ya tambaye ni hade da cire hijabin da ke jikina yana taba jikin
"Subhanallah! Sannu, wannan kam sai dai asibiti, bari in yi wa Maman Khalil magana ta sauke ki."
Na bi bayanshi da kallo bayan ya fita, ni duk haushi yake ba ni, ina gidanmu ya yi ta yi min dadin baki ya auro ni, kamar a duniya babu sauran wanda yake so sai ni.
Amma ga shi tun da na shigo nake ganin bambanci, sannan baya ma nuna shi yana yin wani abu da bai dace ba.
Tare suka shigo da ita, tana sanye cikin doguwar riga ja, da adon fulawa fara, kamar kullum dai ta yi kyau, kamar ba ta da wata matsala.
"Sannu Auntyn Ramla, ya jikin?"
"Da sauki." na amsa mata
"Bari in taimaka mata ta shirya sai mu je asibitin, ka je gurin aikinka ba damuwa " Ta yi maganar hade da kallonsa.
"Ok, to ki kula."
"zan kula, kar ka damu da wannan"
"Allah ya ba ki lafiya, sorry" ya yi maganar tare da kallona cikin yanayin tausayawa.
Ita ce ta taimaka min na shirya, sannan muka fita.
Duk wani zirga-zirga a asibitin ita ce ta yi, har sai da ya rage ganin doctor kawai zan yi, sannan ta wuce gurin aikin ta, bayan ta ba ni 10k a hannuna.
Bayan gwaje-gwaje dai an gano ina dauke da ciki wata biyu, sai kuma malaria.
Ban baro asibitin ba sai karfe biyu, kasancewar dama bamu je da wuri ba.
Ganin motarta a harabar gidan ne ya tabbatar min da ta dawo.
Yarinyar da har yanzu ban san wacece ba, ita ce ta bude min kofar bayan na kwankwasa. Kasancewar maigadin baya nan.
Matar J
[12/16, 20:28] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 8*
Ina shiga Ramla na fara dauka da ke koyon tafiya a falon.
"Kin dawo? Na kira layinki ba a daga ba,." Cewar Maman Khalil a lokacin da take fitowa daga kitchen
"A gida na manta ta." na ba ta amsa ina kokarin zama
"Aiko kin tashi hankalin Abbansu Khalil, har asibitin ya je, aka ce kuma kin taho"
Shiru na yi komai ban ce ba, saboda ni haushinshi nake ji. Asibitin ma bai iya kai ni sai matarshi. Idan da ace daya daga cikin yaranshi ne ba lafiya, shi zai kai su.
"To ya jikin?" ta katse min tunanina
"Akwai sauki sosai, malaria ce." na amsa ta
"To Allah ya sawake." ta yi maganar hankalinta a ka wayarta da bakuwar yarinyar can ke mika mata.
"Eh, ta dawo, ta manta wayarta a gidana ne." ta dan yi shiru, Sai kuma na ji ta ce
"Malaria ce aka ce"
"OK" ta kuma fada, hade da yanke kiran ta ce min
"Ya ce ki dauki wayarki zai kira ki"
Yanzu ma ban bi ta kan maganar tata ba na ce
"Akwai ɗan abun tabawa kuwa?" saboda sosai wata irin yunwa nake ji
"Ba za a rasa ba, bari a yo miki kala"
Zobo ta kawo min da dambun nama ya ji kayan hadi sosai.
Muna taba yar hira ina ci da zobon har na cinye, na kora maganina, sai na dakko filon kujera na aje a kasa na kwanta, ba da dadewa kuwa bacci ya dauke ni.
A cikin bacci na ji muryar Abbansu Khalil yana fadin
"Ya jikin nata?"
"Da sauki." Ta ba shi amsa
"Sosai saukin, na kira wayar ba ta daga ba."
"Ai ba ta koma ɗakin ba ma, bacci ya dauke ta" ta amsa shi
"Na manta ban ba ku kudin zuwa asibitin ba."
"Ai na ba ta wasu kudi a wurina, ban sani ba ko sun ishe ta."
"Na gode miki Sakeena, Allah ya saka miki da alkairi kina bin duk wata hanya da zan samu kwanciyar hankali. Da ace du mata za su su yi koyi da irin halinki to da ko wane gida an zauna lafiya. Sannan babu wata mace da za ta tsoraci kishiya."