← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 44

Sashe 43

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dalilin da ya sanya ni ture shi da karfi, na juya ina neman inda ya jefar min da wukar da ya amshe a hannuna. Har zuwa lokacin hawaye ne ke wanke min fuska. Sosai zubar hawayen ke min dadi, ina jin kamar ina zubar da dukkan damuwata ne.

Kara kwantowa ya yi jikina a hankali ya ce "Kin san idan kina fushi na fi bukatar ki, ko ki sauke fushin nan, ko kuma komai ya faru a kitchen din"

Ni dai komai ban ce ba, har zuwa lokacin kuma hawaye na saukar min.

Ganin ya amshe wukar hannuna ya sa na duke a wurin na ci gaba da kuka mai sauti, shi din ma dukawa ya yi hade da rungumoni, ganin da gaske nema yake ya yi abin da yake so din, ya sanya ni yin amfani da karfina, na kwace jikina, kafin kuma ya yunkura har na bude kofar kitchen din na fita da gudu.

Daidai Khalil na fitowa dakinsu sanye cikin uniform, yadda na fito din ne ya sanya shi fadin "Auntynmu lafiya, ko kin kone ne?" a rude yake tambayar

Komai ban ce mishi ba, na haura saman da sauri, shi kuma ya nufi kitchen din.

Matar J ✍🏻
[12/23, 15:02] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 34*

A dakin na tarar da Affan yana shirya Maama, wannan ya sa na wuce toilet. Saman toilet din na zauna ina sharce hawayena, duk yadda na so in tsayar dasu abun ya gagara. Ban san ko minti nawa na kwashe a cikin toilet din ba, kafin na fito. Gefen gado na zauna shiru, ba na ce ga abin da nake tunani ba, amma zuciyata babu dadi.

Ina zaune a wurin Khalil ya shigo ya ce min za su tafi makaranta.

Bayanshi na bi zuwa kasa, duk sun yi break, amma bread da kwai.

Sai da naga tafiyarsu sannan na dawo ciki, inda Bashir ya shirya abincin break din Saratu ya kai mata.

Tea kawai na iya sha, zuciyata Sam babu dadi, Sai da Uwani ta zo ne na dan ji sauki, musamman yadda Bashir bai fita aiki ba, ba karamin kara min damuwa ya yi ba. Na yi ta sake-sake marasa kyau.

Haka muka gama abincin rana Uwani ta kai mata, ta kwaso kaya break ko spoon ba a wanke ba, da aka kai na dare ma, haka aka kwaso na ranar ba a wanke ba.

Ban taba gajiya ba, ko ina so, ko ba na so, haka nake abinci sau uku in ba ta a rana, sannan kafarta ba ta taba ta kawo sashena ba, ni ma kuma ban taba lekawa nata sashen ba. Haka ma yara.

Ranar da muka cika kwana uku, ne na zuba ido in ga Ikon Allah, in ga abin da zai faru.

Misalin karfe takwas na dare, muke zaune da yarana cikin falo, ni dai sanye nake da doguwar rigar robber material, blue Mai yankakken hannu. Affan sanye da boxer da ya ɗan wuce gwiwa, Sai vest yayin da ya goya Haidar a baya, saboda ya hana Khalil ya yi wa Maama homework.

Khalil ma sanye yake da irin kayan jikin Affan, hannunshi rike da hannun Maama da ke tracing a littafin writing din ta. Assidiq kam kwance yake yana kallon cartoon, ni kuma hankalina a kan wayata yake. Kwankwasa kofar da aka yi ne, ya sanya Affan budewa, Bashir da Saratu suka bayyana.

Lokacin da kwayar idanuna suka shiga cikin tata, Sai da gabana ya yi wata mummunar faduwa, na lumshe idanuna tare da furta "Innalillahi Wa'inna IlaihirRaji'un, La'ila Ha Illah Anta Subhanaka Inni Kuntu minazzalumin" idanun na bude hade da amsa sallamarsu. Shi da ita a kan 2 sitter suka zauna. Ina kallon yadda take bin ko wacce kusurwa ta dakina da kallo.

Affan da ya hade fuska kamar bai taba dariya ba ya kalli Bashir, da kyar ya ce "Good Afternoon Dad?"

Ba na jin ya jira amsawarshi ya yi hanyar upstairs. Khalil MA Sai ya bi bayan shi, bayan ya gaishe shi.

Falon dai ya koma daga ni sai su. A hankali na kalli Bashir na ce "Ina wuni?"

Ya amsa min, lokaci daya kuma yana zungurin Saratu alamun ta gaishe ni. Ni dai na ɗaukarwa kaina, idan har ba ta gaishe ni ba, ni kuma ba zan gaishe ta ba.

Bayan ta gama shan kamshinta ta ce min "Ina wuni?"

Ni ma sai da na sha nawa kamshin kafin na ce "Lafiya" Daga nan komai ban kara cewa ba. Na Ci gaba da danna wayata.

Shi ne ya ce "Mun zo yi miki godiya ne bisa dawainiya damu na kwanaki uku, Allah Ya saka miki da alkairi"

Sai da na dan murmusa kafin na ce "Amin"

"Sai abu na gaba, yau Saratu ta fita daga kwanakinta na aiki, kenan zama zai koma normal yadda kuka tsara. Shi ya sa nake son in ji ya kuke son abun ya kasance?"

Duk mu ka yi shiru, jin shirun ta yi yawa ne ya sa na ce "Ni ba ni da matsala, duk yadda aka tsara hakan ya yi"

Ya juya kan Saratu ya ce "To ke kin ji, ya kike ganin abun zai kasance?"

Sai da ta tura baki kafin ta ce "Ni dai kowa ya yi girkinshi, ba zan iya girkin mutane har bakwai ba"

Ban san lokacin da na dago kai ina kallon ta cike da mamaki ba, a zuciyata na ce "Farawa da iyawa"

Da alama maganar ta zo wa Bashir a bazata, don shiru ya yi, kamar ba zai kara magana ba, Sai kuma ya ce "To ya za a yi kenan, za ki rika girkin a kitchen din part dinki ne?"

"Ga kitchen a waje na kowa da kowa. Duk mai girki ita ke da iko da kitchen, Sai ta gama abin da take yi, wacce ba ta da girki ta shigo"

Ni dai baki bude nake sauraron wannan Ikon Allah, wannan yarinyar ya aka yi duk ta san wannan, anya kuwa ba wani ne yake ɗorata a hanya ba.

Tun kafin Bashir ya ce wani abu na yi saurin fadin "Ma Sha Allah, hakan ma ya yi"

Ni nan bangaren ba ni da matsala, ko cewa ta yi wanda ba shi da girki ba zai shiga kitchen ba. Kitchen dina na ciki babu kayan aikin da babu, komai ina da shi. To me ye damuwata.

Shiru ya ratsa falon, ganin kamar babu mai abun fada, kawai na mike zuwa sama ina fadin "Mu kwan lafiya"

Bayan na zauna saman gado ne na ce "Affan me ya sa ba kwa gaishe da Auntynku?"

Baki bude alamun mamaki Khalil ya ce "Wacece Auntyn tamu? Don Allah Auntynmu ki bari, ni ba ruwana da ita."

Affan ma ya yi caraf ya ce "Ni ma babu ruwana da ita. Ko za ta shekara dubu a gidan nan ba zan yi mata magana ba"

A hankali na sauke numfashi kafin na ce "Babu ruwana, don Allah kar ku daura min jakar tsaba ku hada ni da kaji. Babanku zai yi fada. Kuma mutane za su ga kamar ni na sanya kuke mata rashin kunya"

"Rashin kunya kuma! Mu da ba mu yi mata magana wace rashin kunya kuma" cewar Khalil idanunshi a kaina.
Shigowar Abbansu ya sanya ban ba Khalil amsa ba.

Bayan duk sun fita dakin ne ya ce "Khadija yaran nan kamar suna fushi da ni, musamman Affan, idan ya ganni sai ya hade fuska, ko ba ki lura ba"

Kai na girgiza alamar a'a kafin na dora da "Kana man ce Affan ne, amma ai shi haka yake, wani lokaci ka gan shi kamar mai jinnu"

"To Khalil fa?" ya kuma tambaya

"Khalil kuma yallaboi, na ga ko dazu kun gaisa ai, kuma ranar can da safe ma tare kuka hada break fast"

Shiru ya yi kafin ya ce "Just you're barking them Khadija, don Allah kada ki yi involving yaran nan a cikin zamantakewarmu"

Kamar ba zan tanka ba, Sai kuma na ce "In Sha Allah"

Aje duk wani kishi na yi a gefe, na karbi mijina sosai, shi kanshi na san ya yi mamakin yadda ba tarbe shi. Da safe tare muka shiga kitchen kuka hada breakfast. Ita kam Amarya ba ta leko ba, kuma na daukar wa raina, na gama kai mata abinci, ba dai ta ce ba za ta iya dafa mana abinci ba, muma ba za mu iya dafa mata ba.

Idon Bashir na faka, na turawa mai adaidaitan da ke kai su Khalil makaranta sakon ba sai ya zo da safe ba, Babansu zai kai su.

Yaran na break na ce "Abbanmu yau fa kai za ka kai su Affan school, mai kekensu ba zai samu zuwa ba, mashin din ya lalace"

"Subhnallah! Sai su matsa kar su makara"

Jin haka ya sa na haye sama, na canja kaya zuwa doguwar riga mara nauyi sosai, na nade kaina da veil din, Haidar ma na canja mishi kaya haka Assidiq.

Time da na sakko har sun gama break din, shi ne ya kalle ni kafin ya ce "Ina za ki je" kai na langabe kafin na ce "Ni ma zan raka su ne"

Kallona kawai yake yi, wannan ya sa na mayar da kallo na kan yaran na ce "Ko ba ku so in raka ku"

"Muna so wlh" suka hada baki a tare.

Baki Bashir ya tabe kafin ya ce "in ya so ma ki zauna a can har sai an tashi kin dawo" ya yi maganar hade da daukar key din motarshi da ke kan center table

Muka rufa mishi baya muna dariya.

Burina kawai shi ne Sarai ta son ina da kusanci da mijina, kuma zuwan ta bai hana mu farin ciki ba. Na dauri ɗamarar zama kamar Sakeena, wajen danne damuwata da boye bacin raina a gaban makiyaya.

Time da muka dawo daga kai yara makaranta Uwani ta zo. Har ta share tsakar gida ta ba fulawoyi ruwa.

Cikin girmamawa ta gaishe mu, kafin ta juya wurin aikinta, ni kuma sai da na salami Bashir zuwa wurin aiki kafin na zauna break. Kuma sai a lokacin ne ya leka dakin Saratu. Sai na ji ni kamar wata Sakeena yau, ni ma na rike miji da hidimomina, ashe haka abun yake ban sani ba. Sai kawai na ji ni ina murmushi.
Chapter 43 · 0% Book details