Sashe 12
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mtswww!" na ja dogon tsoki, a bayyane na shiga fadin "Gaskiya ba zan yarda ace ba ni da sirri ba, ace komai nawa kishiya ta sani bayan ni bai fada min komai nata.
Allah ya kaimu ya dawo, wannan karon ma zan magantu."
Dalilin da ya hana ni zuwa sashenta, Sai ma na mike zuwa kitchen, yayin da na aje ledar tarkacen a kan dining.
Aiki nake yi, sai dai raina Sam babu dadi, na kosa ya dawo kamar in sanya igiya in janyo shi.
Misalin 6pm kuwa ya dawo, 6:30pm ya shigo bangarena cikin shirin masallaci.
Time din hakimce nake a kan kujera ina taba wayata. Da kyar na amsa sallamar da ya yi
"Me ya faru na ga kamar ranki bace?"
Ya yi tambayar idanunshi a kaina.
"in yi magana ka ce bana son zaman lafiya." na amsa shi cikin tabe baki
"Ki yi ina sauraronki."
"Me ya sa don Allah ba ka son rufe sirrina?"
"Sirrinki kuma, me kike nufi?" ya yi maganar hade da tattara duk hankalinsa a kaina.
Yunkurawa na yi hade da mikewa zaune na ce
"Ni ba ina son tsara ma yadda za ka zauna damu ba ne, amma yana da kyau ka rika boye sirrinkanmu, me ya sa za ka fadawa matarka ina ciki?"
"Ni din?" sosai fuskarsa ta canja a lokacin da yake maganar zuwa nuna alamar damuwa
"To idan ba kai ba, wa? Ni dai ban taba fada ma wani ina da ciki ba, idan ba ta san ina da ciki ba, me ya sa za ta kawo min wannan?" na karashe maganar hade da dakko mishi ledar da ke kan dinning ina bude mishi.
Kallon abin da ke cikin ledar yake kafin ya ce "Yanzu kawai don ta kawo miki wannan shi kenan sai ki yi zargin ni na fada mata kina da ciki? To wai ma me ye don Sakeena ta san kina da ciki? Mayya ce ita da za ta lasheki, kafin ki yi ciki ba ita ta fara ba. Wai me ya sa kullum kike son tayar min da hankali ne Khadija?"
Rai bace ya karasa maganar, haka yanayinsa ma ya canja.
Ni kaina sai na ji jikina ya mutu,, na kuma yi nadamar maganar da na yi.
Kafin in yi wani yinkuri tuni wayar da yake kokarin kira ta shiga
Hands-free ya sanya lokacin da ya fara magana
" Sakeena!"
"Na'am" na ji ta amsa da alamar tsoro. Kila ba ya kiran sunanta kai tsaye haka, Sai da babban dalili
"Kina ina?"
"ina daki" ta kuma ba shi amsa da yanayin mutuwar jiki a tare da ita
"Zo bangaren Khadija ina son ganinki."
Bai bari ta bayar da amsa ba ya kashe wayar.
Yayin da ni kuma na yi tsuru-tsuru hade da fargabar abin da zai faru.
Ko minti daya ba ta hada ba, ta shigo falon nawa.
"Ke ce kika ba Khadija wannan?" tambayar da ya fara jefa mata kenan bayan ta shigo, lokaci daya kuma yana nuna mata abun da ke cikin ledar da ya karbe a hannuna.
"Eh ni ce" a tsorace ta ba shi amsa, saboda ganin yanayinsa.
"A ina kika samu?"
"Malama Maryam kawata ce da ta yi tafiya, shi ne da muka biya dazu wajen ta, ta ba yara. , sai na dan debar mata na ga abun marmari ne" Har yanzu a tsorace take maganar
"Shi kenan."Ya fada hade da ajiye ledar ya fice ya bar mu a tsaye kowa jiki a sanyaye.
Ni dai a bangarena yadda lamarin ya tsaya haka ba karamin dadi ya yi min ba. Yanzu rigimar tsakanin ni da shi ne. Kai barka bante.
"Me ya faru?" ta katse min tunanin da nake yi
"Ba komai, ya dauka na fita ne wai bayan kun fita"
"Au ho!" ta ba ni amsa hade da ficewa.
Fitar ta ke da wuya na shiga bubbuga kafafuna, cikin rashin sanin abun yi.
"Wallahi idan akwai abin da ya kamata a budewa mata aji a kansa shi ne yadda za su zauna da kishiya. Gabadaya na damalmale komai, na zama sakarya wawiya, ina son cusa kiyayyata a zuciyar mijina da kaina."
Hannu na kai na share hawayen da ke bin fuskata.
Ni sam ban san haka zama da kishiya yake ba. Ashe dole sai ka iya takunka, idan ba haka ba, Sai a samu matsala.
Lallai wannan kalubale ne ga yan'mata masu shirin auran mai mata, kuma suke tunanin cewa, ta gida ta kasa ne, ko an gama yayinta shi ya sa ake son kawo ki, wannan babban kuskure ne muke yi, sai mun shigo kuma zamu gane hakan.
Kamar ni yanzu uwargidana ai babu abin da zan nuna mata, kyau, ilmi, hankali, tsafta, girki, kula da miji duk ta iya.
Akwai wadanda kuma suke da nakasu, amma kuma dole dai ke amarya ki bi su, kafin ke ma ki zama yar gida.
Kamar yadda uwargida ke fuskantar kalubale idan aka mata amarya haka ita ma amaryar ke fuskanta muddin tana da uwargida.
Ni dai yanzu ganau ce ba jiyau ba. Na bata darena na gobe kuma
Don ya yi fushi irin wanda ban taba gani ba.
Matar J✍🏻
[12/17, 06:26] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 11*
Daga sallar magriba zuwa isha'i haka nan na yi su, ba don ina cikin nutsuwa ta ba, tun da na zo gidan, ban taba yin abin da na yi danasani ba irin wannan. Wata zuciyar fada min take yi in gudu gida kawai.
Dama ban yi tunanin zai shigo yi min sai da safe ba, Sai ko ga shi bai shigo din ba. Abin da ya kara dama min lissafi, duk soyayyata da bacci, yau dakyar na samu ya dauke ni, shi ya sa na tashi duk ba na jin dadin jikina. Hatta bakina testless ya zama
Yanzu abokin shawara nake nema, amma na rasa da wa zan yi ta, Ummana ba na son daga mata hankali, bai kamata ace mu biyu da ta aurar kullum cikin kawo mata Matsaloli muke ba.
Ga shi ba ni da wata yar'uwa ko kawa a Abuja bare in fada mata damuwata, don kuwa wannan matsalar ba ta waya ba ce.
Saboda gabadaya duk wata basira tawa ta kare, a duk lokacin da na yi kokarin daidaita abu, sai ya kuma lalacewa.
Haka na wuni zur ina sake-sake, har zuwa dare, lokacin da nake tsammanin shigowar shi, Sai ko ga shi ya shigo din, amma yanayin da ke kan fuskarshi, bai ba ni damar yin magana ba , dole na janye jikina, kila zai fi bukatar hakan.
Haka mu ka yi wadannan kwanakin, gaisuwa ce kawai ke hada mu, ya duba abin da babu a kitchen ya kawo, a haka ya koma dakinta, yayin da ya bar ni da kuka mai cin zuciya.
kwanana ya kuma zagayowa. Wannan karon kam, na daura aniyar sasantawa, ba zan yi kasa a gwiwa wajen ganin na yanke wannan fushin na shi ba.
Abincin da ya fi so na yi, wato tuwo da miyar kuka. A aljihuna na cire kudi aka sawo min kaza na kawata miyar da ita.
Bayan na gama, na fita cikin dogon farin wandona jeans na mata da bakar riga mai guntun hannu, gaban rigar a bude haka ta zauna jikina hade da fitar mini da surar jikina. Dama ga matashin ciki ko ina ya kara cika tubarakhallah
Turare mai sanyin kamshin na sanya, bayan na manna kananan yankunne a kunnena.
Sosai na yi kyau musamman dana tsaya gaban mirror, cikina dan wata hudu kamar ba shi a jikina saboda yadda cikin yake a shafe.
Takwas daidai kuwa ya shigo, abin da ya sanyani farin ciki, duk da babu wata walwala a kan fuskarshi
"Sannu da zuwa." na fada a daidai lokacin da yake zama a kan kujera.
Bai amsa ba, dalilin da ya kara tabbatar min da har zuwa lokacin dai fushi yake yi sosai.
Dukawa na yi a gaban sa hade da dora kaina a kan cinyarsa, na ci gaba da rera masa kuka, saboda ban da komai yanzu sai kukan.
Tsawon lokaci yana ji na, bai yi magana ba, ni kuma ban daina kukan ba.
Kila gajiya ya yi, kaina ya dago tare da fadin "Shi kenan ya isa" fadin maganar ta shi daidai da mikewarsa ya shige bedroom.
Ban yi kasa a gwiwa ba, na bi bayansa ina share ragowar hawayena
"Idan kin san kuka za ki yi min, please get outside" ya yi saurin fada ganin na nufi inda yake kishingide
Dakatawa na yi, hade da yin kalar tausayi, ni ban karaso ba, kuma ban koma baya ba.
Kamar 2mns muna a haka.
Kafin ya daga hannunsa hade da yafito ni "Zo nan."
Na kuma langabewa sosai na karasa gurinsa.
Jikinshi ya janyo ni, hade da kwantar da ni sosai, ina jin yadda kirjinshi ke bugawa da sauri
"Khadija ki dawo cikin hankalinki, don Allah kar ki ɓata mana zama. " A sanyaye ya yi maganar bayan ya kwantar da ni akan kirjinsa yana shafa bayana.
Ban yi magana ba, illa dai na dago hade share hawayen tausayin kaina, daga bisani kuma na koma na kwanta.
"Kina kokwanto ne a kan son da nake yi miki?"
Girgiza kai na yi alamar a'a
"To me ya sa kullum kike tuhumata a kan na fifita wata a kanki?"
"Ka yi hakuri don Allah, sha Allah ba zan kara ba."
"Hmmmm!" kawai ya ce kafin shiru ya ratsa tsakaninmu.
"Ya kamata in sanar da ke wacece Sakeena a wajena, kuma ki san wacece ita."
Ya yi maganar hade da janyeni daga jikinsa, wanda hakan ya nuna mun yana bukatar natsuwata.
Ni kaina ma ina son sanin wacece ita, kuma tun farko ma abun da ya kamata kenan in sani ta yadda zan san ya zan zauna da ita.
Dalilin da ya sa kenan na tattara hankalina ni ma kaf a kansa ina sauraronsa.
"Duk wani namijin da ya samu Sakeena a matsayin mata, to sai dai ya kara aure a matsayin sunnah, ba wai don gazawarta ba."
Ya yi maganar idonsa a cikin nawa.