← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 44

Sashe 17

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Yanzu dai ki kiyaye duk wani abu da zai janyo ki fada ta fada, wannan shi ke zubar da mutunci yarinya ta rika ganin ita din sa'arki ce, kar ki sake ki kai kararta wajen mijinki, duk lokacin da za ki yi maganarta ya zama alkairinta za ki fada. Wannan zai sanya ki kara girma a idonsa."

Har yanzu Sakeena ba ta ce komai ba da alama sauraron nasihar kawar tata take yi.

" Please calm down kawata haba mana."

A wannan karon ziro kaina na yi cikin dabara hade da leka falon, Rahma ce ta sakko daga kan kujerar da take zaune tare da dafa kafadun Maman Khalil cikin sigar lallashi.

A yayin da Maman Khalil din ke tsiyayar da hawaye hade da ajiyar zuciya.

" Kawata ban samu na zubar da hawayen nan inda za a lalllashe ni ba, bar ni in zubar dasu a gabanki, ke ce za ki lallasheni, ba kuma za ki goranta min ba watarana ba, kirjina yana zafi, wani lokaci ina jin kamar zan mutu idan na ga Baban Khalil na ta rawar jiki zai shiga dakin Khadija. Ko ganinta ne bai yi ba, to ya yi ta tambaya kenan, ko kuma ki ga hankalinsa duk ba ya tare da shi. Ranar ma ce mun ya yi wai zai ba ta motarsa shi kuma ya sayi wata. Ki ji fa ni ciko ne ma zai yi min amma da kyar na samu, shi ma ba duka ba, amma wai zai ba ta motarsa."

Ta karashe zancen hade da gyara zama kafin ta dora

" Banza na yi mishi a lokacin, sai kuma ya fara kame-kame wai ta yi mata girma, zai dai duba kila ya siyar ya siya mata karama. Ni dai ban ce masa kala ba. Tun zama na da shi bai taba jaraba sai mun mota ba, sai a kan wata da ko shekara ma bai yi da ita ba."

Ta karasa maganar cikin kukan da ya ci karfin ta hade da narkar da zuciyar mai sauraro.

Ni ma sai na kuma matse bakin Ramla tare da dagata cak mu ka yi waje jikina a mace, saboda da kyar nake jan kafata,

Matar J ✍🏻
[12/22, 14:30] 08080966571: *HASASHENA*

*Page 15*

Jiki a mace na zauna kan kujera hade da sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Shiru na yi na rasa ta ina zan fara tunani, wato ni ina zargin ya fi sonta, ita tana zargin ya fi sona, duk inda kishiyoyi suka hadu to dayan-biyun, kodai wannan ta ji ba ya sonta ya fi son wannan, ko kuma ko waccan ta ji an fi sonta.

Ban taba tunanin Maman Khalil tana da damuwa irin haka a kaina ba, wato da hakuri ta fi ni, da kuma iya tako. Ita shirunta shi ne maganarta. Kuma da alama yana gane yaren nata, saboda ko a mafarki bai taba min zancen mota ba, kuma na kara gasgata shirunta shi ne hukuncinta, idan har zai ga ta cika shirun to ya yi ta sintiri kenan zuwa dakinta.

Kai namiji sawun keke ba a gane gabanshi.

Ni kuma ba na iya shiru ko boye fushina, kuma ya zama dole in koyi wancan dabi'ar tata, ta danne abu ta yadda ba kowa ne zai fahimci kana da matsala ba

Ni ma dole in koyi yin shiru da bakina idan ya yi abun da nake ganin rashin adalci ne, saboda dama yawan yin maganar tawa yana rage kimata a idonsa.

Kuma da gaske Rahma take yi, yawan kai korafi ko yawan kawo kara yana sa ka sirewa mutum, tun yana kamawa watarana sai ya daina kamawa.

Ko ni ya faru da ni, kai tsaye Baban Khalil ya ce ya yi danasanin aurena, wai kullum matarsa tana yabon halina ba ta taba kawo karata ba, amma ni kullum cikin kawo kararta nake, ashe duk salon kissa ne ke hanata yin maganata ko kai karar tawa. Ni ma na karu da wannan.

Muskutawa na yi har yanzu jikina a mace yake, cikin tsananin tunani mai zurfi

Yanzu dai na fahimci inda nake da rauni, zan kuma gyara.

Sannan ni ma dangin mijin ne kawai suka rage min in kama, tun da dai Maman Khalil da kanta ta yadda mijina yana sona, to na daina tayar da hankalina a kan wannan, dama damuwata ko a banzace take kallona, duk da haka zan kara nemo hanyoyin da zan kara rike abuna, ni ma sha Allah sai na zama kamar ita, har ma fiye.

A kasalance na nufi kofar saboda kwankwasawar da ake yi.

Rahma ce tsaye tare da Maman Khalil

Sabanin Maman Khalil, ita fara ce tas, Sai dai ita ma yar gayu ce kamar Maman Khalil, wani kamshi mai dadi na fita daga jikinta

"Na zo ganin yarki ne. Tun da kin ki kawo ta" Rahma ta fada cikin dariyar tsokana

Ni ma murmushi na kakalo, ina ja gefe, "shiga, ga ta nan, ki ganta, ki bar ta a nan, idan gani ne kawai ba ma fada."

Dukkanmu mu ka yi dariya a lokacin da muke zama ni da Maman Khalil, Rahma kuwa Ramla ta nufa da ke ta wasanta a wurin dining

"Ma sha Allah! Kawata Ramla ta fi kyau a zahiri, ban da Amarya ta riga ni tabbas da na karbe Ramla na jefata a cikin yan mazan gidana, amma duk da haka ina yi wa Farhan dina riko gaskiya."

Ta fada a daidai lokacin da take zama hannunta rike da na Ramla.

Mu kam dariya kawai muke yi.

" Kunshin nan ya yi kyau fa, nawa za mu biya gara mu fara toshi."

"Ga me yi mata nan, ni tun da na haifeta ban taba mata kunshi ba, to ban iya ba, ita kuma kullum cikin yi suke, da ya fita su kuma mayarwa." cewar Maman Khalil tana kallon Rahma

Ni kam murmushi kawai nake yi.

"Ma sha Allah! Ai kunshi yana da kyau sosai a wajen mace, to ni ma fa nan bana yi, sai in yi shekara biyar ban yi ba."

Duk muka dan yi siririyar dariya.

Ta kai hannunta hade da shafa kitson kan Ramla, Chuku ne na zanen hausa, ya kamu sosai kan kamar an sudeshi.

" Har kitson ma ke ce ke yi?"

Jijjiga kai na yi ina murmushi

Rike da haba cikin mamaki ta ce" Ke komai kin iya wai?"

Wannan karon dariya na yi sosai kafin in ce" Ba fa komai ba. "

" To me ye ba ki iya ba? Cewar Maman Khalil tana kallona, kafin in yi magana kuma sai ta dora

"Kin iya komai, kamar ba a zamanin kiwa kika zo ba, yaran yanzu bayan rashin kunya babu abun da suka iya, sai kadan ne irinku"

Wannan karon ma murmushi kawai na yi

Ji nake kamar bugun cikina suke yi, ko kuma dai kishinta ne yau ya ci karfinta.

Karar motar Baban Khalil ce ta sanyasu saurin ta shi gabadayansu, Maman Khalil na fadin "Mijinki ya dawo, ga tsarabarku nan ke da yarki, daga Maman Farhan"

Ni ma mikewar na yi, hade da karbar ledar na dan leka ciki, tare da yi mata godiyar da na san tabbas ta gamsu na yaba da kyautarta.

Gefe ya rabe suka fita, saboda bude kofarsa ya yi daidai da niyyar bude kofarsu su ma.

Daga ganin gaisuwar da suke da Rahma ka san an dade tare, akwai kyakkyawar alaka, don kuwa Maman Khalil nan ta barsu tsaye a barandata, ni ma sai na karbi jakar hannunsa, na shige ciki, yayin da na bar su a nan hannunsa rike da Ramla.
Ina raka'ar karshe a magriba ya shigo cikin sauri ya yi alwala zuwa masallaci, saboda har an idar da sallahr bai yi ba suna magana da Rahma.

Bayan na idar da sallahr isha'i na jera mishi abinci a kasa, kamar yadda ya fi so.

Wanka na shiga, bayan na fito na watsawa Ramla ita ma hade da sanya mata rising powder.

Pant kawai na sanya mata, yayin da ni kuma na sanya doguwar riga mai yankakken hannu, ba ta da nauyi ta dace da yanayina da kuma yanayin garin, humrah kawai na shafa a jikina.

Falo na fito na yi zaman da na fi so, wato in hada bayana da kujera hade da ware kafafuwana, iskar fanka na ratsa ni, a yanzu na fi kaunar irin wannan zaman fiye da ko wane kalar zama.

Ramla kwance a kan cinyata ina shafa kanta don ta yi barci a lokacin da ya shigo dakin.

"Sannu uwar hudu. Wai don Allah duk iskar fankar nan ta miki kadan sai kin hada da mahuci?"
Cikin yanayin mamaki ya yi tambayar.

Dariya na yi kafin in yi masa hararar wasa "Wai saboda tsaro, ka ga ko an dauke wuta ba zan sha wahalar tashi zuwa neman mahuci ba ga shi a kusa da ni."

"Anya masu scanning din nan kuwa suna gani me kyau? Gaskiya cikin nan naki ba yaro daya ba ne."

Dariya na kuma yi hade da shafa cikin "To ai dai scanning din nan ba sau daya mu ka yi ba. Kuma dai duk abu daya yake bayarwa."

"To gaskiya kina da girman ciki, sai ka ce za ki haihu yanzu, ko Maman Khalil ma mamakin girman cikinki take yi. A tarihi dai ke ce mace ta farko da cikin farinta ya yi girma kamar daro"

Mahucin kusa da ni na dauka tare da kai masa jifa.

Ya yi saurin kaucewa yana dariya

"Abun da za ka fada kenan ko?" Na karashe maganar ina harararsa.
Kafin ya yi magana na dora

"Kuma fa ina jin nauyinsa sosai, kai ne ma ka ki barina in je gida ka ga dana huta da wasu hidimomin, tun da na yi aure ma fa zuwana daya, su kuma sun ki su zo mun." Cikin yanayin shagwaba na yi maganar.

"Da wannan cikin za ki gidan, kuma duka watanki nawa da auran? Sau nawa kike so ki je gidan a shekara?"

"Ni ban ki ba ma kullum in je"

Dariya ya yi sosai, kafin ya ce "Ina jin yunwa ina son yin wanka wanne zan fara ne?"

"Ka ci abincin sai ka yi wankan idan ka dan huta"

"An gama" ya fada hade da cire rigarsa

"Yaushe rabon da ki cire min kaya ma wai?"
Chapter 17 · 0% Book details