← Book details Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ya danganta, amma mu nan kin ga kauye ne, babu wata matsala idan matar saurayi ko bazawari ta haihu ka je barka da ɗan ihsani, duk gyaran hanya ne. Haka zuwa gaishe da suruka ka yi mata ihsani duk gyaran hanya ne."

Baki na rike cike da mamaki kafin na ce" To ni dai gaskiya ba na bukata, idan za ta je can cikin gida ban damu ba, amma ni ban da wurina"

"Kin ga, ki rufawa kanki asiri ki zuba musu ido, idan kika bari aka fara kasa ki a wannan familyn to za ki ji jiki. Tun da suna yin ki, to kar ki yi abin da zai ɓata ki kuma"

Rike da haɓa alamun mamaki na ce "Menene abin da zai bata ni din, kawai don ba na son bazawarar mijina na zuwa gidana?"

"Ba Za ki gane ba Maman Maama. Amma ki gwada sai dai tsakaninki da mijinki kar ki bari maganar ta je kunnen Saro din. Kuma wlh ki yi hankali da ita, ba ki san wacece Saro ba"

"Wacece ita?" na yi saurin tambaya

"Babu ruwana, idan zama ya hada kin san wacece"

Tsoki na ja, kafin na ce "Ina za ki je?"

"Gidan suna, wata kawata ce ta haihu. Ko za ki je?"

"Da yake ni ce gayyatar ni mijina bai fada"

Dariya ta yi hade da mikewa ta nufi kofar fita, tana fadin "Assidiq na can na ta yi wa Inna rigima, yau aikinshi take yi"

Dariya na yi kafin na ce "Ai rigimarshi da sauki, idan kika hada da rigimar Maama tana kamar shi. Kai Maama ta ba ni wahala, har wata rama na yi"

Duk muka yi dariya a tare, har gate na yi mata rakiya sannan na dawo, a zuciyata ina tunanin wane irin hali Sarai ke da shi da Murja ta ce in bi ta a hankali.

"Da gudun bala'i zan bi ta" na fada a bayyane ina cusgune fuska.

Miji ya tafi for some days ya dawo to an fi marmarin juna, kwanaki ukun da Abban Khalil ya yi kamar kar su wuce, wata irin soyayya muke yi mai tsayawa a zuciya.

Ranar Monday da safe ya tafi tare da su Khalil ya sauke su, shi kuma ya wuce.

A hankali nake shirye-shiryen tafiya ta, duk wasu ƴan kudi da nake adanawa na rika fito dasu ina sayen tsaraba.

Ba karamin dadi na ji ba, lokacin da su Khalil suka fara jarabawa, ji nake kamar in janyo kwanakin su yi su gama.

Ranar Asabar suka yi prize and giving day, lokacin da Rahma ke fada min za ta zo, na dauka da wasa take, amma sai ga ta ranar Juma'a har da gifts nata.

Taron ya yi kyau hade da kayatarwa, ina jin su Khalil sun fi kowa tara dangi a wajen taron nan, dangin mamanshi sun je, ga kuma dangin Babanshi, mu da su da kuma yaranmu mun tasar ma ashirin. Shi ya sa gamu nan zuga guda.

Bamu dawo gida ba sai yamma, Rahma gidansu Maman Khalil ta wuce, mu kuma mu ka yo gida, yau kam hirar kaf a kan graduation ne. Ni kuma a zuciyata jiran umarni tafiya nake yi, saboda na kosa sosai in tafi.

Safiyar Lahadi Rahma ta wuce Abuja.

Kullum jira nake yi, in ji Bashir ya yi min maganar tafiya amma shiru, har sati da yin hutunsu Khalil. Wannan ya sa na ji akwai bukatar in tunasar da shi, tun da ya zo, weekend kafin ya koma.

Safiyar Asabar muna zaune muna hira na ce "Alhajina, ka yi min shiru!"

Cikin rashin fahimta ya ce "Da me?"

Marairaicewa na yi kafin na ce "Ka ce idan aka yi hutu zan je Kano"

Kanshi ya dauke gefe kafin ya ce "To da yaran za ki tafi ko? Amma ya za a yi ki tafi ko bar su suna ta gararanba a gari"

"Da yara kuma?" na tambaya cike da mamaki

"Eh mana, ni ba ni nan, ke ba ki nan, a ina za su zauna"

Baki bude nake kallon shi kafin na ce "Yanzu don Allah Abban Khalil a cikin yaran nan wanne za a yi wa wanka, kamar wasu masu shan nono, to ko Maama ce na ce ba zan je da ita ba, ai ba abun damuwa ba ne, bare Affan da Khalil"

"Ni fa ba na son in ga yarana suna bin gidaje" ya yi maganar with his serious

Baki na bude ina kallon shi, saboda ban san me zan ce ba kuma, ina ne gidajen, gidansu Sakeena ko gidansu

"Idan da yaran za ki tafi, shi kenan gobe ma kishirya, amma idan ba da su ba kam to ban amince ba"

"Kenan yanzu ni idan zan yi tafiya dole sai da su?"

"Kwarai, idan ke kika haife su za ki bar su ne?"

Na yi saurin tarbar numfashinshi da "Sosai ma kuwa, kamar dai Affan da Khalil ba zan rika zuwa unguwa da su ba"

"Ashe kam ba za ki je ba" ya yi maganar hade da mikewa ya bar min falon.

Shiru na yi cike da takaici, ina son yaran nan sosai, amma Bashir nema yake ya tura min kiyayyarsu da karfin tsiya, ta ya zan kwashi yara rabe-rabe har hudu tun daga Ruma zuwa Kano, fisabilillahi an kyauta min kenan.

Zuciyata ta rika wani tukukin bakin ciki da bacin rai, Affan ne ya kawo min wayata da take hannunsu suna game ya ce "Auntynmu, Aunty Yusra na kiran ki"

Na lumshe idon bacin rai kafin na daga kiran.

Gaisawa muka fara yi kafin ta ce "Auntynmu ya maganar tafiyar ne, ke fa nake jira"

Cike da jin bacin rai na ce "Yusra ki tafi kawai, ni ba zan je ba"

"Me ya sa?" ta yi saurin tambayata

Kamar zan yi kuka na ce "Wai Abban Khalil sai dai in tafi da duk yaran nan, yanzu fisabilillahi Yusrah yaushe zan kwashi yaran nan daga nan har Kano, su Khalil basu yi girma da zuwa unguwa ba?"

"Don wannan ya sa kika ce kin fasa?" kamar tana kallo na, kai jinjina mata, ita kuma ta dora da "Gaskiya kam babu dadi, tafiya da yaro ma ko daya ne babu dadi bare da yawa. Amma tun da ya ce haka shi kenan, kudin fa tafiyar daga aljihunshi za su fito, mu gaskiya muna son ganin ki, kawai ki taho"

"Da yaran Yusrah?"

"Eh mana, me ye a ciki, ba fa fitsari ko kashi za ki wanke musu ba"

Ajiyar zuciya na sauke, kafin na ce, "shi kenan idan ya shigo zan ce mishi na amince, duk yadda mu ka yi kuma zan sanar miki"

Cike da murna ta ce "Haba ko ke fa"

Da haka mu ka yi sallama, na shiga kokarin warwarewa, na yi ta tausar zuciyata har zuwa lokacin da ya shigo cin abincin rana.

Fuska a sake na gabatar mishi da komai na abincin, yana ci muna taba yar hira. A cikin hirar ne na ce "To yaushe zan tafi?"

"Ina?"
Sosai tambayar ta ba ni haushi amma sai na share na ce "Kanon"

"Da yaran ko?"

"Yadda kake so ai haka za a yi yallaboi, su ma ka ga sun ji dadi sun dan yi balaguro"

Murmushi ya yi kafin ya ce "Ki shirya ranar Monday sai Salisu ya kai ku"
Lumshe idanun dadi na yi, ganin kai mu za a yi, komai ya zo da sauki ma ai, cike da ɗoki na ce "Na gode Yallaboi, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana"

"Amin" ya amsa, kafin ya ce "Me kike so a matsayin tsaraba?"

Na ɗan yi ahiru kafin na ce "To me zan saya, ya wuce lemo da yar ayaba, wannan kuma ko a hanya ai mun saya."

Kai ya jinjina alamar ya fahimta. A zuciyata na ce "Lallai ma wannan mutumin, yanzu don Allah ni ce zan fada mishi abin da zan yi tsaraba, shi bai san abin da ya dace ba."

Ai cikin kwana biyun nan ba zama, shirin tafiya kawai, kitso, lalle, wanki, guga, zuwa Lahadi da yamma na yi package na duk abin da na san zan tafi da shi, kayan su Khalil akwati guda, haka Maama da Assidiq, ni kuma nawa daban.

Irin yadda su Khalil suke murna, Sai na ji gara ma da ya ce a tafi dasu din, yadda suke farin ciki, kamar za mu kaiwa mahaifiyarsu ziyara.

Lokacin da suka dawo masallacin isha'i ne Bashir ya shigo hannayenshi du biyun rike da manyan ledoji, da sauri na tarbe shi, na ajiye a tsakiyar falon, sannan na shirya mishi abinci shi da yaranshi, yana cin abincin ne ya ce "Ki bude wadannan ledojin, ki ga ko akwai abin da babu."

Na shiga bude ledojin, ledar farko dai tarkacen Assidiq ne, pampers, cerelac, custard, da ɗai Sauran tarkacen shi "

Daya ledar kuma kayan tea ne, manyan gongoni
"Wadannan na yaranki ne, kar ki je ku dora musu hidima"

Murmushi na yi kafin na ce "Mun gode"

Daya ledar ma kayan tea ne, sabulai, omo, Manshafawa kala-kala cike fal.

"Wannan na Umma ne" ya kuma fada yana kallo na

Wani murmushin na kuma yi kafin na ce "Umma ta gode sosai, Allah Ya kara budi"

"Amin" ya amsa yana ci gaba da cin abincinshi.

Daya ledar kuma zannuwa ne da yadin shadda, nan ma kafin in ce wani Abu ya ce "Turmi biyu na Umma ne, turmi daya Maryam, daya Yusra, shaddar kuma ta su Usman ce"

"Yallaboi, wannan ai, hidima muka dora maka, da na san haka zai faru ai da ban yi tafiyar nan ba"

"Ina hidimar?"

"Ga ta ka yi, da gaske abun ya yi yawa"

"Bai yi ba Khadija, Umma ta cancanci komai, suruka ce mai kawaici hade da dattako, Allah dai Ya ara mana rai da lafiya"

"Amin, to mun gode Allah Ya kara budi. Ni kam ko mai ɗangyashin kudin nan da ake ma kirari da gaske ne?" cikin zolaya na yi mishi maganar

Ba shi kadai ba, har yaran sai da suka yi dariya, shi ma cikin dariyar ya ce "Da ba ki sani ba, lallai yarinyar nan na ki wasa ne"
Chapter 34 · 0% Book details