Sashe 37
Hasashena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina zaune a wurin Bashir ya yi horn, yaran suka nufi gate a guje suka bude mishi, tun da ya fito daga motar idanunshi suke a kaina, har sai da na harare shi, sannan ya yi murmushi hade da dauke idanun na shi a kaina.
Bayan ya iso inda nake ne, ya yi amfani da hannunshi wajen jan hancina kafin ya ce "Anya daren jiya ban je fa kwallo a raga ba?"
Wata irin faduwa gabana ya yi kafin na ce "Don Allah ka daina irin wannan maganar, duka Assidiq din watanshi nawa"
"bakwai" ya ba ni amsa hade da zama kusa da ni
"Shi ne kuma kake min fatan ciki, don Allah ka bari, ni to asibiti ma zan je a yi min allura"
"Irin soyayyar da na samu jiya Khadija idan ban yi ajiya ba, ai na zama ragon maza, kuma na fada miki ba na son allurar nan ko, ke ce za ki haife min yaran da Sakeena ta tafi ba ta haifa ba, dama ita guda shidda take so, uku mata uku maza, to ga biyu kawai Allah Ya ba ta iko haifa, kin ga Sai ki cika mata burinta, yanzu dai kin gama da maza, saura mata biyu, daga nan sai ki haifi na ki"
Wata irin dariya na yi mai cike da Nishadin maganar ta shi, ba tare da na ce komai ba. Shi ne ya mika min envelope din hannunshi.
Da hannu biyu na karba, hade da zaro takardun ciki, form din wata makaranta ne, wai MERIT ACADEMY.
Bayan na gama karanta instructions din nasu na mika shi ina fadin "Allah Ya sanya alkairi"
"Amin. Na hadu da Fatima (Maman Hana) ta ce an jima za ta bullo ta ga gida."
Cikin jin dadin maganar na ce "Kai amma kam na gode, Allah Ya kawo ta. Ummanmu ma ta ce kila satin sama ta shigo"
"Allah Ya kawo ta lafiya" ya yi maganar hade da mikewa tsaye ya dago ni gabadaya. Na shiga kiciniyar kwacewa, Sai bayan da na dire ne na ce "Ka manta akwai yara a gidan ne?"
"To menene, ba ke ce jiya kike fada min Affan ya ce yana son Maryam ba"
"Don ya ce yana son Maryam kuma shi ne za ka daga ni a gabansu"
Yadda na karasa maganar ne ya sanya shi yin dariya, kafin ya ce "Kina ba ni mamaki, ke fa ko zama kusa da ke ba kya son in yi idan yaran nan suna gida. Kai jama'a" ya yi maganar hade da rike haɓa alamun mamaki.
Ni kuma yadda ya yi din ne ya ban dariya, shi ya sa na shige cikin dakin ina dariya, yayin da shi kuma ya biyo bayana.
Matar J ✍🏻
[12/23, 12:16] 08080966571: *HASASHENA*
*Page 30*
Tare mu ka yi aikin abincin rana da Bashir, don a, harkar kitchen kam Bashir Oga ne, ko mace sai haka, karfe hudu ya fita da yaran, wai zai kai su gidan ƴan'uwansu ta, bangaren shi, da kuma bangaren mamarsu.
Gidan ya yi shiru har hudu da rabi, lokacin da na ji ana buga min kofa na dauka Maman Hana ce, saboda ita kawai nake jira, sosai nake son matar, Sai dai kicibis na yi da Maman Aiman a lokacin da na bude kofar, murmushi ta yi tana fadin "Ina fatan ban katse miki jin dadi ba"
Ni ma murmushin na mayar mata kafin na ce "Ko daya, dama Ina kaɗaici ne"
Duk mu ka yi siririyar dariya, kafin mu ka shiga, kan kujera ta zauna na kawo mata ruwa da fruit sai mineral gora ɗaya na ajiye mata. Muka shiga hira, da alama tana da sakin fuska sosai kuma ba ta da bakunta.
Muna cikin hira na ga kiran Maman Hana, wani dadi na ji, saboda na tabbatar tana kan hanyar zuwa, ilai kuwa ta ce min ga ta a gate. Excusing din Maman Aiman na yi, na je na tafi bude mata kofa
Tun da ta shigo take yaba gidan da tsarin shi, abin da ya yi mini dadi, tarba ta musamman na yi mata har da abinci, kuma na ji dadi sosai yadda ta ci abincin har sama na yi mata jagora, saboda Maman Aiman ta tafi. Sai gab mangariba ta tafi, inda na yi mata alkawarin da zarar na samu chance ni ma zan zo.
Sai da aka yi sallahr isha'i su Bashir suka dawo, na sha labarai kam wajen Khalil da Maama shi Affan miskilanci hana shi magana yake sai idan ya so.
Washegari ma haka na yi ta samun baki, makotana na kusa, da kuma ƴan'uwan Bashir da Sakeena wadanda suke cikin Katsina.
Haka muka cinye wannan satin, satin sama kuma a kan hidimar makaranta ya tafi, Asabar din karshen satin Ummana ta zo ganin gida, ita da wata Goggona, da kuma Auntyna, sosai su ma suka yaba, musamman yadda Bashir ya gyara min daki, ya zuba min kaya masu tsada haka suka yi ta yi mishi godiya. Karfe hudu suka tafi.
Tun da suka tafi nake tattauna maganar da mu ka yi da Ummata a kan sana'a, ni dai zaman haka ba na son shi. Umma ce min ta yi, in yi sana'ar kayan kamshi, misali humra, kwalakca, freshners, morning fresh, Sai Kuma supliment tun da yanzu su ake ya yi, da kuma atamfofi. Amma kudin sun yi kadan, Sai dai zan fara gwada kadan mu ga abin da Allah zai yi.
Da dare bayan mun kintsa komai, muna kwance na ce "Alhajina ina da magana" sai da ya kara jana jikinshi sannan ya ce "Ina jin ki Hajiyata, za a yi min wayau ne?"
Cikin siririyar dariya na ce "A'a"
"To menene?"
Jikinshi na kara shigewa kafin na ce "Ina son gwada yin sana'a ne kafin aikin ya samu"
"Tunani mai kyau, saboda ni dai aikin nan ma ba lallai ki yi shi ba, ina son kawai ki zauna, ki kular min da yarana, har da na nan" ya kai karshen maganar hade da mayar da hannunshi kan marata
Hannun na dauke ina fadin "Don Allah ka daina min fatar ciki yanzu, ni ba ni da komai"
"To zamu gani ai, me kike son sayarwa?"
"kayan kamshi, da kayan yara, Sai kuma atamfofi"
"Lallai ke Hajiya ce, da na san kina da wadannan kudin ai da na daina fita kasuwa da wurin aiki na yi zamana"
Siririyar dariya kawai na yi ba tare da na ce komai ba, shi ne ya ce "ya abun zai kasance to?"
"Da turaren zan fara kafin mu ga abin da Allah zai yi"
"To Allah Ya taimaka"
"Amin" na amsa kafin mu ka rika taba hira a hankali har bacci ya dauke mu.
Sai Monday su Khalil suka fara zuwa makaranta, kasancewar hutu ya kare, Sai bayan sun tafi na shiga kasuwa sawo kayan hadin turare, kasancewar ranar farko ce, ba karamar wahala na ci ba. Shi ya sa na dawo gida a wahale, har da su amai na sha. Abu kamar wasa sai ga shi na kasa dora girkin rana, saboda aman da nake yi duk ya kashe min jiki, zuwa azhur dakyar na yi sallahr.
Dole na kira Bashir na ce ya zo ban lafiya, after 30mns na ji bude gate din Shi.
"Me ya faru?" ita ce tambayar da ya fara jeho min, lokacin da ya shigo falon ya iske ni kwance saman center cafet.
Dakyar na mike zaune na ce "Ban lafiya, Sai amai nake yi, daga zuwa kasuwa"
"Subhnallah! Sannu, bari mu je asibiti"
Ban yi musu ba, saboda ina jin jiki, shi ne ya dauki Assidiq, ni kuma na lallaba dakyar zuwa wurin motar. Wani private hospital mu ka je ma fi kusa, bayan gwaje-gwaje suka daura min ruwa, inda Allah Ya taimake ni ma, su Affan sai 6pm za su dawo.
So wajen 5:30 aka sallame mu, shi ya sa ku san tare mu ka dawo da su Khali, Maama kam ƴan first day at school, an ci kuka an koshi, sosai ma ni ta ban dariya, musamman yadda ta fada jikin Abbanta tana kuka, wai ita ba za ta kara zuwa ba. Kamar ba ita ce ke bacci da Lunch box da school bag bag.
Bread da miya suka ci, yayin da Bashir ya shiga kitchen yaran na taya shi da wasu abubuwan, ni kam ina kwance.
Yau kam dole a gida ya yi sallahr magana, yana idarwa kuma ya zubo mana jallof din taliyar ya yi, wacce ta ji busasshen kifi.
Muna cin abincin ne ya ce "Yar kasuwa, a haka za a yi kasuwanci, farawa da iyawa da shan ledar ruwa" sai da na kusa shakewa saboda dariya
Cikin dariyar na ce, "Wlh kamshin turarurukan nan ne, suka hau kaina"
"To a canja sana'ar, Babyna baya son kamshin turaren nan"
Sai da na kalli su Khalil, na ga hankalinsu ba a kanmu yake ba, sannan na ce "Wai waye ya fada ma akwai Babyn ne, don Allah kai daina yi min maganar nan"
"Likita ya fada min yau, don haka ki kula da kanki, kar ki jefar min da yaro a wajen kasuwancinki"
Abincin da nake ji na ji babu test ko kadan, kamar zan yi kuka na ce "Don Allah da gaske?"
"Ba na fada miki ba tun ranar can, ni da zarar na jefa kwallo a cikin raga nake ganewa"
Spoon din na ajiye, idanuna suka ciko da kwalla, da, gaske ba na son ciki a yanzu, ban shirya mishi ba, ina bukatar in huta, ni ma in ji yadda mata suke ji, yayin da suke zaman ba ciki ba goyo
Hawayen na dauke hade da mikewa na haura sama, saman gadona na fada na ci gaba da kukana.
Bashir kam bai shigo ba, Sai da ya sallami yara da duk wani homework, sannan ya hauro saman sabe da Assidiq da ya yi bacci. Ni kaina baccin ne ke dauka ta, shi ya sa sama-sama na ji shigowar shi. Gefena ya kwantar da shi ya shiga toilet, sama-sama nake jin buruntunshi, har zuwa lokacin da ya kammala shirin shi ya kwanta a Gefena, ba tare da ya ce min komai ba, abin da ban tsammani ba.